064

149 18 6
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

064.

Ban taɓa sani bacci ma rahama ne sai yau da Idanuwana suka soye babu digo bacci a cikinsu. Sun kada sun yi jajir ga wani ɗan uban nauyi da suka yi min. Duk sanda na rintse su da zimmar bacci ya ɗauke ni sai naji na kasa jurar rintse su ɗin da nayi. Yadda naga rana haka naga dare kiran sallar asuba a kunnena amma na kasa sauko wa daga kan gado da nufin sallah. Ko don ban taɓa shiga tashin hankali da fargaba irin wannan ba shiyasa nake ji tamkar an zare min lakkar jikina. Har aka kammala sallar asuba ina ta faman juye-juye akan gado. Cike da rashin kuzari na zura ƙafafuwana ƙasa na ja ɗuwawuna zuwa bakin gado na sauka, kamar jira ake yi na tsaya akan ƙafafuwana wani mugun jiri ya kwashe ni saura kaɗan ya kadani. In da ALLAH ya taimake ni ina kusa da bangon ɗaki nai sauri dafa shi da hannuna na dama. Da bin bango na shiga bathroom, na Kama ruwa tare da ɗauro alwala, tsabagen yadda jiri ke ɗibata dole sai a zaune nai sallah ina kammala sallah na ɗauki wayata ban daddara ba na sake dialling numbern Ya Haidar, tun a ringing na farko ya yi disconnected kana ya  kashe wayar tasa ga baki ɗaya. Wani kalar kife kaina nayi a gefen gado na dinga sauke numfashi akai-akai. Ina ciki wannan hali na ji an turo ƙofar ɗakin nawa an shigo gyaran muryar da mai shigowa ya yi yasa ni ɗagowa a firgici Babanmu na gani ya harɗe hannunshi a ƙirji fuskarshi a haɗe kamar mai gadin maƙabarta wallahi ban taɓa sani Babanmu yana kama da basawan film ɗin indiya ba sai yau da yai tsaye yana kallona yana wani muzurai yana zazzare idanuwa bashi da bambanci da Amrish puri {mugyambo} wani kalar murɗawa cikina ya yi nai sauri sadda kaina ƙasa muryarta tana rawa nace "Ina kwana Babanmu?"
  "Ke bani wayar ki!
Baba yai magana ciki tsawa haɗe da ƙara murtuƙe fuskarsa, wallahi mantawa nayi da jiri da nake ji na zubura da wani kalar sauri na tashi nesa dashi na tsaya na miƙa masa wayar, yai wani irin fincike ta da ƙarfi har yana haɗawa da yatsuna kana ya nuna ni da yatsa gami da faɗin "Daga yau ko nan da ƙofar gida ba za ki sake fita ba har sai na aurar dake. Munafuka yarinyar kalli yadda take sumui-sumui da kai sai ka ce mutuniyar kirki mtsss!
Baba ya ƙarashe magana tare da jan guntun tsaki ya fice abinsa.
**************
"Innalillahi wai'inna illahim raji'un! Hajja mun shiga uku mun lalace ga dukkan alamu ba ƙaramin shiri  Jeeddah ta shirya akan mu ba. Ba mu kuma san abinda za ta aikata anan gaba ba. Yanzu fa ta sanadin ta daga ni har Nusaiba mun shiga layi zauwarawa. Ni kam nayi mamaki ace Malam Haruna ya sake ni saki har uku ashe magani da muka ƙarbo a wurin boka na ciyar da mijina. ALLAH ya isa tsakanina da Jeeddah shegiya bakar tsinaniya muddin ina numfashi sai na zama sanadi tarwatsa rayuwarta baki ɗaya sai na wulaƙanta mata rayuwa sai na mayar da ita abar tausayi. Ta jira na tashi daga wannan jinya wallahi-azim sai na sabauta mata rayuwa sai na mayar da ita abar kwatance. Da sannu za ta san ko a jerin marasa imani ni ce lamba ta ɗaya.
Duk waɗannan maganganu suna fitowa ne daga bakin Aunty Bahijja tun jiya da Hajja da Nusaiba suka koma wurin bokansu ya sanar dasu asiri da yai musu akan Bilal da Jeeddah, shi ne a bisa kuskure Aunty Bahijja ta ciyar da mijinta kuma asiri ya yi tasiri akansa don gashi nan har ya sake ta saki uku. Tofa tun daga lokaci take ta faman sambatu sai kace kunce hauka.
Sosai Hajja da Nusaiba suka shiga firgici taya haka ta faru? A maimakon su yi nadama su fahimci ALLAH ne ya fara sakawa Jeeddah tun anan duniya amma sai suka ƙara zurfafa ƙiyayar da suke mata haɗe da ƙudurta mummunan shiri akanta.
Ta ɓangare Bilal Shattima ya ɗauke ƙafa gidan Hajja sai ya share mako ɗaya cur bai leƙa ta ba. Gaba ɗaya Hajja ta bi ta rame damuwa tana neman tai mata yawa musamman yanzu da take tsanani buƙatar kuɗi a dalili jinyar Bahijja da take yi dama shi Farouk ba a maganarsa tun farko ba wani damuwa ya yi da taimaka mata ba. Dama Bilal ne gatansu shi kuma yanzu gaba ɗayansu haushin su yake ji domin sune silar rabashi da Jeeddah. Wannan hali ko in kula da Bilal Shattima ke nunawa Hajja yasa ta ƙara ƙulatar Jeeddah tana ji duk duniya a yanzu basu da maƙiyiya sama da Jeeddah.
Haidar Ka'oje ya fito cikin shirin sa na fita office kansa tsaye ya nufo flat ɗin Mommy ya tarar da ita a ƙaramin falonta tana waya, tana ganin sa ta ƙara faɗaɗɗa murmushin kan fuskarta. Ya nemi kusa da ita ya zauna yana jiran ta kammala ta ɗauki lokaci mai ɗan tsayi tana magana har sai da ya gano da wacce take magana ya kuma fahimci inda maganganu nasu suka dosa, saboda haka ne ya tattara hankalinsa akan Mommy tare da kafe ta da idanuwanshi. Can kuma ya ji ta ce "En! Gashi ma zaune kusa dani bara na bashi.
Ta ƙarashe magana tare da miƙa mishi waya nan take ya ji wani irin kalar ɓacin rai sai dai wacce ke so magana dashi darajar ta a wurinsa ta wuce ta nemi magana dashi yaƙi karɓar waya. Da ace ba ita bace wallahi ba zai yi magana da ita ba. Ba don komai ba sai don abunda suke shiri aikatawa a gare shi. A natse ya yi sallama haɗi da gaida ta duk maganganu da take mishi yaƙe kawai yake tare da amsa mata. Ba wai don yana jin daɗin maganar da take mishi ba. Yana gama magana da ita jikinshi a mace ya miƙawa mommy wayarta, Mommy tai mata sallama tare da dawowa da hankalinta akan Haidar yanayi sauyawar fuskarshi yasa ta sakin baki tana kallonshi, wani irin sanyi jikinta ya yi wannan shi ake kira ga bikin zuwa babu zani ɗaurawa. A tunani ta Haidar zai fi kowa farin ciki da faruwar wannan al'amari sai kuma taga akasin hakan tun da tun farko da amincewar sa suka zartar da komai. Sai wani irin ɓacin rai take gani shimfiɗe akan fuskarsa.
   "Ya naga ba ka farin ciki Aliyu? Akwai wata matsala ce wacce ni bansan da ita ba?
Shiru ya yi ba zai iya faɗa mata ainihin abunda ke zuciyarsa ba saboda bayaso yai disappointed ɗin ta.
  "Babu komai mommy kawai dai ina fargaba wani nauyi da zai hau kaina.
'yar dariya mommy tayi tare da kama cheeks ɗin shi "Ka ga ni bana fargaba komai domin ina da yaƙini yarona jarumi ne zai iya. Ko ba komai Zarah tana matukar ƙaunarka Aliyu ta cancanci zama matarka.
  "Mommy ba za ki gane ba ni kaɗai nasan abunda nake ji a zuciyata.
"Ka ga Aliyu banaso ka sa wa ranka damuwa kasan yanayi lafiyarka.
"Tohm Mommy!
Ya faɗa cikin sanyi murya.
"Yaushe za ka shirya ka je Kebbi? Ya dace ka je ka ji nata shirye-shirye duk da mun gama magana da Hajiya Sa'a wani sati za su zo gara su tattaro su zo nan ayi shagalin bikin anan zai fi mana sauƙi ba sai an wahalar da mutane zuwa Kebbi ba.
"in-sha-ALLAHU zan yi ƙoƙari zuwa jibi nima na fiso ayi shagalin anan.
Mommy bara na wuce SY Barade yana jira na a office akwai muhimmin abu da za mu tattauna.
   "Shikenan ALLAH ya tsare nima fita zan yi so nake na je naji dalili da yasa Yaya Usman ya dake Jeeddah duk girman laifi da tai masa ai ba kamata yai mata mummunan duka irin wannan ba. Wallahi ba ka ji yadda raina ya ɓaci sa'ili da Hajiya Fatee tana bani labari yadda ya farfasa mata jiki.
   "Uhm! Mommy ni zan wuce.
Haidar yai sauri katse Mommy don ko kaɗan bayaso zance Jeeddah wani irin ƙunci da tsanar ta yake ƙara hauhawa  a zuciyarsa.
Jeeddah kwace a ɗaki wani irin zazzaɓi ke damunta tun shigowar Baba da ya karɓe mata waya ba wanda ya sake leƙo ta ba balle amsa hali da take ciki. Hatta da Aiman bata gani ba ya saba idan ba ta sami shirya shi zuwa school ba Mama ta shirya mishi ta kan umarce shi kafin ya wuce school sai ya shigo ɗakinta ya gaida ta koda tana bacci sai ya tashe ta amma yau ko take ko leiƙe bata ganshi ba. Misali ƙarfe 2 na rana ta ji muryar Aunty Farida da Khairat jim kaɗan sai ga Khairat ta shigo ɗauke da Baby Airah, kusa dani ta zauna na yunƙura da kyar na tashi zaune ina yatsina fuska a dalili wani irin bala'in sarawa da kaina yake yi  gaba ɗaya jikina tsamin dukan da Baba yai min yake cike da kulawa Khairat take kallona "Sannu Jeeddah yau da safe mama ta sanar da mu abunda ya faru ke kuwa Jeeddah me ya hau kanki da ki ka amincewa ɗan iskan mutumin nan Bilal Shattima? Me za ki tsinta a gidan shi har za yi auren kisan wuta kin koma masa?"
Nan da nan idanuwana suka cicciko da hawaye nai wani kalar langwaɓar da kai na marairaice gaba ɗaya na dawo kalar tausayi "Wallahi nima bansani ba Khairat lokaci da Love ya zo min da wannan zance na rasa me ya hau kaina da na kasa musa mishi, amma har can ƙasan zuciyata nasan abunda nake shirin aikata wa ba abu mai kyau bane, kuma bana ji daɗin hakan.
   "Anya kuwa Bilal Shattima ba asiri yai miki ba Jeeddah?
  "Asiri kuma? Wanne iri asiri Khairat?
"Irin wanda ki ka sani Jeeddah ban da aiki asiri ki duba ki gani har yanzu bakinki bai daina kiran Bilal Shattima da suna Love ba.
Ƙara marairaice murya nayi "ko ma mene ne Khairat a yanzu na dawo hayyacina na kuma yi nadama Dan ALLAH ku sa baki ke da Aunty Farida ku rarrashi Baba kada ya aura min Engr Ameer wallahi ba zan iya zaman aure dashi ba. Khairat ki faɗawa Baba na amince zan aure Ya Haidar.
  Zaro idanuwa Khairat tayi tare da nuna ni da yatsa tana faɗin "Ke ɗin Jeeddah ke ce bakinki ke furta wannan magana? Wallahi na kasa yarda.
Ina gani yadda na haifar wa da Khairat dimbin mamaki sai kawai na ci-gaba da yi mata daɗi baki don dai ta kara yarda da gaske Bilal Shattima asiri yai min. Nayi haka ne ko don Baba da Mama za su sassauto daga fushi da suke da ni ko ALLAH zai sa su haƙura da zance Egnr Ameer. Ai kuwa nayi nasarar dulmiyar da tunani Khairat ta yanda za ta yarda dari bisa dari aikin asiri ke dawainiya dani alhali kuwa tsabar son zuciya ne ya kanainaye ni. Sosai na dinga tsara Khairat ai kuwa ta zauna daram akai, ta bar min Airah ta koma falon Mama anan ta tarar da Ya Kabeer shi ma ya zo Baba ne ya kira su so yake su zama shaida akan irin hukunci da zai zartar akan Jeeddah sai kuma ga Khairat ta zo musu da wani sabon al'amari dama can idan ba ku manta ba daga mahaifiyar Jeeddah har 'yan uwanta basa ƙaunar Bilal Shattima don haka Khairat na faɗa musu ƙirrarren labari da Jeeddah ta ba ta ga baki ɗayansu suka yarda. A yanzu muna wani Irin zamani ne da son kai yai yawa ciki al'umma kowa nashi ya sani to kusan haka ce ta faru da Bilal Shattima don kuwa 'yan uwan Jeeddah da mahaifiyarta sun ɗauki laifi kacokan sun ɗaura masa sun yarda cewa asiri ya yiwa Jeeddah. Baba ne kaɗai ba yarda da wannan labari ƙanzo kurage ba sai ga ƙawar Mama Asabe ta zo musu da labari da ta ji yana yawo gari akan asiri da Hajja, Aunty Bahijja da Nusaiba suka yiwa Jeeddah wanda ya zama silar mutuwar aure Aunty Bahijja da Nusaiba don haka suke cewa har da Nusaiba asirin ya shafe ta shiyasa ita ma Bilal Shattima yai mata saki uku. Sai ga wannan labari ya bazo a gari sai yawo yake kusurwa-kusurwa wasu har da ƙari, da yiwa labari kwaskwarima wannan labari da Mama Asabe ta zo dashi yasa shi ma Baba tsoron zuri'ar Bilal Shattima ya darsu a zuciyarsa. Lallai dole ya yiwa Jeeddah aure domin shi ne kaɗai hanyar da zai sami kwanciyar hankalinsa da na iyalinsa. Baba ya ba wa Aunty Bahijja maƙudan kuɗaɗe da za ta siya min duk wani abu da ya danganci kayan ɗaki, ita kuma Khairat ita aka ba na siya kayan kitchen. Duk lissafi da suke yi ban furta uffan ba. Tun sanda Baba ya dawo ya aika aka kira ni har zuwa lokaci fuskarshi a haɗe bashi da walwala ko kaɗan na nemi kusa da Khairat na zauna tare da sadda kaina ƙasa Airah dake zaune akan cinyoyina ita ce mai ɗan ja hijabin jikina wanda har ya kai ni da ɗagowa karaf muka haɗa ido da Ya Kabeer wani mugun kallo ya watsa min babu shiri na kauda fuskata. Tun lokaci nake ta maimaita maganganu Babanmu akaina  "Ina so ku zama shaida akan irin hukunci da na yanke wa 'yar uwarku Jeeddah na ba da aurenta ga wanda naga ya dace da ita. Idan har tai yunƙuri bijere min a wannan karo ku sani babu ni babu ita kuma daga lokaci da ta bijire min na datse duk wata alaƙa a tsakanin ku da ita. Na gama magana da iyayen mijin nata Ameer ranar juma'a nan ta tafe za a ɗaura musu aure. Kabeer ka yi kokari ka buga katin gayyata gara Bilal da 'yan uwansa su san da cewa ta yi aure ko za su shafa mata lafiya.
   Har Baba ya gama magana kaina yana ƙasa hawaye na bin kumatuna, inaso na tashi na bar falo na koma ɗakina ko zan sami damar yin kuka, amma na kasa yin hakan. Muna nan zaune sai ga Mommy Turai ta zo tun sanda na ji sallamar ta wani irin mashahurin farin ciki ya lulluɓe ni, domin ita kaɗai ce nake sa ran za ta hana faruwar wannan aure musanmman idan ta ji cewa shalelenta nake so. Tana shigo kanta tsaye wurina ta fara zuwa ta ɗauke Airah ta miƙawa Khairat tana faɗin "Ke karɓi 'yarki tana cikin wannan hali ina taga ƙarfin ɗaukar wannan lukuta 'yar taki.
Ta ƙarashe magana tare da miƙar dani tsaye yayin da Khairat da Aunty Bahijja suka sa dariya Ya Kabeer ya ce "Dama mun faɗa Mommy da zarar kin zo gidanan ba za ki ga laifin Jeeddah ba. Sai ma ki buge da rarrashinta kamar yarinyar goye.
  Mommy bata kula Ya Kabeer ba a dalili shatin bulallai jikina da take kallo har da cire min hijabi tayi ai kuwa ta dinga faɗa kamar ta ari bakin kare. Gani haka na ƙara narkewa ina shasshekar kuka cikin muryar kuka nake faɗin "Ni dai Mommy ki yiwa Babanmu magana kada ya aura min Engr Ameer Ya Haidar ɗinki nake so Dan ALLAH Mommy ki taimaka min ki hana aure nan. Babu Kunya balle tsoron ALLAH Jeeddah ta dinga kuka haɗi da yiwa Mommy magiya wai Ya Haidar take so. Jikin Mommy a mace ta saki Jeeddah ta nemi cushion ta zauna sai da ta ja gwaron numfashi kana ta sauke kafin ta dubi Jeeddah ta ce "Jeeddah ki yi haƙuri ki ɗaure ki yiwa mahaifinki biyayya domin kuwa bakin alkalami ya riga ya bushe Aliyu da bakinsa ya gayamin a yanzu baya sonki, a yanzu haka har mun aika gidansu Zarah Malik har an tsayar da lokaci bikinsu sati ɗaya ne tsakanin auren ki da nashi. Don haka ina shawartaki da ki fitar da Aliyu a zuciyarki gudun kada ki je gidan mijinki kina begen wani.
Ina ji fitar waɗannan maganganu daga bakin Mommy Turai sai kawai na tsinci kaina cikin wani irin mugun ƙunci, na ɗago Idanuwana da suka kumbure na kalli Baba da Mama cikin rawar murya na ce "Ku yi haƙuri Baba da Mama in-sha-Allahu a wannan karon ba zan ba ku kunya ba zan yi biyayya akan hukuncin ku, zan zauna da Egnr Ameer nai masa biyayya ba za ku taɓa samun matsala daga gare ni ba. komi runtsi zan zauna dashi koda ace zai dinga yankar naman jikina.
Daga haka na fice da gudu na shige ɗakina na faɗa rub da ciki akan gado na dinga rusa kuka tamkar wacce aka yiwa mutuwa.
Da yamma da Mommy Turai za ta wuce ta ce na haɗa kayana dani za ta tafi gidanta domin tasa a gyara ni. Daga Baba har Mama ba wanda ya musa mata. Dukka yau saura kwanaki huɗu a ɗaura min aure suma sun san dole ina buƙata 'yan gyare-gyare musanman kasantuwa ta bazawara.
ALLAH sarki Mommy Turai macce mai halin dattako mai farar Zuciya yadda take farar tass haka zuciyarta take sam bata damu da irin abubuwan da na dinga aikata wa ɗan ta ba. Ɗaki guda ta ware min a gidanta da zuwanmu ta kira mai aikinta ta gyara min ɗakin ta shigar min da kayana. Mommy da kanta ta haɗa min ruwan wanka da wasu irin kaloli turarukan wanka masu masifar ƙamshi, bayan na fito daga wanka na shirya cikin doguwar rigar material mai gajeren hannu. Na same ta falo
madarar shanu mai ɗan dumi-dumi ta bani cike da wani ƙaramin jug ta ce na kafa kai na shanye ai kuwa na ji daɗin madarar sosai. Da dare ta dafa min kaza wacce ta ji kayan haɗi na musamman ita kan ƙin ci nayi sai kawai na fashe mata da kuka "Mommy ni fa banga amfani waɗannan magunguna da ki ke bani ba saboda ba son mutumin nan nake yi ba.
  Sanyayye murmushi mommy tayi tare da zaunawa kusa dani ta ɗura hannunta akan gashin kaina tana shafawa a hankali "Jeeddah.
  "Na'am!
Na amsa cikin muryar kuka.
"Don bakya so Ameer bai zama hujja da za mu kai mishi ke salaf babu gyara ita fa macce da ki ke gani sai da gyara wadannan abubuwa da nake baki sune za su ƙara linka miki daraja da ƙima a idanuwan mijinki ya ƙarq martaba ki.
"Ni fa Mommy da Ya Haidar ne za a aure min ko kaɗan ba zan miki musu ba duk abunda ki ka bani cinyewa zan yi amma wannan mutumin bana ƙaunar sa ko misƙara zarrati.
"Kin ga Jeeddah banaso kina maganar Aliyu shi ma fa aurensa zai yi ina amfani ki dinga maganar wanda baya ƙaunarki.
"Mommy Ya Haidar yana sona kawai dai ya yi fushi ne a dalili irin abubuwa da na dinga yi masa. Amma da za ku bashi ɗan lokaci zai sauko. Ko kuma kawai ku aura min shi na tabbata da zarar an mana aure komai zai wuce.
"Uhm! Yaro man kaza wanne irin lokaci ki ke so mu bashi Jeeddah? Kin manta a can baya mun baki lokaci ko za ki canza shawara ki amince da auren Aliyu amma ki ƙi. Ke lallai sai  Bilal Shattima, a haka muka haƙura ki ka aure zaɓin ranki. Ke da ki ke 'ya macce ba mu yi miki dole ba sai shi Aliyu da yake namiji shi ne za mu yi wa dole? Jeeddah dan ALLAH ki buɗe idanuwanki sosai ki fahimci gaskiya ki rage wannan so zuciyar naki shine yake hana ki fahimtar masu ƙaunar ki da gaskiya.
Wata irin mashahuriyar kunya ce ta kamani domin duk abunda Mommy ta faɗa gaskiya ne, na cika son kaina da yawa. Cike da kunya na soma cin kazar sai da na cinye ta dukka sannan Mommy ta umarce ni da na shanye romon nan ma ban mata musu ba.
Na ɗauke plate na kai kitchen Ina ciki wanke plate ɗin na ji muryar da a yanzu babu wani abu sama da ita da nake so ji da saurare. Nan take gabana yai mummunan faɗuwa, gashi na gama abunda nake yi a kitchen amma na kasa fitowa sai kawai na jingina bayana a kitchen cabinet ban ankara ba naji saukar hawaye a kumatuna.
Kamar daga sama na ji ƙamshin turarensa haɗe da footsteps ɗinshi yana tunƙaro kitchen, da sauri na goge hawayen fuskata. Da alama unexpected ya gani don reaction ɗin shi ya nuna hakan kallo ido cikin ido muke wa junanmu, kafin ya janye ganinsa ya nufi standard freezer dake kitchen ɗin ya buɗe ya dauki his favorite drinks and water bottle a mugun natse ya fice ba tare da ya sake kallona ba. Yana fita na ja kafirar ajiyar zuciya na sauke. Wannan gani da nai masa ya ƙara rura min wutar soyayyar sa. Jiki a mace na fito ina tafiya kamar wacce aka yiwa dabaibayi a ƙafafuwa. Ya Haidar ne kaɗai a zaune akan dining table yana ci abincinsa a natse da alama Mommy tana part ɗin Daddy, na ɗauki ɗan lokaci ina kallonsa kafin na nufi ɗakin da ya kasance mallakina. A hankali Haidar Ka'oje ya dire spoon ɗin hannunsa cikin plate ya bi ƙofar ɗakin da Jeeddah ta shiga da kallo kafin ya ja wata zazzafar iska ya fesar. Ya rasa dalili da yasa mommy ta kawo Jeeddah gidanan duk da ta faɗa masa dalili nata sai dai shi ko kaɗan bai gamsu da hujjar ta, ta ba.
Gani Jeeddah kaɗai da ya yi a yanzu ya ƙara linka masa tsanarta gaba ɗaya ya ji abinci gaba ɗaya ya fitar masa arai ya ji bakinsa babu apapite ya ture plate ɗin tare da jan guntun tsaki ya nufi ɓangaren sa.
Washegari mommy ta ɗauko mai gyaran jiki ta fara gyara min fatar jikina cikin kwanaki uku na canza ni kaina da na kalli jikina a mirror dake bathroom sa'ili da na je wanka naga nayi bala'in sauya wa hatta da ƙirjina sun ƙara ci-cikowa. Da na tuna duk wannan gyaran da nasha don wancan mahaukaci aka yi shi sai naji mugun haushi ya turnuƙe ni. Ana gobe ɗauri aure Mommy ta ce na haɗa kayana direban ta zai kaini gidan Aunty Farida wai a can za a gudanar da walima zuwa lokaci zuciyata ta ri ga da ta gama bushe na sadakatt! Shiyasa ban mata musu ko gardama ba. Ina zuwa gidan Aunty Farida na shige ɗaya daga cikin ɗakunan baccin ta nai kwanciya ta. Duk wasu hidimomi daga Aunty Farida sai Khairat ke gudanar da abin su. Sai dai abinda yake ɗaure min kai bai wuce har kawo yanzu Engr Ameer bai nemi ni ba. Duk da na alaƙanta hakan da karɓe min waya da Baba ya yi. Ni dama hakan ba ƙaramin daɗi yai min ba domin bana ƙaunar ko sunansa a ambata min, wata irin tsanarsa nake ji a zuciyata fiye da irin tsanar da nai wa Ya Haidar a can baya. damuwa ta ɗaya ce da har yanzu ban yi magana da Love ba na sanar dashi abunda yake faruwa, banaso ya zarge ni da cin amanar sa, shiyasa ina gani Khairat ta shigo ɗakin da nake bayan mun gama magana za ta fita na ce ta ara min wayarta tai shiru kamar ba za ta bani ba sai nai maza na ce da ita Mommy Turai zan kira ta ce da mun iso na ari waya na kira ta wannan karya da na sharawa Khairat yasa ta bani wayarta, ta kuma fice jikina yana rawa na saka numbern Love nai dialling har ta gama ringing ta katse bai ɗaga ba haka na ci-gaba da kira har sai da na jeranta mishi kira goma a na sha ɗaya ne ALLAH ya taimake ni ya yi picking ina jin muryarsa na kidime "Hello....love... Love kana ji na?".
"Ni Ko ke ji ki macuciya, azzaluma mayaudariya!
"Rass!rassss! Sauti dake fita daga ƙirjina kenan babu shiri na miƙe zaune tare da dafe ƙirjina cikin rawar murya na ce "Kafin ka kira ni da wadannan sunaye Love tsaya ka ji ta bakina.
"Me zan ji daga bakinki sama da wanda tsinanne yayanki Kabeer ya zo har majalisar mu ya faɗa min cikin bainar jama'a. Wai har ni Love ɗan uwanki zai yiwa ƙazafi ya ce nai miki asiri? Jeeddah yaushe nai miki asiri? Wannan al'amari kafin gudanar dashi sai da amincewar ki amma haka Kabeer ya rufe idanuwanshi ya dinga zagina har da shaƙe min wuya ya kwakwaɗa min maruka.
"Uhm! Ka yi haƙuri love nima na bi su ta haka ne da zimmar asiri kai min don na samu Iyayena su sassauta fushi da suke dani, daga ƙarshe kuma sai gashi za su aura min mutumin da banaso gobe ne ma daurin aure Love na rasa ina zan tsoma raina naji sanyi Love ka taimake ni wallahi banaso aure nan.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "gaskiya Love Ya Kabeer munafiki ne domin ni ce min ya yi da amincewar ki za a yi wannan aure da har na fusata na fara cilasta wa kaina tsanar ki.
Cikin matsanancin kuka na ce "Wallahi-azim bana sonshi idan da akwai abinda na tsanar a faɗin duniya nan bai wuce wannan aure da wanda zan aura ba.
  "Na sani Love dama tun farko sai da zuciyata ta dinga wasu-wasi akan aure. A yanzu mafita ɗaya ce ta rage mana ki gudu kawai koda za a nemi  ke kin gudu kin ga dole a fasa ɗaura aure, zan nemi wanda zai aure ki a sati ɗaya ya sake ki har sai mun maida auren mu watakila har da albarka 'ya'ya sannan ki dawo, ɓatanki zai sa iyayenki su yi nadama duk sanda ki ka dawo gare su, su karɓe ki ba tare da sun tuna da abinda ki ka aikata musu ba.
Cikin kaɗuwa na zazzare idanuwa "Love guduwa fa kace? Wannan wacce irin gurguwar shawara ce? Gaskiya ba zan ɓoye maka ba zan iya guduwa ba. Ni kenan nai ta samun matsala da Iyayena.
"Love wannan kaɗai ce hanyar da ta rage mana da za mu mallaki juna ciki sauƙi muddin wancan ɗan iskan ya aure ki na tabbata ko za ki daɓa masa wuƙa a ciki ba zai taɓa sake ki ba. Ni kaina Love ta dalilinki nai watsi da mahaifiyar ta da 'yar uwata kuma a dalilin na faranta miki na saki matata Nusaiba saki uku, shin Love duk wannan sadaukarwa da nai akanki ni ban cancanci ki yi ɗan wannan abin akaina ba?" Love komi runtsi komai wahala gara ka rayuwa da masoyinka da ka rayuwa da maƙiyanka. Ni dake muna son junanmu kuma mun ishe junanmu a yanzu mun taka matakin girma za mu iya gudanar da al'amurra rayuwarmu koda babu tallafi iyayenmu.
A haka Bilal Shattima ya ci-gaba da dulmiyar da tunani Jeeddah har yai nasara akanta ta amince dashi nan take ya shirya mata yadda za ai ta gudu sai da dare ta sace jiki ta fito tun dama a gidan Aunty Farida za ta kwana shi kuma zai jirata a ƙarshen layi gidan Aunty Farida. Zai yi ƙoƙari ya aiko mata da ƙaramar wayar da za su dinga communicating. Da wannan shawarar suka tsayar da matsaya guda.
Haka kuwa aka yi wuraren Bayan sallar la'asar sai ga wata budurwa ta zo gidan Aunty Farida wai ta zo gurin Jeeddah a cewar budurwa wurin aikinsu ɗaya da Jeeddah, yayin da ita Jeeddah tasan ɓata ma taɓa ganin koda mai irin kamanunta balle har su haɗa wurin aiki, amma da yake jikinta ya bata 'yar aike Bilal Shattima ce sai kawai ta dinga washe mata baki har dasu tambayar ta sauran collogue ɗinsu. Daga nan ta ja ta zuwa bedroom ɗin Aunty Farida, ta murɗawa ƙofa key. Budurwa ta zuge zip ɗin jakkarta ta fiddo da waya ta miƙa wa Jeeddah hannu na rawa Jeeddah ta karɓa gami da ɓoye ta idan ba wanda zai ganta ballantana a tuhume ta inda ta sami waya ɗin.
Bayan wasu mintuna suka fito daga ɗakin budurwa ta yiwa su Aunty Farida sallama da zimmar gobe za ta dawo walima.
Bayan wucewar budurwar Jeeddah ta koma ɗaki ta shige bathroom suka yi waya da Bilal Shattima.
Misali ƙarfe goma na dare Jeeddah ta gama shirinta tsaf a hankali ta buɗe ƙofa tana sanɗa daidai ta kawo ƙofar fita, sai kawai ta tsikayi muryar Aunty Farida a kitchen tana waya abinda ta ji tana faɗa a wayar ya yi sanadi da jikinta ya ɗauki kakkarwa yawun bakinta suka ƙafe, ta ji tamkar duniya tana juyawa da ita da kyar ta ja ƙafafuwanta ta koma ɗaki, ta faɗa bisa gado tana sauke numfashi kafin zafafan hawaye su dinga bi gefen Idanuwanta. Wayar da ta sakaɗe a cikin skirt ɗinta tai vibrating ta ciro ta kana ta kare a kunnenta da buɗar bakinta sai cewa tayi "Ka yi haƙuri love ba zan iya bijirewa Iyayena ba. ALLAH ya ba ka wacce ta fi ni ina ma fatan alkhairi.
Kafin yai magana nai maza na kashe wayar tare da switch off ɗinta na jefa ta bayan gadon Aunty Farida.
Washegari da misali ƙarfe 11:00am aka ɗaura aure Jeeddah Usman maishadda da Engr Ameer Bello Sardauna ɗaurin auren da yabar ɗimbin tarihi da tarin abubuwan ban mamaki...

Shin wanne irin tarihi ne haɗe da abubuwan ban mamaki daurin aure Jeeddah da Egnr Ameer ya bari?
Duk wacce ta canki amsa daidai na yi mata alƙawari bata damar karanta next Novel ɗina na kuɗi kyauta.
A kafta!!!!!!

#Engr Ameer
#Bilal Shattima
#Haidar Ka'oje
#Jeeddah maishadda
#Aunty Farida
#Ya Kabeer
#khairat maishadda.

 

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now