028

89 12 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

028...

Cikin kakkausar murya Bilal Shattima ya ce "Karki fara mommy billahill-azim kada ki sake hannunki ya sauka a fuskar mahaifiyata. Zan iya jure kowanne irin wulaƙanci daga gare ku amma ba zan lamunci wani daga cikinku ya ɗaga hannu ya dake mahaifiyata ina kallo ba.
   "Yawwa ɗan albarka gaya musu dai idan kuma su ka yi wasa, ka tsitsika igiyoyin aure 'yarsu ba abinda za a yi.
Cewar Hajiya Bintu tana murmushin gefen baki da za a tona zuciyata da an ga zallar farin ciki da take ciki ita fa bata ƙi ta kwaɓe musu gaba ɗaya  burinta a mutu har liman.
Mamaki ne ya kama Mommy da Mama sai kallon fuskar Bilal Shattima suke yi, cikin kaɗuwa mommy Turai ta tambaye shi "Bilal ashe rashin ɗa'ar naka har ya kai har haka? Kafin ya bata amsar tambayarta Ya Kabeer ya iso wajensa a hasale yasa dukkan hannuwanshi biyu ya daki ƙirjin Bilal dasu tare da ture shi ya yi tangal-tangal zai faɗi Abbas dake tsaye a bayanshi ya taro shi yayin da Ya Kabeer ya nuna shi da yatsa yana faɗin "Wannan shi ne kuskure mafi muni da za ka aikata a rayuwarka, bari na tambaye ka Bilal ka kuwa san wacece mommy Turai ka san irin matsayin da take takawa a wajen Jeeddah da har za ka buɗe baki ka faɗa mata maganar rashin ɗa'a, lallai Bilal bakada mutunci ko kaɗan?"
   "Ita ba mahaifiyata ta faɗa ma maganar banza ba ko kuwa uwa ta fi uwa ne?"
Bilal Shattima ya faɗa cikin ɗaga murya.
Gani al'amari yana so ya yi ƙamari yasa babu shiri Hajja ta jawo hannun Bilal cikin kwantar da murya take faɗin
  "Ka ga Bilal kada ka biye musu ku zama abu ɗaya dama abu kaɗan suke jira su shiga rigar mutuncinmu, su yaga ta saboda haka kar na sake jin bakinka ta lafiyar matarka muke yi ba wannan saida halin ba.
"Amma Hajja sai na zuba musu ido suna cin mana mutunci?"
Karaf mommy Turai ta karɓe zance ta hanyar faɗin "matsiyaci irinka mai matatciyar zuciya har wani mutunci ne dashi ai tun da ka yi sake zuciyarka ta mutu ka zo ka tare gindin mace ba ka siɗi ba ka saɗa, wallahi ka dinga gani cin mutunci da wulaƙanci iri-iri kenan.
Wata nurse ce ta taso ta nufo wajensu da nufi taka musu birki taga abin nasu ba mai ƙarewa bane. Cikin faɗa gami da tsawa ta ce "Haba! bayin ALLAH nan fa asibiti ce ba kasuwa ba ko kuma gidan biki tun ɗazu na zuba muku ido ne don naga iya gudun ruwanku ashe al'amari naku ba mai ƙarewa bane. To tun da lamarin naku babu tunani a cikinsa, maza ku tattara ku yi waje ba ma so hayaniya anan haba dallah duk kun bi kun cikawa mutane kunne.
Ta ƙarashe magana tare da nuna musu ƙofar fita da ɗan yatsanta.
Mommy Turai ta kalli nurse ɗin a lalace tana faɗin.
"Idan ma kora za ki yi ga waɗanda ya dace nan ki ingiza ƙeyarsu gaba domin banga amfani zuwansu da kuma tsayuwar da suke yi mana anan ba.
"Ki yi shiru kawai mommy ki ja bakinki ki tsuke mu jira har a fito da Jeeddah ni nasan irin mataki da zan ɗauka.
Ya Kabeer ya faɗa cikin muryar hasala.
Sai da mommy Turai ta kalle Bilal ta sakar mishi baƙar harara gami da yin ƙwafa kana ta juya a fusace ta nufi inda Aunty Farida take tsaye.
Mama ta dubi Hajja ta ce
"Ba ma buƙatarku anan wuri saboda haka ku ɓace mana da gani aiki banza kawai!
Daga haka ita ma Mama ta juyo ta bi sahun mommy Turai, aka bar Bilal Shattima da tawagarsa tsaye sai lokaci Abbas ya sami damar tofa albarkacin bakinsa ta hanyar faɗin "Hajja ku yi haƙuri ku zo mu tafi duk irin wulaƙanci da aka yi muku Shattima ne ya janyo muku ba irin ankarar dashi da ban yi ba akan Jeeddah nan amma yaƙi ji, domin nasan duk dare daɗewa sai irin haka ta faru.
Hajiya Bintu ce tayi sauri karɓe zance tana cewa
  "Atoh! Ba ga irinta nan ba da ya ɗauki shawararka Abbas da yanzu akwai ubanda ya isa ya zagi uwarsa, bai kwaɓar masa da haƙora ba, dama duk wanda ya hau motar kwaɗayi ba inda za ta sauke shi sai a tashar wulaƙanci kaɗan ya fara gani. Na rantse da ALLAH da yau ni ce na tsuguna na haife ka Bilal da sai ka saki Jeeddah ba saki ɗaya ba uku kaff! Za ka rubuta mata...
  "Kin ga Hajiya Bintu banaso zugi da tadda zaune tsaye mi ya kawo zance saki yaro yana so matarsa ita ma tana sonshi sannan kuma da kike faɗin saboda kwaɗayi Bilal ya auri Jeeddah, sai kin faɗa min munafuki da ya gaya miki haka?"
Hajja ta faɗa ranta a matuƙar ɓace.
"Ai abin a bayyane yake duk mai hankali ba sai an gayamasa ba da kansa zai iya gano wa.
"To naji duk ma ta yaya kike kallo wannan al'amari ba damuwa ta bace abu guda nake buƙata daga gareki muddin ba za ki faɗi alkhairi ba ki ja bakinki ki yi shiru. Ban gayyato ki zuwa wajenan don ki tsokano fitina ba.
   "To ai shikenan duk tsutsu da ya kira ruwa shi ruwa kan doka.
Cewar Hajiya Bintu tana wani taɓe baki, ta koma gefe ta rakuɓe ranta fari tass! Kamar auduga.
  Cikin ɓaci rai Bilal ya kalle Hajja ya ce "banga amfani tsayuwar da muke yi anan wuri ba Hajja gara ku zo mu tafi kawai, duk tsiyar su ba su isa su canzawa ɗa da Jeeddah za ta haifa uba ba. Ni matsiyaci nan  nine dai ubansa.
   "Ba za a yi haka ba Bilal kada ka biyewa fushin zuciya ko kuma ka biye musu saboda Jeeddah da ɗan cikinta mu ka zo don haka za mu ci-gaba da jira har sai an fito da ita.
  "Shikenan Hajja fatana ALLAH ya fito da Jeeddah lafiya wallahi sai na nunawa marasa mutunci iyaye nan nata nima ɗan zamani ne.
*After thirty minutes*
_Bayan mintuna talatin_
Wata nurse ta fito daga ɗakin tiyata tai yi wa su Mama albishir an kammala tiyata an fito da Bouncing Baby boy, a lokaci ɗaya suka yi hamdalla, bayan wasu 'yan mintuna aka fito da Jeeddah daga ɗakin tiyata nurse biyu ne suka turo ta akan gadon ɗaukar marasa lafiya, tana lalluɓe cikin farin mayafi kamar matatciya aka shigar da ita ɗaki na musamman Ya Kabeer aka kira ya kama aka kwatar da ita akan gado. Sai da likita ya kashe musu gargadi kada su cikata da surutu, hakan yasa Aunty Farida ce kaɗai ta zauna a ɗakin yayin da Mama da Mommy Turai suka koma bakin theater room su na jira a fito da Baby, Bayan an kammala shirya Baby nurse ta fito musu dashi yana sanye cikin white Baby bodysuit an naɗe da white shawl yaro ƙato gaske dashi kusan weight ɗin shi 5.9kg Mommy Turai ta karɓe shi daga hannu nurse ta leƙa fuskarshi tana faɗin "Kai Ma-sha-Allah! Fatee leƙo ki ga wannan ɗan lukuti dole yasa a yanka 'yarta, ga shi nan tubarakallah Ma-sha-Allahu!
   Washe baki Mama tayi tare da kallon Baby tana faɗin "ɗan nema ɓukeke wofi kawo min shi nai masa rankwashi ya wahalar mu da yarinya ba kaɗan ba.
Ya Kabeer yasa dariya tare da sauri karɓe shi daga hannu mommy Turai yana cewa "A'ah Mama kar mu fara haka dake daga zuwan sabon maigida sai a tarɓe shi da rankwashi.
Su duka suka sa dariya hango su ɗauke da Baby da su Bilal suka yi yasa suka nufo wajensu. Tun kafin su ƙaraso su Mama suka haɗe fuska yayin da Bilal da Hajja sai washe baki suke yi.
   "Al-hamdulillah! Ashe an fito da ita me aka samu ne?"
Cewar Hajja tana leƙe fuskar Baby dake hannu Ya Kabeer.
  A daƙile Mama ta amsa da cewa "ɗa namiji.
"Ma-sha-Allah! ALLAH ya bata lafiya ya tashi kafaɗarta ya bata lafiyar shayarwa.
Kusan a tare Hajja ta jero waɗannan addu'o'i.
Nan ma Mama ce ta amsa mata a takaice da
  "Amin;
Ya Kabeer ba shida niyar basu Baby su gani domin tuni ya gama yi mishi addu'a, yana rungume da shine kawai Hajja da ta fahimci manufarsa sai kawai ta ce "Kabeer kawo shi nima nai masa addu'a.
Ba a so ran Ya Kabeer ya ba ya miƙa mata shi ta karɓe shi tana ƙara washe baki baya tayi masa addu'a ta miƙawa Aunty Bahijja ta karɓe shi tana wani yatsine fuska kamar an mata dole sai ta karɓe shi, ko wani kallon kirki bata yi masa ba ta miƙawa Hajiya Bintu da sauri Hajiya Bintu ta ɗauke fuska tamkar bata ganta ba, gani haka yasa Bilal yai sauri tara hannunshi ta ɗora masa shi, lokaci da idanuwanshi suka sauka akan yaro sai yaji wani irin mashahuri daɗi yana bi sassan jikinshi yanzu wannan yaron ɗa shi ne gudan jininshi, sai da ya ɗauki dogon lokaci yana kallon yaro ba ko kyaftawa sai da Abbas ya zungure shi a kafaɗa yana cewa "Shin Shattima ba za ka bani yaro na ganshi bane ka bi ka wani tsure shi da idanuwa?"
Kusan a tare Mama da mommy Turai suka jefawa Bilal wani irin kallo mai cike da zallar takaici, kafin Mommy Turai ta dawo da ganinta kan Mama ta ce "Kin ga Fatee zo mu bar waje nan zuciyata ba za ta iya jure kallo wannan kayan haushin ba.
   "Humm wallahi kuwa Turai kayan haushi ba kaɗan ba.
Bari waje suka yi da tafiyarsu da kamar mintuna biyar Ya Kabeer ya zo ya karɓi yaro daga hannunsu, duk yadda Hajja take dannar Bilal sai da ya kasa haƙuri domin kuwa su na dosar ɗakin da Jeeddah take Mommy Turai tai sauri taka musu birki da cewa "Ya haka malamai ina za ku je haka zuga guda ba kun ga yaronku ba?" to likita ya ce bataso dogon surutu ku tafi sai gobe idan ta farfaɗo kwa dawo ku dubata.
A fusace Bilal ya kalleta da zimmar mayar mata da magana amma sai Hajja ta kwaɓe shi, dole suka baro asibiti ba tare da sun ga Jeeddah ba.
Sai misali ƙarfe 5:04pm Jeeddah ta farfaɗo a lokaci ta fara jin zafi da raɗaɗi gun da aka yanka, ga ƙishi tana ji ba hali shan ruwa domin likita ya ce kar su bata ruwa sai ƙarfe 6:00pm tayi.
Tun lokaci da Bilal Shattima ya baro asibiti tare da su Hajja bai ƙara komawa ba, tun Jeeddah bata dawo hayyacinta ba har ta dawo ta fahimci baya asibiti sai kawai ta bar abin cikin ranta. A washegari ma tun safe take zuba ido ganinshi har rana ta take bai zo ba  kasa haƙuri tayi ta tambaye Aunty Farida domin ita da Mommy Turai suka kwana da ita yanzu ma mommy ta tafi gida shine ya bata damar tambayar Aunty Farida.
Kai tsaye Aunty Farida ta labarta mata abinda ya faru, nan take yana yi Jeeddah ya sauya ta ji wani irin mugun haushin Bilal ya turnuƙe ta, musanman da ta tuna lokaci da ya sayarda machine ɗinsa don kawai a yi wa Aunty Bahijja surgery, wato ita ce kawai bai damu da ta ta rayuwa ba.
Su na cikin tattauna maganar sai ga A'isha Shattima ta zo dole suka yi shiru, amma Jeeddah tana gani Aunty Farida ta fita ta soma yi wa A'isha Shattima ƙorafi A'isha kam sai haƙuri kawai take bata.
Bilal Shattima bai zo asibiti ba sai da yamma liss shima bai so zuwa ba Abbas ne ya matsa mishi, domin tun jiya yake cike da takaici wulaƙanci da aka yi musu. Lokaci da suka shiga ɗakin bakunansu ɗauke da sallama Aunty Farida ce kaɗai a ɗakin tana riƙe da Baby sai Jeeddah da ke zaune da mug ɗin liptom a hannunta tana sipping a hankali. Kallo ɗaya nai musu na ɗauke fuska yayin da suka gaida Aunty Farida ta amsa musu ba yabo ba fallasa ta miƙawa Abbas Baby ta bar musu ɗakin. Abbas ne ya fara cewa dani "Maman Baby ya lafiyar jiki?"
    "Al-hamdulillah!
na faɗa ba tare da na ko kalle gefen da suke ba.
  Bilal ya matso kusa dani har yana haɗawa da dafa ƙafaɗata yana faɗin "Love ya jikinki?"
Sai da na fara ture hannunshi daga kafaɗata kafin na ɗago idanuwana da ke cike da takaicinsa na wani kafe shi dasu, shima haka ya kafe ni da nashi idanuwa tsawon lokaci na kasa kauda ganina akansa wani irin tuƙuƙi nake ji a cikin zuciyata. Da ƙyar nayi ƙoƙari danne zuciyata ta hanyar kauda fuskata ina faɗin "Sai yanzu ka ga damar zuwa dubani ai da kasani kayi zamanka ba sai ka zo ba?"
Bilal ya yi shiru bai amsa mata ba sai faman shasshafa sajen shi yake yi Abbas yai ƙarfi hali furta "Haba Jeeddah daga farfaɗowarki za ki fara neman tada zaune tsaye.
   "Ka ga Abbas ka ja bakinka ka tsuke ba ruwanka wannan lamari ne da shafi tsakani mata da miji ba huruminka bane. Domin kai ba haka kake yi wa taka mata ba.
  Sai da Abbas ya haɗiye miyau bakinsa kafin ya ce "ALLAH ya ba ki haƙuri ni gyara ne aiki na ba ɓatawa ba.
"To nace banaso gyaran naka ka riƙe kayanka..
   "Jeeddah!
Bilal ya kira sunanta a tsawa ce kana ya ɗora da cewa "wai ke miyasa har abada ba a miki dai-dai duk yadda mutum ya kai da nuna ƙoƙarinsa akanki da ke da 'yan gidanku sai kun nuna gazawarsa?"
   "A'ah! Shattima kada ka biye mata ka tuna da irin condition ɗin da take ciki.
"Kowanne irin condition take ciki Abbas sai na zuba mata ido ta gaya ma magana?"
   "In don ta nine karka damu Shattima ranta ne a ɓace karɓe shi ka zauna ku yi sulhu a tsakaninku zan jira ka a waje.
Daga haka ya miƙawa Bilal Baby ya fita, na raka shi da mugun kallo kafin na ja guntun tsaki gami da furta "Baƙi munafuki kawai!
  Kallona kawai Bilal ke yi daga bisani ya jawo kujera ya kawo daff da gadona ya zauna "Love kada ki biyewa zugar maƙiya su ɓarraka mu dama ba so aurena dake suke yi ba. Ina iya ƙoƙarina amma basu gani kullum cikin aibanta ni suke shin arziki na waye?"
  "Dallah dakata malam! Kada ka sake ka ƙara furta mummunan kalma akan iyayena da kana tsinana abin arziki don me za su dinga aibanta ka? A koda yaushe lalura idan ba ta mahaifiyarka bace da 'yar uwarka ba ka nuna damuwarka akai  Riƙo sakaniyar kashi da kake yi min ya kai maƙura ina kwance a gaɓar rai ko mutuwa ka wofitar dani saboda haka Bilal tun kafin mu kai mataki tara yara da yawa ka cuceni ka barni da ɗaukar ɗawainiyarsu gara kowa ya kama gabansa na gaji. Wallahi haƙuri na ya ƙare ALLAH ya haɗa kowa da rabonsa. Don ba zan iya ci-gaba da zama da kai a haka ba...

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now