19

53 7 0
                                    

Ranar da Sabirah ta koma ko numfashi bata sauke ba Khairiyyah ta ja ta daki cike da ɗoki. Dakyar ta barta ta koma falo domin gaida Ammah da Baffa.
"Daga gani gulma ke cinta bazata iya haƙura ba shiyasa ta jaki daƙi. Allah dai ya shirya" Yaya Mubarak ya faɗa yana kurɓar zobon da Baba Zuwaira ta haɗa domin tarbar mutuniyarta Sabirah.

"Kai Yaya Ba. Bana son sharri. Wataƙila missing ɗina tayi sosai shiyasa" Sabirah ta faɗa tana kokarin kare Khairiyyah.
"Koma ɗakin kiji zakice na faɗamiki"

"Wai kai yaushe zaka girma ka daina shiga shirgin mata ne?" Baffa ya tambaya.

"Ai Baffa babu rana tunda dai ni wan mata ne. Dan ma Allah ya taƙaita basu koyamin gulma da haɗa wuri ba"

"Lallai kuwa ka shahara. Wato har ni mahaifiyarka na iya gulma da haɗa wuri kenan?" Ammah ta saka baki tana harararsa.

"Haba Queen. Kefa sarauniyar duniya tace. Ba dake nake ba da wa'yannan ƙananun kwarin nake"  dariya suka yi aka cigaba da raha Khairiyyah tana can tana jiran Sabirah ita kuwa shaf ta manta da ita. Sai da ta gaji ne ta dawo falon tana aika mata da takubba ta idonta.
"To idan ba gulma ba ki faɗi abinda ke ranki mana kin tsaya kina harararta. Idan kika ɓatamin rai sai na maida ta Kano yanzun nan "

"Ni yaushe nace gulma zan mata. Kawai fa zan bata labarin zuwan da Dr Nura yayi gidan nan yana neman izinin su Ammah akan Sabirah ta fara zuwa therapy" habawa nan da nan ran maza ya ɓaci ina wuta Mubarak ya jefa Khairiyyah. Shi shaf ya ma manta da wanzuwar iyayensu a falon.

"To ubanwa yace masa tana buƙatar taimakonsa banda dai shi wawa ne? Sun rasa patients ne a asibitin da zai zo wani neman izini? Babu alheri a tattare da gayen nan shiyasa kallo ɗaya nayi masa naji ya sire min"

"Ba shi bane yayan Faridah da kake yawan bani labari akan irin yadda yake kula da mahaifiyarsa da ƙannensa?" Ammah tace tana mamakin yadda ya ɗauki zancen da zafi bai ma ji karshen maganar ba.

"Ai a da ne Ammah, yanzu ya lalace" har Ammah zata ce wani abu Baffa ya dakatar da ita da ido. Murmushi kawai yayi irin nasu na manya ya kalli Mubarak yace "Ya isa haka tashi ka wuce ɗakinka ka huta "

"Wallahi daga ke Khairiyyah har Sabiran ku kiyayeni. Sai na ɓallawa yarinya ƙafa idan ta sake ta kula shi. Aikin banza aikin wofi kai. Mutum yayita bibiyar yarinya kamar maye" haka ya fice yana ƙunƙuni sai masifa yake surfawa shi kaɗai. Sabirah dai tunda aka fara diramar kallon ikon Allah kawai take tana kuma mamakin abinda ke sakashi hasala irin haka indai akayi zancen Nura a gabansa. Dukkansu faɗan albarkacin bakinsu sukayi akan yadda Mubarak yayi reacting kafin Sabirah ta wuce kitchen domin ɗaukar abincin da aka dafa na tarbar su. Sosai taji dadin yadda aka nuna farin cikin dawowarta da kuma yadda akayi kewarta.

Ashe bayan sati ɗaya da tafiyarta ne Fiddausi tawa Khairiyyah magana ta Whatsapp akan suna son yin odar awara. Sai take ce mata ai Sabirah taje Kano sai ta dawo za'a cigaba. Bayan wasu awanni sai taga kiranta wai yayansu yace idan Babansu yana gida dan Allah tayi masa magana yana son ganinsa. Bata kawo komai a ranta ba ta sanar wa Ammah da Baffa kuma tayi musu bayanin yadda akayi ta sansu. Anan Ammah take cewa ai tasan Faridah ƴar ajinsu Mubarak ce. Sai bayan maghriba suka zo harda Faridah suka wuce daƙinsu Khairiyyah. Bata san zancen da sukayi ba sai da suka zo tafiya ne tayi musu rakiya Nuran yake faɗa mata dalilin zuwannasu saboda kallon tuhuma da shaƙiyancin da take yi masa.

"Su Yaya Ba dai. Ko dai ko dai?" Khairiyyah ta faɗa tana kallon Sabirah da ke faman aika loma bakinta don sosai abincin yayi mata daɗi.

"Ko dai me? Kin fara zancen iskar naki ko?"

"Ai ba maganar Dr Nura nakeyi ba. Shi nagama tabbatar da cewa son ki yake. Wanda muke zaune a gida ɗaya nake magana"

"Da wa muke zama a gidan nan kuma? Kedai Allah ya yaye miki haɗa wuri Khairee"

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now