035

81 15 1
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

035..

Kowanne su ya nemi kujera ya zauna daga dining area ina iya hango  cikin parlour, saboda kujerar da nake zaune tana facing cikin parlour ne. Shiyasa akan idanuwana suka shigo har suka zauna ina kallonsu.
Aunty Bahijja ta kalle Bilal da ke sanye da apron ta taɓe baki kafin ta ce "Kai kuwa Bilal wacce irin lalacewa ce ta sami ka da ka ke sanye da rigar girki tun da sassafe ko hatta da girki kai ke yi mata?"
Ƙasa da murya ya yi yana faɗin "Kin ga Aunty Bahijja banaso tadda zaune tsaye kun ce haƙuri ku ka zo bata ke kuma gashi kina ƙoƙari shiga abinda bai shafe ki ba. 
   "Daga tambaya sai cibi ya zama ƙari to maida wuƙar ka kira mana hanshaƙiyar taka, don ba gadin parlour muka zo yi muku ba.
Bilal bai tanka mata ba ya juya gami da nufar dining room, suka bi shi da kallo sai lokaci su ka hango ni.
A'isha Shattima tai sauri tasowa ta nufo wurina, kujerar da ke kallona ta ja ta zauna "A'isha amarya ya amarci?"
Na faɗa fuskata shimfiɗe da murmushi.
A maimakon ta bani amsa sai kawai ta buge da faɗin.
"Jeeddah na zo ne na ba ki haƙuri akan abinda Ya Bilal yai miki ko kaɗan ji daɗi ba ace ta sanadi na kin rasa abu mai matuƙar muhimmanci da tsada, dukkan mu ba mu san cewa gwal ɗinki ya Bilal ya siyar ba. Da wallahi ba zan taɓa amincewa ya salwanta miki shi ba. Shiyasa na je gida na zo tare da Hajja da Aunty Bahijja domin na yanke shawarar a kwashe furniture ɗin a sayar a dawo miki da kuɗin duk da ba lallai bane kuɗin gwal ɗinki su dawo gaba ɗaya ba. Amma za ki iya rage asara.
   Tun kafin ta ƙarashe magana nake girgiza kai, kafin na dire fork ɗin hannuna cikin plate, na kalle gefen da Bilal Shattima yake tsaye rakuɓe da jikin bangon dining room ya yi wani iri dashi domin shi kanshi bai yi tsammani fitar wannan maganar daga bakin A'isha ba.
  "A'isha abinda ya wuce bai kamata mu dinga dawowa dashi baya ba. Zance a sayar da furniture ɗinki a dawo min da kuɗi wannan magana banaso na sake jin ta daga bakinki, ki ƙaddara a ranki haka ALLAH ya tsara ni ke da gwal amma ke ce za ki amfana dashi. Takaicina ɗaya da yayanki ya ɓoye min ya barni a duhu har sai da na nemi gwal ɗin. Da tun farko ya fito fili ya faɗa min da duk bata kaimu da haka ba.
  "Gaskiya bai kyauta ba shima idan kika dube fuskarshi ya yi nadama hakan Dan ALLAH ki yafe mishi Jeeddah.
  Ɗan bazawari murmushi nayi tare da miƙewa tsaye na riƙo hannunta gami da faɗin "Zo mu je parlour na gaida Hajja mu bar su zaune sai zuba muke yi.
A hankali suka sauko daga kan steps din dining room suka shiga parlour.
Duk firar da ta shiga tsakani Jeeddah da A'isha Bilal yana ji duk sai ya ji tausayin Jeeddah da wata irin mashahuriyar ƙaunarta suka ƙara linkuwa a zuciyarshi ya ji ta ƙara samun babban matsayi da ya zarce wanda take dashi tun farko a gareshi.
  "Ina kwana Hajja?"
Na faɗa gami da ɗan runsunawa.
   "Lafiya qalau.
Hajja ta amsa ba yabo ba fallasa gani yadda amsa min gaisuwa yasa daga haka na ja bakina na tsuke sai kawai na nemi kujera na zauna.
   "Jeeddah mun zo ne akan gwal ɗinki da 'yan gidanku su ka ce Bilal ya sata wacce ya yi sata domin ta ta ce a kwashe kayan ɗakin a siyar a ba ki kuɗinki. Domin ke kam ba matar rufin asiri bace  ni a tunani ko duk abinda kika mallaka Bilal ya sayar ba za ki ce uffan ba. Saboda ke ce kika liƙe masa ba yadda bai nuna miki bai tashi aure ba ki ka kafe lallai sai ya aure ki ashe dama so ki ke ki tallata shi a duniya a dinga yi masa kallon ɓarawo to ki sani kanki ki ka yiwa domin duk lalacewarshi yana nan a matsayin mijinki.
  Da sauri na ciro kaina ina kallon Hajja da baki buɗe ba ƙaramin mamaki ta haifar min dashi ba.
Kafin na sami lalluɓo kalmar furta wa Aunty Bahijja ta ri gani ta hanyar cewa
  "Kwarai kuwa gara a siyar a baki kuɗinki don mu ba ma so harka da fallasa da tono asiri da iyayenki da 'yan uwanki suka kwarai da shi, ban da kuturun wulaƙanci da reni wayau shi Kabeer yaushe ya yi Kuɗi da zai sa a rufe Bilal a police station.
Tana dasa aya ina miƙewa tsaye domin maganganun su ba ƙaramin ƙona min rai suka yi ba. Sosai idanuwana suka rufe, na ce "Duk abinda za mu yi da ke Aunty Bahijja ya tsaya iya ni kaɗai domin ni nake auren ɗan uwanki amma Iyayena ba sa'ar yin ki bane don haka kada ki sake ki furta magana banza akansu.
  Ita ma Aunty Bahijja miƙewa tayi dama tun faru al'amari take jiraye da Jeeddah, saboda haka a wulaƙance take kallonta kafin ta ce
  "Iyaye naki har wata jar duniya ne su da ba za a furta maganar banza akansu ba, ai sun ri ga sun zama mutane banza tun da suka kasa ba ki tarbiyyar da za ki rufawa mijinki asiri.
Gaba ɗaya jikina ya ɗauki rawa saboda tsanani fusata da nayi har ji nake yi kamar ƙafafuwana ba za su iya ɗauka na ba. Bansan lokaci da na ƙundumo ashar na  antaya mata ba
  "Babba*b....ubanki Aunty Bahijja 'yar iska marar mutumci uwarki ce ba ta yi miki tarbiyya ba ke har kin isa ki zo har cikin gidan ubana sannan ki zagi Iyayena, na zuba miki ido.
   Da mugun mamaki Hajja ta miƙe tsaye domin su dukkan su ba su yi tsammani fitar waɗannan manya-manyan zagi daga bakina ba, Hajja ta shiga tafa hannuwa tana salati. Yayin da A'isha Shattima tai sauri riƙo ni domin har na tunƙare inda Aunty Bahijja take.
   "Ni ki ka zaga Jeeddah?"
Aunty Bahijja ta faɗa tana nuna ƙirjinta da yatsa.
"Na zage ki kin ci kutumar *b....ubanki 'yar iska banza baƙar matsiyaci, munafuka algunguma, baƙar almura wacce bata gadi arziki ba. Maza ki fice min daga gida don ba na ɗan uwanki bane kuma daga yau kada na sake gani shegun ƙafafuwan ki sun tako cikin gidanan.
   Na ƙarasa magana ina huci.
      "Tabbas kin zage ni Jeeddah ta uwa da uba amma inaso ki rubuta ki ajiye ba ki zagi banza ba. Don wallahi-tallahi sai na mayar miki da martani da sai kin yi kuka da hawayenki.
  "Haba Aunty Bahijja miyasa ki ke yi haka ne Dan ALLAH? Ni fa na kawo ku gidanan ne domin neman maslaha sai gashi kin buge da zagin matar gida wallahi Aunty ki gyara halinki domin banga abinda baiwar ALLAH nan ta tare miki ba..
   "Ke rufe mana baki marar zuciya wacce bata kishin kanta, kina jin yadda take zagina ni da mahaifinku da ke kwance a kabari, don tsabagen lalacewa shi ne kike goyon bayanta. To daɗi abin uwa da uban da ya haifi Bahijja shi ya haife ki sakarya kawai.
Hajja ta faɗa tana gallawa A'isha harara.
Ni ma cikin tsanani fushi na ce da Aunty Bahijja
  "Idan ba ki mayar min da martani ba Aunty Bahijja ALLAH ya tsine miki albarka.
Hayaniyar mu ce ta fito da Bilal daga wanka ko kaya bai tsaya saka wa ba ya fito ɗaure da towel, dama yana bari dining room bedroom ya wuce ya yi wanka tun yana cikin bathroom yake jin kamar sauti faɗa ashe kuwa kunnuwanshi gaskiya suka jiyo masa, ya yi tsaye turus! Tsanani mamaki da tsoron ALLAH suka lulluɓe shi sai kallonmu yake yi. Hajja tana zagina Aunty Bahijja tana tayata ba irin kalar zagi da ba su yi min ba. Yayin da ni kuma nake mayar wa da Aunty Bahijja martani da nawa kalolin zagi, don ba zan iya zagin Hajja ba ko ba komai har yanzu da igiyar aure ɗan ta akaina tana da raguwar darajar da ba zan iya zagin ta ba. Sai dai a madadin ta na zagi 'yarta kuma dole ta ji zafi.
   "Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Hasbunallahu wal-imal wakil! Na shiga uku ni Bilal me nake shiri gani haka?"
Bilal Shattima ya faɗa cikin kaɗuwa.
   "Gara ka da ka fito Bilal taho ka ji da kunnuwanka yadda matarka take zuba min ruwan zagi yau ba kalar zagi da ba ta yi min ba ni da Bahijja.
Hajja ta ƙarashe magana tare da rushewa da kuka.
    "Wallahi Bilal idan ba ka ɗauki mataki akan zagin da matarka ta yi mana ba to ka sani ni zan ɗauka ko ba yau ba.
   Cewar Aunty Bahijja tana maida numfashi.
Nima Ina huci na ce "Duk tsiyar ki bai wuce ki ce ya sake ni ba to nima a shirye nake da ya sake ni ɗin haka kawai zan zuba ido a zo har cikin gidana a zagi iyayena....
   "Jeeddah ya isa haka wuce ki shiga bedroom.
Bilal ya faɗa cikin ɗaure fuska, har na buɗe baki zan yi magana A'isha Shattima tai sauri rufe min baki ta ja ni da ƙarfi tsiya ta shigar dani bedroom.
Bilal Shattima ya kalle gun da Hajja take tsaye tana sharar hawaye da gefen hijab ɗinta, ranshi a matuƙar ɓace ya ce "Haba Hajja! Haba Hajja! Wannan wane iri abu ne Miyasa za ki biye wa Aunty Bahijja bayan kin daɗe da sani kanwarta da Jeeddah bata gamu ba?"
Bai jira ta bashi amsa ba ya ci-gaba da faɗin "Gaskiya ban ji daɗi wannan zuwan naku ba. Hajja, Aunty Bahijja ku tuna da irin girman laifi da na yi wa Jeeddah amma ta haƙura ta zauna da ni shi ne don kawai ku ƙuntata mata ku sake haddasa fitina a tsakanin mu za ku zo da sassafe ku ci mata zarafi, gaskiya ba ku kyauta ba.
   "La'illaha inlallahu Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam! Bilal bakinka ne yake faɗa waɗannan maganganu ko kuwa wani Bilal ne aka musanya min dashi?"
Hajja ta faɗa tana zarar ido.
  "Ni ne Bilal ɗinki Hajja ba musanya aka yi miki ba. Kawai dai inaso ki fahimci irin rashin gaskiyar da ku ka shimfiɗa.
  "Uhmm! Hajja kin gani kou kin ga irin illa da nake nuna miki tuntuni akan aure nan nashi kou? To gashi nan yau kin gani da idonki kin haifawa wata 'yar iska ɗa sai yadda tayi dashi.
   "Ya isa haka Aunty Bahijja wai me Jeeddah tai miki da ki ka tsane ta har haka? Domin iya sanina wani saɓani bai taɓa shiga a tsakaninku ba da zai sa ki dinga nuna mata ƙiyayya irin wannan.
  "Shikenan Bilal tun da ka goyi bayan matarka ni zan tafi ga ka nan ga ta ALLAH ya ƙara muku danƙo soyayya.
Hajja tana gama faɗin haka ta juya a fusace Aunty Bahijja ta biyo ta a baya.
Da sauri ya bi su yana kiran sunayensu ba wacce ta tsaye balle ta saurare haƙuri da yake basu, kasancewar towel ne a jikinshi yasa ya kasa bin su ya dawo jikinshi a sanyaye, ya shiga ɗakin da Jeeddah take, ina zaune sai rera kuka nake yi yayin da A'isha Shattima ke rarrashina Bilal ya kalleta gami da faɗin "A'isha tashi ki tafi gida.
Ba tare da ta ce komai ba ta miƙe tare da ficewa, ya  yi tsaye tare da folding hannunshi yana kallona, tsawon lokaci ya ɗauka a tsaye yana ta faman kallona bai yi min magana ba. Daga ƙarashe ya nufi closet ya saka jallabiya milk colour, ya fice abinsa.
Ina gani yadda yai banza dani sai na ji wani sabon haushi da takaincinsa  na tashi a fusace na janyo ɗaya daga cikin akwatuna na shiga loda tufafina a cikin ina yi ina rera kuka, har ga ALLAH ina ji a jikina yau ne ƙarshen zamana da Bilal Shattima...

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now