026

93 12 1
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!* _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250
_ku ƙara haƙuri dani wayana ke bani matsala ga kuma matsalar rashin wutar lantarki abin ba a cewa komai sai godiyar ALLAH_

026...

Kujerar rubber Hajja ta dauƙo ta zaunar dani har zuwa lokaci ɗan banza ciwo mara da nake ji bai lafa ba. Sai ma daɗa ƙaruwa yake Babyna kuma tun sanda ya sha fizga daga hannun Babanshi bai sake matsowa ba. Har yanzu yana nan dunƙule a waje ɗaya. Ga uban gumi nake haɗawa gaba ɗaya wuyan hijabin jikina ya jiƙe sharkaf da zufa Aunty Bahijja da ke kwance ta kalloni tana faɗin "Hajja lafiya ba dai haihuwa za ta yi ba ai kuwa watan haihuwar ta bai kama ba da sauran lokaci?"
Sai da Hajja ta rabani da hijabin jikina kafin ta maida hankalinta akan Aunty Bahijja ta ce "Ba haihuwa bace ba Bahijja rigima ce suke yi ita da Nusaiba har da dambe.
"Rigima kuma Hajja ita Jeeddah tana cikin wannan hali ta ke da ƙarfin hali yin dambe ni fa da A'isha ta shigo ta kira ki wallahi na zaci naƙuda ce ta kama ta ashe haukarta ce kawai ta motsa.
Sosai na ji haushin furuncin Bahijja na ƙarshe akaina, wato ita kallo mahaukaciya take min to shikenan a tafi a haka duk da ina jin zafin ciwon mara hakan bai hanani ɗagowa na watsa mata mugun kallo ba gami da yin ƙwafa tabbas bashi taci akwai ranar da za ta biya.
Hajja ta ci-gaba da faɗin "Ni na rasa me ke damunki Jeeddah yanzu banda lalacewa me ya kai ki dambe da tsohon ciki salon ki ji wa ɗa cikinki ciwo ki tashe mu tsaye Dan ALLAH ki dinga aiki da hankali mana.
Samun kaina nayi da ƙarewa Hajja kallo daga sama har ƙasa sai faɗa take yi tana wani kumfan baki da tada harshe sai ka rantse da ALLAH ɗan ta ke ɗauke da ɗawainiya ta. Akwai ɗan raguwar mutuncinta a idanuwana shiyasa na kyaleta ta ci-gaba da cin karenta babu babbaka. Sai da ta gaji don kanta tai shiru A'isha Shattima ce kaɗai ta goyi bayana don duk faɗa da Hajja take yi A'isha Shattima sai ƙoƙarin depending ɗina take yi.
Magana da Aunty Bahijja ta sake jefa min ta fi komai ci min rai ta ƙara linka min ɓaci saboda sosai na fusata ba kaɗan ba don har sai da idanuwana suka cicciko da hawaye.
"Hajja dama kin hutar da kanki da yi ma Jeeddah faɗa domin kina ɓata miyau bakinki ne a banza maganganuki ba wanda za ta ɗauka balle har tai amfani dashi, haƙuri kawai Bilal yake yi da ita domin shi kaɗai yasan irin baƙar wahalar da yake sha akan azababben kishinta, ba hali ta ganshi da mace koda kuwa 'yar uwarsa ce sai ta nemi ta ɗaga masa hankali. Sai kace kanta aka fara aure dama za ki daina wannan haukar yafi miki domin Bilal da kike gani mijin mace huɗu ne in-sha-Allahu ba zai lalace akan mace guda ɗaya tak ba. Gara tun wuri ki koyi yadda ake sarrafa kishi ake danne shi.
Sai yau zuciyata ta ƙara gamsuwa da cewa Bahijja bata ƙaunata duk da tun a can baya tasha nuna min abubuwan rashin ƙauna ni ce dai ban ɗauke su da muhimmanci ba tun da mijina yana sona amma yau da ta fito ƙarara ta juye min abinda ke ƙunshe cikin zuciyarta akaina sai na ƙara yarda lallai bata ƙaunata.
Duk inda raina yake ya gama ɓaci babban abinda ya ƙara harzuƙa ni bai wuce danganta mijina da mata huɗu da ta yi ba. Saboda haka a mugun fusace na kalleta cikin tsanani fushi idanuwana sun rufe ruff na ce "Sai yau na tabbatar da cewa Aunty Bahijja ke muguwa ce ko a cikin mugaye mutane kina cikin baƙaƙƙe wanda da matuƙar wahala su ji daɗi zaman duniya, in banda mugunta da mugun nufi me nayi miki da za ki dinga danganta mijina da wasu mata to kisani duk mugun nufinki da yarda ubangiji kanki zai ƙare don gashinan kin fara gani aya.
Na ƙarashe magana ina huci gami da wulga mata uwar harara.
Daga ita har Hajja salati da sallalami suka hau yi suna wani tafa hannuwa sai kace na faɗi mugun abu. To ko ma mugun abu na faɗa ai su suka jawo saboda haka a shirye nake da na faɗi abinda ya fi wannan muni matuƙar ba a daina danganta mijina da wata mace ba.
"Jeeddah!
Hajja ta kira sunana tana wani zarar ido kallon sama da ƙasa nai mata na kauda fuska, sai uban huci nake ƙara zubawa ƙirjina sai ya yi sama ya dawo ƙasa. Sosai Hajja ta ƙure ni da kallo kafin ta ce "A'ah babu lafiya wallahi akwai damuwa ke Bahijja maza kama min bakinki banaso shiga sharo babu shanu.
"Na yi shiru Hajja amma wallahi za ta san ta taɓo 'yar halak da ni take zance.
Da mugun ƙarfi na waigo na kalleta na ce "Ai ni na zaci da shegiya nake zance ashe da 'yar halak ne. Ikon ALLAH su 'yar halak manya to Dan ALLAH Dan Annabi 'yar halak idan har ba cika baki kike yi ba in gani a ƙasa kodai ki sa Bilal Ibrahim Shattima ya sake ni ko kuma ki aura masa Nusaiba wannan kaɗai za ki yi da zai gamsar dani kasantuwarki 'yar halak!
"Hajja kina ji sunan Babanmu ta faɗa gatsal ba ko kunya lallai Jeeddah ba ki da tarbiyya.
Aunty Bahijja ta faɗa cike da gundarin tsana da takaincin Jeeddah.
Da sauri A'isha Shattima ta dawo kusa dani tana zungurar ƙafata da ƙafarta sai wani ƙiƙƙita min idanuwa take yi nufinta in yi shiru ita ma tasan aiki banza take yi don ba shiru zan yi ba. Matuƙar Aunty Bahijja ba ta saita shegen bakinta ba ta daina yaɓa min maganganu banza da na wofi nima ba zan daina mayar mata da martani ba tun ba tsoronta nake ji ba.
"Bahijja kar na sake jin bakinki ki kyaleta tayi ta yi ita kaɗai in tagaji dole tai shiru ai ƙarfe ɗaya baya amo.
Hajja ta faɗa tare da jan kujera ta nufi kusa da gadon Aunty Bahijja ta zauna, tana ci-gaba da ba ta baki karta kula ni.
A'isha tai ƙasa da murya ta ce min
"Dan ALLAH Jeeddah ki yi shiru ya isa haka ki tuna Aunty Bahijja yayar mijinki ce bai kamata ki biye mata ba ku dinga musanya yawu ba.
"Shikenan don tana yayar mijina sai na kyaleta ta yaga min rigar mutunci? Da kike zance yayar mijina ce ai ba ita ta haife shi ba balle tai min gadara.
"Shikenan koma menene ki yi shiru da bakinki faɗar irin waɗannan maganganu bashi da amfani.
"To na ji nayi shiru amma wallahi-tallahi daga yau na kula gaba mai tsanani tsakanina da Aunty Bahijja ko a lahira banaso ALLAH ya haɗani da ita.
Har A'isha Shattima ta buɗe baki tai magana aka turo ƙofa sai kawai ta huɗiye abarta.
Bilal Shattima ne ya shigo da 'yar gajeriyar sallama ɗauke da bakinsa Hajja da Aunty Bahijja ne suka amsa mishi sai kawai ya zuba min idanuwanshi jikina ya bani cewa yana kallona, don ni ko kallo bai isheni ba. Na ɗago fusatattun idanuwana na kalle shi dasu yadda ya ga ina aika mishi mugun kallo yasa yai sauri ɗauke idanuwanshi daga kaina. Hajja tayi gyaran murya gami da kiran sunanshi "Bilal!
"Na'am Hajja.
"Ɗauki matarka ka kaita asibiti da take awo a dubata gudun faruwa matsala sannan kuma ka ci-gaba da haƙuri ka daina biye mata ka ji kou?"
Da mugun sauri na maida hankali da idanuwana kansu mamakin furuncin Hajja ya lulluɓe ni kuttt....amma gaskiya matar nan 'yar bala'in so zuciya ce banda kafiri son zuciya irin nata wai ɗanta take ba wa haƙuri akaina ai ni ya dace ta ba wa haƙuri ni da aka ha'inta aka ciwa amana amma tsabagen son zuciya irin nata sai ɗanta take cewa yai haƙuri, kada ALLAH yasa ya haƙura ɗin ya ɗaɗe bai ɗauki mataki akaina ba.
Duk waɗannan maganganu ni da zuciyata ke yi su amma da ka kalleni za ka ga yadda bakina ke musu-musu ko ba ka tambaya ba kasan martani ne nake mayarwa.
"Shikenan Hajja duk yadda kika ce haka za a yi amma duk da haka sai na nunawa Jeeddah kuskure ta na tozarta ni a bainar jama'a.
A fusace na kalleshi na watsa masa baƙar harara kana na ja guntun tsaki tare da taɓe baki, na miƙe rai ɓace duk da ciwon da nake ji a ƙasan marar ta hakan bai hanani fizgar hijabina ko sakawa ban tsaya yi ba na nufi ƙofar fita dashi a hannu duk kiran da Hajja take min ko waigowa ban yi ba nai kunne uwar shagu da ita nai tafiyata, Bilal ya biyoni a baya ina jinshi a bayana, yana kwalla min kira shima nai banza dashi sai da na kawo reception kana na tsaya nasa hijabina tsayawar da nayi yasa shi haɗawa da gudu ya tadda ni reception ɗin. Yana zuwa ya rufe ni da faɗa cikin fusata yake faɗin "wai ke ba ki ji duk kiran da ni da Hajja muke miki bane?"
Sai da na kalleshi na watsar kafin nace "To sai aka yi yaya don naji kuna kwalla min kira, kai bari ka ji Love tura fa ta kai bango na gaji da wulaƙanci da ku ke min kai da danginka ya isa haka. Idan har ka gaji da zama dani babu dole. Amma wallahi-tallahi ba zan ƙara lamunta jin Aunty Bahijja tana danganta ka da wata mace ba, domin mataki da zan ɗauka daga kai har ita kai har ma da baƙar munafuka nan Nusaiba ba zai muku daɗi ba.
Ina ƙarashe magana na juya na fice daga reception don bani da lokaci sauraren amsar da zai bani muradina ya ji abinda ke raina kuma na zazzage masa, da sauri ya biyo ni yana faɗin "wai za ki tsaya na kai ki asibiti ko za ki ci-gaba da nuna baƙin kishinki na hauka ne?"
A mugun fusace na juyo na galla masa harara gami da jan tsaki.... mtsssss!
Ina fita gate na sami adaidaita ina shiga Bilal yana ƙarasowa "kin ga Love ni ban damu da haukarki ko kaɗan ba damuwata ɗaya lafiyar Babyna.
Uffan ban ce dashi ba na umarci mai adaidaita ya ja adaidaita mu tafi, ana na barshi tsaye ya bi adaidaita da kallo har muka ɓacewa ganinsa kafin ya yi ƙwafa tare da cizon gefen baki ya koma cikin asibiti. Kaitsaye asibiti na wuce da kyar na sami gani likita sakamakon yamma tayi scanning aka umarce ni da na je nayi in takaice muku labari ranar na sha wahala sosai bayan na kawo hoton likita ta tabbatar min da lafiyar Babyna. Tun kafin na iso gida naga alamar hakan domin sai kicking ɗina yake yi.
A tunanina Bilal zai dawo gida da wuri sai naga saɓani haka don har nayi bacci bai dawo ba a takaice sai da asuba na ganshi, ko kallon arziki bai haɗa ni dashi ba. Ban ƙara tabbatarwa da Bilal ya gaji dani ba sai yau domin ko ya tambaye ni ya nake ji hakan ya ƙara fusata ni na harzuƙa iya harzuƙa na ayyana wa zuciyata gidanmu zan tafi. Shiyasa yana fita na shiga tattara duk wani abinda yake da amfani gareni. Dama tun jiya a fusace nake na kasa goge hoton ganinshi da Nusaiba da nayi da kuma furuncin da Aunty Bahijja tayi...

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now