9

90 8 3
                                    

KANO
Tun a wunin ranar da Sabirah ta tafi Umma ta gane wautar da ta tafka na ƙin dagewa akan idan ma karatun Sabirah zatayi to tayi shi a Kano ba Gombe ba. Gaba ɗaya gidan ya kacame babu daɗin kallo a da kuwa ko ina fes fes tunda ko an ɓata Sabirah na gyarawa shi yasa ko da yaushe a tsaye take tana aikace aikace babu hutu. Suhaila ma sai ƙunci take tafintanta tayi tafiya. Imam ma sai begen Sabiran yake yana cewa ta tafi dadi ya ƙare domin kuwa hatta girkin Sabiran yafi na Umma dadi. Abbas kuwa ko a jikinsa tunda ba shiga Sabgar kowa yake a gidan ba, amma a kasan ransa yaji dadin tafiyar Sabirah. A cewarsa kowa ya ɗanɗana kuɗarsa.
Bayan kwana biyu kuwa da ta ishi Suhaila da yi wannan yi wancan da sassafe take katse baccinta na jaraba ta bar gidan sai dare take dawowa. Abba kuwa daman yana dawowa kwana ɗaya yayi a gidan ya tafi harkokinsa. Ko tambayar Sabiran da mutanen Gombe Umma batayi ba kuma baiyi mamaki ba. Zancen Bashir ta dame shi dashi akan suna son turowa yace mata yana sane, bai karasa binciken da yake a kansa bane shi yasa daya kammala kuma zai sanar da ita su turo. Yana mamakin son zuciya da rashin hankali irin nata. Banda haka kina azarɓaɓin aurar da yarinya bayan kinsan babu abinda ta sani sai rashin kunya da son jiki kuma yaro saboda kawai yanada kuɗi bashi da wani aibu a wajen ki. Yasha zaunar da ita yana mata nasiha akan yadda ta sakalta Suhaila, ba gata bane kuma tana yin kuskuren da dole sai tazo tana dana sanin yin haka amma ta kasa fahimtarsa. Gani kawai take tunda ba Sabirah bace shi yasa yake sukar abun. Kuma waya ce masa dan Suhaila bata aikin komai a gidan yana nufin bata iya ba? Daman aikin gidan zama ake a koya ba iyawa ake tashi da shi ba? Ita Sabiran da take bauta ai ba zaunar da ita tayi tana mata bitar darasi ba. Duk ta inda ya ɓullo mata tanada kafar kare kanta. Haka yayi ya gaji ya rabu da ita yana mata fatan shiriya ita kuwa Suhaila yana mata fatan Allah ya shiryeta kuma ya bata miji nagari mai hakuri wanda zai juri wauta da rashin iya aikinta. Yaso kwarai ya Kaita wajen yan uwansa ayi mata horo amma yasan halin Umma zuwa zatayi ta tona masa asiri kowa yasan irin halin da suke ciki a gidansa shi yasa ya hakura.
Sati daya da tafiyar Sabirah, Suhaila ta shigo gidan ranta a ɓace tanata bambami da ɓaɓatun da ba fahimta Umma take yi ba. Sai da ta gaji tayi shiru don kanta kafin ta jefo mata tambaya.
"Ke kuma daga ina kike tun safe sai yanzu kuma kin shigowa mutane gida babu ko sallama kinata faɗa"
"Ai duk laifinki ne Umma. Kinsan irin son da nake yi wa Bashir, kin san cewa shi ɗan boko ne kuma ɗan gayu da ya fahimci cewa ban iya turanci ba rabuwa dani zai yi shine kika bari Saburah ta saka kafa ta tafi wata uwa duniya ba ranar dawowa. To wallahi samun zaman lafiya a gidan nan shine ki bani kudin mota naje na taho da ita don naje na samo lambar ta dakyar kuma tayi min rashin kunya"
"Banda abunki idan turanci yake so ai yar jami'a ko wadda tayi makarantar kuɗi zai je nema ba ke yar malam Shehu ba dayake da tabbacin makarantar gwamnati kikayi kuma yasan cewa baki cigaba da karatu ba banda karyar da kika ɗaura wa kanki. Kuma banda ke ƙarya tayi miki katutu har ni da na haife ki zaki ce wa kin kira wayar Sabirah? Yaushe take da wayar da har zaki kirata. A haukanki Gomben nan da Sabon Gari ce ko Wambai da zan baki kudi kije ki taho da ita ko? To wallahi daman inada cikinki ki fita a idona kuma ki barni naji da abinda ke damuna ko na lallasa miki jikinki. Banza kawai mara tausayin uwarta. Banda rashin hankali irin naki har sai na sakaki aiki zakiyi ko haka kika ga Sabirah nayi a gidan nan?" Suhaila ta cika tayi fam ta rasa inda zata tsoma ranta taji dadi. Maganganun Umma sunyi mata ciwo kuma bata taɓa tunanin jinsu daga gare ta ba. So take yi tace ta bata lambar Saburan ta sakata ta dawo dole. Da tasan baƙar wahalar da ta sha wajen nemo lambar da sai ta tausaya mata. Domin babu yadda batayi da Hafsah ba ta hanata. Ita lambar Khairiyyah ma take nema tace ai tunda suka rabu da Sabirah bata sake ji daga gare ta ba. Sai da ta haɗa da laɓewa a soron gidan inda taci sa'a taji Hafsah na waya da Sabirah kuma tana mata tsiya akan sabuwar wayar tata. Wani yaro mara jin magana kuma ya saba ƴan ɗauke ɗauke a anguwa ta samu ta bawa Naira dari biyar tace ya shiga gidan ya sato mata wayar Hafsah. Taci sa'a kuwa babu password nan da nan ta shiga call log ta kofe numbar da Hafsah tayi saving da Rabin rai. Bawa yaron tayi ya mayar kuma akayi rashin sa'a aka kamashi. A tunanin su ma a lokacin yazo ɗaukar wayar shine akayi ta jibgarsa yana ihu yana cewa ba sata yayi ba ɗaukowa aka saka shi yayi. Da aka tambayeshi waye yace Suhaila kuma ya nuna kuɗin da ta bashi. Ai kuwa ganin haka Suhaila ta arta a ɗari tana haki ta samu ta laɓe a gidansu kawarta. Samarin har zasu bita sai Ummansu Hafsah tace su rabu da ita kawai zasu magance abun a cikin gida. Hafsah tayi kwafa tace "amma dai Suhaila anyi jarababbiya wallahi. Umma kinsan duk abun nan akan lambar wayar Sabirah tayi ?"
"Haba dai Hafsah. Ita kuwa me yayi zafi?" Umman ta tambaya da mamaki.
"Allah dagaske nake Umma baki ga ta dawo da wayar ba? Ai tayita nacin na bata lambar na hana shiyasa. Allah dai ya shirye ta kuma wallahi ni kunyar Sabirah nake ji don tana kiranta tasan a wurina ta samu kuma saboda gudun ɓata mata rai ko labarin takurar da take min akan lambar ban bata ba"
"In shaa Allah zata fahimce ki kuma ai ta fi kowa sanin halin Suhailan" haka suka cigaba da jimami da godewa Allah da ba'a sace wayar ba. Gwaggon Hafsah ce tazo akan ta rakata kasuwa sai ta saka wayar a chaji suka wuce shiyasa bata samu damar kiran Sabira ba.
"Nidai Umma don Allah ko bashine ki bani na tafi Gomben. Idan na dawo zan nema na biyaki kudinki idan ma kyautar ce bakya son bani" ta sake faɗa bayan wani lokaci. Ta so ta bata labarin abinda ya wakana amma kuma tasan yanzu tunda haushinta takeji bazata bata goyon baya ba. Daman dai a sha'anin gidan ne bata kwabarta amma duk wani abu da zata yi na jan magana a waje bata so kuma tana nuna mata ɓacin ranta.
"Lallai yarinya har yau baki san wacece Umaimah ba. A duniya akwai wanda ta tsana sama da ni dake ne? Kin cika gajen hakuri wallahi. Sabiran nan zata dawo ba dawwama zatayi a chan ba. Ina zasu iya da kwana da tashi suna mugun gani da baƙar fuskarta. Karki manta yan boko ne kuma yan gayu. Mu ma ba hakuri muke ba dan ya zama mana dole amma su kinsan bazasu iya ba ko don kare mutuncinsu"
"To Umma ya zanyi da Bashir? Na kashe wayata nace ta lalace saboda sai turo min saƙo yake bana fahimta. Shine ya siyo wata sabuwa ya kawo min to wacce karyar kuma zan sake faɗa masa fisabilillahi?"
"Au yanzu ke har waya saurayi ya kawo miki amma banida mutuncin da zan sani? Lallai Suhaila kin riƙa. To ni dai babu abinda zan iya yi miki domin nima na ƙosa ta dawo ko zan huta. Hatta unguwa na daina zuwa saboda bakida amfani. Ki nemi wani ko wata ya ringa duba miki tunda ai ba ita kaɗai ta iya turanci a garin nan ba" daga haka taja tsaki takaici fal cikinta ta wuce dakinta. Duk so da kaunar da take nuna wa Suhaila yanzu Bashir ya fita mutunci a idanunta. Haka suka karasa wunin ranar kowa ransa a ɓace kuma Suhaila sai danna kiran Sabirah takeyi amma tana katsewa. Tunanin ta bai kai akan cewa tayi blocking dinta ba tunda abune da take da amanna bazai taɓa faruwa ba. Haba! Yadda take tsoronta ɗin nan ai abune da ko a mafarki bazata gwada ba.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now