1

256 14 1
                                    

Zaune take a tsakar gida kan tabarma ta saka dukka hannayenta a kuncinta tana tunanin rayuwa da irin kalubalen da take fuskanta a gidan mahaifinta wanda idan ba ka sansu da dadewa ba zaka rantse da Allah cewa ba Umma bace ta haifeta saboda bayyanannen bambancin da take nunawa tsakaninta da yar uwarta Suhaila wadda ta girme mata da shekaru hudu. Sabirah ta kasance baqa qirin. Irin baqin nan me maiqo da naso kuma duk cikin gidan daga kan mahaifanta, Suhaila da qannenta guda biyu Abbas da Imam ita kadai Allah yayi wa irin wannan halittar. Gaba ɗaya danginsu za'a iya cewa babu me irin bakinta dukda cewa akwai farare, baqaqe da wankan tarwada a zuria'arsu.

"Yar baƙa meye haka kin rafka tagumi kamar me takaba?" Imam, autansu me shegen tsokana ya tambayeta yana dariya.
"Wai Imam yaushe na zama sa'ar kane?" Sabirah ta tambaye shi da muryanta me kauri kamar ta maza. Me Imam zai yi kuwa idan ba dariya ba. Sai da yayi me isarsa sannan yasa ƙafa yayi waje wurin wasan da ya baro yaran maƙota nayi. Sabirah tayi kwafa ta share ƙwallar data gangaro kan kuncinta. Tana ji tana gani ƙananan yara sun raina ta kuma babu me tsawatar musu idan kuma ta ɗau mataki cibi ya zama ƙari domin ba ƙaramin aikin Umma bane ta raba dare tana sauke mata jidali da gori akan yanayin halittarta. Bata da me ƙaunarta a gidan sai mahaifinta wanda ba a gari yake sana'ar saida kayan miya ba ƙauyuka yake zuwa duk ranakun cin kasuwa saboda haka sai ayi sati biyu ba'a ganshi ba shi yasa kullum take kwana ta wuni cikin kaɗaici tunda ta gama secondary school tana jiran sakamakon WAEC da NECO kuma Alhamdulillah dayake tanada hazaqa ta ci Jamb dinta sosai sai fatan Allah ya sa taci kuma ya buɗawa Abban nata ta samu tayi jami'a wanda shine babban burinta a rayuwa tunda tasan cewa dakyar ta samu mijin aure ba kamar  ƴar uwarta ba da kullum samari ke sintiri ƙofar gidansu.

"Saburah! ke Saburah!! " Suhaila ta kwala mata kira daga cikin dakinsu inda ta bararraje tun safe tana chatting ita kuwa ƴar aikin gidan tun asuba bata huta ba sai da ta gama duk wani aiki na cikin gidan. Ba sannu balle Allah yayi miki albarka sai dai a nemi abunda za'a yi korafi akai. Hatta tuwon da zasuci a daren ta kammala saboda gudun fadan Umman tasu data tafi anguwa.

"Gani" ta fada a cukule bayan ta daga yalolon labulen dakin. A duniya babu abinda ta tsana sama da Saburan da Suhaila take kiranta dashi kuma ƙememe taƙi ta daina saboda yada girma da rashin damuwa da ƴar Uwar tata.
"Dallah Malama Meye haka kin tsaya min a kai sai kace kin bani ajiya. Kuma wallahi ko haɗiyar zuciya zakiyi sai dai ki hadiya amma Sabura yanzu na fara kiran ki. Da shegiyar baƙar fuska kaman zunubi" ta gama gaggasa mata magana sannan tayi mata nuni da plate din data gama cin farar shinkafa da mai da yajin da ta yanka cabbage da cucumber da tumatir a ciki tace ta dauke taje ta wanke. Ta iya aikin lalata wuri da kwanuka amma ko wanki bata iyaba. Tun suna ƙanana sai dai ita Sabiran ta haɗa tayi musu. Da Abbansu ya fahimci abinda ke wakana ne ya hana ya kuma ce idan ta sake bata wanki koh ita ta kuskura tayi ko bayan ransa ne to Allah ya isa bai yafe ba shine ta samu salama. Amma wankin Ummansu kam ya zame mata jiki. Duk wani aikin wahala na duniya ta iya kuma ya bi jikinta shiyasa idan ta kwanta bacci kamar gawa dakyar take iya tashi sallar asuba. Yawancin lokuta ma sai an idar da sallar take tashi ko idan Abbansu yana gari ya tashe ta. Suhaila daman sallah bata dameta ba kuma itace ta gaban goshin Umman tasu saboda haka ko tasani bata mata faɗa.
"Yaaya fisabilillahi daman saboda dauke miki faranti kike min wannan kiran kaman na makafi? " ta tambaye ta a daƙile tana kokarin haɗiye malolon baƙin cikin daya tsaya mata a maƙoshi.

"Eh shine ko zakimin rashin kunyar taki da kika saba ne iyye? wallahi yanzu zan lallasa miki wannan baƙin jikin naki yayi laushi banza mara sa'a kawai"

"Karki manta da cewa ni yar uwarki ce bai kamata ki ringa zagina da cin zarafina akan abinda banda iko akansa. Besides black is beautiful kuma ba'a siyan irin color ɗina a kasuwa and Alhamdulillah da Allah yayi ni cikakkiya ba me wata nakasa ba" Sabirah tace tana tausar zuciyarta domin azalzalar ta da take yi akan tayiwa Suhaila ɗan banzan duka tunda ba kowa a gidan idan yaso duk abinda zai faru ya faru duka ne babu irin wanda bata sha ba a wajen Umma.
"Dallah Malama rufe mana baki. Sai shegen iyayi da ƙaryar turanci sai kace wata ƴar hamshaƙi ko wadda tayi private school" Taja tsaki tana juya mata baya ta cigaba da chatting. Tasani sarai iyaka hakuri ƙanwar tata tanayi da ita kuma itama wasu lokutan tasan bata kyautawa amma ya zata yi? haka mahaifiyarsu ta koyar dasu dole ta cigaba da yin yanda taso ga Sabiran da mutane da dama na kokonton kasancewar ta ƴar gidansu. Har kunyar haɗa hanya take yi da ita idan Abbansu yana gari domin duk iskancinta bata isa tayi a gabansa ba. Sam baya daukar raini Umman tasu kuwa ya yi ya yi da ita akan irin uƙubar da take ganawa karamar ƴarta mace amma taqi ji har rabuwa sun taɓa yi akan hakan kuma duk wanda zai faɗa taji an kai masa koken ta amma taƙi ta gyara shi yasa ya rabu da ita kuma ya barta da halin ta yakan ce "Habi ki guji ranar dana sani mara amfani. Kin raba kan ƴaƴan ki, kin fifita sauran akan Sabirah saboda son zuciya da jahilci. Ƴa dai tawace kuma ina son abata kuma in shaa Allahu sai ta zama abin kwatance a duniya, sai ta baki mamaki dake da wannan figaggiyar wadda kika koyawa baƙaƙen halayenki kina ganin gata kike mata." Umma sai dai ta murguda baki tana ƙunƙuni tana cewa " A hakan? Da wannan baƙin nata zata zama abar kwatancen? Sai dai wataƙila kana magana ne akan baƙinta wanda dama tunda tazo duniya ya zama abun kwatance. Haba! Banda ƙaddara da bata wuce bawa me za'a yi da baƙi irin na Sabirah. Mtsww" taja tsaki ta cigaba da sabgar gabanta.

Haka rayuwar ta kasance ga Sabirah tun tasowarta. Batasan daɗin uwa ba duk da cewa tana raye, wanda take samun rangwame a wajensa mahaifinta ne da baya zama sai Abbas wanda bai cika shiga sabgar gidan ba dan wasu lokutan har kudin break yana bata idan Umma ta hanata akan tayi mata wani laifi. Sai kuma Ƙawaye idan taje makaranta. Babban abinda yake bata mamaki kuma yake ɗaure mata kai bazai wuce cewar a makaranta ba'a tsangwamarta akan baƙinta ko muryar ta, ko anayi ma bata sani ba sai dai a bayan idonta. Amma duk hakan bai hanata tsarguwa ba domin gani take kowa yana mata kallon wata halitta ce ta tasha bamban da sauran halittun duniya. Akwai wata ƙawarta ta bayan layinsu da take matuƙar son mu'amala da ita domin ta ringa koya mata karatu da turancin da yawancin mutane ke mamakin yanda akayi ta iya shi lura da cewa makarantar gwamnati take zuwa. Hakan ya samo nasaba ne tun yarintar ta da wasu masu hannu da shuni suka zauna a kusa dasu shine aka samo musu lesson teacher dayake zuwa duk dare ranakun mako to shine take zagayewa babu wanda ya sani sai Abbanta take zuwa itama ana yi da ita dayake yaran basuda matsala kuma tanada karance karance harda wanda suka fi karfin ƙwaƙwalwarta. Dalilin haka ne yarinyar ke zuwa gida domin bitar abinda aka koya musu da yan kalaman ta na hausa da take son Sabirah ta fassara mata. Zuwanta biyar ta daina zuwa a cewar ta bazata iya jurar ganin irin cin fuskar da akewa Sabirah a gidan ubanta ba. Wannan shine dalilin da yasa duk amintar Sabirah da mutum to bata taɓa bari yazo gidansu domin gudun irin haka ta sake faruwa.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now