023

78 11 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

Assalamu Alaikum Manyan mata masu kayan harka . Yau kuna tareda Manzil Alwafir Rep/ delegate . Sunana Gimbiya Hassana Abdullahi

Mata da dama su Kanyi Korafi hade da cewa basuda *taste* mata na shiga damuwa har ta Kai ga qaurace ma junansu Sabida wasu Dalilai .
Wadannan dalilai suka sa Manzil Alwafir ta ga ya kamata ta wayar ma ma’aurata Kai (Awareness kenan) domin a magance matsalolin/ rage samun mace macen Aure da matsalolin da ke damuwar mata agidan aure .

Kada ku manta da cewa acikin abincin mu Allah (SWT)ya sanya abubuwa da yawa acikin su, masu Bamu kariya da N’iimta ajikinmu

Jikin ya’ Mace ya kasance abun so ga da’ Namiji a kowanne lokaci.

Daga lokacin da mace ta rasa darajar Farjinta ma’ana ta barshi ba gyara ba kulawa tamkar ta warware passion da intimacy tsakanin ta da mijinta ne.

Products din manzil sun kasu kashi kashi ( categories ) kaman haka ;

*Qarin Niima* - Muna da su kala kala kaman su = Amor Carino ,Asta,smoked heaven, Vibrationzz, tsumi,Back 2 honeymoon, Taurariya,Swan, Bomb oil ,Anwar da Yaqtur.

*Matsewar Gaba* - *Matsi* -    Kaman su-Harisa,Helwa, tightening honey,Dorot,tighten Herbs da Kazar mata.

**Kuzari da shaawa** -HD-Tea,Tea 01, 3rd Avenue, Exclusive honey, Deep sea , ginseng , Nashwa

*Basir kit*- Pile kit &Yoni Herbs

*Infection kit*- infection curing herbs da Sanyi detox herb. Infection yana lalata Niimar Mace ya hana ta Jin sha’awa sannan ya saka mata bushewar gaba da rashin gamsuwa

**Mens Aphrodisiac** Yajin maza, Cold stone , Mens Magnet. Persion hot

*Jego package* - joy stick,Kazar mai jego,yajin jego da sauransu

Domin qarin bayani Zaa samemu a 08036072970/ 08121555525 call/WhatsApp
Taku har kullum *Manzil_ Alwafir Rep*.
*Maman zahra* 💝

023...

Kaman zai yi magana sai kuma ya haɗiye abarsa, ya raɓa gefenta ya wuce zuwa bedroom, raina ya ƙara ɓaci fiye da farko na bishi da mugun sauri yana shiga ɗaki ina shigowa har wani huci nake yi yayin da ƙirjina yai min nauyi kamar an danne min shi da ƙaton dutse, cikin ƙunar zuciya nace
"Bilal gara ka faɗa min daga inda ka fito saboda shi ne kwanciyar hankalinka a gidanan.
   Fasa ƙarasa cire rigar jikinshi ya yi ya juya a fusace ya ce "Jeeddah banaso iskanci ki dawo hankalinki ke duk yadda za ki nemi masifa dani kinsani, wai kin manta da wulaƙanci da kika tatamin ɗazu ne? Saboda reni wayau shi ne har kike da zarrar tarɓe ni da wani sabo.
  "Idan har kana da gaskiya ka faɗa min daga ina kake sa'anan me ya tsayar da kai har tsawon wannan lokaci?"
Murmushin takaici ya yi kafin ya ce "Ai wuyanki bai yi kaurin da za ki min titse ba idan kuma kina gani isarki ta kai taho ki matse bakina ko kiyi min duka watakila idan na ji zafin duka na faɗa miki.
Yana ƙarashe magana ko kallona bai sake yi ba balle ya ga yadda idanuwana suka ciciko da hawaye ya shige bathroom abinsa sai faman jan numfashi nake yi duk yadda naso na hanawa kaina kuka hakan ya ci turu. Domin bansan lokaci da na durƙushe ƙasa na saki maraya kuka wani irin kishi ke cina a zuciya bansan iya adadin lokaci da ya share a bathroom ba sai ƙarar buɗe ƙofa na ji, yanzu ma raɓa ni ya sake yi ya nufi dressing mirror ya goge jikinsa ya yi 'yan shafe-shafensa kana ya saka kayan baccinsa, gaba ɗaya ɗakin ya gauraye da ƙamshin turarensa. Yadda ya nuna min halin ko in kula yaƙara min haushi, sai kawai na ƙarawa kukana sauti, duk da haka bai bi ta kaina ba ya kashe wuta ya haye gado harda su shigewa cikin duvert. Sai da nayi kuka na mai isata kafin na rarrashi kaina domin wanda nake yi kukan domin shi tuni ya yi bacci abinsa ya barni da tafarfasar zuciya. Abinda na fahimta kwata-kwata Bilal Shattima ya daina damuwa da damuwata wato nufinsa ko na mutu ko nayi raina ruwana. A maimakon na kyaleshi sai kawai na miƙe na nufe wurinshi ina cika ina batsewa wata sabuwa masifa nake ji in takaice muku labari a daren ranar daga ni har shi ba wanda ya yi bacci kirki kwana muka yi muna gubza faɗa kamar wasu sababbin ƙarnuka. Hakazalika a washegari ma haka muka tashi sai da muka share kusan mako ɗaya muna faɗa kafin mu daidaita kanmu amma fa na sha alwashi ba zai sake ɗibar min abinci ya kai gidansu ba. Shi kuma tun daga wannan lokaci ya ƙaurecewa ci abincina hatta a shimfiɗa ba ruwansa dani, yayin da ni ma ko a jikina tafi nono fari gara kowa ya riƙe kayansa.
A haka rayuwarmu ta ci-gaba da gudana kullum cikin faɗa da gani laifin juna muke, har ta kai ta kawo maƙota suka san hali da muke ciki, don ba zan manta ba a wani dare da faɗa ya kaure a tsakaninmu har da neighbours ɗinmu sai da suka shigo zance a dalilin kuwa bai wuce na duba wayarsa naga yana chat da Nusaiba 'yar ƙanin mahaifinsa duk da chat ɗin nasu ba na soyayya bane amma ba ku ga yadda na tashi hankalina ba. Da kyar da shudin goshi suka shawo kaina na haƙura.
Sannu a hankali cikina ke daɗa girma gashi har ya shiga wata na takwas amma har zuwa wannan lokaci ko ɗan kafai Baby Bilal Shattima bai siye ba kuma ga dukkan alamu bashi da niyar siya. A wani dare ne har mun kwanta bacci abin ya motso min na tashe shi da yake nayi ta haƙuri ina kallon gudun ruwanshi, domin na zaci ko da munafuci ne zai yi min magana amma ya yi shiru abinsa. "Ya aka yi ne Love ko ba ki da lafiya ne?"
Ya faɗa sa'ili da ya tashi zaune don ni tuni nake a zaune nai mugun ɗaure fuska, gudun kada ya kawo min wargi.
  "Love na gaji da zuba maka ido gara na fito fili nai maka magana domin wannan hali ko in kula naka ya yi yawa.
"Wacce magana ce wannan da ba za a yi min ita ba sai a tsohon dare?"
Sai da na kare wa mummunan fuskarshi kallo musamman da naga yana wani yatsinarta, da yasan yadda ya motsar fuska ke bayyana da muninsa tsakani da ALLAH da ya haƙura ya bar wa wanda yake yi wa kyau su yi. Kafin na ce "Dangane da zance kayan haihuwa da kowane maigidanci yake siya sa'ili da matarsa take ɗauke da ciki musamman ni da wata mai zuwa ne EDD na zai cika.
   Sai da yai min wani kallo wanda zan iya kiranshi na wulaƙanci, don har wani taɓe gungurumin baki yake kafin ya ce "Gaskiya Love kina da matsala na rasa gane abinda yake hawa kanki infact su kayan haihuwa ɗin da kike magana akai ba da kuɗi ake siyensu ba tuni kika kwana da sani banida shi, idan ba neman magana ba miye na tashina cikin tale-talin dare.
   "To shikenan ba ka da shi abin nufi anan haka za ka yi ta zama ba za ka nemi sana'a ba, sai dai kullum idan aka yi magana sai ka bugi ƙirji kace baka dashi, na fahimci har alfahari kake yi da babu ɗinan.
  "Ya isheki Jeeddah karke sake ki faɗa min maganar banza, ai tun kafin na aurenki kinsan bani da aiki kika yaudare ni da mayaudaran kalamanki na aurenki kafin mu yi aure ba cewa kika yi za ki ɗauki hidindimo gida ba?" Shi ne yanzu don tsabagen reni wayau za ki tashe ni cikin tsakiyar dare kina min zance kayan haihuwa. Shin bari na tambayeki miye amfani salary ki da kike bugun gaba dashi da ba za ki iya siyawa ɗanki ko 'yarki kayan sa wa ba ko kuma ki faɗawa hamshazaƙai gidanku su yi miki?" Babanku ma yana da shagon siyarda kayan jarirai ba sai ki faɗa masa ba, ya taimaka kamar yadda ya saba taimakawa ai shi aikin lada ba a gajiya dashi.
  Sosai na harzuƙa da jin waɗannan maganganu nasa, domin har wani zafi can ƙasan zuciyata ke min. ALLAH shi ne shaida ta na fara gajiya da halin Bilal Shattima ta ya duk lokacin da nai masa magana akan abinda ya shafi rayuwarmu sai ya dinga faɗa min maganganu banza. Cike da zallar masifa na hayyaƙo masa "Dallah dakata Bilal! Kai wane irin mutum ne mai matatciyar zuciya, shikenan tun da na ɗaure kaina nace zan dinga ɗaukar responsibilities ɗinmu shine zai ba ka damar ka watsar da neman dogara da kanka, wato kai nufi ni da Babana za mu ta yi ma hidima har ƙarshen rayuwarka? To wallahi idan ma haka zuciyarka ta kimtsa ma gara ma tun wuri ka falka, don ni manufata na ɗan lokaci ne kuma da kake zance Baba babu inda ALLAH ya ɗora masa ɗawainiyarka da ta ɗa da zan haifa.
Kuma ma ai yadda muka yi da kai zarrar mu yi aure za ka nemi koda sana'ar hannu ce ba dole sai aikin gwamnati ba. Amma kai kwata-kwata ba wanna a gabanka to wallahi gara kasani na gaji, Baba kuma ba zai sake taimaka maka da ko kwaldala ce ta ya zan ɗauki nauyi kaina kana na buge da hidintawa 'ya'yanka da ke tafe?"
   Shima jin abinda na faɗa yasa shi hasala ya shiga faɗar maganganu banza nima ina mayar masa da martani a wannan daren sai da muka yi kaca-kaca kafin kowanne mu ya kwanta gami da juyawa juna baya.
Washegari na shirya naje gidan Khairat domin na dubata saboda ta kwana biyu tana faman da zazzaɓi don har drip aka sa mata a gida, daga zuwana fira ta ɓarke a tsakaninmu har muka gangaro akan zance haihuwa da yake cikinta yana gaba da nawa domin ita this month EDD ta ni kuma sai next month.
Daga nan ta shiga nuna min 'yan uban tuli kayan Baby da Jameel ya siya mata ita da unborn child ɗinsu, ga kyau ga tsada sai kallo nake yi ina girgizar kai tare da yabawa a lokaci ta ke tambayata wane tanadi muka yi, tsakanina da Khairat babu ɓoye-ɓoye kaitsaye na fito na faɗa mata gaskiya ko abinda kare bayaso ba mu siya ba. Kuma Love ya ce bashida kuɗi na siyawa kaina ko kuma Baba ya bani. Ba ƙaramin kaɗuwa tayi ba har dasu salati da tafa hannuwa, ni dai sai aikin kallonta nake yi "Haba Jeeddah ai mai zurfin ido da wuri yake fara kuka ko masu babban ƙarfi da wuri suke fara tanadin zuwan haihuwa.
  "Me kike so nayi Khairat ni fa gaskiya nagaji da halin Bilal Shattima fissibilillahi mutum ace ba zai iya tabuƙa komai ba?
   Sai da Khairat ta saki murmushin gefen baki kafin ta matso kusa da ni gami da dafa ƙafaɗata cikin taushin murya ta  ce "Jeeddah kema kinsan ba abinda Bilal Shattima zai iya yi domin shi ba aikin gwamnati ba bai da kuma sana'ar hannu to da me kike so yai miki hidima ko so kike yi yai sata ya kawo miki? Tun farko abinda kowa yake guje miki kenan kika kafe sai shi.
Cikin sauri na katseta ta hanyar cewa
"Dan Allah Khairat abinda ya wuce ki daina tadda shi idan ma kuskure ne na ri ga na tafka shi yanzu hanyar warware shi nake nema don gaskiya ba zan iya ci-gaba da hidimar gidan Bilal Shattima ba. ke abinda ba ki sa ni ba yanzu haka fushi yake yi dani a dalili kawai na ce ya daina kwashe foodstuffs ɗin da Baba ke aiko min yana kai ma Hajja da Aunty Bahijja shikenan fa ya tsire fushi dani, yanzu haka ya daina cin abincina ya daina kusanta ta ni kuma wallahi ko a jikina..

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now