033

83 12 1
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

033...

Har muka iso gida kuka nake yi tsawon rayuwata ban taɓa kuka irin na wannan ranar ba. Nayi kuka har idanuwana sai da suka fara yaji-yaji gashi sun kumbure sun yi luhu-luhu muna shiga gida na shige ɗakinmu nasa na datse ƙofa da sakata, banaso kunnuwana su ci-gaba da ji min abinda zai ƙara linka min ɓaci ran da nake ciki. Na kwanta akan gado tare da yi rub da ciki na tsunduma tunani makomar rayuwar aurena, nasan inaso mijina amma wannan halayyar ta beraye da ya ɗauko sai na ji duk zazzafar ƙauna da nake masa ta fara dusashewa a zuciyata.
A police station kuma Bilal Shattima bai wahala da 'yan sanda ba kai tsaye ya amsa laifinshi aka ɗauki statement, ya tabbatarwa da 'yan sanda ya sayar da gwal ɗin akan kuɗi Naira dubu ɗari takwas lokaci da Ya Kabeer ya ji adadin kuɗi da ya saida gwal ɗin ji ya yi kamar ya kife shi da mugun mari sarƙa Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari ita ce ya siyar akan dubu ɗari takwas, idan ba a ci riba ba bai kamata a faɗi ba, musanman yanzu da kullum grand ɗin gwal ƙara hauhawa yake yi.
Ya Kabeer ya kalle Bilal ya ce "Kai dai ayi mugu na ƙarshe lissafi na tabbata a jikin receipt ɗin sarƙar ka ga ko nawa aka siye ta saboda ba guminka bane shine ka siyar da ita a wulaƙance to wallahi bari ka ji duk ubanda yai maka tsaye a faɗin gari nan sai ka biya gwal ɗinan ko ka tafi gidan yari akansa.
Shiru Bilal ya yi sai wuƙi-wuƙi yake da idanuwana wani constable ya karɓe zance yana faɗin "Kai dai ka ji kunya wallahi ka yi asara banda mutuwar zuciya ka rasa inda za ka yi sata sai a ɗakin matarka, mummunan banza mai ƙaton hanci da gani mummunan fuskar nan taka ba gwal ba ko mutum ɗan adam za ka iya sata iri-irinka ne idan ba a farga ba ku ke zama mugaye 'yan ta'adda, ku addabe jama'a.
  "Yallaɓai ba sata nayi ba ara nayi in-sha-Allahu nan ba daɗewa ba zan dawo mata da abarta watakila ma wacce ta fi ta ta da na ɗauka.
Bilal Shattima ya faɗa cikin tausassa lafazi.
A fusace inspector da ke on duty ya daka masa tsawa domin tun shigowar da aka yi da Bilal a station ɗin ya ji laifi da ya aikata ya ke ji mugun haushinsa.
"Kai dallah! rufe mana baki tsohon ɗan iska masu ja mana zagi a wurin mata, a dalili iri-irinka yasa yanzu mata suka rena mu basa girmama mu ka zubarwa da kanka daraja da ƙima ana magana kana wuƙi-wuƙi da idanuwa, da wani shegen ɗangalalle hancinka.
Haka Bilal ya ci-gaba da shan zagi iri-iri daga bakuna 'yan sanda yayin da daga mai zagin fuskarsa sai mai zagin hancinsa musanman hancinsa ya sha zagi na fitar arziki.
Ya Kabeer ya jaddada wa 'yan sanda kada su sake su bada belinsa har sai ya fito da kuɗi ko sarƙar gwal ɗin.
Tun abin ƙarfe ɗayan rana Bilal Shattima yake a ƙargame a cell har ga shi yanzu ƙarfe 5:30 na yamma, tun ɗan koko da ya sha da safe shi ne a tumbin sa wata uwar yunwa yake ji kamar zai ci babu da ya ji uwar bari babu shiri ya shiga roƙon constable da ya bashi wayarsa ya kira gida ya faɗa musu hali da yake ciki ko abinci ne a ya kawo masa kada yunwa tai mata illa. Da farko constable din yaso ya hana shi gani yadda yake ta faman yi masa magiya yasa ya bashi wayar, abokinsa Abbas ya kira ya sanar da shi yana police station sai dai ya ɓoye mishi ainihin gaskiya abinda ya faru, da cikin gaggawa Abbas ya iso police station ɗin hankalin shi a tashe, lokaci da ya ji laifin da Bilal Shattima ya aikata sai da ya girgiza. Ba irin  kalar magiyar da bai yi ba akan abashi belinsa amma suka ƙi daga ƙarshe sai nuna masa suka yi sai da amincewar Ya Kabeer. Abbas bai yi ƙasa da guiwa ba ya karɓi phone number ɗin Ya Kabeer daga wurin inspector ya kira shi da farko sun gaisa cikin mutumtaka Abbas yana fara zayyano maƙasuɗi kiran nashi Ya Kabeer yai sauri datse kiran, da Abbas ya ci-gaba da kiran nashi sai kawai yai switch off ɗin wayarshi. Sai kawai Abbas ya kwantar wa da Bilal da hankali ya ba shi tabbaci zai shiga ya fita har sai an bada belinsa, yana baro police station ɗin kai tsaye gidansu Bilal ya nufo yana tura ƙofar shiga gidan da Aunty Bahijja  ya fara cin karo ta fito za ta tafi gidanta, bayan sun gaisa ya tambaye ta Hajja ta ce tana ciki "Aunty Bahijja idan ban taƙura ki ba mu shiga daga ciki akwai matsalar da ta kawo ni.
Ya wuce gaba Aunty Bahijja ta biyo shi a baya koda suka shigo Hajja tana bathroom suka nemi wuri suka zauna suna jiran fitowar ta, bata ɗauki dogon lokaci ba ta fito Abbas ya gaida ta amsa tare da faɗin "Abbas kaine a gidan namu?
"En! Hajja.
"To ALLAH yasa lafiya.
"Da dama za a ce Hajja domin Bilal yana police station.
   "Police station kuma?"
Kusan a tare Hajja da Aunty Bahijja suka furta kowanne su tashin hankali ya bayyana ƙarara akan fuskokinsu.
"Kwarai kuwa Bilal yana hannu 'yan sanda a dalili sarƙar gwal ɗin matarsa Jeeddah da ya ɗauka ba tare da saninta ba ya sayar ya yi wa A'isha kayan ɗaki. To shine ta nemi sarƙar ba ta gani ba daga ƙarshe aka yi bincike aka tabbatar da shi ne ya ɗauka. Su kuma 'yan uwanta suka haninta shi ga 'yan sanda su kuma 'yan sanda sun tabbatar min ba zu bada belinsa ba har sai in Ya Kabeer ɗin ne ya janye ƙarar.
  "Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Oh! Ni Hajja shi kuwa Bilal me ya kai shi taɓa abinda ba nashi ba?"
Aunty Bahijja ta ƙarbe zance ta hanyar faɗin "ƙaddara ce Hajja in banda aikin ƙaddara me zai sa shi taɓa kayan Jeeddah balle har ɗan uwanta yasa a kulle shi wallahi Hajja daga Jeeddah har danginta rankataf ɗinsu basu da mutumci basu kuma gade sa ba.
"A'ah! Aunty Bahijja kada ki ɗauki laifi kacokan ki ɗora akan su idan ma su na da laifi na Bilal ya fi su nasu yawa miye kayan ɗaki da zai sa ya ɗauki gwal ɗin matarsa ba tare da saninta ba. Hakan fa yana nufin sata kenan...
"Dakata Abbas ni kam ban haife ɓarawo ba. Kowa ya sani abin mata na mijinta ne hakazalika duk abinda miji ya mallaka na matarsa ne da 'ya'yanta, ba kasan iya adadin hidindimo da faɗi tashi da yake yi akanta ba. Kawai dai sun yi haka ne domin su ci zarafinsa to kuwa kansu suka yi wa domin muddin aka kira Bilal da suna ɓarawo to tabbas sai Jeeddah ta amsa sunan matar ɓarawo..
"Hajja haƙuri fa za ku yi dole ku kai zuciyoyinku nesa idan ku ka ce za ku fusata to gaskiya al'amari nan gaba ɗaya lalacewa zai yi.
"Ni fa shiyasa tun farko banso aure Jeeddah nan ba saboda 'yar gidan ƙanana mutane ce banda ƙaranci saboda wani banza gwal za ta yi ƙarar mijinta.
Aunty Bahijja ta faɗa zuciyarta fal da tsanar Jeeddah.
Abbas ya ja bakinsa ya tsuke sai kallon Hajja da Aunty Bahijja yake yadda  suka murje idanuwansu ga gaskiya suna gani amma sai suka take ta suka ɗauki laifi tare da ɗorawa Jeeddah da 'yan uwanta, sai zagi da tsinuwa suke bin su dashi sai da suka yi mai isarsu kafin suka biyo Abbas zuwa police station ɗin. Lokaci da Bilal ya yi arba dasu duk sai ya ji kunya ta mamaye shi, musamman da ya tuna ƙaryar da ya sharawa Hajja da tambaye shi inda ya sami kuɗi kayan ɗakin A'isha.
Hajja kuka ta fashe dashi yayin da 'yan sanda suka gargaɗa ƙeyarsu waje, gani yamma ta kawo jiki yasa ta kira Baffan su Bilal ta faɗa mishi. Sosai ya dinga faɗa tare da ganin laifin Bilal kuma ko kaɗan bai ga laifi ƙarar Bilal ɗin da aka yi ba. Duk yadda so abashi belin Bilal 'yan sanda suka ƙi dole sai da amincewar Ya Kabeer. Abbas ya kawo shawarar su tafi kasuwa su isko mahaifin Jeeddah domin da matuƙar wahala Ya Kabeer ya janye ƙarar cikin sauƙi. Baffa ya amince da shawarar tashi gudun kada lokaci bada beli ya wuce yasa suka hanzarta suka tafi  Kasuwa a ɗaya daga cikin shaguna Baba suka tadda shi suna lissafi da Abdul Baba yana ganinsu yasan babu lafiya, bayan sun gaisa Baffa ya nemi su keɓance, kana ya kora masa dalilin zuwansu. Sosai ran Baba ya ɓaci a fusace ya kwaɗa wa Abdul kira ya ce ya je ya kira masa Ya Kabeer a ɗayan shagu, tun kafin Ya Kabeer ya ƙara so gun da suke ya hango Abbas tare da Baffan Bilal ga kuma fuskar Baba a haɗe yana zuwa Baba ya rufe shi da faɗa inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Duk da Baba yasan irin muguwar ta'adi da Bilal ya yi amma haka ya ɗorawa Ya Kabeer laifi ya zazzage shi tass! Kana ya tisa ƙeyarsa gaba suka taho police station aka bada belin Bilal, suna fitowa daga cikin police station adaidaita yana sauke Hajja da Aunty Bahijja ɗauke da foodflask sun kawo masa abinci. Haƙuri Baba ya shiga basu sai wani fizgar kai Aunty Bahijja take yi yayin da Hajja ta ji kunya zagin da suka dinga yi wa mahaifin Jeeddah suka sun zargi cewa da sa hannunshi aka rufe Bilal, sai gashi ya tabbatar musu da cewa bai ma da masaniya akan abinda yake faru cike da kunya gami da nadama Hajja ta kalleshi ta ce "Alhaji ai mu ne ya dace mu ba ku haƙuri wallahi-tallahi bansan cewa gwal ɗin Jeeddah Bilal ya ɗauka ba danasani ko kusa ba zan bari ya aikata wannan kuskure ba.
  "Ba komai Hajja ai ba a shiga tsakanin mata da miji duk wanda ya shiga rabon shi kunya, shi Bilal rashin kyauwarshi ɗaya ne da bai tambaye ta ba. Malam Bilal sai ka kiyaye  ko anan gaba kada ka ɗauki abin matarka ba tare da sani ta ba. Ka ga rashin faɗar abinda ya janyo maka.
Baba ya ƙarashe magana tare da kallon Bilal.
Saboda tsanani kunya kasa amsawa Baba Bilal ya yi sai sadda kai ƙasa ya yi.
Tsabar takaici da ya lulluɓe Ya Kabeer yasa yai sauri bari wuri ya nufi inda ya yi parking mota yana jiran Baba.
Daga nan Baba yai musu sallama tare da jadadda wa Bilal bayan sallar isha'i ya zo ya tafi da matarsa.
Ina sallame sallar isha'i Mama ta shigo ɗaki da nake tana ɓaɓɓatun faɗa sai cewa take yi "Na rasa Alhaji wane irin Mutum ne? Fissibillah a zalunci 'yarka ka kasa kwata mata hakkinta sannan kuma wanda ya ce zai bi mata hakkin nata shi ma ka hana shi wannan wane irin sanyi hali ne?"
Ina jin abinda ta faɗa na fahimci tana magana ne akaina kafin na ɗago idanuwana da har yanzu basu ƙarasa sucewa daga kumburin da suka yi ba na kalleta ina faɗin "Mama ni dama nasan da maganar nan ta je kunne Baba laifin Ya Kabeer zai gani amma wallahi-tallahi komai dare daɗewa sai Bilal ya biya ni gwal ɗina ba dai ya ce ara ya yi ba shikenan mu tafi a haka...
"Ke dallah! rufe min baki ba abinda za ki iya ai duk ke ce kika janyo tun farko ba yadda ban yi dake ba akan ki haƙuri da shegen yaro nan matsiyaci ne bai gadi arziki ba, amma ki ka ƙi to ga irin ta nan ɗauki ɗaɗɗaya zai dinga yi miki da kaya har sai kin waye gari ba ki da kayan ɗaki ko ɗaya.
Haka Mama ta dinga faɗar maganganu mararsa daɗi akan Bilal kafin ta ce min na tashi naje Baba yana kirana.
Ina zuwa parlour Baba ya ce na zauna rarrashina ya dinga yi gami da yi min nasiha "Jeeddah ki yi haƙuri da mijinki wata rana sai labari nasan abinda ya yi miki bai kyauta ba kuma ko waye aka yi wa haka dole ya ji zafi amma idan kika yi haƙuri sai ki ga ALLAH ya musanya miki da wani gwal wanda yafi naki na farko da ki ka rasa.
Duk maganganu da Baba yake faɗa iyakacina na gyaɗa kai a fakaice kuma ina sharar hawaye, ina baro parlourn ba daɗewa  sai ga Bilal Shattima ya zo ba kunya balle tsoron ALLAH ya iya zuwa gidanmu, sake haɗa mu Baba ya yi yai mana nasiha kafin ya ce na tashi na bi mijina mu tafi gida zuciyata kamar za ta fashe saboda haushi da takaici Bilal, muna fitowa daga gidanmu nai gaba abina da sauri ya biyo ni ya jera dani sai magana yake min nai banza dashi cikin sa'a muna isowa bakin titi na tare adaidaita ina shiga shima ya shigo ya zauna kusa dani ƙoƙarin kama hannuna yake yi na  daka masa rikitatciyar tsawa gami da faɗin...

*Just to manage*

_Ku yi haƙuri kwana biyu kun daina ji na bani da lokaci typing bikin aure muke yi_

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now