031

86 13 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

031...

Cikin sanɗa Bilal ya iso ta bayan Hajja ya leɓe tare da leƙo da kanshi ta kafaɗarta yana kallon takarda da ta warware ya ƙura wa rubutu idanu, sai kawai ya zazzare idanuwanshi cikin kaɗuwa gami da rawar murya yake faɗin "Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Hajja wallahi sunanki ne da na Ya Faruk aka rubuta.
  "Subhanalillah! Suna kawai ka gani ko da wani abu?"
"En! To ga wani dogon jawabi nan a ƙasan sunaye.
"Maza karato min shi ai ina gani wannan tukunyar jikina ya bani ni ce aka yi wa, kuma wallahi koma waye ya tarowa kanshi bala'i da masifa.
*_"Daga yau mai kama da rana ta yau Faruk babu kai ba mahaifiyarka Hajja, ka manta da ita, ko gawarta za ka gani shimfiɗe a gabanka kada ka tausaya mata ko ka taimaka mata. Dukiyarka kada ta amfana da ita Faruk ka nisanci mahaifiyarka da 'yan uwanka ka tsane su tsana mai tsanani ta yadda duk hali da ka gansu ciki ba za ka iya taimaka musu ba_*
Tun sanda Bilal Shattima ya fara karantawa Hajja takarda jikinta ke kakkarwa kamar mai jin sanyi haƙoranta har haɗewa suke yi da kyar ta iya furta "innalillahi wa'inna illahim raji'un! Ashe duk abinda Faruk ke mana ba yin kansa bane aikin asiri ne?" Amma kuwa Hajiya Bintu ta cikakkiyar azzaluma, muguwa, mutaƙambira tsakanina da ita ALLAH ya isa ba zan taɓa iya yafe mata wannan zalunci da tayi min ba. Sai ALLAH yai mana hisabi shegiyar mata la'anana wacce babu ALLAH da Manzonsa a zuciyarta. Haba wannan kishi na masifa har ina mutumin da take kishi akansa ya mutu baya duniya amma bata barni ni da iyalina muka sheƙi iskar 'yanci ba. To Wallahi-azim nima a wannan karo ba zan kyaleta ba. Ke Mufeeda shiga ɗaki ɗauko min hijabina da ƙaramar jakkata tana nan akan gado a ƙarƙashin pillow, kema ki sako naki hijab yau ni zama bai ganoni ba.
Bilal ya rurrufe ƙofofi suna fitowa wani mugun kallo Hajja ta aikawa ɓangaren Hajiya Bintu tare da yin ƙwafa su na zuwa bakin titi suka tare adaidaita suka shiga sai lokaci Bilal ya sami damar tambayar Hajja inda suka nufa, kai tsaye ta bashi amsa da "Yabo za mu je na kaima malam Alti mai rahunnai layoyi nan ya ƙarya asiri da ke cikin su idan da hali so nake yai mata ƙaiƙai koma ma masheƙiya, duk wani mugun aikinta ya koma kanta.
  "A'ah! Hajja kada ki yi haka adai ƙarya asiri ita kuma ga ta ga duniya da iznin Ubangiji ƙarshenta ba zai yi kyau ba.
"Yi shiru kawai Bilal duk abinda zan faɗa ba lallai bane ka fahimci irin mugun ta'adi da matar nan tayi min ba. Yanzu dai kira min Bahijja ta fito ƙofar gida mu ɗauke ta don ba zan yi tafiya nan ba tare da ita ba.
Bilal ya fito da wayarshi daga gaban aljihun rigar shi sai lokaci ya lura da bashi da enough charging battery shi 7% ya rage ya kira Bahijja ya faɗa mata saƙo Hajja koda suka iso ƙofar gidanta tana tsaye rungume da hannuwanta a ƙirji mai adaidaita yana parking tana ƙarasowa, Hajja ta kalle Mufeeda ta ce "Mufeeda shiga gida ki jirani har na dawo ke kuma Bahijja shigo mu tafi.
Mufeeda ta fita Bahijja ta shigo mai adaidaita ya ja suka tafi kafin su isa tasha Hajja ta zayyanowa Bahijja abinda ke faruwa, sosai Bahijja ta shiga firgici da tashin hankali.
**** *** ****
Tun Jeeddah tana gunji kuka a hankali har ta dawo da dukkan ƙarfinta bata taɓa sani haka sata take da cin rai ba sai yau, taci kuka har ta godewa ALLAH can kuma ta tuna da abokin kuka ba a ɓoye masa mutuwa saboda haka ta tashi da gudunta ta nufi parlour ta ciro wayarta da ke charging, mutum na farko da ta fara kira shi ne Bilal, sai dai kashhh! Layin shi baya shiga gani bata same shi ba yasa ta kira Mama koda kiranta ya shigo wayar Mama Ya Kabeer ya zo gidan dama kowacce wayewar safiya sai ya zo ya gaida Mama, su taɓa fira sannan ya wuce kasuwa suna fira cikin sa'a kuma akan Jeeddah ne suke magana, dangane da rashin aiki Bilal Mama tana ba Aiman tea yayin da wayarta ke aje akan tv stand Ya Kabeer ya miƙe ya ɗauko wayar sai kawai yasa dariya yana faɗin "Yar halak taƙi ambato Mama Jeeddah ce fa ta kira ki.
Ita ma Mama dariya tasa gami da faɗin "Jeeddah kenan wannan abin ai a jini jikinta yake da matuƙar wahala ka ambaci sunanta ba ka ganta ba kodai ta faɗo ga wuri kwatsam ko kuma ta kira wayarka.
Ya Kabeer yana dariya ya amsa kira nata gami da ɗora wayar a kunne shi kafin ya yi magana ya ji  shasshekar kukanta gaba ɗaya ya karaɗe mishi dodon kunne har bai ya ji abinda take faɗa "Subhanalillah! Jeeddah me ke faruwa kuka me kike yi haka? Bana ji abinda kike faɗa idan da hali ki tsagaita kukan nan ki yi min bayani ta yarda zan fahimci dalilin kuka naki.
Cikin shasshekar na ja dogon numfashi muryarta tana sarƙewa na ce "Ya...Ka..beer...!
Sai Kuma wani sabon kuka ya koma kubce min.
  "Please Jeeddah control yourself ki natsu ki yi min magana wallahi-tallahi kukan nan naki yana mugun ɗaga min hankali fiye da ke da ka rera shi domin ke kinsan dalili da yasa kike yi sa.
Da sauri Mama ta dire Aiman ƙasa ta taso hankali tashe ta tsaya kusa da Ya Kabeer gani haka yasa yasaka wayar a speaker, yayin da Mama take jiyo yadda Jeeddah ke gunji kuka ba kakkautawa hakan ya tabbatar mata da babu lafiya cikin tashin hankali Mama ta ce "Jeeddah kina ji na kuwa?"
  "En! Mama.
"To ki natsu ki faɗa mana takamaiman abinda kike wa kuka kin ji 'yar albarka.
"Mama an sace min sarƙana na gwal na nema sama da ƙasa banganshi ba..
Ta ƙarashe magana da wani irin kuka mai cin rai.
"Innalillahi wa'inna illahim raji'un!
Kusan a tare Mama da Ya Kabeer suka furta Mama kam abin ya dake ta sosai saɓani Ya Kabeer da yake namiji, da baya-baya Mama ta soma tafiya har tai nasarar kai wa ga kujera ta zauna daɓass! Tana sake maimaita "innalillahi wa'inna illahim raji'un!
Ya Kabeer ya kwantar da muryarshi ta sigar rarrashi da son kwantar mata da hankali ya ce "Jeeddah ki natsu ki sake dubawa wani gun dabam koda kin sauya mata mazauni ne kin manta da inda kika ajiye.
"Wallahi Ya Kabeer ba inda ban duba ba banganta ba kuma ni wuri guda nake ajiya gwal ɗina cikin jewelry box.
  "To shikenan ga mu nan zuwa gidan naki ni da Mama amma kafin mu zo ki daina kukan nan haka domin kukanki ba zai sa gwal ɗin ya dawo ba.
"Tam Yaya!
Ta faɗa tare da datse kira Ya Kabeer ya kalle Mama ya ce "Mama ko za ki shirya mu tafi can gidan nata domin wannan uban kuka da take risga tana buƙatar ki kusa da ita?"
Ajiyar zuciya Mama ta sauke kafin ta miƙe jiki ba ƙwari ta ɗauki Aiman ta nufi bedroom ɗinta, dashi ta sake wanke mishi jikinshi da ya ɓaci da tea dama already ta yi mishi wanka ta canza mishi tufafi, sannan tasaka hijabinta suna fitowa Baba yana fitowa daga ɓangare shi yana riƙe da hularsa yana gyara karinta.
   "Alhaji yanzu nan Jeeddah ta kira tana kuka wai ɓarayi sun shiga mata gida har sun yi nasarar ɗauke mata sarƙata ta gwal. Shi ne za mu je gidan nata ni da ɗa nan.
Tana nufi Ya Kabeer kasancewar shi ɗa fari bata faɗar sunan shi, sai dai ta kira da ɗa nan saboda alkunya.
   "Subhanalillah! ALLAH ya mayar mata da sabon arziki ki jajjata mata kafin anjima idan na taso daga kasuwa na biya ta gidan nata.
Baba ya faɗa yana ƙarasa kafe hularsa aka.
  "Wallahi Alhaji Jeeddah ta bani tausai ba ka ji yadda take gunji kuka ba gwani ban tausayi.
Ɗan guntun murmushi mai sauti Baba ya saki yana faɗin "Ashe Fatee har kin manta da hali Jeeddah kin tuna sanda tana yarinya ko slippers ɗinta suka ɓata, ta dinga risgar kuka kenan ko wani na siyo mata ba za ta daina mita ɓatar wancan ba. Ai yau aikin rarrashi ya same ku amma ki faɗa mata tasa haƙuri da dangana a zuciyarta Ubangiji da ya bata wancan shi zai sake bata wani, duk abinda haƙuri bai ba ka ba rashinsa ma ba zai ba ka shi ba. Rai ma ya ƙare aka dangana balle abinda rai ya mallaka saboda haka ta daina wahalar da kanta da koke-koke tun da ba mutuwa aka yi mata ba.
Baba ya faɗa tare da nufar ƙofar fita Mama da Ya Kabeer suka biyo shi a Mama tana cewa "Ina zan manta Alhaji amma wannan satar ko babba aka yi wa ita sai ya koka.
Dariya kawai Baba ya yi da sauri Ya Kabeer ya buɗe mishi murfin mota ya shiga kana ya buɗe mishi gate ya fita sannan ya dawo ya buɗewa mama motarsa ta shiga ya ja suka nufi gidan Jeeddah. Kafin su isa Ya Kabeer ya kira Aunty Farida da Khairat ya faɗa musu kowacce su hankalinta tashe ta nufo gidan Jeeddah, yayin da Mama ta kira mommy Turai ta sanar mata.
**** *** ****
Koda su Bilal suka iso Yabo kowanne su ido ya rena fata domin ba su san kalar cakwakiyar da za su tarar a gidan malam Alti mai rahunnai ba. Suna shiga garin Yabo kai tsaye gidan malam Alti suka yi wa tsike, sun tarar da dandazo mutane masu neman biyan buƙatar duniya kasancewar Malam ɗan uwa Hajja ne ta ɓangaren mahaifinta, shiyasa suka kutse cikin gida basu tsaya a ƙofar gida ba. Bayan wani lokaci Malam Alti ya shigo gida ɗakin uwargidansa aka yi wa su Hajja masauki saboda haka a can ya same su kowanne su ya daka ɗan uban tagumi. Bayan sun gaisa Hajja ta kora masa bayani kana Hajja ta fiddo da tarkace tsibance-tsibance ta miƙa mishi a hankali yake nazari akan su kafin ya shiga warware layoyi ɗaya bayan ɗaya ya tattaro dukkan natsuwa shi ya kalle su sun yi jigun-jigun dasu ya ɗago laya ta farko wacce Hajja ta fara warwarewa ya ɗaga ta sama ta yadda za su ganta da kyau ya ce "Wannan layar an yi ta ne domin raba tsakaninki da ɗan ki Faruk da kuma 'yan uwarsa wannan asiri duk wanda aka yi wa shi da wuya yaga daraja da ƙimar mahaifiyarshi, kuma yana ɗaukar dogon lokaci kafin ya ƙarye.
Wannan kuma mai kadangare ana yi shi ne domin taɓa lafiyar gangar jikin ɗan-adam kamar a saƙo mishi ciwon tabin hankali, kuma mijin Bahijja ne aka yi wa shi. Sai kuma wannan na mutuwar zuciya ne da ɗusasshe tauraron ɗan-adam za ki ga mutum yana neman aiki yi ya kasa samu ko kuma zuciyarsa ta mutu ya kasa neman na kansa. Wannan asiri yana nuni da Bilal aka yi wa shi domin naga sunansa ɓaro-ɓaro a ciki amma yanzu Al-hamdulillah...tun da ku ka zo nan ku ƙaddara komai ya zo ƙarshe amma kafin sannan wa kike zargi da yai muku wannan aika-aikar?"
Kusan a tare suka sauke numfashi kafin Hajja ta gyara zamanta tana faɗin "Malam ai babu batun zargi a cikin wannan al'amari sai dai tabbatar wa bana ko shakka abokiyar zamana ce Hajiya Bintu domin tun Alhaji yana raye muke taƙon saƙa da ita ai kasan komai Malam, domin gunka nake zuwa neman taimako amma ban taɓa cutar da ita ko wani daga cikin 'ya'yanta ba, iyakacina taimakon da zan mallake Alhaji a lokaci ikon faɗa nakeso a gidan ba ikon cutarwa ba. Kuma tun daga lokaci da Alhaji ya rasu na watsar da makaman yaƙi na. Ashe ita har yanzu da muguntarta danƙare a zuciyarta, saboda haka wallahi bata ci bulus ba, tun da ba malamai ta fi ni sani ba nima sai nai mata uban wanda tai min.
"A'ah Hajja kada ki biye mata tun dai ALLAH ya toni asirinta sai ki barta dashi za ki ga yadda ƙarshenta zai kasance.
Bilal ya faɗa yana mai tsare Hajja da idanuwanshi baƙar harara ta sakar mishi kafin ta kora shi waje ta shiga zayyanowa Malam Alti muradinta.
**** *** ****
Kafin kace kwabo gidan Jeeddah ya cika da Iyaye da 'yan uwanta fuskar Jeeddah har ta kumbura Idanuwanta sun luhu-luhu alamun tasha kuka ba kaɗan ba. Cikin dusasshiyar murya ta shiga basu labari yadda ta nemi sarƙa bata ganta ba. Duk da haka basu haƙura ba sai da suka rankaya gaba ɗayansu zuwa ɗakinta suka sake bincika wa sai lokaci Ya Kabeer ya shigo ɗakin yayin da Jeeddah ta nuna mishi safe ɗin da ke  cikin closet ɗinta anan take saka jewelry box ɗinta, kuma safe ɗin sai da code yake buɗewa shiru Ya Kabeer ya yi tare da nazarin safe ɗin kafin ya kalle Jeeddah with serious face yana faɗin "ke kaɗai kika san code ɗin safe ɗinan ko kuma har da mijinki?"
Kamar saukar aradu haka naji tambayar Ya Kabeer yayin da gabana yai mummunan faɗuwa, kuma a lokaci ɗaya su Mama suka dawo da ganinsu akaina sai na haɗiye wasu busassu miyau kafin nace "Shi ma yasani Ya Kabeer yanzu haka ma idan ka duba ciki za ka ga credential ɗinshi a ciki.
"Yana da labari ɓatan gwal ɗin naki?"
"Ba shi da Yaya domin a lokaci da na duba banganta ba shi ne mutum na farko da na fara kira amma wayarshi bata shiga.
Ɗan guntun murmushi Ya Kabeer ya saki kafin ya maida ganinshi akan su Mama da tuni suka kakkafe shi da idanuwansu ya ce "Mama ku zo mu je parlour idan har lissafina ya hau daidai na gano ɓarawo sarƙar Jeeddah.
Yana gama magana ya fice da sauri su Mama suka mara mishi baya, yayin da naji faɗuwar gabana ya ƙara tsananta da kyar na cira ƙafafuwana na biyo su. Kowa ya zauna banda ni domin wani irin sabon yanayi nake ji kaina a ciki. Sai da mommy Turai ta umarce ni da na zauna sannan na nemi kusa da ita na zauna gaba ɗayan mu muka tattara hankali da natsuwar mu akan Ya Kabeer. A natse ya shiga faɗin "ina da hujjoji kwarara da ke nuni da Bilal mijin Jeeddah shi ne ɓarawo sarƙarta.
   "Innalillahi wa'inna illahim raji'un!
Kusan a tare suka furta yayin da ni kam suman zaune nayi na saki baki da idanuwa na zama speechless and shock sai rarraba idanuwa nake yi da na kalle wannan sai kuma na dawo da idanuwana akan wannan.
Aunty Farida ce tai ƙarfin hali furta "uhmm...Ya Kabeer kada ka faɗin abinda ba ka tabbatar ba domin gujewa zubewar mutumci.
mommy Turai ta ce "A'ah Farida kada ki katse masa hanzari mana ki tsaya ya faɗin hujjojin nasa, amma ai ba abin mamaki bane idan aka zargi Bilal da sata domin mutumin da bai da aiki bai da sana'a ga mutuwar zuciya ai dole ka same shi da sata..
  "Dan ALLAH Mommy kada ku liƙawa Love sata wallahi ba sh....
"Kada ki yi sauri rantsuwa Jeeddah ki tsaya na kwararo miki hujjoji da nake dasu.
Ya Kabeer yai sauri taka min birki.
  "Haba Ya Kabeer ta ya zan yi shiru bayan ina da tabbaci mijina ba ɓarowa bane.
"Ke! Dallah rufa mana baki sakarya kawai duk yadda kika so ki kare shi ba za ki taɓa iyawa ba gara ki tsuke baki mu ji abinda ɗa nan zai faɗa.
Mama ta faɗa cikin tsawa babu shiri na tsuke bakina.
Yayin da Ya Kabeer ya shiga faɗin "idan har ku ka natsu ku da kanku za ku fahimci abinda na fahimta dangane da satar nan.
Abu na farko da za ku duba tun daga cikin parlour nan akwai abubuwan da dama da ya dace ace ɓarawo ya sata amma sai duk ya bar su kai tsaye ya shiga bedroom. Na biyu kuma da ya shiga bedroom kafin ya kai ga buɗe closet anan ma akwai abubuwan da yawa da zai iya sata amma duk ya wuce su sai ya tafi kai tsaye ga closet da ɓarawon na gaskiya ne dole sai ya fasa safe ɗin kafin yai nasarar ɗaukar sarƙar, amma ba wata alama da ke nuni da an fasa ta, saboda haka da code aka yi using. Da ɓarawo na gaskiya ne da ba yadda za a yi yabar zobe da 'yan kunne da ke ciki al'hali suma na gwal ne duk mai hankali da tunani idan ya natsu zai tabbatar da hujjoji da na kawo tabbas Bilal Shattima shi ne ya saci gwal ɗin Jeeddah saboda haka duk inda ya shiga wallahi-tallahi sai na nemo shi ya dawo mata da gwal ɗinta.
Gaba ɗaya su Mama suka ɗauki salati sai faɗa suke suna sake nanata wa yayin da na ƙara shiga firgici da tashin hankali, nan take ƙwaƙwalwa ta ta shiga tuno min da irin maƙudan kudi da ya siyawa A'isha Shattima kayan ɗaki, lallai biri ya yi kama da mutum babu sauran shakku ko kwakwato tabbas Bilal ne ya ɗauke min sarƙar gwal ɗina ya yi wa ƙanwar sa kayan ɗaki, wani iri ƙaton ƙololo na ji ya zo ya tokare min maƙoshi....

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now