074

142 10 2
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA
Don ALLAH ku yi following ɗin account ɗina, na wattapad da arewabook
Wattpad:jeedddahaliyu
Arewabook:Jeeddah3256

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

074.

Zarah Malik tana gani sun iso daidai entrance ɗin shiga flat ɗin Jeeddah ta kama hannun Haidar ta haɗe da nata cikin sauri Haidar ya kalli hannunta dake cikin nashi, kafin ya yada ganinsa akan fuskarta tayi kaman bata ga irin kallo da yake mata ba. Da so samu ne ya raba hannunsa da nata saboda yasan halin kishi irin na Jeeddah hakan zai iya taɓa ta shi kuma duk abinda zai kawo masa matsala ko rabuwar kan iyalinsa baya maraba dashi. Idan kuma ya yi hakan sai yake gani tamkar bai yiwa Zarah adalci ba. Domin yadda Jeeddah take matarsa ita ma haka take da wannan matsayi. Har Zarah Malik ta tura ƙofar shiga main parlor Haidar Ka'oje ban saniba domin ya yi nisa a tunani ƙarar buɗe ƙofar ne ya dawo dashi ainihin natsuwarsa. Wani irin bugawa ƙirjinsa ya yi tunawa da ya yi shifa namiji ne kuma faɗuwar gaba asarar namiji, sai kawai ya dake har da su ƙawata fuskarsa da murmushi mai kama da na dole.
*Jeeddah*
Sani nayi koda abinci da na garka wa Ya Haidar da amaryarsa zai ruɓe ba zan taɓa iya taka ƙafana a flat ɗin ta da sunan na kai musu breakfast ina gudu naga abinda zai yi sanadi bugawar zuciyata. Don haka magani bari kar a soma, sai yau naga illar rashin 'yar aiki da ina da mai aiki ita  zan tura ta kai musu kaman daga sama idea ya fado min na kira Ya Haidar ya zo ya karɓa musu hakan yasa na ɗauko wayata na kira shi. Ina kammala waya dashi na fito main parlor na zauna ina buga game a wayana don kawai ya kawar min da damuwa da nake ciki. Sai kawai na ji an turo ƙofa a tunanina Ya Haidar shi kaɗai ne. Ina ɗagowa gami da yada ganina a ƙofar shigowa firstly abinda idanuwana ya fara gani Ya Haidar riƙe da hannu Zarah Malik sun yi wani irin azababben kyau farin fata da farar fata kyakkyawa da kyakkyawa a hali da na tsinci kaina a ciki dukkansu biyu ƙwaƙwalwata ta kasa tantance wayafi kyawo.
Wata kalar shassheka nayi na haɗiye wasu busassu miyau masu shegen ɗaci a maƙoshi. Nai maza na kauda fuskata daga kansu na mayar akan screen ɗin wayata. Yayin da zuciyata sai ta farfasa da luguden aradu take har wani dishi-dishi naga screen ɗin wayar ya yi min. Hakan yasa na runtse idanuwana gam! Ji sallamar su a dodon kunnena yasa ni buɗe idanuna duk da haka ban sake yarda na kalle su ba. Da kyar da shudin goshi na tatraro 'yar gajiriyar natsuwar da tai saura gareni na yafawa kaina. Na amsa musu sallama amma fa za ku ji muryata a dusashe take.
"Ina kwana Jeeddah ke kuma har da wata wahala haka? Gaskiya da kinsani ba ki wahalar da kanki da girka mana breakfast ba watakila daren jiya gajiya da hidima da mutane 'yan biki bai bar ki ki yi bacci kirki ba.
   Duk waɗannan maganganun banza Zarah Malik ce take faɗar su sa'ili da suka zauna akan two seater ga ƙugunta ga na Ya Haidar. Kar ku ga laifina don na kira maganar ta da ta banza saboda duk mai hankali zai gane magana ce ta yada min a dunƙule.
"Sweetie ai na gayamiki my Jeeddah ba lazy bace bata ɗauki shiga kitchen a bakin komai ba.
Na tsikayi muryar Ya Haidar yana faɗa sai lokaci na rarrashe zuciyata ta lamunce min da na ɗago idanuwana na kalle su, shiyasa na ɗago a hankali na yada ganina akansu, wallahi-azim saura kiris numfashina ya ɗauke na rasa gane wani irin masifaffen kishi ne dani da bansan yadda zan ɓoye shi ba. Saboda da kalli fuskata nan take za ka gano hali da nake ciki don kuwa har da ƙwalla ta cicciko min a idanuna kiris nake jira na fashe da kuka, idan kuwa hakan ta faru kashina ya bushe ajina ya zube na yiwa kishiya kuka. Ai kuwa idan Aunty Farida ta ji wannan mummuna labari sai ta lakaɗa min duka Khairat kuma sai ta zazzage ni iya son ranta. Da sauri na miƙe tsaye na kalle su a dake na ce "Karki damu amaryar Ya Haidar don na yiwa muku breakfast ba wani kayan gabas bane ai kin ji mijinki ya faɗa miki ni ba raguwar girki bace, duk duniya ba abinda na fiso da ƙauna irin shiga kitchen don haka karki damu daga yau har izuwa kwanaki bakwai na ɗauki nauyi cika muku cikinku.
  Yatsine fuska Zarah Malik tayi gami da taɓe baki domin tun shigowar ta taga yadda Jeeddah tayi ɗan bala'in kyau cikin Mali kamfalar jikinta ta rena shigar jikinta, duk sai ta ji kishinta ya kamata shiyasa tai amfani da wannan damar da nufi ta yada mata magana sai gashi rashe yana neman ya juye da mujiya.
Danƙarerriyar harara Haidar Ka'oje ya galla wa Jeeddah yana faɗin "Honeypie har dani kin fi so kitchen akaina?
Ya yi magana yana kwaɓe fuska har da wani turo baki.
Sai lokaci Jeeddah ta saki murmushi wanda batasan da zuwansa ba tai wani fari da ido tana faɗin "Ai kai Honeybun soyayyarka ta dabance ko kaɗan ba zan taɓa iya haɗa ta da komai ba. Bari na dauko muku abinci sai zuba mu ke yi mu bar amaryar mu da empty stomach.
Ta ƙarashe magana gami da juya wa da sauri Haidar ya dakatar da ita "Jeeddah ki kai mana a dining room mu haɗu mu dukka mu yi breakfast  ɗin.
Ba tare da Jeeddah ta juya ba ta amsa mishi da "Tohm! Ta juya da sauri ta shiga kitchen zuwa lokaci Zarah Malik ranta ya kai kololowa wajen ɓaci amma da yake ta iya takonta sai kawai ta waske, tamkar bata ji zafin abinda Jeeddah tai mata ba. Cike da kissa ta ce "Sweetie bara na je na taya Jeeddah arranging table kar mu barta ita kadai da aiki.
Da sauri Haidar Ka'oje ya tashi ya kama shoulder ɗin ta ya mayar da ita zaune "A'ah koma ki zauna ba inda za ki je kin manta ke amarya ce tamkar bakuwa ki ke a gidanan idan ma kina so a tayata aiki ba gani ba. Sai na je na tayata ɗin. Amma ke kam ba zan bar ki yi kauda kara ba.
Yadda Haidar Ka'oje yai mata magana ciki wata irin kulawa yai masifar sanya ta farin ciki, har sai da ta saki murmushi cikin shagwaɓaɓbiyar murya ta ce "Ni fa sweetie na warke wuri ya rage zafi sosai da ka barni na tayata.
"Auu! Tun da haka ne bara mu yi breakfast mu koma na ƙara dama ɗan kaɗan ki ka bani.
Haidar ya yi magana yana kashe mata idonshi ɗaya.
Ina shiga kitchen hawaye da nake ɓoyewa suka fara bin kumatuna, na kasa aiwatar da abinda na zo yi sai gani na buge da leiƙa su, duk abinda ya faru akan idanuwana sai dai bana ji abinda suke faɗa. Duk da ban ji abinda suka faɗa ba zuciyata ta ƙawata min musanya kalaman soyayya suke yi. Yadda kuka ke so subuce min da ƙarfi yasa na nufi can ƙarshen kitchen island na ɗurkusa tare da saka tafukan hannayena na toshe bakina, na hana wa sautin kukana fita. Dama nasani dole na fuskanci irin kaloli wulaƙanci nan tun da Ya Haidar yanzu ba sona yake yi ba.
A hankali Zarah Malik ta koma jikin cushion ta lafe Haidar Ka'oje ya laƙanci mata hanci kana ya nufi kofar kitchen tare da faɗin "ina zuwa sweetie.
Zarah Malik ta bishi da kallo tana jin kanta on top ta shiga kissima ba dole Haidar Ka'oje ya rirrita ya dinga rawar ƙafa akanta kana ya nuna mata zallar ƙauna tun da a virgin ya same ta ba kaman Jeeddah dake matsayin cin jemage. Nan take ta ƙara ji kanta yana ƙara yi sama ita kanta tasan har gaba da abada ba za a taɓa haɗa tsoho da sabo ba.
Yana tura ƙofar kitchen ina sauri miƙewa tsaye ƙamshin turarensa da na shaƙa ya tabbatar min da shine ya shigo kitchen ɗin. Ban kalle shi ba na shiga goge fuskata da tafin hannuna da wani kalar sauri mai ɗauke da zallar tashin hankali ya nufi wurinta "subhanalillah! Honeypie me ki ke yiwa kuka?"
Ban bari muka haɗa idanu ba nai sauri ɗaukar ɗaya daga ciki casserole dish da na zuzzuba musu abinci, ina faɗin "Ba komai.
Ban san ya iso kusa dani ba sai ji nayi ya rungumo ni ta baya da sauri na mayar da casserole ɗin. wani irin mugun baƙin ciki haɗe da takaicinsa ne suka mamaye ni, na fizge jikina, na daka mishi tsawa da kakkausar murya "Ka daina taɓa ni da hannu da ka gama lagude wancan ƙarmusasshiya matar taka kada ka shafa min ƙazanta a jiki.
Na ƙarashe magana tare da nufi na raba ta gefen shi na wuce da sauri ya riƙo ƙuguna "Haba Honeypie da kinsan yadda na damu na zo gare ki da ba ki yi min wannan wulaƙanci ba.
A maimakon na ji kalaman sa sun yi min daɗi sai na ji wani shegen haushinsa a fusace na ce
"Dallah matsa ka bani guri duk ƙarni mata ka ke yi kada ka haifar min da tashin zuciya.
"Innalillahi wa'inna illahim raji'um! Jeeddah ƙarni fa ki ka ce? Haba sai kace wani kifi.
"Wallahi ka ma fi kifi ƙarni.
Dolensa ya sake ni na sake daukar casserole ɗin na fita zuwa dining room shi ma ya ɗauka guda biyu ya biyo bayanta.
Ba abinda ka ke ji a dining room ɗin sai ƙarar forks cike da yaga Zarah Malik take ci abinci tana wani ɓaɓɓata fuska duk abinda take yi Jeeddah tana hankalce da ita. Ga kuma wani kalar kallo da take jifar Ya Haidar dashi lokaci zuwa lokaci da naga abin ya yi yiwa zuciyata ba za ta iya jurewa ba na tashi tare da faɗin "Alhamdulillah! Idan kun kammala ina parlor.
Ban jira amsawar su ba na wuce Zarah Malik tai dropping fork ɗin hannunta ta kalli Haidar tana wani kwatar da murya "Sweetie me ke damun matarka ne naga kaman bata ciki walwala?
Ba tare da ya kalleta ba ya ce "maybe gajiya hidimar da ta dinga yi ne bai ƙarasa sakin ta ba.
Ya ƙarashe magana yana murmushi tuni Zarah Malik ta fahimci gaskiya ya faɗa mata ba. Don haka sai ta taɓe baki bata sake magana ba har suka kammala ci abinci ta riga shi tashi ta nufi falo wurin Jeeddah sai da ta ƙara lilwanta fuskarta da murmushi kafin ta ce "Jeeddah abinci ya yi daɗi sannu da ƙoƙari ALLAH ya saka da alkhairi.
"Amin!
Jeeddah ta faɗa a gajarce.
Ta nemi kujerar dake nesa da Jeeddah ta zauna kowacce su sai dannar waya take yi ba wacce ke so kallon 'yar uwarta a haka Haidar Ka'oje ya shigo ya tarar da su sai da ya ƙare musu kallo kafin ya nemi kujerar dake facing ɗin su dukkan ya zauna sai da ya yi gyaran murya kafin ya ce "Don ALLAH ku bani aron hankulanku kaɗan zan yi magana mai muhimmanci.
Hakan yasa kowacce su ta dakatar da dannar waya suka yada ganinsu akan fuskarsa.
  "Jeeddah!
"Na'am!
Na amsa ciki shakakkiyar muryata.
"Zarah.
"Na'am sweetie!
Sai da Jeeddah ta taɓe baki ji suna da Zarah ta kira Haidar dashi.
"Jeeddah ga Zarah, Zarah ga Jeeddah duk nasan kun daɗe da sani juna sai dai babu kyakkyawar alaƙa a tsakanin ku. Jeeddah ga Zarah nan ke ce babba Don ALLAH ku haɗe kawunan ku, ku zauna lafiya ke kuma Zarah ki bi Jeeddah ki bata girmanta a matsayin ta na babba. Babu wacce banaso a cikin ku.  kuma babu wacce ta fi wata a zuciyata dukkan ku ɗaya ne. Zaman lafiyarku shi ne kwanciyar hankalina bana so tashin hankali musamman idan ku ka yi duba da mijin naku lafiya bata wadace shi ba. Na kuma tabbata kowacce ku ba za ta so ta rasa ingarman namiji kamata ba.
Ya ƙarashe magana cikin sigar zolaya.
Dukkan mu ba wacce tai yunkuri tofa albarkacin bakinta kowacce sai cin ranta take yi akan furuncin da ya yi na cewa dukkan mu ɗaya ne a zuciyarsa. Gani shiru ya yi yawa yasa ya sake cewa "Babu mai magana a cikinku?
Kaman haɗin baki muka girgiza kai a tare sai da ya yi murmushi gani yadda a lokaci guda muka girgiza kai kana ya ɗora da cewa "To shike nan tun da baku da ta cewa sai dangane da girki na yanke shawarar kwanaki bibbiyu a tsakanin ku shi ma ya yi muku ko a canza?
Wannan karo ban yi yunkuri yi magana ba sai ita ce ta amsa da cewa "Hakan ya yi ba sai an canza ba.
"A'ah Zarah kada ki yi sauri yanke hukunci ba tare da mun ji ta bakin uwargida ba. Jeeddah ya ya hakan ya yi miki ko a canza?
Ya yi tambaya yana kallona sai da na sauke ajiyar zuciya kafin na ce "Kai ma Honeybun da wani zance ka ke kafi kowa sani banida zaɓi ga dukka komai sama da naka.
Murmushi mai sauti ya yi tare da shafar kwatatce sajensa ya ce "Haka ne Honeypie to shike nan tun da shi ma girki kun amince da kwanaki bibbiyu ɗin.
Zubur Zarah Malik ta miƙe cike da kissa ta ce "Ni zan koma ɓangarena nasan nan ba da jimawa ba zan fara baƙi masu zuwa gani dakin amarya, duk da so nayi na ɗan kwata gaba ɗaya jikina ciwo yake min har yanzu da raguwar gajiyar biki a jikina Jeeddah ga sweetie nan na baki aro ya taya ki hira banaso ya naniƙe min gashi zan dinga yi baƙi.
Ta ƙarashe magana tana dariya yayin da Haidar Ka'oje yake tayata don shi aro da ta ba dashi ba ƙaramin daɗi yai masa ba. Domin yana so ya sami lokaci sosai tare da Jeeddah ya kwatar mata da hankali a dalili ya fahimci kaman da akwai abinda ke damunta.
"Uhm!
Jeeddah ta faɗa zuciyata na ƙara mata tururi da ƙuna Zarah Malik bata tsaya jiran Haidar Ka'oje yai magana ba ta juya ta fice abinta, tabar Jeeddah da jinyar zuciya. Haidar ka'oje yana gani Zarah ta fita ya taso da sauri ya nufo wajena, nima na tashe da saurina "ina faɗin ni fa babu wani girki da zan karɓa gaba ɗaya na yafe mata kai zuciyata ba za ta iya jure wannan tsome-tsome ba za ka fi samun natsuwa a wajen ta ko ba komai ita budurwa ce sabani ni da nake bazawara mai maka fyaɗe. Gara ka dauwama a gun da ba za a dinga yi maka fyaɗe ba.
Na ƙarashe magana muryata tana rawa.
Dariya Ya Haidar ya yi wacce ta karawa fuskarsa mahaukaci kyau ya kama hannuna yana faɗin "jiddalolo matar Haidar da ba ki aure ni ba da kin shiga uku na tabbata soyayyata ce za ta murƙushe ki zuwa kabari. Zo nan shalelena wannan mugun kishin naki na rasa inda za ki je dashi. Ban da rigima ko ina ki ka samu wannan kalma ta tsome-tsome.
Ya ƙarashe magana tare da jawo ni zuwa jikinsa duka na kai wa ƙirjinsa ina faɗin "Da dai ba ka aure ni ba da ka shiga uku don ni ban taɓa cewa ina sonka ba balle sonka ya kaini kabari.
Da wani kalar sauri ya cire ni daga jikinsa yana kallon cikin idanuwana da baki buɗe nai sauri sunne kaina ƙasa sai kuma ya yi murmushi yana faɗin "Lallai ma Jeeddah yanzu har kin manta da kalar rokon da ki ka dinga yi min a waya na dubi girman ALLAH da Manzonsa na zo na aure ki.
Ture shi nayi na nufi ɗakina gami da faɗin "Ai cewa nayi ka aure ni ba cewa nayi ina sonka ba.
Ya bi ta da sauri yana faɗin "To ai shike nan tun da bakysona bari na tattara kayana na koma ɓangare Zarah da zama tun da ita tana sona.
Tun kafin ya kai da haura staircase nai wani kalar kukan kura na cafko gefen rigarsa ina faɗin "Daga kai har ita kun yi kaɗan wallahi ba wanda ya isa ya fita da ko tsike a bangare nan sai dai ka je ka sake ɗinka wasu kaya ka kai ɓangare ta.
Sosai Ya Haidar yake kwasar dariya ni kuma sai faman watsa masa harara nake "Jeeddah rigima ta malam Ali zo mu sassata banaso kalmanan ta tsome-tsome ki rufa min asiri ki janye ta kin ji rabin raina?"
Cuno baki nayi "ka ji dashi da wannan salon yaudarar naka yanzu kana bari ɓangarena za ka je na Zarah Malik ka ce ita ce rabin ranka ku dai maza sam bakwa ji kunyar ƙarya.
Murmushin gefen baki ya yi "Ya Rabbi ka sassauta wa Jeeddah wannan azababben kishi nata ko za ta dawo mutum kamar kowa.
"Uhm! Ashe dama da aljana ka ke zaune to ai shikenan ni yaushe za ka je gida ka dauko min motata inaso jibi na je kitso gidan A'isha Shattima?"
Na faɗa domin na kawo ƙarshen taƙaddama ta mu.
"Tun da kitso za a yi min ko yau zan iya zuwa na ɗauko miki.
"To idan ka je ka zo min da Aiman na sami abokin hira.
Sai da galla min harara kafin ya ce "Banaso na ɗauko miki ɗan mutane ki zo kina gallaza masa nasanki Jeeddah da rashin so yara Dan ALLAH idan kinsan ba za ki iya jure ƙiriniyarsa ba ki barshi wurin Mama.
"Wai ni kam sai yaushe kai da Mama za ku fara yi min shaidar arziki kullum cewa ku ke yi banaso yara, sai ka ce kune ku ka yi min kayan cikinsa sai da fa aka yanka ni kafin Aiman ya zo duniya amma duk da wannan kullum nuna ku ke yi kun fi ni sonshi.
Na ƙarashe magana ina maka masa danƙarerriyar harara.
Dariya Ya Haidar ya yi gami da tafa hannuwa "Kai Jeeddah amma ke kam kin shiga uku ɗa fari ki ke wannan tada jijjiyoyin wuya akansa ALLAH yasa daga ni sai ke ne da ki yi abin kunya wallahi.
Sosai na ji kunya ta lulluɓe ni na juya da sauri na nufi ƙofar shiga ɗakina ina faɗin "koma mene ne kaine ka jawo min saura kuma idan ka je ka ba Mama labari ta sami abu gorata min.
Dariya kawai ya yi ya fice ni kuma na shiga ɗaki na kwanta kafin zuwa anjima na shiga kitchen na ɗura musu lunch.
**************
Bayan an cire wa Aunty Bahijja pop da aka yi mata na kariya da ta samu hannu da ƙafa na hannu ya yi kyau na ƙafar ne ya lalace sai an sake sabon aiki ranar aunty Bahijja tasha kuka kaman ba gobe yanzu duk wannan baƙar wahala da tasha na jinya har tana murna za ta koma gida sai gashi murnar ta ya koma ciki. Ga Hajja dake jinyarta ita ma yanzu ta kanta take yi saboda kullum jininta ƙara hauhawa yake ga kuma ciwon sugarta dake yawan motsa mata gaba ɗaya Hajja ta zabge tayi wata baƙar rama. Dalili haka yasa ta kira ƙanwarta Tsahare daga Yabo ta zo ta dinga kula da aunty Bahijja kasancewar mijin Tsahare ya rasu shekara ɗaya kenan da rasuwarsa.
Yanzu Hajja ta kai stage ɗin da ko tsakar gida bata iya fitowa duk tayi laushi kaman ba Hajja ba wacce bata bari ko ta kwana dama kowanne iya shege sai da lafiya ake yinsa.
Aunty Bahijja ta fara nadama musamman da taga yadda al'amurran ta kullum ƙara taɓarɓarewa suke yi sai kawai ta nemi wani dogon casbi ta koma ga ALLAH.
************
Tun daga ranar da aka kawo Zarah Malik har kawo yau ɗinan da ya rage saura kwana ɗaya tak na karbi girki ni nake basu abinci sau uku a yini, sai dai tun daga ranar farko da Ya Haidar ya zo min da ita flat ɗina na taka mishi birki, tun sannan bata sake zuwa ba. Sai dai idan na kammala na kira shi a waya ya zo ya ɗaukar musu. A ciki waɗannan kwanaki ni kaina naga wasu sauye-sauye a jikina yadda skin ɗina ke glowing tabbas na yarda da ingancin mg's skincare products ni kaina idan na kalle kaina a jikin mirror sai na yabi kaina. A gaggauce na kammala shirina na fito riƙe da handbag da car key sai sauri nake A'isha Shattima sai kirana take yi nayi sauri na zo ga wacce za ta yi min ƙunshi ta zo a main parlor na tarar da Aiman yana buga game a tab ɗinsa "Aiman tashi mu tafi.
Sai da ya kwaɓe fuska kafin ya tashi tun da qna katse mishi game ɗinshi ina zuwa gidan A'isha Shattima babu ɓata lokaci aka yi min lalle na salatif maroon color, ina cire lalle A'isha Shattima ta shiga tsantsara min kitso two step dama shi ne style kitsona da matuƙar wahala nayi kitso ba irinsa ba.
Mu yi fiye da rabin kitso da yake kanana tai min sosai a cewar ta gara na nuna wa Zarah Malik akwai bambanci tsakani tsohon hannu da sabo. Sai hira muke zuba wa muna kyalkyala dariya sai kawai mu ka ji sallama Bilal shattima yana shigowa idanuwanshi suka sauka akan fuskata da sauri na sadda kaina ƙasa. Wani irin kallo Bilal shattima yake bin ta dashi sosai ya ga tayi bala'i sauya masa tayi wani kalar kyau. A'isha Shattima da ta ankara da irin kallo da Bilal yake wa Jeeddah tai sauri taro shi ta hanyar faɗin "Barka da zuwa Ya Bilal yau kaine a gidana, nayi ciwo har na warke ba ka zo duba ni ba.
Bilal Shattima ya yi ajiyar zuciya kafin ya nemi kujerar dake kallon Jeeddah ya zauna gaba ɗaya Jeeddah ta ji ta takura ta ɗauki ɗan ƙwalinta ta ɗaura.
"Ina laifi yau da na sami lokaci na zo duba ki ko bakyso na tashi nai tafiyata.
"A'ah! Yi zaman ka bari na kawo ma ruwa.
A'isha Shattima ta ƙarashe magana tare da ficewa daga parlor ta nufi kitchen.
Sai lokaci Bilal Shattima ya yada ganinsa akan Aiman dake ta faman buga game "Aiman zo mu gaisa mana halan ba ka ga Abba ba?
Aiman ya ciro kanshi ya kalle Bilal ya ce "Ina wuni uncle?"
"Aiman ba na ce ka daina kirana da uncle ba?"
Shiru Aiman ya yi yana kallon shi sai kawai Bilal shattima ya maida ganinsa a kaina ya ce "Jeeddah duk laifinki ne da har yau yaro nan yake kirana da suna uncle.
Sai lokaci nai masa kallo tsaf duk ya zabge ƙaton tumbin sa duk ya tsiyaye kaman wanda ya yi sliming.
"Ina wuni Abban Aiman ya gida dasu Hajja?
Na faɗa a maimakon na bashi amsar maganarsa.
"Lafiya ƙalau Hajja ta nan tana fama yau ciwo gobe lafiya.
"ALLAH ya bata lafiya mai amfani.
"Amin! Ina zaune a kamfani haka kawai na ji zuciyata tana so zuwa gidan A'isha ashe da rabon na gamki shiyasa zuciyata ta azalzale ni ta hanani sukuni sai da na zo.

#Haidar Ka'oje
#Jeeddah maishadda
#Zarah malik
#Bilal shattima
#Team zazzafan kishi



KAƊAN DAGA CIKIN LITTAFIN GIDAN RINA

ABUJA*
*11:24am*

Aliyu ya fito cikin shirinsa na farare kaya as usual, farar shadda gezner ce a jikinsa  tana walkiya da daukar ido takalmin ƙafarshi sawun ciki ne suma farare, yayin da ya lulluɓe kwayar idonsa da farin eyesglass wanda ake iya hango brown eye balls ɗinshi. Jikinshi sai fidda fitinane ƙamshin turarensa yake.
Kai tsaye falon momma ya wuce gani bata cikin falon yasa kansa tsaye ya nufi bedroom ɗiinta, ya tura ƙofa ya shiga tana zaune gefen a gado sanye da cotton night gown, tana waya ganinshi yasa ta katse waya tana wuƙi-wuƙi da idanu kamar marar gaskiya.
    Da murmushi shimfiɗe akan fuskarsa ya zauna kusa da ita ya ɗura kansa akan shoulder ta, cikin shagwaɓa ya ce "momma na fito ki yi min addu'a.
Ya motsa fuska ta yi kafin ta ce "ALLAH ya kiyayye hanya, yasa yarinyar ta dace da ra'ayinka.
   "Kai momma wannan addu'a duk ni kadai?"
"Eh mana yaron momma ko tayi kaɗan ne na ƙara ma da wata?
"A'a....momma ta yi ta farkon dai zan amsa miki da Amin.
Ta biyu ce ba zan amsa ba.
Dad'i ne ya lulluɓe momma ta saki dariya har Aliyu ya fice daga bedroom ɗinta tana dariya.
  Sitting room d'in Daddy ya nufa Daddy na zaune da newspaper  a hannunshi yana dubawa, shigowa Aliyu yasa ya ajiye newspaper d'in ya tattara hankalinshi akan Aliyu.
   "Ina kwana Daddy?"
Cewar Aliyu yana mai runsunawa.
"Lafiya ƙalau Sultan hope wannan shirin na tafiya Yola ne?"
yana magana yana nuna kayan jiki Aliyu da yatsanshi.
"Eh! Daddy sallama na zo nai maka.
"Madallah..... ALLAH ya kai ku lafiya, ka kuma kiyayye banaso a sami matsala daga gareka ka ji ko?"
   "Na ji Daddy In-sha-ALLAHU zan kiyayye.
"Shikenan tashi ka ka tafi ALLAH ya tsare hanya ya kai ku lafiya.
"Amin! Daddy.
Daga haka ya fice direbanshi Isah yana zaune a mota yana jiran fitowarshi, kafin Isah ya buɗe masa ƙofar mota har ya buɗewa p
kanshi, ya zauna a back sit Isah ya ja mota maigadi ya buɗe musu gate, Zone 2 suka wuce suka dauki Jamal sannan suka dauki hanyar Nnamdi Azikwe Airport, ba tare da bata dauki lokaci ba Jirginsu ya ɗaga.

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now