ƳAR BAƙA
Written by Aishatu Humaira Bello.
Humylash@wattpad.BABI NA BIYAR (5)
A sukwane Nura ya dawo gidan domin yasan ba lafiya ba tunda har Faridah ta kasa kiransa sai text tayi masa. Akwai wa'yanda sukayi appointment dashi dayawa suna jiransa hakuri ya basu akan yanada emergency a gida su jirashi in Shaa Allah zai dawo bada jimawa ba.
"Ummi! Faridah!! Fiddausi!!!" Ya kwala musu kira da karfi bayan ya shigo cikin gidan. Ko key bai zare ba a jikin mota ya shigo.
"Lafiyar ka kuwa? Meye haka wani abun ya faru ?" Ummi ta tambaye shi a sanyaye daga inda take zaune a falon don shi bai ma lura da ita ba. Zama yayi yana hamdala yana maida numfashi kaman wanda yayi gudu daga asibitin zuwa gidan nasu. Alhamdulillah yake furtawa a kasan ransa tunda yaga Ummin tasa lafiya kalau. Faridah ce ta fito da kumburarriyar fuskanta.
"I saw your message . Meya faru ne dan Allah?" Ya tambaya cikin nuna damuwa yana mata nuni da tazo ta zauna kusa dashi. Tsaki Ummin taja don har lokacin zuciyarta na azalzalarta akan tabi sahun Baban nasu na wanke shi tas kuma ya bata takardarta. Banda Baffanta daya hanata zuwa kotu ai da wani zancen ake ba wannan ba.
"Babanku ne yazo" ta bashi amsa a takaice. Nan da nan ran maza ya ɓaci jijiyoyin kansa suka miqe yana huci.
"Uban me yazo yi gidan nan? Waya faɗa masa inda muke?"
"I don't know Yaya. Kawai ganinsa muka yi kuma Ummi ta kore ni daki bansan me yace mata ba"
"You mean kina cikin gidan kika tafi kika bar Ummi ita kadai da wannan mahaukacin? Ashe dama bakida hankali ban sani ba? What if ya gwada mata akuyancin daya saba? Me yasa baki tsaya tare da ita ba. Why?" Ya hayayyaƙo mata kamar zai kai mata duka.
"Ba ita ta kar zomon ba Nura. Kai a tunanin ka zan tsaya Abdullahi ya dakeni? Ya gwada kuma yasha mamaki. Yanzu dai duk ku kwantar da hankalinku. Allah yana tare damu kuma da ikon sa bazamu wulakanta ba. Ka koma wajen aikin ka babu komai in shaa Allah" dakyar ta samu ta lallabashi ya tafi amma saida ya kira musaddik akan ya tayashi neman mai gadi irin buzayen nan marasa mutunci. Sakacinsa ne da bai saka matakan tsaro a gidan ba amma ai bai taba tunanin baban zai zo inda suke ba. A hanyar komawa yayi ta tsaki yana dukan steering yana ta ayyano scenarios kala kala akan zuwan da baban nasu yayi. Yaji dadi da Ummin tasu take nuna bacin ranta a fili yanzu, hakan yana bashi confidence din aikata abinda ya dade da cin alwashin aikata wa idonsa idon baban nasu.
Yana gama consulting patients dinsa ya dawo gida bai tsaya a shagonsa na dinkin zamani ba. Babu abinda ba'a siyarwa na kayan ɗinki ga kwararrun tailors daya kawo shi yasa ake samun alheri sosai a wajen. Kullum yana zama bayan aiki domin ya duba accounts da kuma tabbatar da tailors din na meeting deadline saboda policy dinsa ne ba'a karya alqawari da customers. Idan sun karbi ɗinkinka yau ance gobe zaka samu to ba makawa a goben zaka zo ka samu sun zama ready. Shi yasa mutane ke rububin kai ɗinki shagon Neelat Fashion House."Sarkin masu zuciya. Ka yayyafa mata ruwan sanyi kafin ta ƙone" Ummi ta fada cikin wasa ganin yanda yake tura abinci da sauri sauri kaman me dambe da plate and spoon din. Hmm kawai ya iya furta wa. Sai daya cinye abincin nan tas dayake baya wasa da cikinsa tunda yasan yunwa yasan irin illar da take yiwa ɗan adam. Cikin hikima Ummi ta ringa jansa da hira har ya sake suka koma normal.
Baba kuwa ya dauki alwashin cewa sai dai Nai'la ta mutu da aurensa tunda tasa hannu ta mareshi. Har ya kwanta abin yana masa yawo a rai. Sai rewinding abun yake. Wai shi yau Na'ila ta gasa masa maganganu masu daci harda wai ko a filin hisabi bata so su haɗu. Dakyar bacci barawo ya saceshi da asubar fari kuwa ana idar da Sallah ya figi mota sai gidan Nura. Bugun kofar yake kaman an aikoshi yana ihun suzo su bude ko ya haura katanga. Dawowar Nura kenan daga masallacin kasa dasu inda yake Sallah kuma yanada dabi'ar yin Sallah a jam'i domin duk inda yake sai dai idan babu masallaci a kusa amma indai akwae to dashi za'a gabatar da Sallah cikin jam'i . Bugu yake iya karfinsa kuma ahalin gidan suna jinsa sukayi biris tashi. Lailayo ashar yake kaman ɗan tasha yana cewa Na'ila ta fito ita da yaranta duk su koma gidansa ai ya'yansa ne kuma ita matarsa ce saboda haka duk suna karkashin ikonsa. Da suka gaji da jin sokiburutsun sa ma kowa kama gabansa yayi ya wuce daki. Sai da suka karya cikin natsuwa duk da kowa da abinda ke yawo a ransa Nura yace Faridah ta fito ya sauke ta a school bayan ya jaddada wa Fiddausi da ko sama da kasa zata haɗe kada ta bude kofar. "Kin dai ji na gaya miki ko ma waye kar ki kuskura ki bude." To take ta cewa tana gyada kai kaman lizard. Faridah na bude wa Nura gate Baba dayake maqale a jikin gate din yayi wuff ya daka tsalle ya shige gidan yanata muzurai. Da ka ganshi zaka san cewa a rikice yake. Nura ya fito a zafafe ya nuna masa hanyan fita da yatsansa " malam get the hell out of my house ! Waye kai da zaka shigo min cikin gida batare da izini ba ?" Ya fada a zafafe yana nuni da cewa bai ma san Baban ba bayan duk wanda yasan Baba yana ganin Nura yasan jininsa ne saboda da kamannin da body build din duk na uban ya dauko. Wannan yana daya daga cikin dalilin da yasa Nura baya son kallon madubi saboda hakan na masa fami.
YOU ARE READING
ƳAR BAƘA
General FictionSabirah baƙa ce. Irin baƙin nan mai maiƙo, ga muryarta mai kauri da amsa kuwwa. Tana fuskantar tsangwama da izaya kala kala a wajen mahaifiyarta da ƴan uwanta da babu wata ƙauna da shaƙuwa a tsaƙaninsu. Shin zata iya haƙuri da ƙulubalen rayuwa ko ku...