052

99 9 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

052..

"Da kyau baƙar munafuka almura wacce bata da aiki sai haddasa fitina.
  Daga Aunty Bahijja har Hajja kallonshi suke yi baki buɗe domin maganarshi ta zo musu a bazata cike da mamaki Aunty Bahijja tai pointing ƙirjinta tana faɗin "Ni Bilal ni ka kira da munafuka almura?"
   "Ke ɗin ko kina da wani suna ne da ya fi wannan?" Ai Aunty Bahijja matuƙar ba ki tubarwa ALLAH ba ki ka nemi yafiyarmu ni da Jeeddah to kisani hakkin mu zai ta bin ki ne har izuwa cikin kabarinki da matuƙar wahala wutar jahannama bata ƙona ki ba saboda sunnah ma'aiki Sallallahu alaihi Wasallam! Ki ka raba.
Bilal Shattima ya faɗa yana huci yayin da yake ji wani irin takaici da tsanar Aunty Bahijja domin duk ita ce silar ruguza masa farin ciki.
  Da sauri Abbas ya ƙarasa kusa dashi ya ja hannunshi suka nufi three seater ya zaunar da Bilal yana faɗin "Calm down abokina Dan ALLAH ka danne zuciyarka yanzu ba lokaci musanya yawu bane saboda mai aukuwa ta ri ga da ta auku....
   "Daina bashi baki Abbas bar shi ya yi min rashin Kunya iya son ranshi, da gani yadda yake wannan haukar kasan ba yin kasa bane, har yanzu da raguwar asiri wancan 'yar matsiyatan a jikinshi.
  Wani irin zabura Bilal ya yi ya hayyaƙo wa Aunty Bahijja kamar zai rufe ta da duka sai faɗin maganganu marasa daɗi yake yi, sai da Hajja tai masa rantsuwa idan ban yi shiru ba ranshi zai ɓaci sannan ya koma akan kujera ya zauna sai ƙwafa yake yi akai-akai gami da girgiza ƙafa, yana sauke zazzafan numfashi Hajja ta dube shi cikin kakkausar murya ta ce "Ban kira ba don ka zo ka shukka min rashin ɗa'a anan ba. Na kira ne domin naji dalili da yasa ba ka ɗaga kiran matarka?"
A hasale ya ciro kanshi ya dubi Hajja adakile ya furta
  "Wacce daga cikin matan nawa?
Bilal ya faɗa yana shan ƙamshi tamkar ba da  Hajja da yake magana ba, sam babu girmamawa sai kace ba Bilal ɗin da yake daraja duk wani furuci da zai fito daga bakin Hajja ba. Amma sai gashi yau yana mata magana cikin gatsali.
   Sosai hanta cikin Hajja ta kaɗa domin ba ta taɓa tsammani fitar wannan tambayar daga bakin ɗa nan ta ba. Za ta iya cewa duk a cikin 'ya'ya da ta haifa Bilal yafi su yi mata biyayya tun shi na yaro ƙarami bata taɓa faɗa ya musanta mata ba. Sai gashi yau yana amsa mata magana gatsal-gatsal kamar yana magana da sa'an shi sani da tai wa Bilal ko Aunty Bahijja dake matsayin yayarshi yana girmama ta matuƙa balle ita da take mahaifiyar shi. Lallai biri ya yi kama da mutum maganar Bahijja akwai ƙamshin gaskiya a cikinta, in banda aiki asiri ta ya Bilal zai mata irin wannan tambaya. Danne mamakinta tayi ta ce dashi "wannan wacce irin tambayar banza ce ka ke min Bilal kana da wata mata ne da ta wuce Nusaiba?"
  "Ohhhh! Nusaiba wai.
Ya faɗa cikin sigar kamar idan mutum ya tunowa da wani abu da ake so ya tuna.
Nusaiba wacce take rakuɓe a jikin bango ta rushe da kuka domin tun shigowar Bilal taga yana yi da ya shigo dashi ta sha jini jikinta, yanzu kuma da ta ji abinda ya faɗa yasata fashewa da kuka domin har ga ALLAH tana son Bilal Shattima ba ta da buri da ya wuce ta shiga tanfatsetse gidan da ya gina musamman yanzu da ta ji labari ya saki Jeeddah har tana murna za ta ci karenta babu babbaka sai gashi tun ba a je ko ina ba murnarta tana ƙoƙari komawa ciki domin uban gayya ya zo mata da wani sabon samfuri wanda zuciya da gangar jikinta ba za su jure ɗaukar shi ba.
   "Ke dallah! Rufewa mutane ƙaton bakinki.
Bilal ya dakawa Nusaiba rikitatciyar tsawa wacce ta gigita ta babu shiri ta haɗiye kukanta, gami da dafe bakinta da ya kira da suna ƙato. Hajja ta kalle shi ranta ya kai ƙololowa wajen ɓaci, ta ce "Daina yiwa 'yar mutane tsawa ni ya dace kayiwa tsawa ba ita ba.
   "Ko kuma ya zo ya rufe ki da duka ba don naga wani rashin mutunci yake taƙama dashi.
Aunty ta faɗa tana danna mishi ƙatuwar harara.
Zuciyar Bilal tana tafarfasa ya kalle gun da Aunty Bahijja take cikin kakkausar murya mai cike da alamar gargadi ya ce
   "Aunty Bahijja ki fita sabgata ko na ta-ta miki rashin mutunci tun daga ranar da kika zama silar rabani da matata farin cikina na daina gani ƙima da darajarki Wallahi-azim idan ki ka kaini bango ko dukanki zan iya gara ki rufawa kanki asiri ki raba kanki dani.
    "Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Bilal Bahijja ce za ka daka yayar taka ce za ka daka? Lallai Bilal ba ka hayyacinka ALLAH ya isa tsakanina da Jeeddah da zuri'arta.
Hajja ta faɗa tare da rushe wa da kuka Aunty Bahijja tana tayata, duk yadda Abbas yaso ya yi sulhu a tsakaninsu ya kasa a fusace Bilal Shattima ya miƙe tare da kakkaɓe rigarshi yabar musu gida. Abbas ya tsaya yana rarrashinsu domin gaba ɗaya sun cika falon da koke-koke sai kace gidan mutuwa da yaga lamarin nasu ba mai ƙare wa bane ya bi baya Bilal har suka iso gidanshi yana yiwa Bilal nasiha da yabi komai a hankali.
   Tun lokaci da Engineer Ameer ya iso gidanshi yake kwance akan sofa dake girke a falonshi furuncin ummarshi ke mishi kai komo a ƙwaƙwalwarshi idan har ummarshi ta kafe lallai sai ya rabuda Jeeddah ba shakka za su yi baƙin arbo domin gani da ya yi mata a yau ɗinan ya ƙara linka mishi zazzafar soyayya da yake mata a shirye yake da ya yi fito-na-fito da duk wanda ya nemi ya yi mishi katanga da ruhinshi domin Jeeddah ita ce rayuwarshi ba ya jin akwai wani mahaluki a doron kasa da ya isa ya yi mishi shamaki da cikar burin shi.
   "Jiddoh ki tashi ki ci shawarma saboda ke na siyo kin ga Khairat tana ƙoƙarin cinye wa ki tashi Dan ALLAH ki ci ko kaɗan ne kada ta cinye.
   Ya Haidar ya yi min magana cikin sigar rarrashi domin tun yamma da muka yi hatsaniya da Khairat nake shan ƙamshi na kasa bari jin haushinta, gani yadda Ya Haidar yake ta faman yi min magiya yasa na tashi zaune ina yatsine fuska Khairat dake zaune akan plastic chair tana cin shawarma ta waigo ta kalleni ta taɓe baki kana ta ɗauke kai. Yanayi kallo da tai min ba ƙaramin sosa min rai ya yi ba, amma shiyasa ba kwafa gami da kwaɗa wa ƙeyarta harara duk abinda nake yi Ya Haidar yana tallaɓe da kumatunsa yana kallona yana sakin murmushi duk yadda naso ya bani shawarma naci da kaina yaƙi dole sai ya yi feeding ɗina ba yadda na iya dole na buɗe baki ya dinga bani.
A takaice kwana uku a asibiti aka sallame ni duka cikin kwanaki uku ɗinan Ya Haidar yana tare dani duk wasu ayyukan shi masu muhimmanci ya jinginar dasu, ta ɓangare Engineer Ameer shima har aka sallame ni yana shigowa ya duba ni wani sa'in har sau biyu yana shigowa a rana Bilal ne dai bai ƙara zuwa ba sai a ranar da za a sallame ni ya shigo da safe yayin da aka sallame ni da yamma. A maimakon Ya Haidar ya kaini gidanmu sai ya wuce dani gidansu kasancewar shi da Aunty Farida ne sa'ili da aka yi discharge ɗina Kuma dama can bakinsu ɗaya shiyasa koda na nuna na fiso ya kaini gidanmu Aunty Farida taƙi goyon bayana cewar ta gara na zauna gidansu domin gudun gulmar 'yan unguwarmu. Koda muka iso har Mommy tasa musu aiki sun gyara min ɗaki da zan zauna ba abinda babu na dangin kayan more rayuwa a ɗakin ƙiri-ƙiri aka cilasta min zama gun da bani da ra'ayi zama. A tunanina Ya Haidar ya yi haka ne domin ya sauƙaƙawa kanshi cimma manufar shi akaina sai naga saɓani tunanina domin tun ranar da na zo gidansu ban sake sanya shi a Idanuwana ba. Sai dai ya kira wayar Mommy ya ce abani ya tambaye ni ya jikina daga haka zai kashe wayarshi. Sosai Mommy take kula dani gami da tattalina ko kaɗan bata bari na cikin kadaici koda yaushe tana tare dani idan ka ga ta gusa daga guna Daddy ne ya dawo. Ta ɓangare Bilal raba dare muke yi muna waya a sati na biyu da rabuwar mu yake bani labari wai ya siyar da gidan da ya gina a cewar shi tun ALLAH bai nufa na tare a cikinsa ba. Saboda haka bai ga amfaninsa sai wani ƙarami ya siya wanda ko kwata kyau da haɗuwar wancan bai yi ba domin wancan upstairs ne wannan kuma flat ne three bedrooms and two parlours lokaci da labari ya je kunne Nusaiba kamar za tai hauka sai dai bata da yadda za ta yi  tsabar baƙin ciki ko walima da tai niyar yi fasawa tayi a haka ta tare, a dare da ta tare sai around 11 o'clock Bilal Shattima ya shigo ko kallon arziki bai haɗa shi da ita ba ya ajiye mata kaji da ya siyo akan bedside ya wuce bathroom ya yi wanka koda ya fito daga wanka ya tarar da ita jingine da bango bathroom, kallo ɗaya yai mata ya ɗauke kai wani kafiri haushinta yake ji yana kammala shiryawa cikin kayan baccinsa ya ɗauki wayarsa ya dawo parlour.
   Yayin da ni kuma yini ranar cikin baƙin ciki nake domin Bilal ya sanarda ni ranar Nusaiba za ta tare har kuka sai da nayi da mommy ta ga idanuwana sun yi jajir da ta tambaye ni sai ƙarya na shara mata ta hanyar cewa kaina ne ke min ciwo hankalinta duk ya bi ya tashi ta ɗaga waya ta kira family doctor ɗin su ya zo gida ya duba ni.
Bilal Shattima yana fitowa parlour ya nemi three seater ya kwanta ya yi dialling number Jeeddah yini yau gaba ɗaya ya kasa gane kanta, lokaci da kiran Bilal ya shigo wayata ina kwance  a ɗakin da ya kasance nawa a gidan a duk lokaci da na tuna cewa yau Bilal zai kwana da Nusaiba a gida ɗaya a ɗaki ɗaya, akan gado ɗaya sai na ji zuciyata tamkar za ta tarwatse.

#Jeeddah Aliyu
#Team Bilal Shattima
#Team Haidar Ka'oje
#Team Engineer Ameer
#Zazzafan kishi
#Sabon Salo

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon