013...

77 10 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!* _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajarsu cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

013...

"Sannunku da zuwa kunsha hanya.
Mommy Turai ta faɗa tana musu ƙasƙantatce kallo gami da yatsinar fuska.
"Yawwa sannu Hajiya kun ganmu sai yanzu.
Cewar inna Rabi wacce ta kasance ƙanwar Mahaifiyar Bilal.
A wannan karon Umma Asabe ce tai magana tana yatsina "Wallahi kuwa ga ku nan zuga guda, yawan nan naku kaɗai ya isa ya gamsar da mu Bilalu ɗan dangi ne gaba da baya.
Inna Rabi ba ƙaramar yarinya bace da za ta kasa gane magana ce Umma Asabe ta yada mata, take taji jikinta ya yi sanyi ta kasa cewa komai sai kawai ta shiga murmushi yaƙe.
"A'ah...ya haka jama'a kun tusa akwatuna lefenku a gaba, ai sai ku buɗe mu gani kada mu buɗe ku ce mu yi muku kaudi.
Cewar Hajiya Turai tana murmushin zallar takaici domin tun basu buɗe ba yanayi akwatuna su kaɗai ya isa ya zama shedar babu abin a zo a gani a ciki ta faɗin hakan ne kawai don ta ƙara cin zarafin su.
Hajiya Bintu wacce ke zaune tana nuƙurƙusar baƙin ciki, saboda taga Bilal zai aure 'yar masu hannu da shuni sai yanzu da taga dangin Jeeddah su na yada masu da maganganu masu ɗaci sannan ta sami natsuwa ranta yai fari kal......ta wani zakuɗa manya mulamulai ɗuwawunta ta washe haƙora kamar wadda aka yi wa kyautar kujerar makka. Ta kai dubanta gefen da Bahijja take zaune tallaɓe da haɓa sai rarraba idanuwa take yi ta ce "A'ah... Bahijja me kike jira a zaune da ba za ki tashi ki buɗe musu akwatuna ba?" ai Bilal ya yi namijin ƙoƙari matuƙa mutumin da duniya ta sheda ba shi aiki fari balle na baƙi ya danƙaro ɗan uban lefen iri wannan ai dole a yaba masa kai tabarakallah ma-sha-Allahu yaro ya yi ƙoƙarinsa.
Wani irin gumi ne ya karyowa Bahijja domin tasan duk abinda Hajiya Bintu ke faɗa gatse ne da tsabar isgilanci da kuma so tadda zaune tsaye shiyasa tun farko bata so a zo da ita ba domin gudun iri wannan, sai gashi ta kasa ta tsare sai da ta biyo su. Jiki a mace Bahijja ta tashi ta fara zipping babbar trolley ɗin inda atamfofi da laces ke ciki duka ba za su haura kala goma sha biyar zuwa ashirin ba, tana ƙoƙari buɗe ƙaramar Umma Asabe ta dakatar da ita tana cewa "karki yi gaggawa Malama Bahijja ɗan dakata kaɗan mana mu gama gani wannan sai ki buɗe ta gaba, saboda naga daga budewarki har na fara cin karo da abin mamaki, gara ki bari mu sha kallo a tsanake ko ya kika gani Hajiya Turai?"
Ta ƙarashe magana tana kallon Hajiya Turai.
"Wallahi kuwa Asabe saboda ni banga abin rawar jiki anan ba.
Umma Asabe ta ƙara yatsine fuska gami da sunkuyawa ta shiga fiddo kayan daga cikin akwati tana watsawa kan tabarma, kuma duk wacce ta ɗauko a wulaƙance take jefawa kan tabarma gami da kirgawa ta ƙarshen da ta ɗauko cikon ta ashirin ta miƙe tsaye tana jujjuya ta kafin tasaki sallati tamkar wacce tai mugun gani kana ta kalle Hajiya Turai cikin zaro idanuwa ta ce "Ikon Allah ikon ma'aiki ashe dai har yanzu da raguwar atamfar cote d'ivoire a duniya Hajiya Turai duba ki gani ita ce ko kuma idanuwana ne ke min gizo kinsan idanuwan tun na haihuwa ne?"
"La'ilaha illallahu Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam! Wallahi ita ce Asabe ba wani gizo da idanuwanki ke miki ai ni na zaci tuni kamfani ya daina bugata.
Hajiya Turai ta faɗa tana karɓa atamfar daga hannun Umma Asabe, sai wani zare idanuwa take yi kamar taga abin tsoro.
Jin iri maganganu da suke faɗa yasa Hajiya Amina wadda ta kasance 'yar ƙani mahaifin Baba, ta matso kusa tana leƙen atamfar daga hannun Hajiya Turai ta shiga tofa albarkacin bakinta.
"Ai Hajiya Turai atamfar ce akwai quality da ƙarkon tsiya ga ta kuma da haƙuri wahala sai ki ga talaka ya daɗe yana morar ta.
"Ikon Allah wanda yafi gaban mamaki.
Hajiya Turai ta furta tana wani girgiza kai.
Umma Asabe ta kalli Bahijja wacce ke rakuɓe ta ce
"Malama Bahijja taso ki buɗe mana ɗayan akwatin mu gani duk da kyakkyawar juma'a tun daga Laraba ta ake ganewa.
Jikin Bahijja a mace ta taso ta sake buɗe musu ɗayan trolley ɗin, sai kawai suka haɗa baki suna rafka sallati gami da tafa hannuwa sakamakon gani tarkace da ke cikin jakkar ta farkon ma tafi kyau gani saɓanin wannan mai ɗauke da takalma set biyu haɗe da handbag guda ɗaya tak sai sabulai da man shafawa wanda basu wuce rabin dozen ba, sai wata mahaukaciyar necklace mai zuɓin gold mai haɗe da kwalamin zobe girmansa har ya wuce a misalta shi sai veils guda biyu old design da hijab guda uku. Duk cikin kayan ba abinda ya ja hankali Hajiya Turai iri fake gold necklace ɗinan, ta ɗauko ta tana kallo can kuma ta ce "Asabe tayani gani wannan haukar ko sun zaci mu jahilai ne da ba za mu iya banbance tsakanin real gold da fake one ba?"
Sai da Umma Asabe ta fara jan guntun tsaki kafin ta ce
"Bari kawai Hajiya wannan kayan takaici da yawa yake tsakani da Allah Jeeddah ta gama cutar kanta kwata-kwata ba abin nunawa anan wuri lefe kala ashirin ba na babu na nuna wa sa'a tirr....da wannan kayan takaici.
"Kema kya faɗa Asabe sauƙin mu ɗaya babu baƙon ido a gidanan da haka za a dinga yamaɗiɗi da mu gaba ɗaya unguwa ta ɗauka an kawowa 'yar mu lefen matsiyata.
Ran Hajiya Bintu yai fari fess...har batasan lokaci da dariya da take danne wa ta subuce mata ba, ta shiga kwasar abarta hankali kwance sai da tai mai isarta kafin ta taso daga gun zamanta ta nufi wajensu Hajiya Turai cike da su haddasa fitina ta karkace baki ta ce "Kina da gaskiya Hajiya mutane wannan zamani basu gadonka amma suna gadon maganarka, yanzu nan sai ku ga ana yaɗa tarkace nan a waya {social media} amma zance na gaskiya yarinya nan ta cuce kanta ba kaɗan za ta yi asarar budurcinta a wofi ALLAH na tuba ko a zamanin mu ba a kai lefen iri wannan ni da farko na zaci ko bazawara ce sai da na tambaya aka ce min sabuwa ce dal a leda, to Allah ya kyauta shiyasa addini ya yarje da bincike kafin aure don gujewa irin wannan.
Inna Rabi da taga al'amarin yana neman wuce gona da iri ta taso cikin tausassa murya ta ce "Haba Hajiya Bintu ya kike neman ki zama haddasana shi fa arziki yana tsakani mata da miji ki ka sani ko ita ce abokiyar arzikinsa? Gaskiya ki gyara halinki domin duk mutum mai cikakken hankali ba zai aikata kwatankwacin abinda kika aikata ba.
Shiyasa Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam ya hore mu da mu faɗi alkhairi ko mu yi shiru.
Cike da masifa Hajiya Bintu ta hayyaƙo wa Inna Rabi tana faɗar "Ke rufe min bakin Rabi tun kafin na zage naci miki mutuncin anan wuri, wato ni ce karkatacciyar kuka mai daɗin hawa kou? In banda reni wayau kina dai ji da kunnenki iyayen yarinya ne suka fara magana don na tanka, na tofa albarkacin bakina shine za ki taso min da wani guntun wa'azi ki to wallahi ahir ɗinki. Kai...ku ji min mata dallah ban da guntun iskanci me ya hana Bilal ɗin ya nemi daidai ƙarfin aljihunshi saboda son zuciya da ya tsotsa a nono ya buge da yi ma 'yar mutane asiri to kuwa duk wanda ya hau motar kwaɗayi ba inda za ta sauke shi sai a tashar wulaƙanci, wallahi kaɗan ku ka fara gani. Ku kuma ku yi gaggawa raba 'yarku da Bilal idan ba haka ba kun dingi gani ƙasƙanci da kayan haushi kenan.
Ta ƙarashe magana tana kallon su Hajiya Turai.
Baki buɗe inna Rabi da raguwar 'yan uwan Bilal ke kallon Hajiya Bintu wacce hankalinta kwance tamkar ba mummunan abu ta faɗa ba.
"Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Bintu ki ji tsoron haɗuwar ki da mahaliccinki.
Cewar wata Gwaggo Bilal wacce tun fara taƙaddamar take kallonsu sai kuma yanzu da Allah ya bata ikon yi magana.
Saboda tsananin mamaki da ya lulluɓe inna Rabi da Bahijja kasa furta kalma ko ɗaya suka yi sai bin mutane da idanuwa suke yi shiyasa Gwaggo Sa'a ta samu damar yin magana.
Uwar harara Hajiya Bintu ta watsawa Gwaggo Sa'a gami da cewa "Kin ji ki da wani zance Sa'a saboda tsananin tsoron Allah ne yasa na faɗin farar gaskiya da ku ɗin ku ke ɓoyewa ke ni fa ko a bakin kura nake idan gaskiya ta zo sai na faɗe ta ehee.
"Kai dallah ya isa haka!
Hajiya Turai ta daka musu tsawa gami da ɗaga musu hannu tana ci-gaba da faɗin "Ai gaskiya Hajiya Bintu ta faɗa in banda aikin asiri me Jeeddah za ta tsinta a jikin ɗanku. Kin ga Asabe dan Allah ki sallame mutane nan nagaji da gani kayan takaici akwai, drinks da snacks da aka tanadar musu suna kitchen ki basu. Rago da kaji kuma ku bar mana kayanmu domin yawan lefensu yawan tukuici da za mu basu infact waɗannan tarkace nasu basu ma cancanci tukuici daga garemu ba. Basu kawai za mu yi ko don wannan uwar zuga da suka yo sai kace wanda suka kawo abin kirki, wannan tambaɗaɗɗe lefen nasu ko mutum ɗaya ya isa ya kawo shi amma saboda tsabagen kwaɗayi suka haɗa ayari guda ki basu snacks da drinks ɗin kada su yi zuwan banza.
Ta ƙarashe magana gami da shigewa parlourn Mama.
Umma Asabe ta bi su da kallon wulaƙanci kana ta nufi kitchen ta fiddo musu da kayayyakin da Hajiya Turai ta umarce ta da ta basu, bayan ta kammala ɗaukowa ta kalle su da girar ido ɗage ta ce "To malamai da Hajiyoyi mun fa gode da ƙoƙari ga wannan in kun tashi ku tafi dashi.
Inna Rabi ce tai ƙarfin hali furta "Hajiya ai da kun barshi kawai.
"To ai ke baiwar Allah ba ke kaɗai mu ka bai wa ba idan bakyaso raguwar abokan tafiyarki suna so.
Ba wanda ya ƙara tanka mata suka shiga jidar kayayyakin suna fita dasu ƙofar gida inda masu adaidaita ke zaman jiran su. Bahijja ita ce ta ƙarshe da tashi har ta kusa fita ta tuna da kuɗi da aka bata dubu goma ta bayar a matsayin hanjin lefe, sake dawowa tai ta miƙawa Umma Asabe wacce ke ta faman banbami faɗa sai da ta karɓe kuɗi kana ta tambaya na menene cikin sanyi murya Bahijja ta faɗa mata hanjin lefe ne, wata uwar harara ta buga mata gami da tsaki kafin ta samu furta wata magana marar daɗi Bahijja tai sauri barin wajen.
A ɗaki kuma Hajiya Turai ta tusa Mama a gaba sai zayyane mata kalar lefen take yi tsabar takaici da baƙin ciki Mama kasa magana tayi sai wani iri tuƙuƙi take ji a zuciyarta.
Bayan dangin Bilal sun tafi Umma Asabe da Amina suka tattare kayan suka mayar cikin akwatin, kana suka nufo parlourn Mama dashi sai a gabanta suka dira su Umma Asabe ta ce "Hajja Fatee ga lefen Jeeddatul Baba nan sai ki buɗe ki ganewa idanuwanki, domin gani da ido ya kore ji ga su nan daga atamfofi har laces babu na kirki a ciki duk tsofaffin yayi ne.
Zuciyar Mama tamkar za tai tsalle ta faɗo ƙasa ana ciki haka sai ga Jeeddah da ƙawaye ta sun shigo ƙawayen keso gani kayan lefen Kafin su tafi shiyasa ta shigo dasu. Wani matsiyaci kallo da Hajiya Turai ta watsa musu cikin masifa gami da takaicin Jeeddah ta daka musu rikitatciyar tsawa cikin hargowa ta ce "Ku me ya shigo daku yi parlour nan? Jeeddah tana ƙoƙari buɗe baki tai magana ta sake daka musu tsawa wacce tafi ta farko ƙara "Dallah ku fita ku ba mu wuri ko ba ku ga magana mu ke yi ba? Kun wani faɗo mana gatsal ku dai yaran zamanin nan sai a hankali ba ku da ta ido ko kaɗan. Ba za ku fita bane ina magana kun ja ku tsaya wato sai na gama banbami faɗa kuna tsaye maza ku fice munafukai banza masu bin gidan ƙawaye domin ɗaukar rahoto daɗin abin kowane shege bai rasa guntun kashinsa a ɗuwawu.
Haba wa tun kafin ta dire aya suka fice da sauri wasu su har suna haɗawa da gudu, Jeeddah ta juya za ta bi su a baya Hajiya Turai ta fizgota a fusace "Dawo nan munafuka wacce bata gudun abin magana banda shasshanci miye na gayyato ƙawaye me za su gani anan tarkace banza nan ko me?" Wallahi Jeeddah da wannan kayan takaici da aka kawo miki gara babu sau dubu dasu babbar atamfa a ciki lefenki ita ce chiganvy ita ma ba ta kwatano ba shine har da ɗebo ƙawaye su zo su gani su shiga gari su sami na yaɗawa.
"Ai da ki bar su Turai su gani in yaso su shiga gari su ta yamaɗiɗi da 'yar banza mai kunnuwan ƙashi.
Mama ta faɗa cikin hasala jin take kamar ta taso ta rufe Jeeddah da mugun duka.

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now