075

123 15 4
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*
_________________________________

*Abishirinku mata 'yan kwalisa masu son su faranta wa mazajensu rai, ku gamsar da su iya gamsuwa to ga dama ta same ku da za ki saka maigida ihun daɗi da haɗaɗɗun kayan mata daga kamfani Manzil Alwafir masu kyau da inganci, Hajiya za ki mallake mijinki a tafin hannunki ba Boka ba malam maza ki garzayu wurin gimbiyar haɗa mata mai bada gudunmawar gyara shimfiɗar aure Hajiya Hassana Abdullahi*

*_Muna da kaya kamar haka_*

Smoked heaven
Asta
Ashana
Yaqtur
Nashwa
3rd Avenue
Back to honeymoon
Kazar Mata
Tsumi
Dambun mata
Sanyi herbs
Helwa
Anwar
Deep sea
Vibrationzz
Wet and tight
Ashwa
Halwa
Helwa
Garden knot
After dark intense
Bomb oil
Yoni balm
Swan
Taurariya
Lazeez
Persion hot
HD tea
Mazan Arewa
Tightening honey
Jego package
Bridal package
Durot

Domin ƙari bayani sai a tuntube mu a waɗannan lambobi 08036072970 08121555525
_________________________________

075.

Ko kaɗan ban yi mamaki ji fitar waɗannan maganganu daga bakin Bilal Shattima ba. Saboda tun fil'azal bakinsa, ba shi da kimtsi a duk lokaci da yai niyar fitar da zance ba ruwansa da tauna wa ko saita linzamin harshen sa faɗa kawai yake. Amma duk da haka ya kamata ya iya gane jiya ba yau ba. A Yanzu banida wata alaƙa dashi da zai dinga furta min iri-iri waɗannan maganganu gudu kada na ja zance da nisa ya sami damar ci-gaba da faɗa min maganganu da suka danganci soyayya sai kawai na ce dashi "Abban Aiman halan ka ya rashin lafiya ne?
"Uhm! Kin ga duk na rame ko? Wallahi duk rashin ki ne Jeeddah duk namiji da ya rasa ki a matsayin matar aurensa wallahi ya tafka babbar asara. Shiyasa har gaba da abada ba zan daina kukan rasa ki da nayi. Na kuma tabbata har abada Haidar Ka'oje ba zai taɓa rabuwa dake ba balle na saka ran dawowar ki gare ni. Na tabbata rabuwar ku sai dai mutuwa wacce tsakani ni dashi ba a san gawar fari ba.
"Uhm! Na faɗa ban sa miyasa nake ji wani kalar tausayinsa yana ratsa gaɓɓan jikina.
Sai da ya ja zazzafar iska daga bakinshi kana ya furzar kafin ya sake cewa "Ke kam da alama kin sami natsuwar zuciya don ga shi nan kin yi fresh ki yi ƙiba abinki sabani ni da na dawo wani susu, dama an ce ba ka sani muhimmanci abu har sai ka rashi shi. Sai yanzu na gane irin mugun muhimmanci da ki ke dashi musanman a ciki rayuwata.
Cikin rauni murya dana zuciya na ɗago na kalle shi na ce "Kai ma idan ka saka wa ranka dangana Bilal Shattima za ka manta da komai kaman yadda na manta, ka yi haƙuri kai mikawa Ubangiji al'amurran ka da sannu za ka ga haske. Ka ɗaure ka yi aure a hankali za ka ji na fice maka a rai gaba ɗaya rayuwar da muka yi za ta zama tarihi a gareka.
Murmushi ya yi mai matuƙar ciwo yana ji aransa ina ma zai iya maida hannu agogo baya, ina ma ace rabuwarsu ta kasance mafalki da kuwa idan ya falka baya tunani zai sake kwanta wa da nufi bacci. "Bana tunani sake aure nan kusa Jeeddah asalima na ƙudurta wa raina ni da aure har abada amma tun da ki ka yi magana In-sha-ALLAHU zan yi ƙoƙari na nemi wacce za ta iya haƙuri zama dani.
Yadda yai magana ya ƙare min tausai shi har idanuwana suka cicciko da ƙwalla A'isha Shattima take tsaye tun ɗazu a jikin ƙofar shigowa ta ƙaraso jikinta a sanyayye dire  plastic jug gaban Bilal mai ɗauke da zobo cikin sanyi murya ta ce "Maganar Jeeddah gaskiya ce yaya ka yi kokari ka yi aure In-sha-ALLAH za ka manta da ita.
"Haka ne A'isha amma mantawa da Jeeddah ba abu mai sauki bane.
Ya faɗa yana murmushi mai matuƙar ciwo.
Kaɗan ya sha zobo da A'isha Shattima ta kawo mishi ya ciro kudi masu yawa ya ba Aiman ya ce ya siye chocolate kana ya ciro wasu ya miƙawa A'isha  ya miƙe tsaye yana faɗin "A'isha bari na tafi domin ina dab da rushe muku da matsanancin kuka.
Ya ƙarashe magana yana kallon Jeeddah ta gefen ido A'isha Shattima tayi dariya "Naga alama gara ka tafi ɗin don ko ƙawata ka ƙarya mata zuciya.
"Wai haka ne Jeeddah na ƙarya miki zuciya?
Hawaye da tun ɗazu nake ɓoye wa suka silalo min a kamatu, ban amsa mishi ba kamar yadda ban ɗago na kalle shi ba. Ya juya ya nufi ƙofar fita yana faɗin "Sai anjima A'isha.
"Tohm! Yaya.
Har A'isha Shattima ta ƙarasa min kitso zuciyata tana min wani irin muka yi sallama na nufo gida akan hanyata na tsaya wurin masu siyarda fruits ina jira akawo min nayi nisa a tunani Bilal Shattima har ga ALLAH yayi matuƙar bani tausayi kaman daga sama Ameer Sardauna yaga motar Jeeddah fake a wurin masu siyarda fruits, da wani kalar sauri ya saka signal ya gangara gefen titi yai parking. Jikinsa na wani kalar rawa ya ɓalle murfin mota ya fito jikinsa sanye da ƙanana kaya black jeans haɗe da t-shirt dark blue in color ƙafarsa sanye ciki black sneaker 👟 kasancewar nayi nisa a tunani shiyasa ban ji shigowar sa cikin motata ba sai kawai na ji saukar muryarsa a dodon kunnena "Maijiddah!
A kidime na waiga backseat inda yake zaune ya zuba min rikitattun idanuwanshi da babu komai a cikinsu sai rikici. Nan take wani kalar mashahurin tsoro ya lulluɓe ni, jikina ya ɗauki rawa tsabar tsorata da nayi har hadewa haƙora na ke yi zufa sai tsatsafo min yake yi a sassan jikina da ka kalle ni za ka tabbatar da cewa a tsorace nake.
Wani irin kallo Ameer ke mata tamkar zai cinye ta musamman da ta karawa idanuwanshi kyau na Musamman.
"Hajiya a ina za a saka miki fruits ɗin?
Muryar fruits vendor ce ta sani waiga wa gefe inda yake tsaye na haɗiye wasu busassu miyau, muryata tana rawa na ce "Ka saka min a backseat.
Ya buɗe ɓangare da Ameer yake yana ganinsa sai kawai ya miƙa masa ledar a sakamakon wani kalar kallo da yake yiwa fruits vendor ɗin. Cike da zallar tashin hankali na kirga kudinsa na bashi.
"Maijiddah ba ki yi farin ciki ganina ba ko?
Nan ma shiru nayi babu amsa sai faman wuƙi-wuƙi da idanuwa nake yi.
"Shike nan tun da ba ki yi farin ciki ganina ba sai dai ni ina farin ciki ganinki har bana iya tantance adadin farin ciki da nake ciki. Maijiddah Babanki bai kyauta min ba tsakani da ALLAH Babanki bai da tausayi, haka kawai yai fatali da zazzafar soyayya da nake miki ya aurawa Haidar Ka'oje ke alhali na fi Haidar ɗin sonki. Kowa kallo mahaukaci yake min maijiddah yes nasani ina da lalura amma wallahi-azim soyayya da nake miki ta gaskiya ce ko kaɗan lalura ta bata shafi so da ƙaunar da nake miki, shiyasa na yanke shawara zan je na nemi lafiyata idan ALLAH yasa na dawo to tabbas zan dawo ne da dukkan ƙarfina don sai na kwato ki a hannu wancan Haidar ɗin. Ina so ki sa aranki komi dare dadewa zan dawo gareki.
Har ya dasa aya a zance sa nayi zugun ina kallonshi "Ba za ki yi min magana ba Maijiddah?
Na kauda fuskata na kalli titi ina yadda motoci ke da komo.
"Idan fa ba ki buɗe baki ki ka yi min magana ba, ba zan taɓa fita daga motar nan ba.
Ya faɗa cike da gargadi da sauri na dawo da ganina kan fuskarsa "Ka ji tsoron mahaliccin ka Ameer ka tuna ni matar aure ce kada ka tsalleke iyakar ka.
"Da ace bana tsoron mahaliccina da yau ba zan barki ki koma gidan Haidar Ka'oje, don haka ki bini a hankali mu rabu lafiya.
Ban iya cewa komai ba iyakacina na ja bakina nayi shiru, sai zuba yake min tun ina fahimtar inda maganganu sa da kuma inda suka dosa har na dawo bana fahimtar komai, ni dai muradina mu rabu lafiya kaman yadda ya faɗa. Sai da ya gaji don kansa kana ya fita sai koma ya dawo saiti da inda nake ban ankara ba ya zura hannunshi ya cire min key ɗin mota, ya ce da Aiman "How far my boy?
"I'm fine uncle shikenan rana ka manta ba ka bani bicycle 🚲 ɗina da chocolate da biscuits ɗina ba ko?
Aiman ya faɗa yana turo baki dariya Ameer ya yi kafin ya ce "Ai tunawa dasu da nayi yasa na cire wa mommynka key domin ko nace ta jira na kawo maka ba za ta jira ba ta matsu ta gudu ta barni.
Dariya Aiman ya yi yana faɗin "To yi maza ka ɗauko min uncle.
"An gama my boy.
Ya faɗa haɗe da juyawa da sauri jim kaɗan sai gashi ya dawo ɗauke da keke ya buɗe boot ɗin motata ya saka ya sake komawa ya dauko shopping bags guda biyu ya miƙawa Aiman yana faɗin "Ga chocolate da biscuits ɗinka my boy sai mun sake haduwa ka kula min da mommynka sosai.
Hankali Aiman ya karkata ga shopping bag ɗin da yake kokari buɗewa shiyasa ko kaɗan bai fahimci me Ameer yake faɗa ba.
Yayin da Ameer ya dawo side ɗin nake sai da ya ƙare min kallo kafin ya miƙo min key ɗina ina miƙa hannuna da nufi na karbi key ɗin na ji ya furta "Tsalki ya tabbata ga Ubangiji mahalicci wannan kyakkyawan hannu tabbas duk wacce tai miki wannan ƙunshi Maijiddah kwararriya ce ina ma ace na kasance miji a gareki da ba abinda zai hanani kwana ina kallo wannan zane lalle.
Da azabar sauri na ɓoye hannuwana ciki mayafina ina ya mutsa fuska sai kawai ya saki miskilin murmushi ya mayar min da key inda ya ɗauke shi.
  "ALLAH ya tsare ya kai ki gida lafiya ki tsumaye dawowata Maijiddah.
Ya faɗa tare da juya wa ciki sauri ina kallonshi ta mirror har ya shiga motarsa ya halba ta kan titi kana na sauke ƙarfaffiyar ajiyar zuciya na je mota na nufo gida. Tun kafin na ƙarasa parking lot na hango Ya Haidar da Zarah Malik suna zaune akan fararen kujeri rubber a daidai ƙofar shiga flat ɗin ta. Kallo ɗaya nai musu na ɗauke fuska ina jan tsaki rai ɓace na fito daga mota na kama hannu Aiman nayi tamkar ban gan su ba na wuce flat ɗina. Wanka na fara yi kana na yiwa Aiman sai na wuce kitchen na ɗura abinci koda aka yi kiran sallar magariba har arranging dining table nayi na sake yi wanka tare da alwala na gabatar da sallah ban tashi ba sai nayi sallar isha kana na zauna gaban dressing mirror na tsantsara kwalliya lips ɗina ya ji red lipstick doguwar rigar cotton material na saka na saki kitsona ya sauka a gefe da gefe wuyana ban ɗaura ɗan ƙwali ba sai na yafa siriri mayafi na fice zuwa main parlor sai uban ƙamshin khumara nake yi. Aiman na tarar har ya fara bacci akan kujera na tashe shi muka nufi dining room na zuba mishi abinci.
Cike da kukan shagwaɓa Zarah Malik take kallo Haidar Ka'oje "Sweetie za yi mugun kewarka wallahi kwanaki biyu nan ji su nake tamkar shekaru biyu.
Kyakyawan murmushi ya sakar mata tare da jawo ta jikinshi ya sumbace forehead ɗin ta yana shafar gadon bayanta "Nima zan yi kewarki matata ki kwatar da hankalinki banaso abinda zai haifar miki rashin natsuwa komai ƙanƙatarsa kin ji my sweetie?
Ta gyaɗa kai tare da raba jikinta da nashi ta juya ta nufi upstairs tana faɗin "Sai da safe sweetie kada mu shiga hakki Jeeddah nasan tana can tana jiranka.
  "Sai da safe!
Ya faɗa da sanyi murya tare da ficewa ina tsaye a gefen Aiman dake ci abinci Ya Haidar ya turo ƙofa gami da sallama na amsa mishi ba yabo ba fallasa, Aiman yana ganinsa ya ture plate ɗin abincinsa ya nufe shi "Daddy oyoyo!
Da sauri ya ɗauke shi ya rungume yana juyi dashi. Na taɓe baki cike da tu'ajjabi nake kallonsu ban taɓa gani yaro mai ƙarfin hali irin Aiman haka kawai za ka dinga kira wani da suna Daddy alhali ba shi bane asali mahaifinka nasha zaunar dashi na faɗa masa Ya Haidar ba shi bane asali mahaifinsa. Bilal Shattima da yake kira da uncle shine asali wanda ya haife sa banaso ya ci-gaba da yaudarar kansa, yana kallo Ya Haidar a matsayin mahaifi. Duk da banga laifin Aiman ba, koda ya buɗe idanu Ya Haidar ya sani sakamakon sakaci Bilal da rashin kulawa da al'amarin sa yasa sam Aiman baya kallonshi a matsayi uba.
Yana ɗauke da Aiman suka shigo dining room ɗin. Sai lokaci na ƙare masa kallo yana sanye da ƙanana kaya blue trouser jeans 👖 haɗe da white long sleeve shirt ya yi stocking da belts mai tambari D&G shigar tayi masifar yi masa kyau muna haɗa idanuwa ya sakar min tattausa murmushi har yana haɗawa da kashe min ido da sauri na ɗauke fuska na dawo da ganina kan Aiman ina faɗin "oya zo ka ƙarasa ci abincin ka in kuma ka ƙoshi mu je ka yi brush ka kwata gobe akwai school.
"Na ƙoshi mommy.
Aiman ya faɗa har ya juya sai kuma ya juyo cike da rigima ya ce "Mommy ina ki ka ajiye key ɗin motarki na ɗauko bicycle, da shopping bags ɗina?"
Harara na maka mishi a tsawace nace "Wuce ka bani wuri banaso surutu wofi.
Cike da rigima ya ce "Ni mommy kekena nake so kin ga bani da keke a nan gidan Dan ALLAH ki ɗauko min abina.
Ya Haidar ya kalle ni ranshi ya fara ɓaci a dalili yadda yaga Aiman dab da fashe wa da kuka
"Jeeddah Please kar ki saka shi kuka mana ke kwata-kwata ba ki iya lallaɓa yaro ba. ina ki ka ajiye key ɗin  na ɗauko mishi keke ki huta da rigimarsa.
"Ka duba kan centre table.
Na faɗa a dakile ni fa tun ɗazu da na ganshi da Zarah Malik nake ji haushinsa. Ya juya tare da kama hannu Aiman suka fice, yana fito da keke daga boot ya kalle Aiman yana murmushi "Iyee Aiman ɗan mommy ashe mommynka naji da kai da ta siya maka irin wannan keke mai kyau da tsada.
Karaf Aiman ya karɓe zance yana faɗin "Daddy ba ita ta siya min ba ina wannan mutumin wanda ya taɓa zuwa dani gidansa har ku ka yi faɗa da daddare har ni da mommy muka dinga kuka to shi ne ya siya min tun a wannan rana don kun yi faɗa ne shiyasa bai samu damar bani ba sai yau da muka haɗu dashi a wurin siyar da fruits, har ya shiga motar mommy ya ma daɗe ciki motar yana ta yiwa mommy magana. Sai na tuna masa bai bani kayana ba....
"Ya isa Aiman.
Haidar ka'oje ya katse shi wani irin abu ya ji ya tokare mishi maƙoshi nan take zuciyarsa ta shiga ƙawata mishi wato fitar da Jeeddah tayi ba wajen kitso da ƙunshi kaɗai ta je ba har wajen wannan mahaukaci mutumin. Wato shine dalili da yasa take wani ɗaɗɗaure masa fuska. Rai ɓace ya shigo parlor ɗauke da keken yayin da Aiman yake biye dashi riƙe da shopping bags. "Aiman wuce ɗakinka ka yi brush ka kwanta gobe sai ka hau keke naka.
Haidar ya faɗa fuskarsa a haɗe Aiman bai musanta masa ba ya wuce ɗaki da Jeeddah ta ware masa. Ba tare da Haidar ya kalle Jeeddah ba fuuu ciki fushi ya wuce ɗakinshi dake sama mamaki ne ya lulluɓe ni sakamakon gani yadda Ya Haidar ya haura sama ba tare da ya ko kalli gefen da nake ba. Ya kuma san shi nake jira ya zo yaci abinci.
Raina ne ya yi mugun ɓaci wani ɓangare na zuciyata ya shiga gayamin ai dole ya yi min haka tun da ni ɗin ba Zarah Malik bace wacce yake so da ƙauna yanzu tun da girki ya zagayo kaina bari ya wulaƙanta ni, ya nuna min dama can ba ƙaunata yake ba. Hawaye na ji suna bin fuskata na juya tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki na shiga dakin da Aiman yake har bacci ya ɗauke shi nai mishi addu'a tare da kashe wuta na rufu mishi ƙofa na wuce ɗakina. Ina ciki cire kayan jikina na ji an turo ƙofa da ƙarfi, har sai da na tsorata Ya Haidar na gani fuskarshi mugun haɗe "waye siya wa Aiman keke?
Sai na ji wani kalar faɗuwar gaba yayin da tsoro ya lulluɓe ni sai kawai nai kokari ɓoye hali da nake ciki na tsinci kaina da faɗin "Babanshi ne ya siya mishi.
"Ƙarya ki ke yi Jeeddah wannan mahaukaci ne ya siya mishi sannan kuma don tsabar iskanci da rena igiyar aurena da ki ka yi har da bashi dama shiga miki mota kuna hira. To bari ki ji wannan shi ne gargadi na farko kuma na ƙarshe da zan miki idan hakan ta sake faruwa wallahi-tallahi sai ranki ya yi mummunan ɓaci banza da batasan inda yake mata ciwo ba. Mtsss! Ya ƙarashe magana tare da jan dogon tsaki ya juya tare da buga min ƙofa yabar ni tsaye na kasa tabuka komai, ko ban tambaya ba zan iya canka mai shegen surutu nan ne Aiman ya gayamasa, ai kuwa da safe sai naci ƙarniyarsa sai na bubbuge masa baki nan nasa mai surutu tsiya.
Yadda naga ya ɗauki zafi yasa ban bi ta kansa ba dama tun can haushinsa nake ji bana kuma farin ciki haɗa jiki dashi baya na gama sani ya yi wadaƙarsa da Zarah Malik. Na sauya kaya jikina zuwa sleeping gown na bi lafiyar gado.
Shiru-shiru Haidar Ka'oje yana jira yaga Jeeddah ta zo ta bashi haƙuri amma bata zo ba gashi yana matuƙar ji yunwa ya rasa gane wacce irin kalar ƙwaƙwalwa ce a kokon kan Jeeddah, har ya kwanta sai kuma ya tashi kasancewar yasan kanshi ne zai cuta ita ɗin ba damuwa tayi dashi ba shi kaɗai ke haukarsa akanta. Sai da ya fara wucewa dining room ya cika cikinsa ya koma ɗakinsa ya yi brush ya kwata, sai kuma ya kasa bacci sai faman juyi yake akan gado ya riga ya gama sani daɗin kwanciya da macce a gefensa. Zubur ya tashi ba tare da ya tsaya shawartar zuciyarsa balle ta kawo mishi wani ƙamli da ba'adi a hankali ya tura ƙofa ta ciki diff light ya hango ta kwance idanuwanta fess akansa hakan ya tabbatar masa ita ma ta kasa bacci.
Ya nufi kusa da ƙafafuwanta ya zauna cikin daurarriyar fuska ya ce "Ki tashi za mu ya magana.
"Bani da wannan lokaci za ka iya komawa waje wacce ka ke so nasani ita ma tana can tana jiranka yau ba za ta iya bacci ba tun da baka kusa da ita kaima nasan kafi so kasancewa can fiye da nan don haka ka tafi kawai na yafe mata kai.
Har ta kai ƙarshen zance ta yana kallonta "Reni wayau ki yawa ne dashi Jeeddah ki yi min laifi amma tsabar wulaƙanci ba za ki iya buɗe baki ki bani haƙuri ba. Yanzu da ace na biye miki za ki barni na kwana da yunwa ina fushi dake.
"Ni fa bana so harka da ɓaci rai Ya Haidar tun da ba sona ka ke yi ba nima ba zan sake haɗa jikina da wanda baya ƙauna ta.
"Wai miye matsalar ki ne Jeeddah?
"Kaine matsala ta Ya Haidar nasani baka farin ciki da wannan aure namu saboda haka kada ka yaudari kanka ka tashi ka koma waje wacce ke ba ka farin ciki.
"Kishi, kishi, Jeeddah ba abinda ki ka iya ki ka fi kwarewa dashi Jeeddah da wuce zafin kishi idan ki ka ci-gaba da nuna wannan mugun kishin naki za ki yi ta wahala a banza.
A fusace na tashi zaune na kunna bulb haske ya gauraye ɗaki idanuwana har sun fara canza launi musamman yadda ya danganta ni da rashin iya komai wato manufar sa Zarah Malik ta fini a shimfiɗa hakan ma yake nufi ɗayan ɓangare zuciyata ya ce dani cike da zallan masifa na ce "To tun da ban iya komai ba me zai hana ka saukewa min na kama gabana yadda ka ke min kallo ban iya komai ba a haka wasu ke haukar sona...
Tun kafin na dasa aya Ya Haidar yai min ɓari makauniya, sai da naga wuta haɗe da jajaye taurari sun mamaye wa ganina, abinda ban fahimta ba shin marina ne Ya Haidar ya yi ko kuma naushi ne ya kai min tsakani da ALLAH na kasa tantance wa, don sai da na fado daga kan gado na dunƙule waje ɗaya.

#Haidar Ka'oje
#Jeeddah maishadda
#Zarah Malik
#Ameer Sardauna
#Team zazzafan kishi.



***************








ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now