018...

93 8 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA
  
   *Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku ta karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune Kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya kacal_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

018...

Washe gari lafiya lau sun ka tashi tamkar saɓani bai taɓa shiga tsakaninsu ba. Sai nunawa junansu soyayya da tattali suke yi. Tana gama haɗa breakfast tayi wanka ta shirya cikin atamfar Hollandais vlisco ɗinkin skirt and blouse, kitso take so ta je gidansu Bilal Shattima A'isha Shattima tayi mata dama tun can asali ita ke mata kitso ko aure da tai bata canza ta ba. A dalilin hannun A'isha Shattima ya karɓeta sosai ta taɓa gwada sauya kitso wurinta gashinta ya fara karyewa dole ta dawowa gunta. Tana gama shirinta ta nufi kan gado inda Bilal Shattima ke lulluɓe cikin bargo yana sharar bacci sai ɗan ƙaramin minsharinsa ke tashi, sai da ta fara galla masa harara kafin ta ja bargon jikinsa ta yaye shi tare da ta linkewa ta ajiye shi a gefe kana ta hayo gadon dai-dai saitin kunnenshi ta ɗora bakinta ta kira sunanshi da ƙarfi "Bilallll!
A mugun firgice ya tashi zaune yana murtsuka idanuwanshi yayin da Jeeddah ta tintsire da dariyar ƙeta, nan take ya ƙarasa wartsakewa ya fizgota da ƙarfi ya shigar da ita jikinsa ya matse ta sosai sai ihu take tana mishi magiya "wayyo Allah kwalliya ta Love za ka ɓata min kwalliya please ka kyaleni.
   "Ba zan kyale ki ba sai kin biya tashina da kika yi infact kece kika jawo na ɓata miki kwalliya akan wane dalili za ki yi min ihu irin wannan a kunne wato so kike ki fasa min dodon kunne kou?"
Ta marairaice murya ta dawo kalar tausayi ta ce
  "Dan Allah ka yi haƙuri Love so nake ka tashi kayi wanka za ka kaini gida wurin kitso inaso naje da wuri saboda har lalle za ai min.
A kasalance ya ɗagota gami da zare ta daga jikinshi yana faɗin "Gaskiya Jeeddah ba ki da kirki yanzu saboda kitso da lalle ina cikin baccina mai daɗi za ki tashe ni.
Saukowa tayi daga kan gado ta ja hannuwanshi gami da faɗin "to ai kaine za a yi wa kwalliya saboda haka dole ne yau ka haƙura da bacci nan naka da baya ƙarewa.
Ba yadda ya iya tun da ta sako shi a gaba dole ya miƙe ya shiga wanka koda ya fito har ta kimtsa gado, a gaggauce ya shirya cikin brown colour filtex material a dining room ya tadda tana jiranshi su yi breakfast su na gama breakfast ta ɗauko handbag ɗinta. Shi kuma ya fito da machine tana cikin rufe ƙofa sai ga Jessica ta fito daga apartment ɗinta da plaster a damtse hannunta inda Jeeddah ta yanke ta da akayi mata ɗimki, a ɗan tsorace Bilal Shattima ya saci kallonta kafin yai maza ya dawo da ganinshi kan Jeeddah wacce ta kammala rufe ƙofa ta zare keys, ta nufo wajensa hango Jessica da tayi yasa ta murtuƙe fuska ta wani ɗauke kai tana zuwa ta ce "Mu tafi malam naga kana wani muzurai kamar marar gaskiya.
   Ɗan tari ya yi yana wani gyaran murya kafin cikin kwantar da murya ya ce "Love za ki yi min wata alfarma indan na tambaya?"
Wani kallon tai masa kafin ta taɓe baki gami da cewa "faɗi alfarmar taka kuma Allah yasa zan iya don ni ba kowace alfarma nake iyawa ba.
  Shiru ya yi sai faman shassafa kwantatce sajensa yake yi, alamar yana jin tsoron furta abinda ke ranshi.
  "Love ya ka yi shiru ka yi magana mana na faɗa maka sauri nake yi, kai kuma sai ƙoƙarin ɓata min lokaci ka ke yi wallahi banaso na rasa lalle nan gashi ƙarfe 11:00am muka yi alƙawari da mai lalle ɗin ta ce min tana da amare da za ta yi ma.
Sai da ya kauda fuskarshi don ba zai iya haɗa idanuwa da ita ba kana ya ce "Inaso da amincewarki mu je mu yi ma Jessy sannu da jiki, kinga abinda ya faru da ita ke ce sila kuma bai dace ba mu ganta mu wuce batare da mu tambaye ta jikinta ba.
A razane Jeeddah take kallonshi sai yau ta ƙara tantance reni wayau Bilal Shattima na musamman ne. In banda ya gama rena mata wayau zai wani nemi alfarmar zuwa gun wata ko wata wacce a yanzu ba wanda ta tsana sama da ita saboda haka a mugun fusace ta kalleshi ta ce "Ga hanya nan Bilal Shattima ai ba dabaibiya nai maka ba balle ka nemi alfarmata, kana da 'yanci yi duk abinda kake so Jeeddah bata isa ta hanaka ba je ka kawai abinka.
  Sani ya yi har gaba da abada ba za ta taɓa amincewa buƙatarsa ba. Muddin ya ce sai da amincewarta to tabbas ba zai yi abinda yake gani shi ne daidai ba, shiyasa bai ƙara tanka mata ba ya kafe machine ɗinsa ya nufi wajen Jessica.
Jeeddah wani abu taji ya daki zuciyarta tabi Bilal Shattima da idanuwa, fahimtar tayi idan ta sake furta wata kalma daga bakinta ba abinda zai hanawa zuciyarta bugawa saboda haka ta juya cikin sassarfa ta nufi gate ta tura ƙaramar ƙofa ta fita yadda ta maida ƙofar da ƙarfi ta rufe yasa Bilal Shattima waigawa hakan bai sa shi fasa tunƙarar wajen Jessica ba. "Jessy ya hannunki hope kin ji sauƙi?"
Ya faɗa sa'ili da isa wajen Jessica sai da Jessy tai murmushi kafin ta ɗauke idanuwanta daga kan gate ɗin da Jeeddah ta fita, kana ta ce "Na ji sauƙi sosai oga Shattima.
  "Thank God! Allah ya ƙara sauƙi za mu fita zan kai madam gida.
Bilal Shattima ya faɗa yana sake kallon ƙofar da Jeeddah ta fita.
"ALLAH ya kiyaye hanya.
Jessica ta faɗa tana murmushi.
Daga haka Bilal Shattima ya juya ya tashi machine ɗinsa ya fice koda ya fito Jeeddah har ta kusan kai bakin titi ya ƙara speed ya cimma ya taka birki a gabanta ya ce "Love shi ne kika yo tafiyarki ba ki tsaya jirana ba kou?"
A mugun fusace ta kalleshi kana tai kwafa gami da faɗin "Ai ni ba gantalalliya bace da zan tsaya ɓata lokacina ina zaman jiranka sai kace kaine mutum na ƙarshe da ya rage a duniya mai abin hawa.
  Duk da ya ji zafin maganarta sai kawai ya yi ƙoƙarin danne zuciyarsa ta hanyar kwantar da murya ya ce "Allah ya ba ki haƙuri ni banaso fitina zo ki hau mu tafi kada ki rasa lalle ƙarshenta ni za ki ɗorawa laifi.
   Sai da ta kalleshi ta watsar kafin ta ce "wallahi da na hau machine ɗinka gara na taka daga nan har gida a ƙafa.
Sororo ya yi yana kallonta kafin ya yi murmushi mai kama da na yaƙe ya ce "Da nai miki laifi me da za ki ce ba za ki hau machine ɗina ba naga dai lafiya lau muka fito daga gida?"
   "Ka ga Bilal Shattima karka nemi ka rena min hankali ni ba ƙaramar yarinya bace da zan kasa fahimtar manufarka ba....
"Dallah Jeeddah dakata!
Ya katseta cikin tsawa yanzu kam ya kasa controlling temper ɗinshi rai ɓace ya ci-gaba da faɗin "Ke wacce irin Fitinaniyyar mai rai ce? Duk yadda mutum ya kai da danne zuciyarshi akanki sai kin kai shi bango, kwata-kwata lamarinki ba kishi bane tsabagen reni wayau ne kawai da samun wuri. Ki zo ki hau machine mu tafi tun kafin raina ya gama ɓaci na nuna miki nawa kalar rashin mutunci.
  "Mtsssss....! Aikin banza wai kai kana tsammani wannan buyagi naka zai sa na hau machine ɗinka, ashe kuwa kana da sauran sani akaina.
Mamaki ne ya lulluɓeshi sai kallonta yake da baki buɗe, ta raɓa gefenshi ta tai tafiyarta yana gani tana ƙoƙarin tsayar da adaidaita yasa shi hanzarin parking machine ɗinshi. Yana zuwa wajenta bai yi wata-wata ba ya Riƙo hannunta tare da fizgota cikin ɓaci ran da bai taɓa ji irinsa ba ya ce "Enough is enough Jeeddah nagaji wallahi-azim na gaji da wannan mugun halin naki mekika ɗauke ni ne humm?" Sakarai ko mahaukaci ko kuma wanda bai san ciwon kanshi ba. Faɗin wannan kallo kike min daga cikin sunayen nan da na lissafa?"
Ya ƙarashe magana yana wani irin huci don shi ma Bilal Shattima mugun hot temper ne dashi, idan kuma yai fushi ya kan zama out of control idanuwanshi gami da zuciyarshi rufewa suke yi sai aikata abu ya dawo daga baya yana regretting.
   Itama goganyar taku ba baya ba saboda haka yadda taga ya fusata ko a jikinta, sun manta da suna kan hanya a bakin titi kowane su bala'in da masifa nacinsa. Cikin ɗaci rai ta fincike hannunta daga riƙo da yai mata kafin ta ce "Duk wannan ihu da tada jijiyoyin wuya da kake yi ba shi zai sa na hau machine ɗinka ba. Idan kuma har da gaske kake yi ka gaji dani ba sai ka ɗauki mataki ba. Wallahi gara na haƙura da fitar nan yafi  min da na hau bayan machine ɗin mayaudari irinka wanda bai san girman alƙawari ba.
  "Muddin ba za ki hau machine ɗina ba sai dai ki fasa fitar kuma ki sani duk randa kika kaini bango idan na shukka miki rashin mutunci duk zuri'arku ba za su iya taimaka miki wajen nome shi ba. Ki yi a hankali domin nima ɗan iskan kaina ne, juya maza ki koma gida kuma ki jira za ki ga abinda zai biyo baya, ba dai taƙamar ki rashin ɗa'a ba? To ni ne nan maganinki mahaukaciyar banza mai mahaukacin kishi.
   Cabdijam! Tun Lokaci da Bilal Shattima ya fara zari Jeeddah tai sanyi sai aikin kallonshi take yi,  bata taɓa tsammanin ya iya zari har haka ba. Saboda kafin sun yi aure muddin tsau-tsayi ya gitta ta ganshi da wata mace koda 'yar uwarsa ce, haka za ta saka shi a gaba ta ƙare masa rashin ɗa'a iyakacinshi yai ta bata haƙuri. Ashe kallon kitse take wa Rogo Bilal ɗin da take wa kallon salihi ba ruwanshi sai gashi yau ya shayar da ita zallar mamaki.
   "Wai uban me kike jira ne da kika yi tsaye kina zare ido, wuce ki koma gida daga yau na kashe zuwa kitso da lalle?"
Tsakani da Allah na tsorata matuƙa da jin fitar waɗannan zafafan maganganu daga bakin Love ɗina, ban ƙara shiga firgici ba sai da naga ya zaburo kamar zai doke ni. Babu shiri na juya da mugun sauri na nufi gida, ina shiga parlour na zube ƙasa nasa kuka mai sautin gaske "wai dan Allah dama haka aure yake yau farin ciki gobe akasin hakan ko kuma nawa ne ya zo da haka duka-duka yaushe muka yi aure da za a ce mun fara samun saɓani irin wannan?" Ni dai gaskiya nasan banda laifi ko kaɗan ko manafuki ɗan ƙasan wuta ba zai ce nayi laifi ba don kawai na nuna ina kishin mijina duk mace da tasan kanta dole tai kishin abinda takeso ashe nuna kishi wa abin ƙaunarka zai zama illah?
Ina ci-gaba da rare kuka ina wannan zance zuci don kuwa wani sashe na zuciyata har gaya min yake yi "Daina wahalar da kanki Jeeddah dama can Bilal Shattima ba sonki yake yi ba ki ce kika liƙe masa, shiyasa ya ke wulaƙantaki son ranshi.
Bilal Shattima yana gani Jeeddah ta koma gida cike da takaicinta ya ja machine ɗinsa ya ƙara gaba, da gangan ya ƙi komawa gida kaitsaye shagon abokinsa Abbas ya nufa, yana zuwa ya zayyane masa hali da yake ciki kasancewar baya ɓoyewa Abbas duk wani abu da yafe shi.
Cike da takaici Abbas ya buɗe bakinsa ya ce
  "Ka gani kou Shattima dama tun farko sai nai maka gudun irin haka, gashi nan aure duka wata uku kacal har kun fara samun saɓani Ina dalili wannan masifar?"
Abinda nake so ka sani Shattima mace mai baƙin kishi irin Jeeddah za ta iya kashe mutum, har lahira gara kayi taka tsantsan da lamarinta.
Harara Bilal ya gallawa Abbas sosai ya ji zafin maganganunshi akan Jeeddah a hasale ya bashi amsa ta hanyar faɗin
   "Subhanalillah...haba Abbas wannan ai mugun fata ne kake mata, Inaso Jeeddah kuma In-sha-Allahu har na koma ga Ubangijina ba zan mata kishiya ba wannan alƙawari na ne.
'yar bazawarar dariya Abbas ya yi gami da faɗin "Kai dai gaskiya ce ba kaso a faɗa kaima kasan da cewa Jeeddah za ta iya kisan kai akanka don gashi nan ka fara gani alama tun da har ta iya yankawa neighbour ɗinku wuƙa, ba fata nake maka ba amma muddin ba kayi saurin taka mata birki ba kaine next.

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now