A fusace Nura ya figi motar suka baro gidansu Janan zuciyarsa na masa zafi akan abinda Ummi tayi shirin aikatawa. Da me Janan tafi Khadijansa? Me Janan take dashi banda farar fata?
"Nura kayi hakuri ka yafe min. Nasan na zalunce ka sai Allah ya dubi niyyarka da biyayyarka a gareni ya taka min burki tun kafin na kai ga yi wa rayuwarka mummunan lahani" Ummi ta faɗa muryarta a raunane.
"Hmm" kawai Nura ya iya furtawa saboda tun da abun ya faru kokarin yi wa Ummin uzuri yake akan bata san da zancen ba kawai zumunci tazo. To kuwa Allah ma yana gani akan wannan figaggiyar yarinyar bazai mata biyayya ba domin da ya aureta gwara ya mutu a haka daman Khadijah ce kaɗai ta saka yake ganin zai iya zaman aure da ita kuma Ummi ta bari ta suɓuce masa. Har suka ƙarasa gida ya ajiye ta babu wanda ya sake cewa wani abu domin shi bai ma san me zai ce da Ummin ba. Ita kuwa tsabar kunya da dana sanin abinda ta aikata ne suka hanata sukuni.
Yana ajiye ta gidan Musaddik ya nufa saboda shi kaɗai ne yasan halin da yake ciki kuma yake da tabbacin da zai bashi mafita.
"Ikon Allah. Yau za'a yi ruwa da ƙanƙara babban yaya a gidan ƙanwarsa daya rantse bazai taɓa zuwa ba." Musaddik ya faɗa bayan ya buɗe masa ƙofa sunyi musabaha.
"Banda lokacinka Musaddik. Ina ita Faridan take da bazata zo ta gaisheni ba?"
"Kada ka manta this is her forte, nan gidanta ne saboda haka baka isa kace zaka nuna mata isa ba. Baiwar Allah tunda nace kana hanya ta shiga kitchen tana kokarin neman abinda zatayi da zai burgeka." Ya maka masa harara. Daga jin muryarsa yasan cewa yana cikin damuwa shiyasa yake tsokanarsa don ya kwantar masa da hankali. Tsaki Nura ya ja ya zauna akan two seater yana jingina bayansa da kujerar. Ruwan daya gani akan center table ya dauka ya kwankwaɗe yana mayar da numfashi kamar wanda yayi gudun fanfalaƙi.
Kafin Musaddik ya tambaye shi abinda ke faruwa ya rattabo masa abinda ya faru kafin yazo gidan. Tausayi sosai Nura ya bawa musaddik kuma yaji haushin abinda surukarsa take kokarin aikatawa.
"Yanzu dai fushi ba naka bane. Kamata yayi ka godewa Allah da ya kawo mana mafita. Idan ma saboda wannan yarinyar ta hanaka auren Khadijah kaga yanzu matsala ta kau. Tunda babu yadda za'a yi ta amince ka auri wannan fitsararriyar yarinyar da bata da kamun kai."
"Hmm. Kuma don nine Sarkin marasa kunya na rabu da ita ba tare da nayi mata bayani ba wajen shekara guda kuma kawai sai na koma mata nace na dawo? Haba Musaddik wallahi ko ƴan gidansu bazasu bari ta kulani ba ko da ta yafe min balle ma ganin danayi mata na ƙarshe ya nuna cewa ko ni kaɗai na saura a duniya bazata saurareni ba"
"To yanzu ya kake so ayi? Ka hakura da ita da auren gabaɗaya kake nufi ko me ?"
"Kamar hakanne. Allah ya sani banida kwarin gwuiwar da zan iya sake ce mata wai ina sonta bayan bazan iya fighting akan soyayyarta ba to ya kake gani idan na aureta wata matsala ta taso tsakaninta da mahaifiyata ko ƴan uwana? Bawai ina son aurenta don in cusguna mata ko na hanata samun farin ciki bane, so nake ya kasance daga ranar da ta aureni har zuwa ranar da mutuwa zata rabamu ta kasance cikin farin ciki da annashuwa ba tare da an ɓata mata rai ko sakata kuka ba" Ya faɗa kamar zai yi kuka kuma a lokacin ne Faridah ta shigo da ƙaton tray a hannunta ta aje a gabansa kafin tace.
"Barka da yamma Boss. Ya aiki, yasu Ummi? Yau dai Allah ya amshi addu'a ta kazo gidana"
"Barka kadai Faridah, fatan kuna lafiya kuma babu wata matsala?"
"Idan ma da akwai sai ka bari sai kun keɓe sai ka tambayeta ba a gabana ba" Musaddik ya ɓalla masa harara.
"To ai shikenan kunfi kusa"
Ita dai Faridah dariya kawai take musu saboda babu halin ta shiga faɗan. Tana shiga kowannensu zai ce ta ware shi ko tayi son kai. Duk yadda Musaddik ya kaɗa ya rawa kuma ya nunawa Nura cewa wannan ce damarsa da zai komawa Khadijah ya gyara tsakaninsu ƙi yayi wai shi bazai iya rashin kunya ba. A karshe ya bashi haushi ya tattara zancen ya watsar suka ɗauko wata hirar. Ya daɗe sosai a gidan kafin yayi musu bankwana ya wuce.
YOU ARE READING
ƳAR BAƘA
General FictionSabirah baƙa ce. Irin baƙin nan mai maiƙo, ga muryarta mai kauri da amsa kuwwa. Tana fuskantar tsangwama da izaya kala kala a wajen mahaifiyarta da ƴan uwanta da babu wata ƙauna da shaƙuwa a tsaƙaninsu. Shin zata iya haƙuri da ƙulubalen rayuwa ko ku...