038

77 10 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

*Ya ALLAH ka jiƙan Abba Bello ALLAH ka sada shi da Rahamar ka Ya ALLAH ka haskaka kabarin sa Ya ALLAH ka albarkaci 'ya'ya da ya bari ka ba wa 'yan uwanshi da masoyansa dake faɗin duniya haƙuri rashinsa ALLAH ka sanya mana dangana ga Zuƙatan mu. Ina daɗa miƙa saƙon ta'aziyya ga ɗaukaci masoya magoya bayan Abba Muhammad Bello tabbas mu yi rashin ɗan takara nagari. Oh! ALLAH forgive him, have mercy on him grant him with Aljannatul Firdausi we loves you Abba but ALLAH loves you more We’re still proud of You you’re gone but your good heart and kindness towards other peoples still remains in their hearts.*😭😭😭😭😭

_Dan ALLAH ina barar addu'a zuwa ga Abba Muhammad Bello ga ma'abota karanta wannan littafi_

038...

Banza tayi dashi gami da ture hannuwanshi daga kafanɗunta. Ta wuce ta gefen shi ta nufi kan gado ta kwanta duk da haka Bilal Shattima bai daddara ba ya sake biyo ta ya kwanta a bayanta tare da rungume ta. Cikin sanyi murya ya ce "Love please banaso fushinki ki faɗa min abinda ke damunki sai ki yi ta cin rai kina fushi ko ni ne na ɓata miki rai?
Rai ɓace ta tashi zaune tana ya motsa fuska "I'm fine ba abinda ke damuna banaso yawan tambaya Please ka kyaleni nai bsccina.
Yanda ya ga tana amsa mishi magana kamar bata so sai kawai ya yi wa kanshi ƙiyamullaili ta hanyar furta
   "Shikenan ki kwanta ki yi baccinki.
"Uhmm! Ta faɗa tare da sake bin lafiyar gado.
Ya ɗauki dogon lokaci a zaune yana kallonta kafin ya tashi ya shiga bathroom.
Washegari wasai Jeeddah ta tashi ba kamar yadda ta dinga cin rai a daren jiya ba. Ta kammala ayyukan ta na yau da kullum kana tai shirin tafiya office.
Bilal Shattima ya fito daga bathroom ɗaure da towel ya kalle Jeeddah da ke tsaye a gaban mirror tana rolling veil mahadin brown Eypyt Abaya da ke sanye a jikinta ta cikin mirror ta kalle shi gami da faɗin "Love breakfast ɗinka yana kan dining ni zan wuce office banaso nayi latti.
  Ta ƙarashe magana gami da ɗaukar handbag ɗinta.
  "Idan kin dawo daga office ki biya gida ki duba jikin Hajja jiya hawan jininta ya tashi.
   "Subhanalillah! ALLAH ya bata lafiya. in-sha-Allah idan na taso zan wuce ta can na duba ta.
   "Shikenan ALLAH ya tsare.
Bilal ya faɗa tare da ci-gaba da goge jikinshi.
Daga haka ta fice abinta.
Da Jeeddah ta taso daga office sai da ta tsaya akan hanya ta siyawa Hajja fruits mai kyau sai da aka cika babbar leda baƙa kana ta nufo gidan. Wuri ta samu a Kofar gidan tai parking kana fito da ledar da ke ɗauke da fruits ɗin ta shiga gidan tun a tsakar gida take kwaɗa sallama har ta iso ƙofar parlour Hajja ba wanda ya amsa mata sai kace wacce ta shigo gidan kurame alhali tana jin surutun mutane yana tashi a cikin parlour. Ta daɗe tsaye a bakin ƙofa sakamakon ba a bata izinin shiga ba can sai ga Mufeeda ɗiyar Aunty Bahijja ta leƙo ta gaidata ta amsa mata gami da miƙa mata ledar hannunta. Mufeeda ta koma ciki kana Jeeddah ta biyo ta a baya Hajja tana kwance a tsakiyar parlour kan  ƙatuwar katifa. Aunty Bahijja tana a gefenta a zaune. Sake yi sallama Jeeddah tayi tare da durƙusa wa ta gaidata Hajja gami da tambayarta lafiyar jikinta. Can ciki ta amsa mata ta miƙe tare da zaunawa akan kujera batare da ta kalle Aunty Bahijja ba ta gaidata ta amsa mata a wulaƙance.
Dama ban saka ran za su amsa min a mutunce ba domin a yanzu ba wacce suka tsana suke nuna wa zallar ƙiyayya sama dani, tun abin yana damuna har ya zo ya daina saboda nasan dalili da yasa suka tsane ni ɗin.
Mufeeda ta ajiye ledar fruits kusa da katifar Hajja Aunty Bahijja ta daka mata mahaukaciyar tsawa cikin hargowa take faɗin "Ke Mufeeda zo maza ki ɗauke mana wannan shegiyar ledar ki fita da ita waje, banda kuturun wulaƙanci a rasa abin kawo wa Hajja sai lemo da ayaba mtsss! Aikin banza kawai.
Ko kallonta ban yi ba domin kulawa ma yabawa ce sai kawai na fiddo wayana daga handbag na buɗe Data, na shiga WhatsApp direct group ɗinmu na family na shiga a dalili tarin messages ɗin da nagani sai na zaci wani abin kirki ne ake tattaunawa, ashe pictures ɗin da aka ɗauka a wajen dinner ne ake turowa duk wani wanda ya ɗauki pic da Ya Haidar idan har ɗan uwa ne kuma yana cikin group ɗin ya turo. Sai ƙara taya shi murna ake yi sai lokaci na fahimci ba wai iya dawowarshi ake taya shi murna ba hadda sabon kamfaninsa na motoci da zai buɗe nan da two weeks. Har zan fita daga group ɗin sai kuma na fasa na shiga buɗe pics ɗin ɗaya bayan ɗaya sai da na buɗe kusan guda bakwai kafin na ci karo da wanda ya ɓakanta min rai ya haddasa min bugawa zuciya gami da sanya ni takaici shine wanda Ya Haidar ya ɗauka tare da Zarah hannuwansu sarƙe da juna, da sauri na kashe data ɗin na maida wayana jakka. Ina shiri tashi sai ga Nusaiba ta shigo niƙe-niƙe da kaya hannuwanta dukka biyu ɗauke da manya-manyan shopping bags har guda huɗu fuskarta shimfiɗe da fara'a, tana shigo wa ta fara faɗin "Aunty Bahijja albishir ki.
   "Goro.
Cewar Aunty Bahijja tana zuba murmushi kafin na ji abinda za ta sake faɗa nai sauri miƙewa tsaye gami da ɗaukar handbag ɗina na ari murmushin dole na yafawa fuskata ka na ce "Hajja ni zan wuce ALLAH ya ƙara afuwa yasa zakkar jiki ce.
"Amin!
Hajja ta amsa mata a takaice daga haka Jeeddah ta juya har ta kai bakin ƙofar ta tsince muryar Aunty Bahijja tana faɗin "Faɗa min Nusaiba haƙƙarmu ta cimma ruwa ko kuwa da saura? Don da gani wannan farin ciki da 'yan uban kaya nan da ki ka shigo dashi tarkon mu ya kama tsuntsuwa.
Kafin na ji irin amsar da Nusaiba za ta bata har na bankaɗa labulle na fice, wani irin mutuwar jiki nake ji shiyasa na kasa wucewa gidana na wuto gidanmu. Tun kafin na iso ƙofar gidanmu na hango wata dalilliyar mota ƙirar Benz a parker nesa da ita kaɗan nai parking, tun a tsakar gida na fara shaƙar ƙamshin turarensa gabana yai mugun faɗuwa har sai da na dafe ƙirjina da hannu, a kasalance na nufo parlour Mama duk takona ɗaya sai na ji gabana ya ƙara faɗuwa sai da na ja iska mai zafi daga bakina kana na fesar ta ƙofufin hancina, a maimakon na ji sauƙi sai naji na ƙara shiga wani yanayi mai wuyar fassarawa da kyar nai sallama gami da yaye labulle.
Mama ta amsa min yayin da Ya Haidar ko ɗagowa bai yi ba balle nasa ran zai amsa min sallama Aiman dake kwance a jikinsa yana game a wayar Ya Haidar ɗin ya taso da gudu ya rungume ni yana faɗin "Mommy oyoyo! Saura kaɗan ya ya jefar dani kasancewar babu ƙarfi kirki a jikina nai sauri dafa hannu kujerar dake kusa dani. A hasale na ture shi gami da kai masa rankwashi "Miye haka Aiman wai kai miyasa kullum ba ka yi abu cikin natsuwa kalle yanda ka tashi kada ni?"
Na faɗa a tsawa ce tuni jikinsa ya ɗauki rawa domin ba ƙaramin razana shi nai ba. Mama ta ɗauki ƙaramin throw pillow kujera dake kusa da ita ta jefa min ranta a ɓace ta ce "Ke dai kin shiga uku da zafin rai duk lokaci da ki ka shigo gidanan sai kin ɓatawa yaro nan rai, ko ki sa shi kuka ina dalili wannan mugun hali kin ɗauki zafin rai kin ɗorawa kanki.
Turo baki nayi ina gunguni ƙasa-ƙasa jikina ne ya bani yana kallona shiyasa nima na maida ganina akanshi, tabbas kuwa rikitattun idanuwanshi da tun fil'azal suke rikita ni su na kafe akaina, sai faman kallona yake ba ko kyaftawa hakan yasa na kasa tantance me kallon nashi yake nufi muryarsa ce ta daki dodon kunnena sai natsuwata ta dawo jikina har nai nasarar jin abinda yake faɗa "Zo nan my boy zo ka ci-gaba da game dinka, da nasan zaluntar ka za ta yi da wallahi ba zan bar ka ka je gunta ba.
Wani mugun kallo na watsa masa kafin na taɓe baki na ingiza ƙeyar Aiman ina faɗin "je ka inda ba za a zalunci ka ba tun da ni kallon azzaluma ake min.
   "Wallahi Jeeddah idan ki ka saka shi kuka sai ranki ya yi mummunan ɓaci.
Mama faɗa cikin hasala.
Ya Haidar ya baro wurin zaman shi ya ɗauki Aiman tare da komawa wajen zamanshi ban san abinda ya raɗa mishi a kunne ba sai naga Aiman yana dariya, na galla musu harara karaf sai akan idon Ya Haidar ya yi min wani kallo mai kama da na wulaƙanci-wulaƙanci, kai na ma wulaƙanci ne domin bai yi kama da na arziki ba, ya wani kauda fuska.
Na zauna akan kujerar dake kusa dani, sai lokaci na gaida Mama ta kwaɗa min harara gami da faɗin "Sai da kika gama sa min yaro kuka sannan za ki gaida ni to riƙe abarki banaso.
    "ALLAH ya ba ki haƙuri Mama.
Na faɗa ina murmushi.
   "Shin ba ki ga Aliyu bane da ba za ki iya gaida shi ba?"
Mama ta watsa min wannan tambaya gami da tsare ni da idanuwanta, cuno baki nayi ina faɗin "Na ganshi mana Mama gaba yake dani shiyasa nima na share shi don banga amfani gaida mutumin dake gaba dani ba.
Na ƙarashe magana tare da murguɗa baki, cikin sauri ya ɗago idanuwanshi ya kalle ni fuskarshi dauke da tsantsa mamaki, kafin ya girgiza kai gami da maida dubanshi ga Mama yana faɗin "Wallahi mama ƙarya take min tun dawowa na bakina bai haɗu da nata ba ko a wajen dinner kowa ya tayani murna dawowa na banda ita.
Na ɗago na banka mishi baƙar harara, kafin na ce "ƙarya yake min Mama ki tambaye Khairat har da gift na bashi tsabar wulaƙanci ko ya nuna min ya gani.
  Daƙuwa Mama tayi min tana faɗin "ungo nan! Kin ci gidanku Jeeddah ka ji min sakarci Aliyu sa'an ki ne da za ki ce yana miki ƙarya wallahi ki kiyayeni dole sai ya nuna miki ya ga kyautar taki.
  "Kyaleta kawai Mama dama mai hali baya bari halinsa, da wannan gift ɗin nata gara babu
Harara na sake galla mishi ji nake kamar na tashi na wanka mishi mari naji dalili da zai sa ya riƙe hannun Zarah har su ɗauki hoto wallahi na kasa daina jin haushi riƙe mata hannu da ya yi.
Mama tashi tare da faɗin "Aliyu bari na kwashe tuwona kada ya ƙone na dawo mu ci-gaba da zance da muke yi kada ka biyewa wannan sokowa za ta haifar maka da ciwon kai da maganganunta na wofi.
Mama ta ƙarashe magana haɗe da ficewa "Kai Mama!
Na faɗa da ƙaramin sauti ina ƙara cuno baki shiru ya biyo baya ba abinda ka ke ji sai bugun zuciyoyin mu sai kuma karar Ac dake parlourn.
    "Mtsss! Wai ke nan har tutiya ki ke da wannan ƙazamin gift ɗin naki?
Kamar daga sama na tsince maganar shi da mugun sauri na ɗago na kalle shi sai nunawa Aiman yanda zai buga game ya ke yi tamkar maganar ba daga bakinsa ta fito ba.
Kalmar ƙazanta da ya kira ba ƙaramin sosa min rai tayi ba duk ɗazu na ji sanda ya ce gara babu da gift ɗin na kyaleshi ne saboda mama ta nan yanzu kuma da bata nan dama ta ce da zan wake masa allon sa, a mugun fusace na ce "Kyautar da na ba ka za ka kira da ƙazanta?" lallai ma Ya Haidar wulaƙancinka ya wuce yanda na zata to ka dawo min da kayana dama can tilas ta min aka yi ba da son raina na ba ka ba.
Ya ciro kanshi da sauri ya kalleta zuciyarsa na mugun harbawa furuncin ta na ƙarashe ya tsaya masa rai ya girgiza kai kana ya runtse idanuwanshi na ɗan wani lokaci kafin ya buɗe su tass! Akan fuskarta sai faman gunguni take yi da ya rasa gane me take faɗi.
Wani iri abu yake ji yana masa yawo a maƙoshinsa da kyar ya iya buɗe bakinsa ya ce "Waye ya tilas ta miki?
     "Aunty Farida da Khairat!
Na faɗa gaba gadi har wani hura hanci nake yi domin na ƙara tabbatar mishi da bashi da wani muhimmanci a gareni. Wani irin kallona yake yi ya kasa ɗauke ganinsa akaina ya sake girgiza kai yana cewa...

_ku yi manage da wannan IN-SHA-ALLAH anjima zan sake wani update_

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now