072

132 15 3
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba  ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn Whatsapp
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare
 
Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki sannan akwai na amare special Wanda inkinyi using baki Kuma bukatar kiyi Wani gyaranjiki domin keda kanki zaki shaida cewa fatar taki ta wanku tarwai😍08062991549

Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free

Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏

Sabulu
Herbal whitening black soap 4k

Akwai students package 10k

Beauty kit 12k
15k

Flawless skin beauty kit
18k
23k

Face serum 4k
Face soap 2k

72.

A hankali Amarya Zarah ta sakko da ƙafafuwanta akan interlock jikinta lulluɓe da lafayya pink in color ƙanwar mahaifiyata ta taimaka mata ta ƙarasa fito da gangar jikinta daga cikin mota. Wata daga cikin yan rakiya amarya ne ta ce "Ya kamata mu kai ta apartment ɗin uwargida kaman yadda ake yi a al'adance.
Ƙanwar mahaifiyata mai suna Hajiya kareema ta ɓata fuska tare da faɗin "Haba Aunty Rabi ai duk sauri unguzoma ta bari a haihu duk sauri da mu ke yi dole mu fara shigar da ita ɗakinta ta fara kwasar albarka ɗakin aurenta. In yaso daga baya sai a kaita can duk da ni banga wani amfani kai amarya wurin uwargida ba. Duk duniya babu macce da ke so kishiya.
  "Duk da haka kareema gara mu kai ta ɗin. Tukuna dai mu fara shigar da ita apartment ɗinta kaman yadda ki ka ce.
Daga haka suka wuce da Zarah Malik apartment ɗinta tun lokaci da suka fara wannan taƙaddama Zarah Malik ta ji wani irin kololo ya tokare mata maƙoshi har ga ALLAH bata so abinda zai haɗa ta da Jeeddah saboda wani irin mugun kishinta take ji. Musamman da take da cikakkiyar masaniya saboda rasa Jeeddah da Haidar Ka'oje ya yi yasa mahaifinta ya bashi ita domin ya huce masa haushin rasa Jeeddah ɗin da ya yi.
Har cikin bedroom ɗinta suka kaita baya ta zauna na wani ɗan lokaci a gefen lafiyayye kuma tsadadden gadonta ƙirar Chinese bed, kana aka nufo apartment ɗin Jeeddah da ita still kanta yana lulluɓe ciki lafayya. Jeeddah tana jin sallamar su gabanta yai mummuna faɗuwa duk ta bi ta rikice khairat tai maza ta rada mata ki dinga faɗar "Hasbunallahu wal-imaal wakil! Cikin zuciyarki In-sha-ALLAHU za ki ji sauki da raɗaɗi abinda ki ke ji. Jeeddah ta gyaɗa kai kana tayi abinda khairat ta umarci ta. Aunty Farida ce ta tashi da sauri tana fara'a "Sannunku da zuwa bismillah ga wuri ku zauna.
Aunty Farida ta faɗa tana ƙara faɗaɗɗa fara'ar kan fuskarta.
Bayan Hajiya kareema ta zaunar da Zarah Malik akan kujerar dake facing ɗin Jeeddah kana ta zauna kusa da ita sai lokaci Jeeddah ta haɗiye wasu mugaye miyau ta sami damar furta "Barkan ku da zuwa amarya barka da zuwa.
  "Barka Jeeddah ya hidimomi?
Cewar Hajiya kareema tana murmushi yaƙe saboda tana taya 'yarta kishi musamman da taga Jeeddah ba abinda Zarah Malik za ta gwada mata sai fari da kyakkyawar fuska amma idan ta ɓangare diri da kyawo sura ne to fa ita ma Jeeddah ba baya ba.
"Al-hamdullilah!
Jeeddah ta faɗa daga ji yadda take musu magana kasan ƙarfin hali take yi.
Aunty Rabi ce ta gyara zamanta kana ta yi musu addu'a kafin ta zarce da faɗar "Jeeddah ga ƙanwarki Zarah nan mun kawo miki amana duk da ita amana abu ce mai matuƙar wahala riƙo. Don ALLAH Jeeddah ku zauna lafiya ke ce babba idan har ki ga Zarah tayi ba daidai ba a matsayin ki na babba ki zaunar da ita ki fahimtar da ita kuskure ta. Ke kuma Zarah sai ki gyara ki kuma bata girman ta da ALLAH subhanahu wata'ala ya bata ku haɗe kawunan ku, ku zauna lafiya shi ne kwanciyar hankalin mijinku.
Kaɗan ne daga cikin tawagar Zarah Malik da basu tofa albarkacin bakinsu ba. Yayin da jin su kawai nake yi asalima na matsu su tashi su bar min falona. Wani irin takaici da haushin su nake ji ban da kuturun wulaƙanci ta aure min miji sannan ku zo kuna bani amanarta.
Suka miƙe tare da yi mana sai da safe har suka fice kaina yana ƙasa sai da na tabbatar da sun gama fita sa'annan na ciro kaina idanuwana sun jiƙe da hawaye, aunty Farida ta hau rafka sallati tana tafa hannaye "Miye haka Jeeddah Dan ALLAH ki rufa mana asiri ki yi gaggawar shanye hawaye nan naki kada ki janyo mana abun faɗa.
  "Da ki san abin da nake ji a cikin zuciyata Aunty Farida da ba za ki faɗi haka ba.
"Duk abinda ki ke ji Jeeddah na taɓa ɗaɗɗana kwatankwacin sa kishiya nan nima an min ita ba ma guda ɗaya ba har biyu amma ban yi wannan shirmen da ki ke yi ba.
"Aunty Farida kowa da irin tasa zuciya wani ya kan iya shanye ɓacin ransa wani kuma sai ya bayyana ta hanyar zubda hawaye ki barta tayi kuka watakila hakan ya sanyaya mata zuciya.
In ji Khairat tana kwato da kaina akan kafaɗarta ina ji abinda khairat ta faɗa na shiga rare kuka ƙasa-ƙasa.
  Don ALLAH ku yi following handle ɗina na wattapad da arewabook
Wattpad:jeedddahaliyu
Arewabook:Jeeddah3256
"Mtss!
Aunty Farida ta ja ɗan guntun tsaki tare da miƙe wa tsaye tana faɗin "ai shike nan sai ki yi ta kuka mu gani ko kukanki shi zai hana Haidar kwana da amaryarsa.
Furuncin Aunty Farida yasa na karawa kukana sauti har suka yi min sallama suka wuce ina sharar hawaye bayan tafiyar su aunty Farida na koma bedroom na sauya kayan jikina zuwa na riga da wando na bacci.
Amarya Zarah Malik tana zaune a gefen gado tare da ƙawaye ta suna jiran zuwan ango da abokansa misali ƙarfe 10:15pm Haidar da su Sy Barade suka yi sallama a kofar ɗakin Zarah cikin sauri Zarah Malik ta ƙara gyara lafayyarta.
"Amarya ba kya laifi koda kin kashe ɗa masu gida ya gajiyar biki?
In ji ɗaya daga cikin abokan Haidar mai suna Zaheed.
Zarah Malik ta ƙara sunne kanta Haidar Ka'oje ya saki murmushi ya nufi kusa da ita ya zauna ya ɗan zuguri kafaɗarta da tashi kafaɗa cike da jin kunya ta ɗago ta kalle shi ta gefen ido ba ƙaramin kyau yai mata cikin gray color shadda dake jikinsa, wani irin sonsa ta ji yana daɗa hauhawa a zuciyarta.
'yar gajeriyar nasiha abokan nasa suka yi musu kana suka yi musu addu'ar zaman lafiya da zuri'a dayyiba sa'anan suka yi musu sallama.
Don ALLAH ku yi following handle ɗina na wattapad da arewabook
Wattpad:jeedddahaliyu
Arewabook:Jeeddah3256
Bayan Haidar Ka'oje ya raka abokansa ya wuce apartment ɗin Jeeddah kansa tsaye ya tura ƙofar ɗakinta tana tsaye gaban dressing mirror tana tufke gashi kanta cikin sanyi murya yai sallama ta amsa mishi can ƙasan maƙoshi, kana ta wani kafe shi da idanuwanta sosai taga yai mata kyau ta saki ajiyar zuciya. A hankali Haidar ya isa dab da ita ya sakar mata tattausan murmushi "Barka da dare uwargida ran gida.
Sai da ta ja numfashi tare da sauke wa kana ta amsa mishi "Barka dai ango da fatan an yi taro lafiya?"
"Lafiya ƙalau Al-hamdullilah!
Tsawon lokaci suka ɗauka a tsaye ba tare da sun sake tanka wa juna ba. Haidar yana gani idanuwan Jeeddah sun cicciko da ƙwalla yai sauri ɗauke fuskarshi da barin kallonta kana ya juya cikin sanyi jiki yana faɗin "Sai da safe Jeeddah ki tabbata kin rurrufe kofofi kafin ki kwanta.
Bai jira jin ta bakinta ba ya ƙarasa fita na bi shi da kallo hawaye da nake kokari mayar wa suka silalo min a kumatu kamar wacce aka yi dole haka na ja ƙafafuwana na bishi koda na isa falo har ya fice da na ɗan buɗe ƙofa na leiƙa na hango shi ya nufi apartment ɗin Zarah Malik. Da sauri na toshe bakina da tafukan hannayena.
Zarah Malik ta ji shiru-shiru Haidar bai dawo ba sai ta miƙe zubur ta nufi jikin window ta leiƙa ta hango Haidar Ka'oje yana fitowa daga ɓangaren Jeeddah, duk sai ta ji wani irin sai kuma ta haɗiye takaicinta domin tasan duk jarabar su yau dai dole su haƙura da juna. Daga yau har zuwa kwanaki shidda da ke tafe dole Haidar ya kasance da ita don haka bata tsananta wa kanta ba. Ta dawo ta zauna inda ta tashi.
Kai tsaye  Haidar ɗakinshi ya wuce ya yi wanka tare da saka pajamas kana ya nufo ɗakin Zarah ya tura ƙofa tare da sallama ta amsa mishi tana mai sakar masa sanyayye murmushi shi ma ya mayar mata da martani "I'm sorry sweetie na bar ki ke, kaɗai na shiga wurin Jeeddah nai mata sallama sannan na tsaya a ɗakina na ɗan watsa ruwa, na so na zo ki yi taya ni wanka sai kuma nayi tunani wannan kunyar taki ba za ta bari ba.
Ya yi magana cikin zolaya.
Murmushi kawai tayi tana mai sadda kanta ƙasa. Kusa da ita ya zauna yana mai kama hannunta ya haɗe da nashi a hankali yake massage ɗin tafin hannunta hakan ya haifar wa da tsigar jikinta tashi.
"Sweetie tashi ki yi alwala mu yi sallah mu godewa da ubangiji da ya nuna mana wannan rana mai tarin albarka.
Cikin sunne kai ta furta "Ina da alwala.
Don ALLAH ku yi following handle ɗina na wattapad da arewabook
Wattpad:jeedddahaliyu
Arewabook:Jeeddah3256
Ya saki hannunta yana mai miƙe wa tsaye "To shi mu yi sallah.
Shi ya jagoranci su suka yi sallah bayan sun kammala yai mata tambayoyi na abinda ya shafi sallah da wanka tsalki cike da kunya tai mishi bayani gwargwadon abinda tasani.
"Ma-sha-ALLAH! Dama ina da yakini my Zarah haziƙa ce sai ki mana addu'a ko?"
Cikin natsuwa ta shiga kwararo addu'a yana amsa wa da Amin. Bayan sun shafa addu'ar, Haidar ya tashi ya je ya kawo musu abubuwan taɓawa daga ita har shi fresh milk 🥛 kaɗai suka sha. Ta riga shi tashi ta shiga bathroom tayo brush kana shima ya shiga ya wanko nashi baki koda ya fito har Zarah ta cire kayan jikinta ta maye gurbin su da wata sexy sleeping gown milk colour wacce ta bayyanar da surar jikinta ga wani kalar ƙamshi na musamman dake fita daga jikinta.
Sosai ta birkita wa Haidar Ka'oje ƙwaƙwalwa nan take natsuwar sa ta fara bari jikinsa. Har ya iso bayanta bai ɗauke idanuwanshi daga kanta ba, yana zuwa ya rungume ta, ta baya kana ya karɓi perfume bottle ɗin da ta gama fesawa ya ajiye akan mirror tun anan ya fara sumbatar gefen wuyanta kafin ya juyo da ita ya yi connecting lips ɗinsu. Daga nan komai ya canza sosai Haidar Ka'oje ya ba Zarah wuta don har sai da ta rena kanta don bai mata da wasa ba.
Duk yadda Jeeddah taso bacci ya ɗauke ta yaƙi zuwa sai faman juyi take yi akan gado har karfe biyun dare ta buga idonta biyu. Can kuma ta tashi ta shiga bathroom ta ɗora alwala ta shiga zuba nafilfili sai da ta ji ƙafafuwanta sun fara tsami kana ta kwanta anan wuri da tayi sallah nan take bacci yai awon gaba da ita.
Kiran sallar asuba ne ya tashe ta, tana fitowa daga bathroom Haidar Ka'oje yana mata knocking, zuciyarta tana bugawa da ƙarfin gaske ta buɗe masa ƙofa idanuwanta suka sarƙe da nashi
Don ALLAH ku yi following handle ɗina na wattapad da arewabook
Wattpad:jeedddahaliyu
Arewabook:Jeeddah3256

Ku yi manage da wannan na je unguwa ban samu nayi da yawa ba.

#Haidar Ka'oje
#Zarah Malik
#Jeeddah maishadda
#Team Zazzafan kishi.

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now