020...

93 8 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*
_{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku ta karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune Kamar haka*
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

Ina matan da suka amsa sunansu mata ba muna mata ba, gare ku haɗaɗɗun mata 'yan gayu da suka san kansu??
Ku garzayo domin farantawa mazajen ku rai
Ta hanyar ƙamsasa jikin ku da nau'ukan turarukan mu.
Muna da turaren miski mai kyau ɗan Sa'udiyya
Akwai oils perfumes masu dan ƙaren ƙamshi da ɗauke hankali maigida muna da na kamfanonin da suka amsa sunan su irin su :-
Kamfanin
Almas
Surrati
Naseem
Sannan da na fesawa
Kala daban-dabam
Duk a IHSAN COLLECTION'S and More
Muna turawa ko wanne gari 😊😊 domin ƙula hulda kasuwanci damu sai a tuntuɓe a waɗannan lambobin
08036487230
09071926759

020...

Yau tun da sassafe Jeeddah ta tashi sakamakon sauƙin da take ji jikinta yai mata, duk da haka adaddafe ta kammala shirinta na tafiya makarantar da take koyarwa. Kasancewar tayi kusan four weeks bata je ba sakamakon rashin lafiyar da take fama dashi, damuwarta ɗaya principal ɗinsu da ba kasafai yake karɓa uzuri ba. Shiyasa tun jiya da ta ji jikinta ya yi kwari sosai tasa aranta yau za ta je school ɗin musamman da ɗalibai sun kusa su fara third term examination ta kagara ayi hutu kafin a koma cikinta ya shiga four months watakila zuwa lokaci laulayi da take yi zai ragu.
Tana kammala shirinta ta nufi kan gado inda basaraken nata ke kwance yana aikin nasa na bacci. Cikin kwantar murya ta shiga kiran sunanshi gami da ɗan bubbuga damtse hannunshi "Love.....Love! Na kammala shirina ka tashi ka sauke ni school dan Allah ka tashi mana kada nayi latti.
Ta ƙarasa magana cikin marairaicewa tamkar wacce ta tashe yaron goye tana tsoron kada yai mata kuka.
Ya tashi zaune yana yatsina fuska muninsa ya ƙara bayyana dama mutum mai muni idan ya tashi daga bacci fuskarsa batada kyau gani, hancin nan nasa ya ƙara maƙalewa can sama cikin murya wadda bacci bai wadace shi ba ya ce "wai miye haka ne Love?" ke dai wallahi ba ki ƙaunar ki ganni kwance ina bacci sai kin ƙiƙƙiro dalilai da zai sa ki tashe ni.
"Ka yi haƙuri Love ba haka kawai na tashe ka ba dama so nake ka aje ni school, kasan rashin fuel ɗinan da ake yi abin hawa na da matuƙar wahala samu musamman da safe.
"OMG! Yanzu fissibilillah Jeeddah saboda tafiya school ne yasa kika katse min baccina bayan kinsan na tsani ina bacci a tashe ni?" Yanzu nan sai ki jawo min headache kina wani zance rashin abin hawa kin fita ne ba ki samu ba balle ki yi complaint ki je kawai In-sha-Allahu za ki samu ki jirani zan zo ɗaukar ki.
Ya faɗa gami da komawa ya kwanta har da jan duvert ya lulluɓe jikinsa, sosai ta ji ba daɗi a ranta ta zaci zai yi duba da ba wadatatciyar lafiya ce da ita ba ya kaita school ɗin in yaso idan ya kaita ya dawo ya ci-gaba da baccin nasa. Amma sai taga saɓanin tunaninta, ta miƙe jikinta a sanyaye ta ɗauki handbag ɗinta ta buɗe ƙofa tana dab da fita ta waiga ta kalle shi ya bata baya sai kawai taji zuciyarta ta karaya wani ɗan maraye kuka ya subuce mata, tai sauri maida ƙofa ta rufe gudun kada ta haɗu da ɗaya daga cikin neighbours ɗinsu su ganta tana kuka, ya zama abin tsegumi shiyasa ta gaggauta goge fuskarta da gefen hijabin jikinta. ALLAH ya taimake ta tun kafin ta ƙarasa bakin titi ta sami adaidaita, ƙarfe takwas dai-dai tana cikin makaranta, duk wadda ya kalleta farat ɗaya zai gano akwai damuwa a tattare da ita duk jikinta ya nuna bata da wadatatciyar lafiya amma hakan bai ɓoye damuwar da ta ciki ba. Cikin hukunci Ubangiji har aka tashi bata yi amai ba sai miyau ne kawai da take ta faman zubdawa akai-akai. Daidai inda Bilal Shattima ya saba tsayuwa idan ya zo ɗaukarta ta nufa saidai bata ganshi ba, sai kawai ta fito da wayarta daga handbag tai dialing numbershi wayar tana ringing har ta tsinke bai ɗaga ba. A takaice sai da tai mishi kira da ya kai goma bai ɗaga ba. Ranta yai matuƙar ɓaci a hasale ta maida wayar jakka kana ta nufi gate ɗin fita duk gaisuwar da maigadi ke mata bata iya amsawa da baki ba sai hannu ta ɗaga masa. A gefen titi ta tsaya tana jiran abin hawa duk adaidaita da ta tsayar yana ɗauke da passengers ko kuma ya ƙi tsayawa sai kace abin magani ga jiri sai ɗibarta yake ga 'yar uban rana na kuɗarta, tun tana iya tsayuwa da ƙafafuwanta har ta zo tsayuwar na neman gagararta gani haka yasa ta soma tafiya a hankali a gefen titi, tana tafe tana tofar da yawu da ke cika mata baki. Tafiya tai mai nisan gaske kuma har zuwa lokaci bata sami abin hawa ba. Wani irin murɗawa cikinta ke yi mata ga wani irin amai da ya turnuƙe ta da sauri ta gangara gefen titi inda babu kwalta ta durƙusa ta shiga kwara amai mai kumfa a dalili bata ci komai ba. Sosai take kakkari tun tana fitar da kumfa har ta zo ba abinda ke fita sai azabar murɗawa da cikinta ke mata kamar hanjin cikinta zai tsin-tsike, sannu a hankali ta fara gani duhu yana mamayewa ganinta numfashinta nayi sama-sama tun tana iya fizgar numfashin nata har ƙarfinta ya ƙare ta ji komai ya tsaya mata cakk ta sulale ƙasa ɗan raguwar numfashinta ya bar jikinta. Gashi idan ta faɗi babu mutane sosai a dalili rana ta take, ba kasafai mutane ke wucewa a ƙafa ba. Sai dai masu wucewa akan ababen hawa, su kuma ba lallai bane su ganta ba.
A hankali ya gangara da motarsa gefen titi a dalili kira da ake yi wa wayarsa ƙa'idasa ce baya receiving call idan yana driving, gani yadda abokinsa Umar ke kiransa babu kakkautawa daga kiran ya tsike zai sake kira, hakan ya tabbatar masa da kiran nashi mai matuƙar muhimmanci ne sai kawai gangara gefen titi yai parking domin ya amsa kiran nashi, yafi 10 minutes yana magana da Umar kafin ya ajiye wayar yana ƙoƙarin yi wa motar key ya hango ta yashe a ƙasa, shiru ya yi yana nazarinta yanayin suturar jikinta da kuma handbag ɗinta da ke yashe a gefenta ya tabbatar masa da mai hankali ce ba mahaukaciya ba. Da sauri ya ɓalle ƙofar mota ya fito sanye yake cikin shadda royal blue in colour babu hula akansa, sumar kansa baƙa wulik akanannaɗe ta kwanta luf-luf gwani sha'awa kyakkyawar fuskarshi ma'abuciya kwarjini ɗauke da kwantatce saje mai haɗe da gemi wadda tsawonsa zai iya kai kamu ɗaya da rabi bima'ana gemin nasa yana da tsayi sai da ba irin sosai ɗinan ba. Dogo ne fari tass yana yi tafiyarsa kaɗai zai tabbatar maka da shi ɗin mai ƙarfi ne domin ya tara kwanji duk da shadda ce a jikinsa hakan bai hanawa muscles ɗinshi bayyana ba. Ya soma tattaki tare da nufar wurin da take kwance duk taƙonsa ɗaya sai ya ji matsanancin faɗuwar gaba zai iya cewa tun rasuwar matarsa rabon da ya ji faɗuwar gaba makamancin wannan.
Yana isa wajenta ya sunkuya saitin inda fuskarta yake hijabin jikinta ya rufe mata fuska shi ya hana shi gani ainihin fuskarta ta, cikin zazzaƙar muryarsa ya ce "Bawar Allah lafiya kike kwance a gefen titi idan ba ki da lafiya ki ƙoƙarta ki isa gida, kwanciyarki anan ba daidai bane, kina ji na kuwa?"
Jin shiru bata amsa ba yasa ya yi kasadar kai hannunshi da nufi jaye hijabinta da ya hana shi gani fuskarta, hannunshi yana sauka akan hijab ɗinta faɗuwar gabansa ya ƙara tsananta kasancewar shi namiji shiyasa ya danne abinda yake ji. Sannu a hankali ya janye hijab ɗin. Fuskarta ta bayyana idanuwanta a rufe ruff, yayin da ya ƙura mata nashi idanuwa tsawon lokaci ya ɗauka yana kallonta kafin ya ja iska daga bakinsa ya fesar sai lokacin ya lura da babu numfashi a jikinta, yai sauri durƙusawa ya kama hannunta bai tsaya wata-wata ba ko neman taimakon wani ba, ya cicciɓe ta cakk ya nufi motarsa da ita a backseat ya shimfiɗe ta kana ya koma ya ɗauko mata handbag da takalminta da suka zame daga ƙafafuwanta. Cikin gaggawa ya zagayo ya shiga mota ya fizge ta da ƙarfi ya haura kan titi, kaitsaye wani private hospital ya nufa da ita cikin gaggawa suka karɓe ta babu ɓata lokaci suka dukufa dubata, ɗaki na musamman aka kaita tare dasa mata drip sai lokaci da yaga numfashinta ya dawo normal hankalinsa ya kwanta. Yayin da ita kuma sai sharar bacci take abinta.
*After some hours*
{Bayan wasu awanni}
"Congratulations sir madam tana ɗauke da three months pregnancy.
Doctor ɗin ya faɗa sa'ili ya da aka kawo masa test result ɗin ta, shine ya aika ɗaya daga cikin nurses ta kira masa shi.
"Ba matata bace.
Yai sauri katse Doctor ɗin bai kuma karɓi result ɗin da yake miƙo masa ba. Da alamun ranshi ya ɓaci da dangantashi da ita da likita ya yi.
Gani yadda doctor ya tsare shi da idanuwa yasa shi cewa "Doctor bani da wata alaƙa ko dangantaka da ita tsintar nayi yashe a gefen titi shine na taimake ta na kawo ta asibiti, saboda haka ka ajiye result ɗin a wurinka kafin mijinta ko 'yan uwanta su zo.
Daga haka ya buɗe ƙofar ofishin likitan ya fita, kaitsaye ɗakin da take kwance ya sake komawa har yanzu bacci take yi numfashinta yana sauka a hankali alamun samuwar sauƙi.
Ya jawo plastic chair ya zauna saitin da yake iya gani fuskarta.
Can ya tuna da handbag ɗinta da ya baro cikin motarsa ya tashi da sauri ya fita jin kaɗan sai gashi ya dawo ɗauke da takalma da handbag ɗinta, ya zauna inda ya tashi ya yi zipping handbag ɗin wayarta ya dauƙo saidai kash! Wayar na ɗauke da security code ya ja ɗan siririn tsaki ya tsani wannan ɗabi'a da mutane ke yi na sakawa waya security code, yanzu ina amfani ga waya amma ba hali ya kira wani nata. Tun lokaci da ya zauna dai-dai da second ɗaya bai ɗauke idanuwanshi daga kanta ba. Kamar daga sama ya ji vibration ɗin waya akan cinyoyinshi da sauri ya kai dubanshi ga wayarta love shine suna da ya gani yana yawo akan sensor ɗin wayarta, a natse ya yi picking up...

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now