010...

106 9 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI...!*
        _{Sabon salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

010...

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajarsu cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

Naceba🙋‍♀️
Kina bukatan jikinki yazama so fresh ba kwarzane ko daya ballantana kuraje ko tabo, sunburn,acne, ko knuckles? Kije kigwada products na mg's insha Allah zakiga ynd fatarki zedawo fiye da tsammaninki zakigyara jikinki naturally batare da kinbata fatarki ba jikinki yayi fresh kiyi smooth kizama kalar Madara kirar models kiringa walwali kina haskawa duk inda kikayi😍
Kidena kokonto cewa kingwada baki Dace ba insha Allah kijaraba products dinsu bi'iznillah zakiji dadinshi🙏 kayansu akwai kamshi especially sabulun kamshin yakama jikinki ko kindade da wanka jikinki zaidinga fidda ni'imtaccen kamshi bayinki ma zakiji kamshin dazai Kama😍sunada kit special domin amare Wanda indai kinyi using kit dinnan Baki bukatar kikara Kai kudinki gurin dilke domin ainihin yanda fatarki zehaska yagoge kidinga shining abun sewanda yagani😍

Mai bukatar kayan mg's chat:08062991549,07046881166,07067210195
Call:08064532391
Hausawa nacewa adade anayi sai gaskiya Kuma siyan nagari maida kudi gida🤝
💯 tested nd trusted
Natural/organic🥰
Akwai discount a medium kit👇👇
Medium kit
Normal price 17k Now 15k
Babban kit 20k
Now 18k

Valid for only 2days.
  

Cikin tsiwa Khairat ta ce "Ba kin fiffita son zuciyarki fiye da zaɓi da iyayenki suka yi miki ba?" Ai sai ki zuba ruwa a ƙasa kisha don kuwa Baba ya aminta da aurenki da Bilal Shattima, amma ki sani Mama bata farin ciki domin Haidar take so ki aura saidai bata da yadda za ta yi tun da Baba ya ri ga da ya amince.
   "Al-hamdulillah!
Jeeddah ta furta very excited yayin da fuskarta ta cika da annuri sai uban murmushi take zabgawa, kallo takaici Khairat tai mata ta ja tsaki domin ta fahimci lamarinta hadda rashin sani ciwo kai yo....ban da rashin sani ciwo kai an  gayamiki mahaifiyarki bata farin ciki da aurenki amma tsabar sakarci kina hamdalla. "Tsakani da Allah duk wanda ya ce Jeeddah tana da cikakken hankali haƙiƙani gaskiya sai in tsoronta yake ji.
Khairat ta faɗa a cikin zuciyarta.
   "Tirƙashi! Amma gaskiya Jeeddah kina da taɓi hankali kou?"
Khairat ta tambaya saboda gaskiya ta kasa ɓoye mamakinta gara ta bayyana shi a fili da tai ta ƙunshewa cikin zuciyarta.
   "A'a kware ce akaina {asibitin mahaukata}.
Jeeddah tai magana gami da gallawa Khairat harara.
  "Ba shakka biri ya yi kama da mutum ba sai kin faɗa ba duk mutum mai cikakken hankali da tunani ba zai aikata  kwatankwacin abinda ke ɗinan kika aikata ba. Infact na kasa yarda Jeeddah wai farin ciki kike yi za ki aure zauna gari banza ɗan zaman kashe wando.
Khairat ta faɗa tana taɓe baki.
   Sosai furucin Khairat ya ɓata min rai na fahimce burinta a koda yaushe ta gani cikin baƙi ciki, tana ɗaya daga cikin mutane da ke adawar aurena da Bilal Shattima, ni kuma ko a jikina muddin dai zan kasancewa da zaɓin raina duk wanda zai shiga ɓacin rai ruwansa. Saboda haka na kalleta cikin rashin damuwa na ce "Duk abinda za ki faɗa ba damuwa ta bace dama muradin maji hajji sallah, burina na kasance da Bilal Shattima a ƙarƙashin inuwar aure to tun da Baba ya amince ita ma Mama da sannu za ta yi na'am dashi.
   Girgiza kai Khairat tayi yayin da takaicin Jeeddah ya ƙara ɗarsuwa a ranta bata taɓa gani mutum mai tosasshiyar ƙwaƙwalwa irinta ba amma ba komai a jure zuwa rafi da tulu wata rana zai fashe.
Khairat ta koma ta kwanta tana da yaƙini ko za ta kwana tana nunawa Jeeddah illar da ke tattare da iri wannan aure ba za ta taɓa saurarenta ba. Saboda ta riga da tasawa ranta Bilal Shattima shi kaɗai ne zai zauna da ita kaɗai ba tare da yai mata kishiya ba
Saboda haka Khairat ta shafawa kanta lafiya ta koma ta kwanta.
Ina gani Khairat ta kwanta har da su jan duvet na ja tsaki ƙasa ƙasa na cire kayan jikina na maye gurbinsu da na bacci, daga ni har ita kwana mu ka yi muna jin haushin juna.
Ko da safe ba wacce ta kula wata har suka yi shirin fita aiki, Khairat ta riga ta ficewa a parlourn Baba ta tadda ta zaune kusa da Mama.
Kaina a ƙasa na shigo tare da sallama Baba ne kaɗai ya amsa min, na sake gaida su nan ma shi kaɗai ya amsa min da fara'a saɓani Mama da ta amsa min adaƙile. Kusa da Baba na zauna saboda banga fuska ba a wurin Mama ba sai hira suke yi ƙasa, ƙasa ita da Khairat.
   Baba ya tattaro natsuwarsa gaba ɗaya akaina cikin sanyaya murya ya fara magana "Jeeddah jiya nida Mamanku mu yi magana akan zance aurenku, tsawon lokaci nan da nai shiru ban yi magana ba na zuba miki ido ne a dalili ina tunani ko za ki canza ra'ayinki, ki amince da aure ɗan uwanki sai dai kashhh...haƙata ta kasa cimma ruwa bani da wani zaɓi face na amince da naki zaɓi duk nasan iri matsalar dake tattare da zaɓin naki.
Baba ya ɗan numfasa gami da kallon Jeeddah so yake ya karanci yanayin ta yayin da Jeeddah ta sadda kai ƙasa tana wasa da babban yatsar ƙafarta.
   Kana ya ci-gaba da faɗin "shin kin amince za ki aure Bilal duk da bashida wata kwakwarar sana'a?"
   Ɗagowa Jeeddah tayi gami da satar kallon Mama da Khairat a lokaci ɗaya suka galla mata uwar harara sai da gabanta ya faɗi tai sauri maida kanta ƙasa, gani shiru nata ya yi yawa yasa Baba cewa "Ke nake saurare Jeeddah shin kin amince da Bilal ɗin ko kuma kin yarda za ki aure ɗan uwanki?"
Haba ji ya ambata mata Haidar tai sauri ɗagowa cikin sarƙewar lafazi ta ce "A'a Baba abar zance ya Haidar ɗinan na amince da Bilal.
Baba ya sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya dama yasan da matuƙar wahala ta amince da aure Haidar ya tambaya ne kawai saboda Mama ta ƙara tabbatar da ba laifinsa bane shima ya goye bayanta ne a dalili ba shi ke mata zaman aure ba gara a aura mata wanda take so shine kwanciyar hankalinsu gaba ɗaya.
   "Shikenan dama so nake na ƙara jin ta bakinki tun da kin aminta sai ki ce dashi ya turo da magabatansa banaso a  ɗauki dogon lokaci gara na aurar daku kowa ya huta. Amma da son samu ne ki shawarce shi ya nemi sana'ar hannu komai ƙanƙantarta yafi masa zama haka nan ke kuma tun da kin kafe lallai sai shi dole ki dinga tallafa masa da salary ki tun da ba abinda kike yi dasu nima in-sha-Allah zan taimaka da abinda bai fi ƙarfina ba. Allah ya sanya alkhairi ya ƙara haɗa kanku Allah  yasa mutuwa ce kaɗai za ta raba ku.
    "Amin Baba! Nagode Allah yasaka maka da gidan aljanna firdausi.
Jeeddah ta faɗa cike da farin ciki tana zabga fara'a kamar wacce aka yi ma bushara da gidan aljanna.
Takaicinta ya lulluɓe Mama da Khairat kasa haƙuri Khairat tayi saboda mugun takaici Jeeddah da take ji ta miƙe tare da yi wa Baba da Mama sallama ta fice abinta ba tare da ta sake ko kallon gun da Jeeddah take zaune ba.
Cikin karya murya  Jeeddah ta shiga sharowa Baba ƙarya ta hanyar cewa "Baba ai kwana nan zai fara aiki a shagon siminti na yayansa Faruk.
   "Madallah hakan ma ya yi Allah yasa ya fara a sa'a.
Baba ya faɗa fuskarshi cike da fara'a dama shi fargabarsa ɗaya rashin aikin Bilal to tun da ya sami sana'a, shikenan bashida wata damuwarsa ta ragu.
   Zuciyata fal farin ciki na miƙe tare da yi wa Baba da Mama sallama Baba ne kaɗai ya amsa min yayin da Mama ta bi ni da kallon takaici, ina fitowa wajen gidanmu jikina na rawa nai zipping handbag ɗina na ciro wayata cikin zumuɗi na yi dialling number Bilal Shattima.
Bilal Shattima dake kwance akan gadonsa ya yi rashe-rashe yana baccinsa na asara domin sai ranar ta fito hatse-hatse yake tashi, can cikin baccinsa mai daɗi ya ji ringing ɗin wayarsa yana ratsa dodon kunnensa kasancewar special ringing tone ya sakawa Jeeddah yasa ya gano ita ce mai kiran nashi da ba don ita bace koma waye ba zai katse baccinsa mai daɗi ya saurare shi ba, idanuwanshi a lumshe ya shiga lalluɓe inda wayar take har yai nasarar ɗora hannunshi akanta ya ɗan ware idanuwanshi kaɗan yai receiving tare da karawa a kunne cikin murya wadda bacci bai gama sakinsa ba ya furta "Hello.. Love!
"Good morning Love!
Jeeddah ta furta cike da farin ciki.
  "Morning Love ya aka yi ne?"
"Love do you know how happy I'm?
    Murmushi ya yi mai ƙaramin sauti kafin ya furta "Huhmm...tell me the reason please kinsan banaso jan rai.
   Sai da Jeeddah ta kai dubanta gefe da gefen hanya taga babu mutane sosai, tana gudun kada wani ya ji ta kana ta ci-gaba da faɗin "Albishirinka Love!
"Huhmm goro amma Please ki hanzarta faɗa min ko menene wallahi bacci nake yi kiranki ne ya tashe ne, kisan kuma idan ban yi bacci nan ba headache ya ta damuna.
Bata damu da korafinsa ba dama tasan hali kayanta da shegen bacci tsiya, cikin zumuɗi ta ce
"Nan da ɗan wani lokaci biyu za su zama ɗaya, wannan bacci da kake yi kai kaɗai zan dinga tayaka kana ji saukar numfashina ina jin naka a takaice dai Baba ya amince da aurenmu har ya umurce ni da na faɗa maka ka turo magabatanka, a sa mana rana Love ina cikin tsanani farin ciki burinmu ya kusa cika.
Ta ƙarasa magana very excitement.
Bilal Shattima dake kwance baisan lokaci da ya miƙe zaune ba, nan take ya wartsake daga raguwar bacci da bai ƙarasa sakinsa ba saboda ko kusan bai yi tsammanin Baban Jeeddah zai aminta da ƙudirinta ba. Lallai tashi ta same shi jego da kara.
   "Love ba ka yi farin ciki bane naga ka yi shiru ko duk tsabar daɗi ne ya ƙumeka ka kasa magana?"
"Huhmm...Love I'm very speechless saboda farin ciki na rasa me zan faɗa, lallai safiyar yau ta kafa tarihi a rayuwarmu.
Ya ƙarashe magana yana dariya.
   "Haka ne Love abinda muka daɗe muna zaman jira sai gashi ya zo mana ciki sauƙi, saboda haka kada ka sa sanya ka gaggauta turowa Don Allah. Wallahi I'm eager to have you as my wedded husband
   "in-sha-Allah Love ba zan yi wasa da wannan opportunity ba.
Daga haka fira ta tsinke a tsakaninsu sai da ta iso gate ɗin makaranta sannan suka yi sallama da alƙawari zai zo ɗaukar ta.
Tun da asuba da Haidar ya dawo daga masallaci ya kasa komawa bacci yana gani ƙarfe 9 tayi ya  shiga shiri saboda Daddy ya gayamasa da ƙarfe goma za su tafi gidan su Jeeddah, bayaso ya ɓata lokaci shiyasa ya shirya tsaf cikin manyan kaya na tsadaddiyar farar shadda. Ƙamshinsa ya gauraye ko'ina, ƙarfe 9:15am yai wa katafare parlourn Daddy tsinke fuskarshi cike da fara'a da ya kasa ɓoyeta yai sallama Daddy da ke zaune akan three sitter yana duba newspaper ya ɗago da mugun sauri ya sauke ganinsa akan fuskar Haidar baisan sanda ya tintsire da dariya ba "Gadanga ƙusar yaƙi yau kaine sanye da manyan kaya lallai ta tabbata aure kake so.
   Cikin sigar shagwaɓa Haidar ya ƙaraso wajen Daddy yana ya mutsa fuska "Wai Daddy kana nufi ba ka shirya ba?"
  "Ba ga zahiri nan ka gani ba gani sanye da jallabiya in tambaye ka mana wai yaushe gari ma ya waye Aliyu da har za mu fita neman aure?"
  "Daddy da ƙarfe goma ka ce za mu tafi gashi yanzu har 9:15am don Allah Daddy ka tashi kayi wanka.
Haidar ya yi magana gami da wafce newspaper da ke hannu Daddy ya jefa ta akan kujera da ke nesa da Daddy.
   'yar dariya Daddy ya ƙara yi tare da furta "Amma gaskiya Aliyu ka cika gaggawa da yawa dawo min maza da newspaper na ba yanzu za mu tafi ba sai 10 o'clock on dot kuma dole ka jira zuwan Alhaji Ahmed da Alhaji Bashir kasan dai ba daga ni sai kai za mu je neman maka aure ba?"
   "Mommy... mommy!
Haidar ya shiga kwallawa Hajiya Turai kira da sauri ta fito daga bedroom ɗin Daddy ta shirya cikin gown na sequence atamfa sai walwali da ɗaukar ido take don ba ƙaramin kyau atamfar tai mata ba. Jikinta sai fidda ƙamshi tsadaddun turaruka yake ga wuya da hannuwanta sun sha ado na Dubai gold.
    "Ya aka yi ne Auta iri wannan kira haka har ina?"
Hajiya Turai ta faɗa sa'ili da ta ƙaraso ta zauna kusa da Daddy.
"Mommy please karki zauna ki tashi ki ɗauko mayafinki, saboda kema dake za a je kuma dan Allah ki yi ma Daddy magana ya tashi ya yi wanka wallahi lokaci yana ƙurewa kuma Baba da ƙarfe goma yake fita kasuwa gara mu yi sauri kada mu tarar da ya fita.
Haidar ya ƙarashe magana cikin magiya da kwantar da murya ba ƙaramin dariya ya ba mommy da Daddy ba a tare suka shiga kyakyatawa daga bisani Daddy ya tsagaita da dariya ya kalleshi still da raguwar dariya akan fuskarshi ya ce "kwantar da hankalinka sarki zumuɗi tuni nayi wanka kaya kawai zan canza.
   Da sauri Haidar ya riƙo hannun Daddy ya shiga jan shi "Tashi mu je Daddy yau da kaina zan zaɓa maka kayan da za ka saka kasan yau special day ne kwalliya sosai za ka yi, ka fito uban ango sakk.
Miƙewa Daddy ya yi yana dariya shirmen Haidar.
Ƙarfe goma daidai suka isa gidansu Jeeddah tare da tawagar abokan Daddy hatta da mommy sai da Haidar ya taso ƙeyarta gaba, Mama na ganinsu sai da gabanta ya faɗi ko kaɗan bataso faruwar hakan ba. Sai dai bata da yanda za ta yi saboda mai gayya mai aiki ya gama zantar da hukunci. Jikinta a mace ta yi ma Mommy iso zuwa cikin parlournta.
Bayan 'yan gaishe-gaishe da ya shiga tsakaninsu kana Alhaji Bashir ya zarce da faɗar dalilin zuwan nasu "Alhaji Usman sai ku ganmu da sassafe nan ba sanarwa wallahi ɗanka ne ya fitine mu akan lallai sai mun zo a tsayar da lokaci bikinsu.
   Har Alhaji Bashir ya dasa aya a zancensa Baba yana kallonshi gami da shafa geminshi, can dai ya ga shirunsa ba shi bane mafita ba gara ya fito fili ya faɗa musu farar gaskiya.
Kafin ya kai da yin magana Alhaji Abubakar Ka'oje ya cafe ta hanyar cewa "Wallahi Alhaji Usman ɗa nan naka ba ƙaramin azalzalata ya dinga yi ba dole na taso su Alhaji Bashir nace gara dai ayita ta ƙare jiranan ya isa haka ka bashi matarsa mu huta da fitinarsa.
Alhaji Abubakar Ka'oje ya ƙarashe magana yana 'yar dariya.
"Ai Aliyu yana da gaskiya Alhaji Abubakar sauƙin mu ɗaya abin ya zo da na gida.
Cewar Alhaji Ahmed shima yana dariya gami da kallon Aliyu da ya sadda kai ƙasa yana ta faman zabga murmushi.
Ajiyar zuciya Alhaji Usman maishadda ya sauke kana ya gyara zama cikin muryarsa mai cike da dattako ya ce
  "Da ba ku wahalar da kanku ku ka zo ba da ni da kaina zan zo har gida na same ka Alhaji Abubakar domin maganar da kasani a baya a yanzu ta canza zani, Jeeddah dai tayi tsaye, tsayin daka ta tuma tara ta ce Bilal take so ba yadda ban yi da ita ba akan ta amince da ɗan uwanta amma ta ƙi. Wallahi duk tsawon lokaci nan da ka ga ina ta noke-noke don kawai su daidaita tsakaninsu ne ita da Aliyu, to kuma hakan ya gagara samuwa shiyasa na yanke hukunci a barta ta aure wanda take so gudun kada mu yi abinda za mu dawo daga baya muna danasani har ya zo ya taɓa mana zumunci, shi sha'ani aure da kake gani Alhaji Abubakar...
   "Dakata dan Allah Alhaji Usman!
Daddy ya katse shi cikin fusata kana ya zarce da faɗin
"Idan za ka yi magana ka tafi kaitsaye domin ni Kwata-kwata ban gane inda wannan dogon sarhin naka ya dosa ba, sai kwana-kwana kake yi.
Yadda Daddy ya yi magana kaɗai zai tabbatar maka da ransa ya fara ɓaci. Yayin da Alhaji Usman maishadda ko a jikinsa domin ya tabbata sai irin haka ta faru.
Lokaci da Haidar Ka'oje ya ji bayani da Baba ya fara take jikinsa ya ɗauki rawa, hankalinsa yai mugun tashi shikenan ya rasa Jeeddah, tun da ya ji Baba ya fara wannan dogon bayani da wuya ya aura masa ita wani iri tausayinsa kanshi ya lulluɓe shi. Ya tabbata sai ya sha baƙar wahala kafin ya iya yakice sonta a zuciyarsa.
Baba ya kalli Daddy cikin natsuwa da tausassa lafazi ya ce "Dan Allah Alhaji ka yi haƙuri nasan ba a kyauta muku ba musanman idan aka yi duba da tsawon lokaci da Aliyu ya ɗauka yana jiran Jeeddah, sai dai ba zan iya mata dole ba saboda haka ina mai ba ku haƙuri banaso ayi abinda zai zo ya taɓa zumunci.
    "Innalillahi wa'inna illahim raji'un.... innalillahi wa'inna illahim raji'un!
Haidar ya shiga furtawa yana sake maimaita wa yayin da hannunshi yake dafe da saitin zuciyarsa, idanuwanshi suka firfito jijiyoyin kanshi suka yi burɗu-burɗu gwani ban tausayi.
  "Ka gani kou Alhaji Usman ka ga hali da ka jefa ɗana kou?"
Alhaji Abubakar Ka'oje ya faɗa a fusace gami da miƙewa ya nufi wajen Haidar ya zauna akan hannu kujerar da Haidar ɗin yake zaune akai ya rungumo kafaɗarsa yana bubbuga gadon bayansa gami da jijjiga shi, kafin ya kalli gefen da Alhaji Usman maishadda yake ya shiga zazzaga masifa da tijara dama gashi mafaɗaci gaske "Amma wallahi Alhaji Usman ka bani mamaki ashe bare yafi ɗan gida infact yaushe aka haifi Jeeddah da har za ka kasa tankwarata ta bi abinda muke so. To wallahi idan wani ya abu ya sami yarona ba zan taɓa yafe maka kai da 'yarka ba saboda haka ka yi addu'a kada wani abu ya same shi.
   Daddy ya ƙarashe magana yana ɗaga harshe Mama da Mommy da ke parlourn Mama suka jiyo hayaniya, dama Mama tana cikin ba wa Mommy mummuna labari da gudu suka shigo parlourn yayin da Alhaji Usman maishadda ya lafe jikin kujera ya zubawa Alhaji Abubakar Ka'oje idanuwa, saboda yasan su aka yi wa laifi a yadda ya hau ɗinan kalaman haƙuri ba za su yi tasiri akansa ba gara ya kyaleshi ya faɗi iya abinda ke ransa. Sosai Alhaji Abubakar Ka'oje ya harzuƙa sai faɗar maganganu marasa daɗi yake yi Hajiya Turai ta fashe da kuka tana faɗin "Saboda Allah Yaya kana gani ka yi mana adalci kenan?" kana sane da yadda Haidar ya kwallafa ranshi akan Jeeddah, ka kuma san yanayi ciwonsa ba a son ɓaci ransa amma duk da haka ka yanke hukunci haramta mishi aurenta.
   Kafin Alhaji Usman maishadda ya yi magana Daddy ya cafe da cewa "Daina ɓata yawun bakinki Hauwa duk abinda ya yi da saninsa ya kuma yi ne domin ya ƙuntata mana kuma ki sani Hauwa na raga masa ne don kasantuwar shi ɗan uwanki da wallahi-tallahi sai na nuna masa ba a yi min haka a zauna lafiya.
Gani yadda Alhaji Abubakar Ka'oje ya harzuƙa yasa Alhaji Ahmed da Alhaji Bashir suka shiga bashi haƙuri suna kuma ɗorawa Alhaji Usman maishadda laifi, domin su a ganinsu babu dalili ko wata hujja da zai sa ya ce ba zai yi wa 'yarsa aure dole ba. Mata nawa aka yi wa dole kuma suka zauna sai 'yarsa ce zai ce ba zai mata dole ba sai kace tafi sauran mata.
    Haidar da ke dafe da zuciyarsa ya ciro idanuwanshi ya bi mutane dake parlourn da kallo Kowane da irin ɓaci rai da ya hango tattare akan fuskokinsu more especially Daddynshi.

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now