021...

84 9 1
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune Kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

*Abishirinku mata 'yan kwalisa masu son su faranta wa mazajensu rai, ku gamsar da su iya gamsuwa to ga dama ta same ku da za ki saka maigida ihun daɗi da haɗaɗɗun kayan mata daga kamfani Manzil Alwafir masu kyau da inganci, Hajiya karki damu za ki mallake mijinki a tafin hannunki ba Boka ba malam maza ki garzayu wurin gimbiyar haɗa mata mai bada gudunmawar gyara shimfiɗar aure Hajiya Hassana Abdullahi*

*_Muna da kaya kamar haka_*

Smoked heaven
Asta
Ashana
Yaqtur
Nashwa
3rd Avenue
Back to honeymoon
Kazar Mata
Tsumi
Dambun mata
Sanyi herbs
Helwa
Anwar
Deep sea
Vibrationzz
Wet and tight
Ashwa
Halwa
Helwa
Garden knot
After dark intense
Bomb oil
Yoni balm
Swan
Taurariya
Lazeez
Persion hot
HD tea
Mazan Arewa
Tightening honey
Jego package
Bridal package
Durot

  _Muna tura kaya a duk gari da ku ke_

Domin ƙari bayani sai a tuntube mu a waɗannan lambobi 08036072970 08121555525

021...

Tun kafin yai magana Bilal Shattima ya riga shi cikin sauri da rawar murya ya ce "I'm very sorry for keep you waiting Jeeddah nasan kina fushi dani amma firstly ki tsaya ki fara jin uzurina kafin ki yanke min hukunci.
Bai yi gaggawar katseshi ba sai kawai ya kyale shi ya gama faɗi abinda ke ranshi, kafin ya yi wani gyaran murya cikin zazzaƙar murya nan tashi mai cike da izza da zallar taƙama yake faɗin "Na tsince matarka yashe a gefen titi cikin mayauwaci hali nayi ƙoƙari na kawo ta asibiti cikin hukunci Ubangiji likitoci sun yi nasarar shawo kan matsalarta. Ka yi gaggawa ka zo ka same ta a Saraki specialist hospital Ali Akilu road a room 03.
Daga haka ya dantse kiran ba tare da ya jira jin abinda Bilal Shattima zai faɗa ba. Haka kawai daga jin muryar Bilal da ya yi sai ya ji kwata-kwata bai kwanta masa a rai ba asalima wani shegen haushinsa na rashin dalili ya ji ya kanainaye masa zuciya shiyasa yai saurin katse layin.
Ta ɓangaren Bilal Shattima sororo ya yi gami da bin wayar hannunshi da kallo sake kiran layin Jeeddah ya yi saidai har ya tsinke ba a ɗaga ba. Cikin tsanani firgici ya ja machine ɗinsa ya nufo asibitin.
Ya mayar mata da wayarta cikin handbag ɗinta gami da miƙewa ya kai handbag ɗin akan bedside drawer ya aje juyawar da zai ya yi ya ji tana salati, da sauri ya isa wajenta "Sannu Maijidddah ya kike jin jikin naki?"
Ya kira ta da maijiddah ne a dalili ya ji Bilal Shattima ya kira ta da Jeeddah.
Sannu a hankali ta ƙarasa ware idanuwanta akanshi, tun daga kyakkyawar fuskarshi ta bi shi da kallo har ta dire idanuwanta akan ƙafafuwan shi da ke cikin brown sandal.
Ajiyar zuciya na sauke wacce ta fito fili, kafin na kawar da idanuwana daga kanshi inaso nai mishi magana sai dai babu halin yin hakan sakamakon miyau da ya cika min baki taff, sai kawai nai yunƙura na tashi zaune a dalili na fahimci ina bisa gadon asibiti ne, kuma jikina ya bani wannan mutumin shine ya kawo ni saboda na tuna da inda na faɗi sai kuma yanzu da na falka nagani kwance akan gadon asibiti, bana ko tantama cikin hasashena.
  "Za ki shiga bathroom ne na kira nurse ta taimaka miki?"
Sai kawai na tsince kaina da nuna mishi bakina da ɗan yatsa abin mamaki sai na ji ya ce dani "Kina so ki zubda yawu kou?"
Na sake gyaɗa kai, kafin na ƙarasa sauko da ƙafafuwana ƙasa har ya ɗauko tissue box ya zaro ta ɗan yawa, kana ya kananaɗe ta a maimakon ya miƙo min sai ya ce min "Zubar da yawu anan kada ki tashi ki jira na kira nurse ta taimaka miki, har yanzu jikinki bai yi kwari ba.
Sai da na ɗago na kalle shi kafin na maida ganina akan tissue da ke riƙe a hannunshi, ko ya fahimci ba zan iya zubar da yawu tissue yana hannunshi sai kawai na ji ya sake cewa "Kar ki damu maijiddah ki zubar kawai lalura ce kin ji?"
Na jinjina kai gami da matsowa na tofar da miyau akan tissue da ke riƙe da hannunshi ni kaina sai da naji kunya saboda yanayi miyaun nawa ga kumfa ga kaurin tsiya kusan dai yadda yawun laulayi ciki yake, amma sai naga shi ko a jikinsa hankalinsa kwance ya nufi dustbin ya jefa tissue ciki. Kana ya juyo ya kalle ni yana faɗin "watakila kina da buƙatar shiga bathroom bara na kira nurse ta taimaka miki.
Ya ƙarashe magana gami da nufar ƙofar fita ya buɗe ya fita, ƙofar na bi da kallo kafin na sauke wata ajiyar zuciya har tafi ta farko fitowa a fili lokaci guda na ƙarasa saukowa a hankali nake bin bango har nai nasarar shiga bathroom. Ina jin sautin muryar mutane su na magana ƙasa-ƙasa   nai sauri kus-kure bakina na buɗe ƙofa koda na fito har ya fice iya bayanshi kawai nagani, nurse ɗin da ke tsaye tai saurin zuwa ta kama shoulder na da taimakonta na koma bisa gado na kwanta.
Wani drip ta sake saka mata kana nurse ɗin ta fice bata daɗe da fita ba Jeeddah ta ji an turo ƙofa a tunaninta ko shine koda ta juyo sai kawai tai tozali da fuskar Bilal Shattima da sauri ta kawar da fuskarta, yayin da shi kuma ya ƙaraso wajenta da rawar jiki yana faɗin "Subhanalillah... sannu Love kin gani kou dama sai da nai gudun faruwar hakan amma kika kafe lallai-lallai sai kin je school ɗinan...
Tun kafin ya ƙarashe magana Jeeddah tai wani irin juyowa ta zuba mishi wani mugun kallo wanda hakan ne yasa shi haɗiye raguwar kalamanshi. Sosai ta ji wani irin haushinsa ya lulluɓe ta cikin fusata ta tashi zaune tana faɗin "Lallai sai yau nasan ba ka ƙaunata Bilal ba ma ta lafiya ta kake yi ba ƙoƙarin ɗora min laifi ka ke yi duk abinda ya faru dani ba kai bane sanadi kira nawa nai maka tsabar wulaƙanci ka ƙi picking shine za ka zo kana min wani borin kunya.
  A sanyaye ya kama hannunta ta fizge cikin tsawa ta ce "Ka fita banaso ganinka daɗin abin ba kai kaɗai nake dashi ba a duniya balle ka wulaƙanta ni. Ba don da ALLAH ya haɗa ni da mutum nagari ba mai kyakkyawar zuciya ya gani yashe a gefen titi kamar wata marar gata ya ɗauko ni ya kawo asibiti da yanzu ALLAH ne kaɗai yasan hali da zan shiga kai kana can kana sharar baccinka da yafi ni muhimmanci.
  "Jeeddah..... Jeeddah Dan ALLAH ki tsaya ki ji ta bakina wallahi-tallahi  neighbours ɗin mu ne suka yi gobara gidan Ahmad bank manager ɗinan na shirya kenan na taho picking ɗinki sai ga Officer Abdul-ganiyu ya yi min knocking koda na buɗe ƙofa naga yadda gidan ke ci da wuta shine mu ka je taimaka musu na manta da na bar wayana a charging da kyar aka samu wutar ta mutu komai basu fitar ba an dai auna arziki tun da rai ya fita kin ji dalili da ya hanani zuwa picking ɗinki in time. Wallahi sai in kin so ki ga laifina ne kawai amma tun kafin mu yi aure ban taɓa ƙin zuwa dauƙar ki ba sai in da babban uzuri kamar wannan. Amma Dan ALLAH ki yi haƙuri kin ji rabin raina?"
Ya ƙarasa magana tare da zaunawa kusa da ita, ya sake kama hannunta a wannan karo bata hana shi riƙe hannun nata ba saboda ta gamsu da kwakwaran dalili da ya bata, amma duk da haka taƙi sakin ranta. Shi kuma sai kanfa-kanfa yake da ita.
   "Please Love ki sakin ranki mana.
Ya faɗa yana wani kwantar da murya, ɗan murmushi tayi kafin ta koma ta kwanta.
  "Love ina mutumin da ya kawo ki asibiti nai masa godiya duk da tun a waya na fahimci ɗan reni wayau ne yana ji da kansa.
Ya ƙarashe magana yana wani taɓe baki.
Kallo mamaki ta bishi da shi kafin ta ce "Ban san inda yake ba sai in zuwa za ka yi ka tambaya nurses ɗin da ke on duty.
Yadda tai magana yasa ya gano har yanzu da raguwar haushinsa a zuciyarta sai kawai ya ja bakinsa yai shiru da yaga shiru nasu yana neman yi yawa ya fito da wayarshi ya kira Hajja da Aunty Farida ya faɗa musu hali da Jeeddah take ciki.
**** *** ***
  Zaune take gaban Bokanta da ke cikin wani ƙauye a cikin ƙaramar hukumar Binji local government, dama lokaci zuwa lokaci take kawo masa ziyara a duk lokaci da wata buƙata ta taso  mata wurinsa take zuwa. Cikin kwantar da murya ta fara magana "Ran boka jikan Baidu ya daɗe kamar dai yadda na saba zuwa da buƙata ta kuma a biya min ita yau ma na zo da wata buƙata ina fatan haƙata za ta cimma ruwa, duk da akasarin ayyukan da aka yi min a can baya ba a taɓa samun matsala ba. Shiyasa har gobe bani da inda nake kai kukana a share min hawaye face wurinka.
Hajiya Bintu ta ƙarasa magana cike da ladabi har wani sunkuyar da kai take yi, shi kuma jikan Baidu tun daga lokaci da ta fara magana yake aikin kallonta da jajjaye idanuwanshi kwala-kwala masu matuƙar ban tsoro, kana ya ƙara matso da ƙwayar dake cike da wasu koraye ruwa ya shiga faɗin wasu kalamai cikin wani yare. Tsawon lokaci ya share kafin ya ɗago ya kalleta cikin kakkausar murya ya shiga faɗin "Hajiya Bintu shekaru da dama da suka shuɗe mu ne muka yi miki aiki da kika shiga tsakani ɗan kishiyarki Faruq da mahaifiyasa, hakazalika mu ne muka yi miki asiri da Bilal ya kasa samun aiki muka kashe masa zuciyar nema ba ma wannan kaɗai ba hatta da mijin Bahijja mune muka tura masa baƙaƙen aljannu suka mayar da shi taɓaɓɓen. Saboda haka kada ki saka shakku akan aikinmu faɗin buƙatarki gaba gaɗi kowacce iri ce za mu tabbatar da mun biya miki ita?"
   "Godiya nake Boka jikan Baidu wadda yafi uwa da ubana domin su tuni suka shura gareni, yayin da kai har yanzu kake ganiyar share min hawayena. Boka na zo na gayamaka ne na kashe maciji na manta ban sare kai ba, wallahi ina cikin damuwa saboda sai yanzu na gano na tafka babban kuskure tabbas mu yi nasarar kashewa Bilal zuciyar nema kana mun dusashe kowacce hanya da zai bi domin yai dogaro da kanshi sai gashi kwatsam ya auro 'yar masu kuɗi, wacce take ƙoƙari rusa min daɗen burina na gani na hanawa Hajja cin moriyar 'ya'yanta Boka in takaice ma labari tun zuwan Jeeddah gidan Bilal daga shi har uwarsa da 'yar uwarsa Bahijja suka yi ban kwana da talauci, su ci mai kyau su sha mai kyau zuciyata ba za ta iya jure ganinsu a cikin walwala da wadata ba. Saboda haka na garzayu gunka domin kai kaɗai ne za ka iya magance min damuwata, Inaso duk yadda za ka yi Boka jikan Baidu ka wargaza jin daɗinsu ya koma baƙin ciki indan aka yi nasarar yi min hakan ni kuma na ɗaukar wa aljannu alƙawari shayar dasu jini na daga kowacce irin dabba suke muradi.
Wata irin kafirai dariya ya kece da ita sai da ya share lokaci yana tintsirar dariya, wacce ke nuni da muguntarsa ta wuce misaltawa kafin ya tsagaita da dariyar tasa ya kalleta gami da turɓune fuska, sai fuskar tashi ta dawo tamkar ta gwaggo biri "Buƙatar ki za ta biya Hajiya Bintu, yanzu faɗa min me kike so ayi musu?"
  "Boka so nake a shiga tsakani Bilal da matarsa ahana musu zaman lafiya, ka haddasa rashin jituwa a tsakaninsu ta haka za ta janye duk wani tallafi da take ba su.
Har ta dasa aya a zancenta Boka yana aikin kallonta, duk da ya kasance mushiriki amma sai yake gani rashin imanin Hajiya Bintu ya yi yawa bai taɓa gani bala'in kishi irin nata ba mutumin da take kishi akansa tuni ƙasa ta lulluɓe shi, baya gidan duniya amma ba ta saduda ba kullum cikin bin kishiyarta da 'yayanta da sharri take.
  "Ki sa aranki buƙatarki har ta biya domin matar Bilal da kike gani ita ma mace ce mai zazzafan kishi kamar ke ɗinan, saboda haka zan yi amfani da zafin kishinta na tarwatsa zamansu. Kuɗin aikina dubu ɗari sannan kuma za a yi wa aljannu yanka su sha jini na jan raƙumi idan kuma kuɗi za ki bada a siya musu sai ki bada dubu ɗari.
  "Shikenan Boka ai kafin na zo nasa ɗanta Faruk ya turo min da kuɗi saboda haka da ƙudinta ɗanta zan tarwatsa rayuwar ɗaya ɗan nata.
Ta ƙarasa magana tana dariya mugunta, nan take ta zuge jakkata ta fiddo da kuɗaɗen da ya buƙata wasu baƙaƙen layu guda biyu ya miƙa mata ki samu asirtatce wuri inda babu wanda zai gani ki binne su ki zuba ido za ki ga abinda zai faru...

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now