7

60 9 0
                                    


Goma da arba'in da uku tayi musu a cikin gidansu Khairiyyah wanda yake a Federal  Lowcost. Yaya Muhammad ne ya dauko su daga tasha don sun same shi ma yayi parking yana jiran isowarsu. Sai tsokanar Sabirah yake wai yar kauyen Kano tazo birni. Ita dai ba abinda take sai murmushi saboda ta dade bata ganshi ba kuma batayi tunanin zai sake da ita har haka ba. Hira suke da Abba yana tambayarsa aiki. Anan taji cewa an kusa aurensa. Da sallama suka shiga falon da yake tashin sassanyar kamshin turaren wuta hadin yan Maiduguri.
"Waalaikumussalam ! Maraba lale da mutanen Kano" Inna ta fada cikin sakin fuska tana fitowa daga kitchen da tray a hannun ta. Kafin su amsa kuwa Khairiyyah ta fito da gudu tana ihu Oyoyo oyoyo ta rungume Sabirah cike da karaɗi da tsananin murna.
"Wai dan Allah yaushe zaki girma ne ?" Yaya Muhammad ya tambaya yana dariya. Amincin yaran yana burge shi.  Guri suka samu suka zauna aka gaggaisa da tambayar ya bayan rabuwa da yan uwa da abokan arziki.
"Ai sai ki kaita daki tayi wanka tazo taci abinci tunda da sauran lokaci kafin azahar" Inna da suke kira da Ammah tace tana hararar Khairiyyan da ta kasa nutsuwa kamar ta mayarda Sabira cikinta tsabar dokin zuwanta.
"Ya hanya mutuniyar ?" Ta sake tambaya karo na ba adadi. Sabirah ta murmusa tana neman kofar banɗaki.
"Dan Allah fitsari ya matse ni Khairee. Ki bari na rage marata tukunna"
"Bazaki gane yanda nayi missing ɗinki bane. Ga zani nan zakiga sabon  soso a leda da sabulu sai kiyi wankan gaba daya ki fito muje ki karya. Da kaina na shiga kitchen saboda ke" Sabirah sai mamakin tarbar da ta samu take, hatta me aikin gidan sai da tayi mata oyoyo yau dai ga Sabiran da aka ishe su da labarin ta tazo. Tanata mamaki da yaba tsari da tsaftar bandakin tayi wanka ta fito. Da gajiya a tattare da ita shi yasa ruwan zafin yayi mata dadi tunda wannan ne karo na farko da ta taɓa fita daga cikin garin Kano. To ina ma take zuwa ? Ko hidima ake yi a dangi sai dai taji labari ba zuwa ake da ita ba. Idan ta haɗu da dangi to zuwa sukayi gidansu kuma basu wani cika zuwa ba saboda halin Umman. Danginta ma daidaiku ke raɓarta balle kuma na su Abba.
Tana fitowa tasamu Khairiyyah ta aje mata kaya sababbi irin free sized gown din nan da turare da man shafawa. Mamaki ne ya cika ta wai ita ake wa tarba haka kamar wata yar sarki ko wani hamshaqin mai kudi? Wani bangare na zuciyarta yana faɗa mata ai ya kamata ayi mata fiye da haka ma amma mafi rinjayen ɓangaren kuma yana fada mata duk bogi ni, da an kwana biyu zasu fara hantararta da zagi da cin mutunci saboda yanayin halittar ta. A haka dai tanata tunani marasa kan gado ta shirya tana jiran shigowar Khairiyyan domin yunwa na sakadar cikinta. Kaman tasan tunanin da take yi sai ga Khairiyyah ta shigo tana cewa " wai canza fata kikeyi ne ko daman haka kike dadewa a toilet?" Ganin da tayi mata a shirye tsaf sai tayi shiru tana jan hannunta zuwa falo.
"Ashe tun tuni ta shirya Ammah wai bakunta take yi kamar ba gidan su tazo ba"
"Kinsan ita kanta baya rawa kamar naki ai " Ammah ta faɗa tana mika mata cup din da ta haɗa mata tea me kauri.
"Fara da wannan ki warware hanjin ki, Abbanki yace baku ci komai ba kuka fito. Ya hanya? Ya kika ga garin namu?" Haka ta ringa janta a jiki har ta ɗan ware tana amsa mata tambayoyin ta . Kafin ta gane me ke faruwa ta tayar da abincin tas kuma yayi mata dadi sosai da sosai. Bayan sunyi azahar Abba yace shi zai koma Ammah kuwa ta kasa ta tsare tace ai sai ya kwana. Babu yadda ya iya haka aka gyara masa dakin Mubarak da yake school. Chan ya wuce don ware gajiya kafin Baffan su Khairiyyahn ya dawo daga aiki.
A dakin Khairiyyah kuwa hira ce ta ɓarke tsakanin aminan juna. Yawancin labarin littafin da suka karanta ne sai na Kawayensu. Khairiyyah sai sharri take yiwa Sabirah data nuna mata waya wai ba saban ba anyi waya ba zama kuma. Tace karta damu da ta biya ta zata tura mata applications na karanta novels da kuma yadda ake sauke su a karanta. Dariya kawai tayi tace mata to don tasan idan ta biye mata ba gajiya zata yi ba sunyi ta fama kenan har dare.

Abba ma yaji dadin tarbar da aka yi musu kuma yayi amanna cewa ko bayan ransa Umaimah (sunan Innar) zata riƙe masa Sabirah amana kamar ƴar da ta tsugunna ta haifa. Da maigidan ya dawo da kansa yaje har dakin Mubarak din suka gaisa saboda yana matukar girmama shi. Bayan sun gaisa ne ya gyara zama yace.
"Yaya daman ko baka zo ba ina tunanin zuwa Kanon na same ka"
"To! Da fatan dai lafiya ba wani abu ke faruwa tsakanin ka da Umaiman ba"
"Haba yaya ai mun girmi wannan kuma, a da chan ban kawo karar ta ba sai yanzu da muka kusa aurar da ɗa" ya faɗa yana dariya domin kuwa har hankalin Abba ya tashi.
"To to madallah, har hankalina ya tashi. Wacce magana ce wannan takwara ? ( Dayake duk sunansu na asali Muhammad)"
"Umaimah kullum da zancen ƴar wajenka take kwana take tashi, babu ranar da za'a wuni a kwanta batayi zancanta ba duk da cewa bata fito ta fayyace min halin da gidanka yake ciki ba nasan tabbas akwai matsala dangane da yarinyar shi yasa nace zan rokeka alfarma da ka bar mana ita ta dawo hannun mu. Ni kuma nayi maka alkawarin in shaa Allahu bazaka taɓa yin dana sanin zamanta anan ba"  sai da Abba ya numfasa cikin jin dadi domin da kudirin da yazo kenan amma sai yaji kunyar sanarwa ƴar uwarsa tunda bai san ya mijin ta zai dauki maganar ba.
"Alhamdulillah. Ɗa ai na kowa ne kuma bani da haufi akan Umaimah. Bani da abinda zance sai dai nayi muku godiya kuma nace Allah Ubangiji ya baku ikon sauke nauyin da ya hau kanku, Allah ya kaɗe fitina yasa wannan ya zama dalilin shigarku aljannah. Hakika Sabirah na bukatar zama a cikin ahali irin naku. Nagode da karamci Muhammad. Dan Allah kada ku bari ta sake yin kuka akan yanayin halittar ta. Ku bata kwarin gwuiwa"
"Haba Yaya babu komai wallahi. In Shaa Allah zakayi mamakin yadda zata koma idan kuka hadu bayan wani lokaci domin kaf mutanen gidan nan kaunar ta suke yi sosai. Kuma in shaa Allah zamuyi iya bakin kokarin mu wajen wanke mata tabon da akayi mata." Nan Abba ya zauna ya fayyace masa duk irin halayen Habi da Suhaila da abubuwan da suke mata saboda ya fahimci girman abun. Ran Baffah ya ɓaci matuka ya ringa al'ajabi da kokonton kasancewar Habi mahaifiyar Sabirah.
"Ko dabba tana son ƴaƴanta. Anya Habi ce ta haife ta? Anya babu wani boyayyen al'amari akan yarinyar nan?"
"To ni dai iya sanina itace ta haife ta. A lokacin nayi tafiya na dawo na samu ta haihu dukda cewa nayi mamakin kalar yarinyar tun a wancan lokacin amma banga wata alamar da zata nuna ba ƴata bace tunda dai na barta da ciki haihuwa yau ko gobe kuma nasan Ubangiji yana iya yin yadda yaso ga bawansa "
"Haka ne kam. Allah ya shirye ta ya ganar da ita gaskiya. Allah Ubangiji ya bamu ikon rikonta amana." Suka amsa da amin suka cigaba da hirarrarrakinsu akan siyasa, yanayin ƙasa da abubuwan da suka shafe su. Ammah kuwa ganin shirun yayi yawa don har sunje masallaci anyi maghrib da Ishaa suka sake komawa dakin Mubarak din shine ta biyo sahu.
"Haba bawan Allah. Kai haka akeyi kawai sai ka maƙale min dan uwa ka hana ni hirar yaushe gamo da shi?" Ta tambaya cikin sigar tsokana.
"Tuba nake ranki ya dade. Yanzu muke shirin shigowa cin abinci"
"Ya kamata dai, ga yara chan sunata jira hatta Muhammad ya ƙosa" tashi sukayi suka bi bayanta har suka isa falon inda aka baje ƙatuwar ledar cin abinci. Al'adar gidanne cin abinci tare. Khairiyyah da Sabirah daman sun dade a falon suna kallon wani Indian series da take ta zuzuta shi. To ita ina taga lokacin wani kallo ma? Kuma bata tunanin ma dish dinsu na aiki domin taga hamshaqiyar ta daina zuwa dakin Umman kallo.
Suna ganin shigowar su Baffan suka miƙe suna masa sannu da dawowa don lokacin da ya dawo suna daƙi yace a bari ya gaida Abba kafin ya shigo su gaisa da Sabirah. Fuska a sake da fara'a ya amsa yana tsokanarta "mutanen jami'a kufa yanzu manyane kun fi karfin wulakanci" Khairiyyah ce ta biye masa suka cigaba da barkwanci Ita kuwa sai murmushi take. Nan aka baje aka ci abinci cikin nutsuwa. Khairiyyah da Sabirah a plate daya, Muhammad da Abba a plate ɗaya sai Ammah da Baffa suma a plate ɗaya. Da tayi niyyar haɗawa Baffa da Abban yace a'a a haɗa masa da mutuminsa Muhammad. Bayan sun gama cin abinci sun kwashe komai an kai kitchen inda me aikin take jira su gama ta wanke ne Sabirah tafara naɗe hannun riga tana kokarin farawa.
"Baki ma da hankali. Daga zuwanki ko kwana bakiyi ba zaki fara wanke wanke. Ki fito mu wuce tun kafin Ammah tazo ran kowa ya ɓaci" haka tanaji tana gani ta bi bayan Khairiyyan zungui zungui suka nufi dakinta. Anan ta tuna da gift bag din ta miƙa mata akan takai falo. Ai kuwa tace sai dai su kai tare. Suna zuwa tun kafin Ammah ta buɗe take saka mata albarka cikin tsananin farin ciki. Da aka miƙawa Baffa nashi shima albarkan ya saka mata kuma yarinyar sai ta burge shi. Yaya Muhammad ma godiya yayi da tsokanarta cewa tunda Mubarak baya nan duka biyun sun zama nashi. Oganniya Khairiyyah kuwa ihu ta saka tana cewa ai Sabirah ta gama burgeta. Ta gama mata komai a rayuwa.
"Sannu drama queen. Ko ticket din hajji aka baki ai sai haka. Mutum ace banda kwadayi da shan zaqi babu abinda ya iya. Bari na debi rabona kafin ki cinye " Yaya Muhammad ya faɗa yana kokarin karban ledar hannun khairiyyah. Ai kuwa ta daka tsalle ta rungume ledar tayi daki da gudu tunda tasan basa shiga dakinta itama bata shiga nasu. Wannan dokar Baffansu ce.
"Kai dai anyi babban kobo wallahi. Ko da yake kunfi kusa. Sabirah je ki kwanta ki huta kinji Allah yayi miki albarka mungode kwarai Allah ya bar zumunci ya saka da alheri"Kuka ne ya kusa kufce wa Sabirah wai itace yau ake cewa taje ta kwanta ta huta kuma ake kwarara mata addu'a akan abinda tasan mutanen gidan sunfi karfi? Anya ba mafarki take yi ba kuwa? Duk zumudin da take yi akan sabuwar wayarta sai ya gushe ta samu wuri ta kwanta. Da Khairiyyah ta dameta da tambaya ma cewa tayi kanta ke ciwo kuma da gajiyar hanya shi yasa tayi mata sannu ta kashe musu fitilar dakin suka kwanta duk da ita ba baccin takeji ba sai ta dau wayarta ta cigaba da karatu.
Duk da cewa da gasken akwai gajiya a jikinta amma bata kai wadda take yi a kullu yaumin a gidansu ba. Mamaki take yi da irin tarbar da aka yi mata kuma gata a kwance a saman gado da katifa mai taushi ba irin tata ba da bata da maraba da tabarma kuma shekarun baya Abban ya canza musu katifu sai Umman ta dauke tata ta siyar wai ai babu abinda waccan tayi kuma tunda Abban ba shiga dakinsu yake ba bai san abinda ya faru ba. Haka ta ringa wasikar jaki har bacci ya kwashe ta.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now