25

72 9 0
                                    


Lokaci yana ta ja kuma a duk wucewar rana Sabirah tana sake sanin kanta da darajar da Allah yayi mata gashi tayi sa'ar kasancewa da mutane masu kirki da addini da kuma sanin ya kamata. Ta fara sakewa da jama'a sannan ba kasafai take zama tana tunanin abubuwan da suka shuɗe a rayuwarta ba tunda ga makaranta ga sana'ar da Allah yayiwa albarka domin kullum bunƙasa take yi kuma suna ƙara koyan wasu abubuwan suna yi ga kuma karatu daya ɗau zafi tunda a aji biyu da uku ne ake ainihin karatu, aji ɗaya yawanci gabatar da course ɗin ake yi.  Da kanta ta zaunar da kanta tayi karatun ta nutsu akan Yaya Ba da Dr. Nura domin ita ba wawuya bace tasan tabbas akwai abu mai kama da so a zuciyoyinsu kuma ita a halin da ake ciki ba soyayyah bace a gabanta. Tana da burika dayawa da takeson ta cimma a rayuwarta sannan tasan idan su basu zageta ko sunyi mata gori a kan halittarta ba to tabbas wani nasu zai mata kuma bata fatan ta kasance dalilin samuwar ɓaraka a zumuncinsu domin ko wannensu ya taka muhimmiyar rawa wajen mantar da ita rayuwarta ta baya da kuma samar mata da farin ciki da annashuwa. Wannan shine dalilin da yasa ta rage yawan waya da Mubarak, Nura kuma chatting don sai tayi sati biyu ma bata hau Whatsapp ɗin ba. Nura dai ya damu sosai duk da cewa baya son takura mata saboda ya shaƙu da ita sosai komai nasa faɗa mata yake yi. Bai taɓa yarda da wani mahaluƙi kamar yadda ya yarda da Sabirah ba. Ta zama abokiyar shawarar sa da adana sirrinsa kuma ko da wasa bata taba yin hirar abinda ya shafe shi da Khairiyyah, Amatu ko Hafsah ba. Lokacin da ya bata labarin rayuwarsa tayi kuka ta gode Allah kuma ta sake fahimtar cewa kaddararta mai sauƙi ce akan ta wasu kuma ta sake godewa Allah daya rabata da gidansu ta hanya mai sauƙi ba tare da tashin hankali ba. Mubarak kuwa  dayake yana da wadda ke ɗauke hankalinsa da cin lokacinsa ga kuma aiki da yake yi tuƙuru shiyasa bai wani damu ba. A hankali ma dai sai da suka daina waya kullum kamar yadda suka saba ya koma sai ayi kwana biyu zuwa uku babu wanda ya nemi ɗan uwansa. Da khairiyyah ta lura da hakan ta ɗan damu kuma zuciyarta ta bata akwai abunda yake faruwa amma sanin cewa shi Mubarak ɗin bai furta cewa yana son Sabiran ba shiyasa tayi shiru.

Suna aji ana musu lecture ne kiran Umma ya dinga shigowa wayarta babu kakkauta wa. Ta so ta basar saboda tasan Umma bata taɓa kiranta ba amma sai ta kasa saboda tunanin cewa ko wani abun ne ya faru da Abba. Neman izinin malaminsu tayi sannan ta fita daga ajin wanda shine karonta na farko na yin hakan.  Sallama tayi bayan ta katse kiran ta sake kira sai dai muryar Suhaila ce ta doki dodon kunnenta.

"Baki iya gaisuwa bane malama?" Ta faɗa tana yatsina fuska kamar tana ganinta.

"Eh ban iya ba. Menene kike ta kirana kamar wadda tayi miki sata?" Sabirah ta mayar mata da martani.

"Saburah ni kike wa rashin kunya? " Suhaila ta tambaya cikin matsanancin mamaki baki a sake, cire wayar tayi daga kunnenta ta kalli screen ɗin ta tabbatar da cewa Sabira ce akan layi kafin ta mayar kunnenta.

"Dan Allah Malama akwai abinda nake mai muhimmanci kika addabeni da kira ki faɗamin dalilin kirana ko kuma dan Allah ki barni na koma aji" Wani ashar Suhaila ta lailayo ta maka wa Sabirah sai dai kafin ta dasa aya Sabirah ta kashe wayarta ta juya ta koma aji. Sosai mamaki ya cika Suhaila ko dayake rashin hankalinta ne ya ja mata. Tsaga billenta tayi ta kira Sabirah akan ta taimaka ta aiko mata da kuɗi domin bashi yayi mata katutu gashi bata da hanyar samun kuɗi kuma Umma ta hanata tunda ba jituwa suke ba kuma ko shaye shaye take bata isa tace zata tambayi Abba ba. Abbas ma hanata yayi yace yanada abubuwan yi masu muhimmanci da kuɗinsa sai dai a gaba idan Allah yasa ya samu zai iya bata ɗari biyar. Shine ta kira Sabiran ita ma ta tafka mata rashin kunya. Ƙoƙarin tura mata saƙo tayi da lambar account ɗinta kuma sai ta fasa tana tsinewa Sabirah a ranta kuma ta ɗau alwashin indai suka haɗu sai tayi mata shegen duka ta sauke rainin daya shiga tsakaninsu.

Sam babu abinda ta tanada na haihuwa ballantana ayi maganar zuwa asibiti awo. Hankali kwance take sabgoginta saboda ita dai tunda Allah ya cece ta ta bar gidan Bashir gani take bata da sauran matsala a rayuwarta kuma iyayen ma sun zuba ma ido domin ganin gudun ruwanta. Tunani ta dinga yi na hanyar samun kuɗi gashi ita ba wata kadara gare ta ba ko wani abu mai daraja da zata siyar. Nan ta fara bankaɗa kayan Umman tana neman inda tayi ajiya domin ta samu ta biya wata fitininniyar mata mara haƙuri ko da rabin kuɗin da take binta ne ko ta samu ta sakar mata mara tayi fitsari. Babu inda bata duba ba amma ko sisi bata samu ba, har wurin ajiyar Umman da da babu wanda ya sani sai ita ta bincika bata samu ba. Bata san cewa tun zuwanta gidan Umman da daina ajiya a daƙinta ba saboda tasan halinta sarai ita kuwa bazata zauna ta kassara ta ba ga zaman gida gashi Abba ya daina tafiye tafiye ballantana tayi bushasharta yadda take so da kudinsa ko ta fita yawon gulma da neman magana. Haka ta gaji ta koma daƙinsu tana tunanin mafita.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now