39

44 10 0
                                    

Khairiyyah ta canza sosai kuma tana kokarin wanke laifinta a wurin Khadijah shiyasa take kaffa kaffa da ita da kuma kokarin kaucewa duk wani abun da zai sake saka wa tayi mata yaji irin wanda tayi mata. Yaya Mubarak kuwa ya kasa sukuni a gidan saboda har yanzu yana mamakin irin canzawar da Khadijah tayi masa. Daga gaisuwa bata bari wani abu ya sake shiga tsakaninsu, lokuta da dama ma tana ganinsa take tashi ta wuce ɗaki abunta.

Khadijah kuwa duk irin damuwar da ta shiga game da Nura bata bari an gane halin da take ciki ba. Harkokinta take kamar kullum tana murmushin yaƙe. Idan ta tuna yanayin da ta ganshi a airport sai ranta ya ɓaci. Tana son ta yakice shi a zuciyarta amma zuciyarta taƙi bata haɗin kai.  Hafsah kaɗai ta faɗawa yanayin da take ciki itama kuma sai bata kwarin gwuiwa take akan tayi duk yadda zatayi ta cire shi a ranta tunda dai shi mayaudarine mara imani. Zagi da Allah ya isa ba kalar wanda Nura bai samu ba a wurin Hafsah saboda an taɓo aminiyarta da bata cancanci hakan ba sam saboda a irin yadda take ɗaukan kanta ya kamata ace ta samu mai ƙaunarta tsakani da Allah kuma ya shirya yaƙi da duk wanda zai kawo musu tangarɗa a alaƙarsu.

Babu abinda yafi ci mata rai irin yadda ya fita a rayuwarta ba sallama, bai faɗa mata wani dalili ba sannan yayi hakan bayan ya furta yana sonta da ƴan kwanaki. Kuma ai shi ba ƙaramin yaro bane ta tabbata yasan ita ma tana jin wani abu a game dashi ko da bai kai nasa ba sannan kuma ai sun shaƙu da junansu wannan ma abun dubawa ne. Da tafara ire iren tunanin nan take saurin neman abinda zai ɗauke mata hankali daga yin hakan saboda sosai take jin zafin abinda Nura da Mubarak suka aikata mata kuma bata tunanin zata sake yarda da wani namiji. Ta godewa Allah ma da tunda suke da Ammi bata taɓa tambayarta akan saurayi ba ko tayi mata wata magana da zata nuna cewa tana zumuɗi ko ɗokin aurar da ita.

Sun koma makaranta an cigaba da karatu suna harkarsu daga ita sai Amatu kamar yadda suka saba tun farkon zuwansu makarantar. Suna shan zagi da tsinuwa a wurin mahassada kuma an musu laƙani da masu girman kai da ganin kowa bai isa ba amma ko a jikinsu, basu ma san anayi ba. Iyakar su da kowa sallama da gaisuwa daga nan kuma basa ƙara bi ta kansu.

Damuwa dai har ta so ta fara kawo mata tangarɗa a wajen karatunta sai da ta dage da addu'a sosai sannan ta samu sassauci. Ga business sai samun customers take yi ta inda bata zato saboda amincin kayansu kuma  nasibin da Allah ya bata. Har mamaki take idan ta shiga Instagram taga anyi order ko taga baƙuwar lamba tayi mata magana a WhatsApp. Maman Amatu ma sari ta fara yi a wurinsu saboda ita ma ƴar komai da ruwanka ce. So take yi ta samu inda ake koyar da ɗinki ta cigaba daga inda ta tsaya a shagon Nura saboda sun fara shawarar fara business ɗin ɗinka kaya da yadinsu su siyar ita da Ammi. Tasan amfanin neman nakai shiyasa bata wasa da duk wata damar da zata samu.


_______

Abun duniya ya fara haɗuwa yayi wa Ummi yawa domin ta kasa gane kan ƴaƴanta gabaɗaya. Gidansu da kullum yake cike da annashuwa yanzu kamar maƙabarta ya koma. Nura idan ya fita tun safe sai dare ya tsala yake dawowa haka Fiddausi ko da yaushe tana ƙunshe a ɗakinta. Faridah ma sai tayi sati bata kirata sun gaisa ba. Gashi ta tuntuɓi ƙawarta Hajiya Amina akan zancen haɗa yaransu sai ce mata tayi ai babu tabbas a zancen sannan babu ranar dawowarta ƙasar sai ta dawo ta tantance idan Nura yayi mata.

"Amma ai ba haka muka yi dake ba" Ummi ta faɗa ƙirjinta nayi mata nauyi.

"Kamar ya kenan Hajiya Na'ilah? Daga faɗar magana da wasa sai ki dauke ta da muhimmanci? A ƙarni na ashirin da ɗaya fa muke. Ba'a yiwa yara auren dole balle ma a yadda nake matukar son Janan bazan taɓa hanata abinda take so ba ko nayi mata dole. Idan har kina son haɗa zuri'a dani to ki jira dawowar shalele tukunna komai yana hannunta"

Baki Ummi ta sake tama rasa me zatace. Wato ita ce banza da batasan zafin haihuwa ba har da za'a dinga gasa mata magana. Ta riga da ta ɓata rawar ta da tsalle a wajen yaranta kuma bata san ta inda zata bi ta gyara ba. Ta hana Nura muradin ransa saboda son zuciyarta gashi tun ba'a je ko ina ba Hajiya Amina ta fara nuna mata iyakarta. Gashi ita bata da abokin shawara dama da yaranta take tattauna duk wata matsala da ta taso amma yanzu ai sai suyi mata dariya.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now