017...

91 8 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

  *Ga masu buƙatar a tallata musu hajarsu cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

     _*Gare ku masoyana ma'abota karantar litattafai na ga wata dama ta same ku ta karanta littafai na har guda uku a cikin farashi mai sauƙin gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune Kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga mai buƙatar guda ɗaya kacal_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250
*For those who have interest contact me on my cell phone number only WhatsApp 07032566172*

017...

Tana buɗe ƙofa taci karo da fuskar Ya Kabeer babu annuri kwata-kwata akan fuskar tashi. Take duk wani bala'i da masifarta ya rikiɗe izuwa tsoro har batasan lokaci da ta dafe saitin zuciyata ba saboda bugawar da take mata kamar za ta fashe. Cikin tsanani tsoron da ta kasa ɓoyewa ta sauke idanuwanta ƙasa cikin rawar murya ta furta "Ya Kabeer kaine sannu da zuwa shigo mana?"
Kusan duk a lokaci guda ta watsa masa waɗannan tambayoyi.
   Wani irin shegen takaicinta mai haɗe da zallar haushinta ya ƙara lulluɓe Ya Kabeer, dama tun ɗazu da officer Abdul-ganiyu ya kirashi a waya ya zayyane masa ta'asar da tayi yake ji haushinta yanzu kuma da yai ido biyu da ita sai ya ji haushin nata ya ƙara linkuwa fiye da ɗazu. Bai furta uffan ba ya raɓa ta gefenta ya shiga parlounta ya zauna, jikinta yana rawa ta maida ƙofa ta rufe ko ba a faɗa mata ba za ta iya cankar dalilin zuwan nashi gidanta a dai-dai wannan lokaci. A tsorace take matuƙar tsorata shiyasa ta kasa zama ta ja tai tsaye tana rarraba idanuwa. Wallahi sai yanzu nake nadamar abinda na aikata domin kuwa Ya Kabeer baya tolerating nonsense, yanzu haka na fi tsoronshi sau dubu akan Babanmu domin shi Baba komai girman laifi da mu ka yi masa sai dai yai mana faɗa da nasiha. Mama ce gwanar duka ita ma sai an kaita bango take duka, saɓanin Ya Kabeer da abu kaɗan zai wa mutum dukan mutuwa kuma wallahi idan yai duka sai mutum ya kwanta jinya shiyasa nake bala'in tsoronshi.
   "Ke don ƙaniyarki ba gunki na zo ba da za ki wani koma bayan kujeri ki laɓe maza dawo nan, shegiya yarinya mai neman ɗauko mana Dala da Gwauron Dutse.
Faɗa ya Kabeer ya katse min zance zuci da nake take naji tsoronshi ya ƙara kamani.
"Dan ALLAH Ya Kabeer ka yi haƙuri wallahi sharrin zuciya ne ba zan sake ba.
Ta faɗa cikin muryar son yi kuka.
  "Na rantse da Allah idan ba ki zo ba kika bari ni na zo mai hana na ɓalla ƙasusuwanki gidanan sai ALLAH.
Yana rufe bakinsa ta rugu ta zube gabanshi ko ta ina jikinta rawa yake yi, ta wani kwantar da murya tana bashi haƙuri kamar saliha yadda ya zuburo daga jikin kujera a fusace yasa ta ƙara tsorata ta zubura da suna ta miƙe tsaye tsananin tsoratar da tayi yasa ta kasa miƙewa sai kawai ta faɗi zaune daga zaune ta dinga jan ɗuwawunta sai jin tai taci karo da kujerar dake bayanta, babu saura wata hanyar guduwa dolenta sadakatt! Rai ɓace Ya Kabeer ya nuna ta da yatsa kafin ya ce "Ke don gidanku yaushe kika yi mijin da za ki iya kisan kai akanshi?" To wallahi bari ki ji in faɗa miki gaskiya wannan dabbaci da kika ɗaukowa kanki ba inda za kai ki sai ga halaka, in banda kina daƙiƙƙiya akan ɗa namiji marar tabbas za ki yankawa 'yar mutane wuƙa to ki godewa Allah da yasa Jessy tana da haƙuri da indan ta makaki kotu da duk ubanda da yai miki tsaye sai kin je prison. Mahaukaciyar banza da wofi. Ina tabbatar miki muddin Baba ya ji wannan maganar wallahi sai ya ci ƙaniyarki. Har yanzu na kasa yarda ke ɗinan Jeeddah za ki iya yankar jikin ɗan adam saboda kishi. Ban taɓa tsammanin rashin hankalinki ya kai har haka ba. To ki buɗe kunnenki da kyau ki saurareni nan gidan ba na mijinki bane kuma ba ki gadonsa ke kaɗai, ballantana ki hanawa 'yan haya sakatt! mu nan kasuwanci muke yi ba ki isa ki karya mana kasuwancinmu ba, idan ba za ki iya jure gani Bilal yana kula Jessy ba sai ki nema muku wani gida ba abinda ya dame ni. Ba gara Jessy daku ba tun da ita tana biyan kuɗin haya duk ƙarshen shekara ku kuma fa?" A batin sidam kuke zaune to wallahi ki kiyayeni. Ni ba Baba bane da ke jure iya shegenki ko yanzu kinci darajar igiyar aure da ke kanki da sai na nakada miki shegen duka. ko kallon banza kika sake yi wa Jessy sai kubar gidanan sai ku je can ku ƙarata ke da mijin naki ɗan gold autan maza, kuma ina ƙara gargaɗinki wannan mugun kishin da kika tsirowa kanki na jahilci tun wuri ki watsar da shi kin ji na gayamiki.
Sosai maganganu Ya Kabeer suka ci wa Jeeddah rai saidai bata da yarda za ta yi iyakacinta ta bashi haƙuri kuma duk yadda ta kai da bashi haƙuri hakan bai sa ya haƙura cikin sauƙi ba, sosai yacici mata mutunci ya wanke mata allonta ciki da waje, sai ga Bilal ya dawo bai ji mamaki gani Ya Kabeer ba saboda dama ya kwana da sani Jessica tace sai ta faɗa mishi, shima hakan ba ƙaramin daɗi yai masa ba gara tun wuri iyayenta su san hali da ake ciki gudun abinda zai iya faruwa anan gaba.
  Ya Kabeer ya kalli Bilal Shattima yana fitar da numfashi mai ɗan zafi, tsakani da Allah hadda Bilal ɗin haushinsa yake ji don gani yake yi shi ne ya sakarwa Jeeddah dama tai yawa shiyasa ta fara wannan mugun hali.
Shi ma Bilal bai tsira daga faɗa Ya Kabeer ba rufe idanuwa ya yi yaci masa mutunci iya son ranshi, kana ya miƙe ya ya saka su gaba zuwa apartment ɗin Jessica, sai da Jeeddah ta bata haƙuri, sannan Ya Kabeer yai tafiyarsa ko haƙuri da Bilal Shattima bi shi har wajen gate yana bashi bai tsaya sauraren shi ba ya faɗa motarshi yai tafiyarshi. Dama can Ya Kabeer jininsu bai haɗu da na Bilal ba. Jeeddah tana gani Ya Kabeer ya tafi a fusace ta shiga apartment ɗinsu sai cika take tana batsewa, domin ita gani take yi bata yi laifi da za ta bada haƙuri ba. Ya Kabeer ya yi haka ne don kawai bayaso aureta da Bilal. Take ta ayyanawa ranta ba za ta sake zuwa gidanshi ba. Kuma ko a waya ba za ta ƙara kiransa ba a takaice ma blocking ɗinshi za ta yi. Tana cikin zance zuci ta ji Bilal ya turo ƙofa ya shigo ya ci karo da ita tsaye riƙe da curtain rod na window ta cire hijabin jikinta, babu ɗan kwali akanta dama ta tsife rabin kitso kanta bata shace ba sai yai wani buzuzu, ga idanuwanta sun kode sai kawai ta dawowa Bilal Shattima abin tsoro musanman da ta tsare shi da mugun kallo da dakwa-dakwa idanuwanta. Sai da gabanshi ya faɗi rass! Sai kawai yai ta maza ya wuce ta batare da ya tanka ta ba kaitsaye ya wuce bedroom yana cikin cire kayan jikinshi tai bala'in banko ƙofa da ƙarfi ta shigo ta sake jingina jikinta ga bango. Tana harare-harare.
   "Wai Jeeddah miye haka ya za ki shigo min ɗaki ba sallama, sannan kuma kin wani tsare ni da kallon reni wayau dallah wuce ki gyara sumar kanki gaba ɗaya kin yi wani wujuga-wujuga dake ni wallahi tsoro ma kike bani.
  Bilal ya ƙarashe magana gami da jan guntun tsaki, kana ya nufi ƙofar shiga bathroom don har yanzu da raguwar haushinta shimfiɗe a ƙasan zuciyarshi, kafin ya kama handle Jeeddah ta rugu tasha gabanshi ganinsa da tayi yanzu ya dawo mata da image ɗin abinda ya faru da safe cikin masifa ta ce "Kai har ka isa kayi wanka a gidanan ai indan ka ga kayi wanka Bilal Shattima ka faɗa min alaƙar dake tsakaninka da Jessica da har ka iya ware yatsunka ka kwaɗa min mari saboda ita?"
   Kallon ƙasan ido yai mata kafin ya yi murmushin takaici yana girgiza kai, shi wallahi tausai ta yake ji gani yake yi kamar akwai noti da ya kwance a ƙwaƙwalwarta. Lamarinta sam bai yi kama da na lafiyayyun
mutane ba. Shiyasa ya rarrashi zuciyarsa ta hanyar riƙo damtse hannunta ya nufi gefen gado da ita duk yadda ta so ta kwace ta kasa saboda ƙarfinsu ba ɗaya ba, tana ji tana gani sai da ya zaunar da ita da ƙarfin tsiya. Kana ya zauna daff da ƙugunta yasa ɗayan hannunshi ya zagaye ƙugunta ya riƙe ta da ƙarfin gaske ya kwantar da muryarsa ya shiga faɗin "Jeeddah Please ki natsu ki bani aron hankalinki mu yi magana ta fahimtar juna...
  "Babu sauran wata magana da za mu yi a tsakaninmu kawai so nake ka faɗa min tsawon wane lokaci ka dauka kana cin amanata?"
  "Jeeddah ki daina jifa ta da iri waɗannan zafafan maganganun naki wallahi suna matuƙar sosa min rai. Kamata ya yi kafin ki tuhume ni ki tsaya ki yi nazarin girman laifin da kike zargina dashi...
  "Dallah ya isa kai har kana da wata kalma da za ka kare kanka da ita bayan da idanuwana naganka kuna musanya numfashi kai da ita hadda marena kayi akanta. Shine don ka gama rena min wayau za ka ce ina zarginka wato ma zarginka nake ko Bilal?"
Ta ƙarashe magana tare da rushewa da sabon kuka da sauri ya jawo ta jikinsa dama already ba kaya a jikinsa daga shi sai boxer briefs, da ƙarfi ya haɗe bakinshi da na ja'ira ya shiga bata zazzafan kiss yasan bai da amsa da zai bata da ta wuce wannan gara ya kashe bakin tsiyar nata, duk ture shi da take yi yaƙi sakinta da ƙarfi tsiya ya raba ta da kayan jikinta, duk yunwa da take ji sai da tasha murza ta jigata matuƙa a hannunshi. Jikinta ya yi mugun weak har ya yo wanka ya fito tana yashe bisa gado tana rera kuka.
Hayo gadon ya yi ya ɗagata yana faɗin "Love please I'm sorry wallahi-tallahi banso kuka nan naki. Ko kaɗan banaso abinda zai ɓata miki rai balle har ki zubda hawayenki, a tunanina ke ce wacce ta dace ta bada kyakkyawar sheda akaina amma sai gashi kina zargina da aikata abu mafi muni da ɗimbin zunubi zina...
  "Ni fa bance kana zina ba...
   "To ki faɗa min uban me zan tsinta a tattare da Jessy wanda babu shi a jikin matata?"
Ya katse ta a fusace gani yadda ya fusata yasa saitin ƙwaƙwalwarta ya fara dawowa dai-dai sai kuma jikinta yai sanyi musamman da ta tuna da Bilal Shattima ba mazinaci bane to miyasa ta kasa tuna hakan tuntuni gashi nan ta jawo kanta al-bala'u, domin muddin maganar nan taje kunnen Baba batasan wane iri mataki zai ɗauka akanta ba. Saboda abinda ta aikata ba ƙaramin abu bane da Baba zai zuba mata ido ba tare da ya ɗauki mataki ba. Cike da nadama ta kalli Bilal Shattima idanuwanta suna tsiyayar hawaye ta ce "Na shiga uku Love dan Allah ka yi haƙuri ka yafe min wallahi bansan me ya hau kaina ba. Na rasa dalilin da yasa idan naga wata mace ta raɓe ka sai na fita daga hayyacina. wallahi-azim Bilal ina matuƙar ƙaunarka ina maka wani irin so da zuciyata ba za ta jure ganinka da wata mace ba. Haƙiƙa zan iya haɗiye zuciya na mutu saboda azababben kishinka da nake ji dan girman ALLAH Love karka so kowa mace sai ni kaɗai. Idan ka riƙe min wannan alƙawari wallahi zan yi ta faranta maka, har izuwa ƙarshen numfashinta duk abinda kake so shi zan maka.
   Shi wallahi dariya ma ta bashi sai kawai ya rungume ta a jikinshi yana bin gaɓɓan jikinta ta ko ina da kisses, kafin ya ɗauke ta cakk zuwa bathroom ya taimaka mata tai wanka kasancewa jikinta bai da kwari a dalilin yunwar da ta yini da ita. Bayan ta gama wanka ta fito ɗaure da towel, ta zauna akan stool gaban dressing mirror kallonta ya yi cike da kulawa gani tana runtsar idanuwa hannunta dafe da cikinta yasa shi matsuwa kusa da ita ya dafa shoulder ta yana leƙen fuskarta yace "Love da alamu fitinarki yau bata barki kin ci abinci ba kou?"
Saidai ta harareshi kafin tace "kwanciyar hankali ke sa a ci abinci ni kuma bani dashi sai yanzu da na dawo cikin natsuwata na fahimci ina jin yunwa.
Ɗan guntun tsaki ya yi saboda ya ji haushin yadda ta zauna da yunwa akan wani kishinta na rashin dalili, sai da ya dungure mata kai kafin ya nufi ƙofar fita yana faɗin "ki kimtsa jikinki ki sami ni a parlour na haɗa miki tea ki fara da shi kafin na dafa miki noodless, na tabbata kishin Bilal Shattima bai bar ki kin mana girki ba.
Da kallon so ta bishi dashi kafin tai magana har ya fice da sauri, sai da tafara busar da sumar kanta da hand dryer da rabi yake a tsafe kana ta shirya cikin sleeping dress cotton half gown mai gajeren hannu, koda ta fito har ya haɗa mata tea mai kaurin gaske tana ƙarasa sha ya fito ɗauke da plate ɗin soyayyar indomie. Tare suka ci hatta da plate da mug ɗin da tasha tea sai da ya wanke su kafin ya dawo parlour ya zauna kusa da ita cikin kwantar murya ya ƙara nusar da ita kuskuren da ta tafka na yankar Jessica da tayi, haƙuri ta ƙara bashi kafin ta kwanta akan three sitter. Miƙewa Bilal Shattima ya yi yana faɗin "Love ina kika ajiye tsinke {Kibiya} da comb na ƙarasa tsife miki kitso nan don ba zan barki ki kwana da rabin kai a tsafe ba.
Shagwaɓe fuska tayi tana turo baki gaba tana faɗin "Love bacci nake ji ka bari sai gobe.
  "Ki yi baccinki ni kuma ki bar ni nayi aikina kawai ki faɗa min ina kika ajiye tsinken.{Kibiya}
Sai da ta ƙara turo baki kafin ta ce "zo ka duba bisa two sitter ɗinan ina gani kamar anan na barsu.
Ya duba cikin sa'a ya ga comb tsinke Kuma sai da duba under sofa ya ganshi, ya ɗauke kanta ya ɗora akan cinyoyinshi ya shiga tsife mata raguwar kitso kanta da kasa ƙarasa tsifewa saboda zazzafan kishinta da ya motsa.

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now