35

53 9 0
                                    

A daren ranar Nura yasha kuka kamar wanda aka ce masa Ummi ta mutu. Ya rasa me zai yi da kuma irin tunanin da zai yi gashi bai kamata ya kira Musaddik a wannan lokacin ba ko ma ya kira yasan ba ɗauka zaiba. Bashi da wani abokin shawara ko na kuka Musaddik ne kwaya ɗaya tal kamar rai.

Tashi yayi ya ɗauro alwala yayi nafila raka'a biyu ya ɗan samu salama sannan ya kira Khadijah wadda a lokacin har ta gaji da jiran kiransa ta kwanta bacci har yayi nisa bata ji ƙarar wayarta ba lokacin da yake kira. Message ya tura mata akan ta taimaka a taya shi da addu'a wani babban al'amari yana faruwa dashi sannan kuma duk rintsi duk wuya tasani cewa yana sonta kuma bai shigo rayuwarta da niyyar yaudarar ta ba.

Da Khadijah taga message ɗinsa lokacin da ta tashi Qiyamul lail kamar yadda ya kasance al'adarta sai da gabanta ya faɗi. Koma menene zata tayi shi addu'a akan Allah ya kawo masa sauki saboda haka bayan tayi sallar asuba sunyi azkhar da karatu ne ta tura masa da martani.

"Allah yana jarabtar bayinsa ta sigogi kala daban daban. Nayi amanna cewa koma menene kana da ƙarfin zuciyar da zakaci jarabawar ba tare da ƙosawa ko sarewa ba. Ina maka fatan alheri a kodayaushe sannan na yarda dakai kuma nayi imanin cewa baka shigo rayuwata don ka yaudare ni ba amma nasan cewa bawa baya wuce ƙaddararsa" tana tura masa ta cigaba da sabgogin gabanta. Wanki ta tara da guga saboda haka tunda ta aje wayar bata sake bi ta kanta ba sai ƙarfe biyu bayan tagama abubuwan da zata yi zata shiga makaranta suyi wani assignment da Amatu.

"Tashi mu tafi Hajiya na shirya" Ta faɗawa Khairiyyah dake kwance tana sana'ar danna waya. Tsabar danna wayarta ma da power bank take yawo saboda koda yaushe wayar ba chaji.

"Gaskiya ni babu inda zan sake fita. Kina gani fa tun 8 na fita ban dawo ba sai 12 yanzu kawai ki sake fitar dani saboda kin maidani drivern ƙarfi da yaji"

"Haba Khairee. Kinsan dai ni ban wani ƙware a tuƙin nan ba kuma ke kika sabar min da hakan. Idan bazaki kaini ba kawai ki faɗa ba sai kin ja min rai ba" Ta faɗa a fusace daman da sauran haushinta a ƙasan ranta.

"Eh bazan je ba Khadijah. Ai ke ba uwata bace da zaki sakani yin abu dole. Idan kuma taƙamar ki iyayenki ne suka siya motar kada ki manta kafin kisan meye arziƙi da arziƙin mu kika tarar da mu ba matsiyata bane mu balle kice wa...." Katse ta Khadijah tayi da wata irin tsawa jikinta har rawa yake saboda ɓacin rai kafin tace.

"Kada ki kuskura kice zaki zageni Khairiyyah. Shiru ba tsoro bane kawai gudun magana ne kada ki kuskara ki faɗamin maganar banza tunda ke kwata kwata bakya tauna magana kafin ki furta ta. Aikin banza aikin wofi kawai. Kin fi kowa sanin cewa abun duniya bai dame ni ba kuma banda banzan halin da zan miki gori akan wani abun banza wai ita mota. Kece mota ke gabanki gaki gata nan ki kwaɗa ki cinye. Banza mara hankali kawai" taja mugun tsaki ta wuce fuu ta fita a gidan. Napep ta hau ta wuce makaranta ranta na suya.

Khairiyyah dai jikinta ne yayi sanyi. Faɗa sukayi da Yaya Sa'ad shine ta sauke haushinta akan Khadijah sai kuma aka yi rashin sa'a ita ma acike take da ita. Amatu kasa gane kan Khadijah tayi saboda bayan gaisuwa bata sake bari wata magana ta haɗa su ba har sukayi abinda zasu yi kowa ta kama gabanta. Da ta tambayeta ina motar cewa tayi bata sani ba. Kuma indai mota ce ta ɗau alwashin bazata sake shigarta ba ita ba matsiyaciya bace. Ko a da da basu da komai bata kai kanta inda Allah bai kaita balle yanzu kullum ƙara hankali take da sanin cewa duniya batada tabbas.  Motar banza motar wofi harda khairiyyah zata so ta zageta akanta.

"Nasan bazai wuce Khairiyyah ce ta ɓata miki rai ba. Kiyi haƙuri kuma ki ƙara akan wanda kikeyi. Tunda kinsan halinta ki daina bari abubuwan da take suna ɓata miki rai" Amatu ta faɗa. Tasan cewa Khadijah na haƙuri da Khairiyyah sosai kuma ita ma a lokuta da dama abubuwan da take yi suna bata haushi duk da cewa ko da wasa Khadijah bata taɓa mata ƙorafi akan ta ba amma ta gama karantar su dukansu.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now