2...

229 11 1
                                    

*💥 ZAZZAFAN KISHI.....!*
_{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattapad-jeedddahaliyu

©HWA

Assalamu Alaikum I'm Zarah Dange 07034400732 face behind LADY APHRODISIAC AND MORE dealer in all kind of supplement and herbal aphrodisiacs kayan mata. Kayan mu will make you last on bed and permanently end the pain and embarrassment of weak eraction and premature ejaculation.

*Muna hadin bridal package and postnatal combination of natural herb's and supplement.

*Akwai hadin uwar gida mai da tsuhuwa yarinya
*Akwai hadi na infection (sanyi herbs).

*Akwai Zuma Mai saukar DA niima nan take tare da dandano Na mussaman.

*Muna kalolin gumbar Kamar gumbar madara, gumbar Aya, gumbar ridi, gumbar kasko, yar kicihi, Alhaji ba nan kake ba d.s .

*Akwai kalolin tsimi kamar Dan la'asar, tabaje, tsimin yar gata d.s .

* Muna DA kalolin gari nasha kamar sa buzu kuwa, sinadarin aya, abin sirri ne, emergency, rakumi DA akala, runbun dadi, kinfi Amarya d.s.

*Muna special kaza, danbu, ciccibi, Yan shila,zuciya d.s

*Akwai Na matsi different types DA sabulu na tsalki.

Ta bangaren supplement muna da na gyaran skin da kuma herbal aphrodisiacs supplement , akwai different oils both retail and wholesale, supplement Kamar su Juliet eve, royal jelly, ultimate maca, suprodine, frozen detox, frozen collegen, majakani, amirna, khusus, dara, cantik ayu, pesona d.s
We have capsules, pills, chocolate, and different coffee that will make you sweet, firm, tight, young, beautiful and healthy.
Delivery is nation wide 07034400732

_Na sadaukar da wannan littafi ga Zarah Bb_

02...

A wani yammacin ina kwance a ɗaki Mama ta kwalla min kira, na fito ina zunbure baki saboda a tunanina wani aiki za ta saka ni. Yau kwana mu biyu da dawowa hutu amma kauda kara ban yi mata ba ina daki na nade bisa gado, sai dai ta kashe ta bani naci, ɗan banza son jiki ne da ni ga shegiyar ƙiwa duk lokaci da Mama ta saka ni aiki sai ranta ya ɓaci saboda na dinga jan jiki kenan, tamkar banida lakka a jiki har sai ta hasala ta karɓe abinta tayi da kanta. Ba don Mama tana tsawata min ba da ba ƙaramar malalaciya ce ni ba. Yadda Mama taga ina zunburi baki gaba yasa ta galla min harara tare da faɗin "Sakin ranki magge uwar son jiki ba aiki zan saka ki ba aike ki zan yi shagon Bello Rahusa ki siyo mana sabulun wanki, gobe da sassafe Musa zai zo ya yi wa Alhaji wanki sai yanzu na tuna da babu sabulu.
Jin Mama ta ambaci sunan shagon Bello Rahusa yasa na ƙara turo baki gaba, Saboda na tsani zuwa shagonsa a dalili majalisar samarin unguwa da ke kusa da shagon nasa masu masifar kallon tsiya haka kawai za su dinga bin mutum da shegun idanuwansu har sai ya ɓacewa ganinsu.
"Je ki ɗauko hijabinki mana.
Mama ta katse min zance zuci da nake, gyara tsayuwa ta nayi gami da langwaɓe kai na yi narai-narai da idanuwa na ce "Gaskiya ni dai Mama ba son zuwa shagon Bello Rahusa nake yi ba, da za ki haƙura da dare idan Musa ya zo karɓa abincinsa sai ya siyo miki.
Na ƙarasa magana ina wani kwantar da murya.
"Ai nasan da Musa zai zo karɓar abincinsa amma na aike ki, ke dai har abada ba za ki daina halin ƙiwa ba.
"Ba wai zuwan ne banaso yi ba Mama ƙarttin banza nan da ya tara gaban shagonsa ne banaso bi ta gabansu, sun dinga bin mutum da kallo kamar wasu tsofaffin mayyu...
"Dallah...karɓi ki je ki siyo min abinda na aike ki ko ina ruwanki dasu balle har kallonsu ya dame ki.
Yadda Mama ta buga min tsawa yasa na karɓi kuɗin hannunta babu shiri na nufi ɗaki ina gunguni na sako dogon hijab har yana ja a ƙasa na saka wasu silifas na roba na Mama da ke aje a ƙofar parlour na fice rai ɓace ina tafe ina cin rai sai uban tsaki nake zabgawa tun kafin na ƙarasa shagon na hango majalisar kamar da gayya suka yi min don ta cika tafff babu masaka tsinke sai tashin muryoyinsu ka ke ji suna gardama har ba ka iya tantance mai magana a cikinsu, wani mashahurin takaici ya rufe ni har ji nake kamar na juya na koma gida, sai kuma na tuna da Mama muddin ban siyo mata aikenta ba za ta iya cin ƙaniyata tun kafin na isa kusa dasu na sadda kaina ƙasa, yanayi da naji ƙafafuwana suna harɗewa ya bani tabbacin su biyo ni da kallo musamman da na tsikayo muryoyi kaɗan daga cikinsu ne ke ci-gaba da magana. Da ko kafin na kawo kusa dasu tun daga nesa nake jin surutunsu sai kace masu cin kasuwa. "Tirrr......wallahi kun yi asara gantalallu banza da wofi marasa aiki yi.
Na faɗa cikin zuciyata, wani ƙarin abin takaici ina shiga shagon na tadda mutane cike tafff ba maza ba, ba mata ba kai in takaice muku har da ƙanana yara raina ya ƙara ɓaci ko kusa ba zan iya ratsa wannan tulin cikoson mutane don kawai siyen sabulun wanki, sai na nemi ɗaya daga cikin deep freezer da ke farkon shigowa shagon na jingina bayana gami da folding hannuwana a ƙirji "Kai wallahi mutane akwai su da shegen son banza tsiya don kawai Bello Rahusa yana siyarda kayansa akan farashi mai sauƙi tamkar dai yadda ake ba da wa akan sari a kasuwa shiyasa Mutane unguwarmu suka daina zuwa kasuwa har ma da na wasu unguwanni da muke makwabtaka dasu saidai su zo shagonsa su yi ta bin layi a wofi mtsss...!
Na ƙarasa zance zucina da siririn tsaki. Kamar daga sama na ji ana ture ni gami da ƙoƙarin buɗe murfi freezer da nake jingine akai, cikin tsananin masifa na yadda idanuwana akan mutumin da ke ƙoƙarin ture ni wani mummunan gajeren saurayin ne baƙi wulik dashi baƙinsa har wani naso yake yi tamkar ya shafa gawayi "Malam ba ka gani ne halan kai makaho ne da ba ka lura da ina jingina jikin freezer nan bane?"
Na watsa masa tambaya cike da tsiwa saboda masifa har wani ƙanƙace idanuwana ke yi.
"Amma dai malama kina sane da nan wuri masana'anta ce ba wurin kwanciya ba, idan bacci ki ke ji ki koma gida ki kwata, amma haka kawai kin zo ki sami freezer mutane kin ɗale sai zuba gyagyaɗi ki ke yi.
Ya bani amsa yana min wani kallo da ke kama da na reni wayau.
Na yi ƙwafa gami da janyewa na koma gefe na bashi waje saboda na fahimci tsagerancinsa ya fi nawa ina kallonshi ta gefen ido ya buɗe freezer ɗin yana faɗi "Da dai yafi miki ki tsaya da ƙafafuwanki kamar kowa.
Ya ƙarashe magana tare da dauƙo Coke na gwagwani ya ɓalle ya shiga sipping na ɗan sace kallonshi karaff muka haɗa idanu nai saurin kawar da kaina gefe ina taɓe baki.
Matsowa ya yi daff dani ya miƙo min Coke ɗin "Bismillah 'yan mata naga sai satar kallona kike yi kina haɗiyar yawu da dukkan alamu ta biya miki a rai.
A fusace na kalle shi tare da galla masa uwar harara cikin masifa da bala'in na ce "Ka ga bawan Allah karka nemi ka kaini bango nai maka rashin mutunci ba ruwanka da ni kayi sabgar gabanka.
'yar dariya ya yi mai sauti kafin ya ce "Ke kam kin cika masifa halan sunanki Hafsah?"
"Bansani ba.
Na faɗa a fusace har ina haɗawa da murguɗa baki.
"Mi kika zo siya na taimaka na karɓo miki domin na tabbata mutane nan ba raguwa za su yi ba sai ma su daɗa ƙaruwa?"
"Wai kai ba ka gane yaren hausa ne nace kyaleni banaso cusa kai ba kwarjini.
"Da gaske?"
Ya faɗa yana ɗage girar ido, sai kawai na kawar da fuskarta gami da murguɗa masa baki, ban ankara ba na ji ya wafce kuɗin hannuna yana faɗin "Yanzu kam kuɗinki sun shigo hannuna ko bakyaso dole ki faɗi abinda aka aiko ki siya.
Narai-narai nayi da idanuwa Kamar zan sa kuka cikin rauni murya na ce dashi "Sabulun wanki.
Saboda banida wani zaɓi da ya wuce na faɗa masa ko banza ba zan iya ratsa yawan mutane da ke shagon ba.
"Wane irin sannan guda nawa?"
Ya faɗa yana leƙen fuskata, muryarta can ƙasa na furta "Viva dozen ɗaya.
Ba tare da ya sake magana ba ya nufi ainihin cikin shago ba a ɗauki longtime ba sai gashi ya fito da leda baƙa a hannunshi ya miƙo min na karɓa ya sake miƙo min canji shima na karɓa gami da furta "Nagode!
Ina ƙoƙarin bari shago ya ce "Ji mana 'yan mata.
Na tsaya tare da waigowa.
"Ba ki faɗa min sunanki ba, ba ki Kuma tambaye nawa sunan ba.
"Sani sunana ba sauƙi ne dashi ba kamar yadda ka wafce min kuɗi, sannan kuma ka adana sunanka bana da buƙatar ji.
Daga haka na juyo cikin sauri na fice daga shagon, na nufi hanyar gida ina tafiya ina mita abinda ɗan baƙi saurayi nan mummuna ya yi min.
Bayan kwana uku da haɗuwata dashi na fito da yamma liss zan tafi kasuwa ina cikin tafiya saura kaɗan na isa titi ida zan hau keke napep na ji ana min horn da machine a bayana, banza nayi ina mai ci-gaba da tafiyata cikin natsuwa saboda ina da tabbacin ba akan hanyarsa nake ba tsabar iskanci ne kawai yasa yake min horn.
"Yan mata ki dinga tafiya kina waiwaya bayanki saboda machine ba ruwanshi da ke kyakkyawa ce buge ki zai yi ya rage miki sadaki.
Nan take na sheda murya mai magana shiyasa ma na kalleshi na watsar gami da taɓe baki ina faɗin "idan machine ɗin bai damu da kyawona ba ai ma mallaki machine ɗin ya damu tun da har ya iya tantance ni ɗin kyakkyawa ce a haɗuwarmu sau ɗaya takk!
Dariya ya yi tare da ya rage gudun machine ɗinsa yana tafiya slow-slow, "Gaskiya kam ba karya ke ɗin kyakkyawa ce domin tun lokaci da idanuwana suka yi tozali da ke tun daga ranar kawo yanzu bana cikin natsuwata kin hanani sukuni ki haddasa min...
"Dallah Mallam ya isa haka a'ahh!
Nai gaggawa katse masa hanzari ina maka masa uwar harara kamar ƙwayar idanuwana za ta diro ƙasa ta faɗo.
"Tirƙashi! Gaskiya ke kam masifaffiya ce irin wannan harara ai sai ki sare min ƙarfi guiwa.
Yayi magana tare da zuba min matsakaita idanuwanshi wanda zan iya cewa sune kaɗai farare a cikin halittar jikinsa.
"Uhmm!
Na furta ina kyaɓe baki.
Na dai san labarin gizo bai wuce na ƙoƙi ba duk wannan kame-kamen da yake yi ƙarshenta cewa zai yana sona.
"Ina za ki je da yamma nan ki ka ci irin wannan kwalliya salon wani yai min snatching.
Dama nasan za a yi haka shiyasa na juya a natse ina ƙare masa kallo sai lokaci na lura da kayan da ke jikinsa yana sanye cikin farin filtex material na maza irin mai taushi nan ɗinki boda kanshi ɗauke da baƙar hula ba laifi ya yi min kyau ainun, kun san dai tsarina ba son kyakkyawan namiji nake yi ba shiyasa ɗan baƙi saurayi nan na kan machine roba-roba yai awon gaba da rabin zuciyata. Tsakani da Allah ban taɓa cin karo da mummuna kamar sa ba, nan take naji nayi na'am dashi don shine ainihin kalar da nake wa kaina hasashe, kalar da ba wata ɗiya mace da za ta so sai kawai na saki mishi tattausan murmushi ina wani fari da idanuwa tare da faɗin "Kasuwa zan je ko kana da saƙo?"
"Kai haba! Ai kuwa faɗuwa ta zo daidai da zama nima Kasuwa na nufa hau mu je na rage miki hanya.
Ya ƙarashe magana gami da tsayar da machine ɗinsa yana nuna min bayan machine ɗin nasa da hannunshi.
Girgiza kai nayi ina masa kallon uku saura Kwabo haka kawai daga haɗuwar mu don ya yi insisting ɗina na hau machine ɗinsa, sai kawai na hau saboda gani Jeeddar mahaukata nufinsa kawai na ware ƙafafuwa na ɗale kai ina ba zan iya wannan kasadar ba.
"Yi haƙuri ɗan samari don kuwa ka taki rashin sa'a bana hawa machine.
"Haba wai da gaske kike yi?"
Ya faɗa yana min kallon mamaki.
"Ai ya wuce wai don ga zahiri nan ka gani.
Na ƙarasa magana gami da tsayar da adaidaita.
"Don Allah malam ka yi haƙuri ka tafi abinka mata ce mu sami misunderstanding ne shine tai fushi ta ƙi hawa machine ɗina.
Kamar daga sama na tsikayo muryarsa yana faɗawa mai adaidaita labarin ƙanzo kurege. Atoh dole nace Labarin ƙanzo kurege don bansan yaushe na zama matarsa ba. Kusan adaidaita uku na tara yana faɗa masu abin da ya faɗawa na farko zuwa lokaci raina ya kai maƙura wajen ɓaci, cikin fusata na ce dashi "Wai malam mikake nufi da ni ne?"
"Ba wani abu mai wahala bane na neman a gunki cewa kawai nayi ki hau machine ɗina.
"Gaskiya kai kam kana da matsala ina mamaki kai ba kurma ba amma ba ka fahimta abubuwa ciki sauƙi.
A tunanina zai hasala yai tafiyarshi ga mamakina sai kawai naga ya yi murmushi gefen baki ya ci-gaba da yi min magiya fahimtar nayi muddin ban hau machine ɗinsa ba zai kyale ni in hau adaidaita ba gashi kuma yamma sai ƙaratowa take yi ina jin tsoro a rufe kasuwa na haɗu da fushin Mama, bani da zaɓi da ya wuce na hau machine ɗin nasa har muka iso kasuwa yana zuba min fira tamkar ya shekara da sanina ni kan bayan uhmm ko a'a ba abinda nake cewa dashi a tunanina da ya sauke ni zai yi tafiyarsa saboda ina da yaƙini ya faɗi kasuwa zai taho ne don kawai na amince na hau machine ɗinsa, amma kuma sai naga saɓanin tunani nawa domin kuwa wurin da aka tanada domin ba da ajiyar ababen hawa ya kai machine ɗinsa duk ƙoƙarina nagani na shige cikin kasuwa sai da ya cimmin, muka jera side by side duk naji ni wani iri nakasa sakin jiki, ko ba komai ina gudun haɗuwa da idon sani ya ganni tare dashi ya je ya tseguntawa Babanmu.
Kasancewar underwears na zo siya asalima sune maƙasudin zuwa na kasuwa, sai Mama da zan siyawa kayan haɗin zobo da na kunun aya sai gashi na haɗu da wannan ɗan anace Sarkin naci mutum kamar mayye. Ni abinda yafi ɗaga min hankali bai wuce ta ya zan nufi shagon sayar da braziers da panties al'hali yana biye da ni gaskiya da kunya na siye waɗannan abubuwan tare dashi ai sai ajina ya zube a gabansa. Can dabara ta faɗo min na kalleshi cikin kwantar da murya nace "Mr bita zai-zai shagon Babanmu zan shiga saboda haka ka tsaya anan ka jira ni, saboda ba mutunci bane ya ganni tare da kai.
"Haka ne amma gaskiya karki daɗe domin idan naga kin yi shaƙo zan biyo sawunki.
Ya faɗa with serious tone.
"Karka damu duka ba zan wuce good 30 minutes ba.
"Shi kenan ki hanzarta please.
Na juya ba tare da na sake tanka masa ba, dama daga wuri da nace ya tsaya da shagon da nake siye underwears
babu tazara sosai sai dai ina da tabbaci ba zai gano inda na shiga ba domin sai da na fakaice idanuwanshi kana nai wuff na afka shagon.
Koda na shiga shagon 'yan mata uku na tadda a ciki suna duba braziers da panties bayan na gaisa da mai shago dama ya sanni saboda regular customer ɗinsa nake, nan take ya shiga jido min latest bra and panties na shiga duddubawa wanda ya yi min na kuma yarda da quality sa. Dozen biyu na panties na ɗauka mana bra Kuma na ɗaukawa kaina shidda Khairat kuma biyar.
"Yunusa waɗannan nake so miye price ɗin su?"
Na tambaye mai shagon tare da nuna masa kayan da yatsana.
"Panties kowane dozen ₦6k amma ki bada ₦5500 su kuma braziers ki barsu duka akan ₦8500.
"Cabdijam! Yunusa halan cin su ake yi da za ka zabga min wannan uban kuɗi?"
Na faɗa ina zaro idanuwa tamkar wacce taga abin tsoro kafin Yunusa ya bani amsa naji saukar muryarsa a bayana yana faɗin....

*Comments & share fisbilillah*

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now