042

84 14 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

042..

"Ke yanzu Farida har kin ga abin dariya anan wuri ina kallo yarinya ta koma mahaukaciyar ƙarfi da yaji?"
   Sai da Farida ta tsagaita da dariya kafin ta ce "ALLAH Mama furucinta dariya ya bani.
"Mtsssss!
Mama ta ja guntun tsaki gami da shigewa bathroom Aunty Farida kuma ta ci-gaba da dariyarta yayin da Jeeddah ke ci-gaba da rera kuka.
Bayan sallar isha'i sai ga Baba ya zo asibiti ya duba ta anan yake ji labari abinda ya faru, zaunawa ya yi ya dinga yi mata nasiha duk abinda Baba yake faɗa jin sa kawai take yi don ba lallai bane tai amfani da nasiharsa ba.
Washegari da safe sai ga Bilal Shattima ya sake zuwa duk da kashedi da Aunty Farida tai masa gani ya yi ba zai iya haƙuri rashin sani hali da matarsa take ciki ba. Shiyasa ya kamo hanya ya zo asibitin. Kamar dai yadda tai masa jiya yau ma haka tai masa zan ma iya cewa na yau yafi muni domin sheƙe masa kwalar riga tayi, tana faɗin sai ya sake ta. Gaba ɗaya ta yakushe masa wuya, hargagin ta ya janyo hankalin Mama dake bathroom, ta fito da gudu tana zuwa ta shiga ɓamɓare hannuwan Jeeddah daga jikin wuyan Bilal da kyar Mama tai nasarar raba hannuwanta ga wuyan Bilal Shattima zuwa lokaci Mama ta harzuƙa matuƙa sai kawai ta kashe ta da ɗan bala'in mari wanda ya dawo mata da ainihin natsuwarta. Gani yanda Mama take ta zuba mata faɗa ita kuma sai kuka take yi yasa Bilal ya fice daga ɗakin ranshi a jagule.
Sosai Mama ta dinga ɓalɓale Jeeddah da faɗa ita kuma sai kuka take yi yanzu ba wanda ta ƙula alaƙa mai kyau dashi irin kuka, sai da yamma Mama ta kira Mommy Turai ta sanar mata da abinda ke faruwa, ta ɓangaren Mommy kuwa tana zaune ne a parlournta tana gama waya da Mama ta tashi da sauri ta shiga bedroom ta ɗauko mayafi da handbag ɗinta sai da ta fito compound ta tuna da direbanta ya tafi gani gida, da sauri ta juya ta nufi apartment ɗin Haidar Ka'oje a parlour shi ta tadda shi ya saka laptop a gaba yana fitar da wani zane mota yanda Mommy ta tura ƙofa da yanayi da ta shigo dashi yasa shi ture laptop gefe ɗaya yana tambayarta "Mommy Lafiya dai?"
Sai da Mommy ta zauna akan hannu kujerar da Haidar yake zaune akai kafin ta ce "Ina fa Lafiya Aliyu yanzu nan na gama waya da Hajiya Fatee tun jiya Jeeddah tana asibiti.
     Taɓe baki ya yi kafin ya kalli mommy ya ce "Subhanalillah! Wacce Jeeddah?"
Harara Mommy ta galla masa gami da faɗin "Banaso tambayar wofi Aliyu duk faɗin garin Sakkwato wacce Jeeddah nake da ita?"
   Ɗan guntun murmushi ya yi tare da faɗin "ALLAH ya ba ki haƙuri Mommy ita kuma ALLAH ya bata lafiya. Halan haihuwa ce?"
  "Mtsssss! Wacce irin haihuwa kuma Aliyu ana haihuwa ne babu ciki ko ka ganta ɗauke da ciki ne?"
   "Taya zan san tana da ciki ko bata dashi Mommy tun da ba wani abu da yake haɗa ni da ita ba.
   "Saboda har yanzu kana fushi da ita ko?"
   "Haba Mommy fushi me? Ni fa tuni na daɗe da goge shafinta a rayuwata ke ma shaida ce akan hakan.
   "Huhmm! To naji tashi ka shirya ka kaini asibiti kasan jiya Audu direba ya yi tafiya.
Ɓata fuska ya yi mommy ta ce "Ko ba za ka je bane naga sai ya motsa fuska ka ke yi?"
   "Ni na isa nace ba zan je ba kawai dai ina kan wani aiki ne mai matuƙar muhimmanci zuwa dare nake so na kammala shi shiyasa throughout ban fita ba.
  "Duk muhimmancin sa na tabbata bai kai lafiyar 'yar uwarka ba, saboda haka jingine sa za ka yi ka tashi mu tafi.
  Bai ce komai ba ya miƙe ya shiga bedroom ɗinshi ya canza kayan jikinshi zuwa ash colour shadda bai sanya hula ba gashin kansa a gyare yake tsaf sai kyali yake gwani sha'awa, yana riƙe da key ɗin mota ya fito parlour take ƙamshin turarensa ya gauraye parlour Mommy ta ɗago ta kalleshi da murmushi akan fuskarta ta ce "Ko kai fa.
  Yai gaba tare da yin gunguni ƙasa-ƙasa ta yanda mommy ba za ta ji abinda yake faɗa ba. Kafin Mommy ta ƙaraso parking lot ya jawo mota ya iso wajenta da sauri ya fito ya buɗe mata backseat ta shiga ya maida ƙofa ya rufe maigadi ya buɗe musu gate sai da suka ɗauki hanya mommy ta ce "Ban taɓa gani ɗan banza yaro butulu irin mummunan miji nan na Jeeddah ba, in banda butulci iri na ɗa namiji yaushe Bilal ya yi arziki da zai ƙaro aure. Don yana munafuki ya je ya ɗaura auren sa a ɓoye. Kuma wani abin takaici bai faɗawa Jeeddah ba  sai da taji a bakin shanu talla, kai ALLAH ya wadaran namiji mai hali iri na Bilal.
   Da sauri Haidar ya furta "mijin Jeeddah ya ƙara aure which means an yi mata kishiya unbelievable Mommy taya haka ta kasance,?"
Ya ƙarashe magana ɗauke ɗimbin Mamaki shimfiɗe akan fuskar sa.
   "Uhmm! Bari kawai Aliyu butulci ne irin na Bilal ɗan banza yaro mummunan tsiya.
Mommy ta ci-gaba da kwashe wa Bilal Shattima albarka yayin da Haidar Ka'oje ya lula a duniyar tunani.
Akwai wata rana da Jeeddah ta zo gidansu zai maida ta gida suna kan hanya idanuwanshi suka sauka akan zoben hannunta wanda shi ne ya bata, yanda zoben ya yi matuƙar kyau ga yatsanta yasa shi kamo hannunta ya matse cikin nashi yana murza zoben a hankali ƙoƙari fizge hannunta ta shiga yi gani haka yasa ya sumbace yatsunta kafin ya saki hannun nata ya kalleta da murmushi akan fuskarshi yana faɗin "A duk lokaci da na kalle zobe nan na yatsanki Jeeddah sai na tuna da girman alƙawari da nai miki wanda daga ni sai mahalicci na muka san dashi, a koda yaushe addu'a ta ALLAH ya bani ikon riƙe wannan alƙawari.
  Runtse idanunta tayi cike da takaici ta sake buɗe su akan fuskarshi tsananin takaicinsa ya lulluɓeta, cikin fusata ta ce "Duk wani alƙawari da za ka ɗaukar min a gareni na banza ne Ya Haidar domin ka kasa ɗaukar min alƙawari da idan mun yi aure ba za ka yi min kishiya ba. Shiyasa har gobe na kasa alfahari da soyayyarka na wofitar da ita kana kuma na karɓi Bilal Shattima da hannu bibbiyu domin shi ne mutumin da yai min wannan alƙawari da kai ka kasa yi min. Saboda haka ka manta da wani alƙawarinka akaina domin ni ba zan taɓa aurenka ba. Na sha faɗa maka ba zan iya aure kyakkyawan namiji ba baya cikin tsarina dama za ka yi min alƙawari ba za ka yi min kishiya ba da na ɗaure na aure ka ko don wannan mugun naci naka amma ina ka kasa yi min yanda nake so kai ma ba za ka sami yanda ka ke so ba, don haka ba zan aura ba ka je can ka nemi matarka ni dai na gama zaɓina Bilal Shattima shi ne namiji da ya dace dani.
   A lokaci ba ƙaramin zafin maganganunta ya ji ba amma kuma sai yai ƙoƙarin danne wa ta hanyar cewa "Karki ce haka Jeeddah ina da yaƙini koda ALLAH ya ƙaddare ni da aure mace fiye da ɗaya ba abinda zai canza soyayyar da nake miki domin ƙaunarki daban take a cikin jinina. Kuma Inaso ki sani da kyakkyawa da mummuna duk ALLAH ne ya halicci su. Kada kishi ya rufe miki ido ki zama jahila al'hali kina da iliminki, namiji da kike gani duk muninsa ba zai rasa wacce za ta so shi ba.
  "Whatever!
Ta faɗa tare da taɓe baki ya girgiza kai gami da cewa "Shi kanshi Bilal ɗin wanne tabbaci kike dashi akanshi da ba zai miki kishiya ba?
   "Ya Haidar Please mu bar wannan magana na fahimci koda za mu kwana anan ba za ka taɓa fahimta ta ba. Amma inaso ka sani na fidda hakkin ka ba zan aure ka ba Bilal Shattima shi nakeso kuma shi zan aura.
   Runtse idanuwa ya yi tunawa kaɗai da ya yi da maganganunta sai da yaji wani abu mai kama da mashi ya soke ƙahon zuciyarsa, hakan yasa ya manta da driving yake yi kuma yana tafiya ne akan babban titi muryar mommy da ya tsinkaya tana salati yasa shi dawowa cikin natsuwarshi ashe ya saki hannunshi saura kiriss ya buge motar da ke gefensa.
   "Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Aliyu kanka ɗaya kuwa tunani me ka ke yi da zai ɗauke maka hankali har ka manta da tuƙi ka ke yi?"
  Ajiyar zuciya ya sauke gami da saukar da glass din mota ya leƙar da kanshi ya ba wa mai motar da yai kusa bugu haƙuri kana ya maida glass ɗin.
  "Wai Aliyu ba magana nake da kai ba za ka faɗa min abinda ke damunka ko kuwa sai na fusata?"
Mommy ta faɗa a tsawa ce.
   Sai da Haidar ya sake sauke numfashi kafin cikin sanyi murya ya ce "Ki yi haƙuri Mommy domin ni kaina basan takamaiman abinda ke damuna ba.
   "ALLAH ya kyauta amma ka dinga kula sosai domin wannan kasada ce da sai da rai kana tuƙi kana tunani.
   "in-sha-Allah zan kiyaye.
Daga haka suka iso asibiti gun da aka tanada domin parking motoci ya nufa ya yi parking kana ya fito Ya buɗe wa Mommy ƙofa ta fito karɓa handbag ɗinta ya yi ya riƙe mata, suka jero zuwa cikin reception duk wanda ya kalle su sai sun burge shi duk da kasantuwar su na uwa da ɗa ba sai an faɗa maka ba kasan akwai shaƙuwa mai tsanani a tsakaninsu. A ƙofar shiga ɗakin da Jeeddah take suka tarar da Mama da Aunty Farida zaune akan farare kujeru rubber, bayan gaisuwa da ta shiga tsakaninsu kana mommy ta tambaye jikin Jeeddah Mama ta ce "jiki da sauƙi za a ce amma yanzu nan ba daɗewa ba likita ya gama gwada Bp ɗinta ya tabbatar mana jininta ya hau sosai idan har bata cire damuwar da ta ɗorawa kanta ba, da wuya bai zama mata hawan jini ba.
   "Subhanalillah! Kai ALLAH ya wadaran Bilal sam bai yi wa Jeeddah hallaci ba.
   Mommy tayi magana cike da takaici.
   "Ni fa banga laifi Bilal ba hakan ma da ya yi ya min dai-dai ba taƙamar take yi yai mata alƙawari ba zai mata kishiya ba, kin ga yanzu dole ta rage wa kanta wannan zazzafan kishin nata.
   Haidar Ka'oje ya yi magana yana taɓe baki.
A masifance Mommy ta ce "Kar na sake jin bakinka a cikin zance nan Aliyu dama ku maza duk halinku ɗaya.
  Dariya Mama da Aunty Farida suka sa gani yanda mommy ta hayyaƙo wa Haidar. Cikin dariya Mama take faɗin
  "Yi shiru abinka Aliyu kada a sauke haushi  akanka kishiya dai ce da 'yarta bata so an kuma ri ga da an yi mata ita.
   "Daɗi abin kishiya ba a kanta farau ba kuma kanta ƙarau ba.
Mommy ta faɗa gami da nufar ƙofar shiga ɗakin gaba ɗayansu suka biyo bayanta yayin da Mama take faɗin "Ko dai ba a kanta farau ba an dai yi muku zuwan bazata  kuma ba yanda za ku yi gara tun wuri ku sawa zuciyarku salama.
  Mommy ba ta sami damar bata amsa ba a dalili ta iso cikin ɗakin ta hango Jeeddah kwance ta ba wa ƙofa baya da sassarfa mommy ta nufe ta "Sannu Jeeddah!
Mommy ta faɗa gami da shafa kitso kan Jeeddah jin muryar mommy Turai da nayi yasa ni tashi zubur na fashe mata da kuka ina faɗin "Mommy Dan ALLAH ki taimake ni ki sa Bilal ya sake ni wallahi ba zan iya ci-gaba da zama dashi ba tun da ya zama munafiki mai ƙarya alƙawari.
  Kafin Mommy tai magana Ya Haidar ya daka min gigitatciyar tsawa wacce sai da hanjin cikina ya kaɗa "Ke dallah yiwa mutane shiru! In banda sakarci saboda auren wata za ki kashe naki a dalili wannan banzar kishi naki yasa mijin naki yai aurensa ba tare da ya faɗa miki ba. Alƙawari da kike cewa ya ƙarya dama na banza ne ya ɗaukar miki iya na fatar bakinsa ne.
   Ya ƙarashe magana yana min wani mugun kallo ji nai ba zan iya jure kallo da yake min ba nai sauri sadda kaina ƙasa yayin da na shiga rera kuka ƙasa-ƙasa. Ina jin lokaci da mommy ta rufe shi da faɗa yayin da Mama da Aunty Farida suke goyon bayansa. Kyale su mommy tayi ta dawo kaina ta zauna kusa dani gami da sanya ni cikin jikinta tana bubbuga bayana, kana ta shiga gayamin maganganu na kwantar da hankali da haifar da natsuwa tsawon lokaci ta share kafin ta samu ta ciyo kaina na daina kuka na dawo ajiyar zuciya. Ina ji Mama tana ba wa Ya Haidar labari haukar da na dinga yi sosai naji zafi labari da Mama ta bashi domin kuwa girke min dariya ya yi zan iya cewa tsawon zamana dashi ban taɓa gani ya yi dariya irin wannan ba. Wato ya yi farin ciki da kishiya da aka yi min ban ƙara tabbatar da hakan ba sai da na saci kallonshi da zarar mun haɗa ido sai ya saki min wani arne murmushi wanda ke nuni da yana cikin zallar farin ciki. Hakan kuwa ba ƙaramin ƙona min rai ya yi ba fushina yaƙara ɗaɗuwa har na kagara ya tafi, sai da aka yi kira sallar magariba sannan ya fita inda ALLAH ya taimake ni sanda ya dawo daukar mommy bai shigo ɗakin ba a waya ya kira ta.
Kwana na biyar a asibiti Sa'annan aka yi discharge ɗina, kuma har aka sallame ni ba wanda na ya zo duba ni daga gidansu Bilal idan aka cire A'isha Shattima domin ita kusan kullum da yamma sai ta zo kuma sai dare take tafiya.
Lokaci da aka sallame ni banso na koma gidana ba a cewa ta na gama zaman aure da Bilal Shattima amma Baba yana ji wannan furuncin nawa saura kiriss ya lakkaɗa min duka faɗa kuma ba kalar wanda bai min ba daga ƙarshe da kanshi ya dawo dani ɗakina, a cikin kwanaki biyar duk na bi na rame na fita hayyacina.
   Bayan sallar isha'i Bilal Shattima ya dawo gida a lokaci na shiga wanka koda na fito ɗaure da towel yana zaune a gefen gado tallaɓe da kumatunsa, kallo guda nai masa na ja guntun tsaki a duk lokaci da idanuwana suka sauka akan fuskar shi sai naji kamar na shaƙe masa wuya har sai ya daina motsi. Ya bi ta da kallo yanda yaga tayi baƙar rama ba ƙaramin tausayinta ya darsu a zuciyarshi ba, ya tabbata shi ne silar wannan ramar ta ta. Shi kansa yasan bai kyauta mata ba tun da yasan duk duniya ba abinda ta tsana irin kishiya kuma ya yi mata.
  A dare ranar parlour na kwana duk yanda ya kai da son rarrashina ya kasa domin kuwa dawowa masa nayi tamkar wata 'yar kwaya sai zafafan maganganu nake ta gaggaya masa. Tun daga ranar da na dawo ban sake kwana ɗaki ɗaya dashi ba, abinci ma na daina girkawa sai yunwa ta ci ni sosai nake iya haɗa ruwan tea nasha ko kuma nasha farau-farau fura, shiyasa na kara lalace fiye da tunani mai karatu ba ma zan iya misalta muku yanda na dawo ba. Hatta da office na daina zuwa ko wanka nayi iyakacina na nemi riga na saka I can't even remember when last da na shafa mai balle aje da zance kwalliya, yau ma Kamar kullum ina zaune a parlour abin duniya ya taro ya min yawa sai ga Aunty Farida ta zo direbanta ya dinga shigowa da boxes kusan set biyu amma different colors the same design, bayan ta zauna ko gaisawa ban bari mu yi ba nace da ita "Aunty Farida waɗanan akwatuna na menene?"

*Ku yi haƙuri kwana biyu kun daina ji na kusan jiki da jini*

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now