05...

131 8 1
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

05...

Bilal Shattima ɗa ne ga marigayi Alhaji Ibrahim Shattima, ya yi karatunsa tun daga primary har zuwa degree duk anan gari Sakkwato.
Mahaifinsa mai kuɗin gaske ne domin sana'ar canji yake yi matansa na aure biyu Hajiya Bintu ita ce uwargidan mai 'ya'ya shidda duka mata a hali Yanzu biyar daga ciki sun yi aure autarta kawai tai saura sai Hajja mai 'ya'ya haɗu biyu maza biyu mata Faruk shi ne babban yana aiki da hukumar custom har ya kai matsayi controller sai Bahijja ita ma tayi aure har da albarka 'ya'ya biyar.
Bilal ne ke bi mata sai auta A'isha kafin Alhaji Ibrahim Shattima ya rasu ya haɗu da kariyar arziki a dalili 'yan damfara da ya haɗu dasu suka damfare shi kuɗi masu yawan gaske shi ne dalili kamuwarsa da hawan jini sai da ya yi jinya mai tsawo kafin Allah ya karɓi ransa kusan sai da jinya ta cinye ɗa abinda yai saura na daga dukiyarsa abinda ya rage bai taka kara ya karya ba.
Hajiya Bintu mace ce mai mugun kishi bala'i ga ta kyashi da hasada ga dan karen mugun hali ko kaɗan basu zaman lafiya tsakaninta da Hajja, wani irin zama suke yi wanda hakan ya shafi 'ya'yansu sosai suke nunawa junansu ƙiyayya tamkar ba uba ɗaya ne ya haife su ba. Tun kafin Alhaji Ibrahim Shattima ya rasu yaso matuƙa ya haɗa kan iyalisa sai dai hakan bai samu ba a dalili kowacce su tana da nata ɓakin hali.
Bayan rasuwarsa Allah ya daukaka Faruk ya yi kuɗin gaske sabon kishi da hasada Hajiya Bintu ya dawo sabo dal gani haka ta fantsama malaman tsibo da bokaye har tai nasarar raba tsakaninsa da mahaifiyarsa.
  Abincin da Hajja za su ci gagararsu yake yi akan idanuwanta zai aiko driving shi ya kawowa Hajiya Bintu kayan abinci haɗe da maƙudan kuɗi, ita da ta haifeshi ko kwara gero bai iya haɗa ta dashi hatta da karatun Bilal ita kaɗai ta dinga faɗi tashi har ya sami kwalin degree a fanni accounting, kasancewar lokaci da aka raba masu ɗan gado da yai saura daga dukiyar da Alhaji Ibrahim Shattima ya bari duk da ba wata abar a zo agani bace amma da yake Hajja tana da tanadi sosai ba ta saka nata da na yaranta gaba ta cinye ba sai tai dabarar siyen dabbobi shanu, tumaki da awakai ta kai ƙauyensu Yabour ƙaninta yana mata kiwo cikin amincewar Ubangiji yasa mata albarka a ciki.
Dasu ta dinga biyawa Bilal kuɗin makaranta har ya kammala degree successfully, yai bautar ƙasa a Anambara State a lokaci Bilal bashida buri da ya wuce ya kammala karatu ya sami aiki ya tallafawa mahaifiyarsa da Aunty Bahijja kasancewar ita ma cikin wahala take a dalilin lalura rashin lafiya da mijinta ya kamu dashi ya daina fita ko nan da ƙofar gida don ko magana ba kasafai yake yi ba. Tamkar mai taɓi hankali ko shafar jinnu Gashi matansa biyu Bahijja ita ce uwargidan mai 'ya'ya biyar amarya kuma huɗu sai rayuwarsu ta dawo kowa tasa ta fishe sa kai za ka nemo abinda za ka ciyar da kanka da 'ya'yanka har ma da mijin nasu duk yadda Hajja ta haɗa 'yan kuɗi ta ba Bahijja taja jari 'yar sana'ar cikin gida ciyarwa baya bari jari yai kauri saboda duk wani responsibilities na yara yana kanta, duk da makarantar Gwamnati yaranta ke karatu amma a cikin wahala take matuƙa.
  Shiyasa Bilal yaci buri samun aiki mai kyau da nagarta domin tallafa musu, duk lokaci da ya zauna yana kwantar wa Hajja da Aunty Bahijja hankali ta hanyar faɗin zarrar ya kammala karatu ya sami aiki wahalar su ta zo ƙarshe. Ranar da wannan furucin nasa ya faɗa kunnen Hajiya Bintu tai kwafa haɗe da furta saidai in bata raye, Bilal zai sami aiki daga lokaci tasa aka yi masa asiri da ya rasa mai ɗaukarsa aiki ya sha yin interview ba adadi amma daga karshe idan list ɗin wanda aka ɗauka aiki sai ya ga babu sunansa, duk da haka Hajiya Bintu bata barshi a haka ba sai da tasa bokan nata ya kashe masa zuciyar nema, balle ya nemi aikin ƙarfi tunda na Gwamnati ya kasa samuwa, komai  Hajja ce ke masa.
Ita ce ci da shansa hatta da sutura sai in ta bashi kuɗi yake iya ɗinkawa kansa, ko kuma Jeeddah ya ɗinka masa gaba ɗaya wahala ta taru tai wa Hajja yawa ga Faruk yana da shi amma bai iyawa taimaka musu da ko kwandala har ta kawo ko gida ya zo saidai ya tsaya iya sashen Hajiya Bintu kwata-kwata ya manta a rayuwarsa da yana da mata sauƙinsu ɗaya matarsa tana da kirki kuma tana ƙoƙarin taimaka masu lokaci da Hajiya Bintu ta gano saida ta nemo hanyar da ta bi ta dakile hakan. Gaba ɗaya an wanke wa Faruk tunani a cire masa mahaifiyarsa da 'yan uwansa a zuciya. Shigowar Jeeddah rayuwar Bilal ya kawo wa Hajja sauƙi wasu wahaloli, Domin kusan rabi salary ta wuri hidimarsa yake ƙarewa.
    *WANE NE HAIDAR?*
Asalin sunansa Aliyu Abubakar Ka'oje su shidda cif iyayensu suka haifa kuma dukkansu maza ne.
Mahaifinsa Alhaji Abubakar Ka'oje haifaffen garin Kebbi ne a cikin karamar Bagudo cikin garin Ka'oje, duk wanda yasan gari Ka'oje yasan Fulani ne farare masu masifar kyau, shiyasa Aliyu yake da tsananin kyawon domin ko mahaifiyarsa Hajiya Turai ba baya ba tana da matuƙar kyau gata fara sol shiyasa ma ake mata laƙabi da Turai kasancewar mahaifiyarsu buzuwa ce mahaifinsu shi ne haifaffen garin Sakkwato, kun ga kenan Aliyu Haidar gadon kyau ya yi gaba da bayansa.
Alhaji Abubakar Ka'oje Cikkaken ɗan boko ne ya riƙa manyan mukamai da dama a ƙasar mu ta Najeriya, kafin yai Retirement ya tsunduma kasuwanci man fetur da gina gidaje da manyan malls yana sayarwa, yana da manya kamfanonin da ke harka gine-gine, jahohi da dama a takaice dai babban ɗan kwangilar gina gidaje ne da shimfiɗa manya tituna da kwalbatoti a Najeriya. kuma yana cikin jerin gwano manyan masu kuɗi da suka yi sura a Najeriya ya yi fice sosai musamman yanzu da ya tsunduma harka siyasa gadan-gadan.
Haidar yana fama da matsalar ciwon zuciya wanda dashi aka haife shi, saboda ciwo da yake ɗauke dashi yasa mahaifanshi da 'yan uwanshi suke tausaya masa haɗi da ririta shi,  suna kan-kanfafa dashi shiyasa ya tashi a sangarce domin ciwo nasa baya buƙatar a ɓata masa rai sai abinda yake so ake masa ko kaɗan basa so ɓacin ransa, sakamakon wannan gata da suke nuna masa ya haifar masa da rashin juriya abu kaɗan ya isa ya saka shi kuka ƙiri-ƙiri ya dawo mai raguwar zuciya. Ko kaɗan bashi da juriya kamar ba namiji ba.
Ko wata mace ta fi shi juriya shiyasa da zarrar Jeeddah ta ɓata mishi rai sai ya saka ta a gaba yai ta kuka, har ciwonsa ya tashi shiyasa kullum yana gadon asibiti don kuwa ko da yaushe cikin ci masa mutunci take. Musanman da ta fahimci ciwonsa na tashi.
   Mustapha Abubakar Ka'oje shine babban ya yi aure har da 'ya'ya uku kasancewar matarsa tana ɗaukar dogon lokaci kafin ta haihu, yana zaune a Abuja shi ke kula da branch company ɗinsu da ke nan Abuja.
  Sai mai bi masa Suraj Abubakar Ka'oje shima ya yi aure matansa biyu yaransa shidda uwargidan ita ce mai yara huɗu amarya kuma biyu, shi kuma yana Kano shi ke kula da kamfanin su na Kano. Sai Abdulwahab Abubakar Ka'oje da ke zaune a Lagos da matarsa ɗaya da 'ya'yansa biyu, Sai kuma Sageer Abubakar Ka'oje shima matarsa ɗaya saidai bata taɓa haihuwa ba shi kuma yana Kebbi shi ke handle ɗin branch ɗinsu na Kebbi. Hisham Abubakar Ka'oje kuma shi ke riƙe da da na Kaduna shima bai daɗe da yin aure ba, don matarsa yanzu ma take ɗauke da cikinta na fari, Sai auta Aliyu Haidar Ka'oje da ke riƙe da kamfanin su na nan Sakkwato.
Aliyu Haidar ya yi karatunsa na primary school anan Sokoto ya yi secondary a Abuja a gidan Mustapha ya zauna har ya kammala karatunsa, kana ya wuce Emily Carr university of Art&Design Canada ya yi degree sa a fanni Zane. Aliyu tun yana yaro Allah yai masa baiwar zane-zane babu abinda bai iya zanawa duk abinda ya kalla sau ɗaya tak nan take zai zana sa ya fito rangaɗaɗau shiyasa yai karatunsa a wannan fanni yanzu haka duk wani gida da za a su gina ko malls shi ya ke fitar da zane, kuma a gefe ɗaya yana aikinsa personal yana aiki da wani Company ƙera motoci dake Canada yana musu zane, su na biyansa maƙudan kuɗi.
A takaice dai Aliyu artistic genius ne, don ba abinda baya iya zanawa, kwararre ne a wannan fannin.
Duk duniya bashida damuwa ko matsala face ta Jeeddah yana mata mahaukacin so yayin da ita kuma take masa mahaukaciyar zazzafar ƙiyayya.
*BACK TO STORY*
Har ya shigo ɗakin ya zauna kusa da ita bata sani ba a dalili tayi zurfi a nazarin tuno da rayuwarta ta baya. A hankali ya ɗora lallausan tafin hannunsa akan gadon bayanta ya shiga yi mata tafiyar tsutsa, ta zubara da sauri ta miƙe zaune sai yawo take yi da idanuwanta akan fuskarshi tamkar wacce taga abin tsoro, kafin ta ja tsaki "mtsss...!
Ta dauki ɗan kwalinta da zimmar rufe sabon kitsonta two step mai zigza da ya sauko akan kafaɗunta, ba ƙaramin kyau kitso ya yi masa ba shiyasa yai saurin fizge ɗan kwali ya duƙulƙule shi cikin hannunsa na hagu, a mugun fusace ta kalleshi da masifaffun idanuwanta wanda babu komai cikinsu baya ga tsana da haunshinsa kana tai kwafa tare da kawar da kanta gefe, tana wani cin magani.
Duk da kallo da take masa bai hana masa ɗora hannunsa na dama akan kitson kanta yana shafawa cikin shauƙi, wannan karon ma a fusace ta kai ma hannunsa bugu, kana ta ture shi sannan ta shiga zazzaga masa masifa tana faɗin "wai kai wane irin mugun mayye ne marar zuciya, da baisan ciwon kansa ba sau nawa zan gayamaka ka daina raɓar inda nake ka fita sabgata nace bana sonka ko ana dole ne?"
   A hankali ya shiga furta "innalillahi wa'inna illahim raji'un! Ya dafe saitin da zuciyarsa take wani irin bugawa tamkar za ta faso ƙirjinsa ta faɗo.
   Ko kaɗan bata ji tausayinsa ba sai ma kafiri tsaki da ta ja tace "Ba ciwon zuciya ba Allah yasa ciwon rai ke damunka ba abinda ya shafe ni matuƙar ba ka daina raɓar inda nake ba, na dinga kartama rashin mutunci kenan, gara ka yi wa kanka faɗa ko ka tsira da 'yar lafiya da tai saura gareka.
    Shiru Haidar ya yi still hannunshi na dafe da zuciyarsa, ya sassauta muryarsa ya ce "Miyasa kika tsaneni Jeeddah miyasa kika juyar da soyayyar da kike min ta koma zallar ƙiyayya me nayi miki, na roƙe ki a wannan karo ki ɗaure ki faɗa min laifi da nai miki da na cancanci irin wannan muguwar tsanar daga gareki domin haka kawai ba za ki tsaneni ba dole da akwai ɓoyayyen dalili da ke kaɗai kika san shi?"
Nai wani ɗage girar ido ina kallon sa a fakaice nace "sonka dai ne bana yi ko ada can da nace ina sonka soyayyar ƙurciya ce da rashin sani me so yake nufi a yanzu kuma da na gama mallakar hankali kaina sai na gano ni da kai sam bamu dace ba saboda haka ni da kai babu kare bi damo, ka je can ka nemi mai sonka.
   Murmushi yaƙe ya yi yana jujjuya kansa a kuma lokaci guda zazzafan hawaye na bin kumatunsa kai wallahi soyayya masifa ce. Har sai yaushe zai daina ɗanɗanar ɗaci da ke cikinta?"

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now