17

62 7 0
                                    

Sun fara jarabawa lafiya kuma course ɗin da ta rubuta na farko taji daɗin jarabawar sosai domin kuwa ji tayi kamar ita ce ta tsara tambayoyin da akayi musu. Amatullahi ma sai murna take tana yi mata godiya akan taimakon da take mata da kuma yadda take sake bata ƙwarin gwuiwa wajen ganin sun jajirce. Suna hanyar zuwa masallaci domin yin Sallar azahar daga nan kuma su koma Library su cigaba da karatu ne Amatullahi tace.

"Wai nikam Sabirah yaushe amincin mu zai yi kwarin da zaki nuna min fuskar ki?"  Dariya Sabirah tayi tana kokarin basar da zancen sai kuma taga rashin dacewar yin hakan saboda ko babu komai tasan cewa Amatullahi ƙawar arziki ce kuma bata nufinta da sharri.

"Ba wani abu bane fa Amatu. Kawai dai Ni baƙa ce sosai to bana son a dinga kallo na ko yaɓa min maganganu marasa daɗi"

"Amma dai kinsan ko kowa zai miki haka ni bazan yi miki ba. Kuma ai baƙi yafi fari kyau kuma kala ce da ba'a siyanta a kasuwa. A yau idan kika so komawa fara akwai hanyoyi dayawa da zaki bi amma baƙi fa? Babu"

"Idan na faɗa miki dalilin da yasa nake dagewa tuƙuru domin nayi karatu na fito da sakamako mai kyau sai kinsha mamaki" kallonta Sabirah tayi tana neman ƙarin bayani. Nisawa Amatullahi tayi ta fara bata labari.

Mahaifinsu yayi arziki lokacin da yake da rai, ba wai hamshakin mai kudi bane amma kuma Allah ya masa wadatar da zai lura da iyalinsa sannan da ƴan uwa da abokan arziki. A lokuta da dama zai hana su abinda suke so domin ya kyautata wa ƴan uwansa da yaransu. Kwatsam sai Allah ya jarabeshi da cutar da sai da ta kusan talauta su kafin Allah yayi masa rasuwa. Anan ƴan uwansa suka fito da maitar su a fili suka yi kokarin danne musu hakkin su na gado. Akwai yayan mahaifiyarsu Barrister ne shine ya shiga ya fita ya kwato musu hakkinsu kuma su uku ne duka mata. Tun daga wannan lokacin kuma kowa ya juya musu baya babu wanda yake waiwayarsu yaga ya suke rayuwa ko ya taimakawa mahaifiyarsu da wani abu. Ita kaɗai take faɗi tashi dasu, babu irin sana'ar da batayi indai zata kawo mata kuɗi. Ita kaɗai take tallafar rayuwarsu, cinsu, shansu, suturarsu da iliminsu. Idan ka gansu zaka rantse da Allah cewa su ƴan gata ne. Dayake mamansu karatun secondary kaɗai tayi shiyasa bata nemi aiki ba ta zauna a gida tana tarbiyyar su da ɗaukar nauyinsu. Sai da suka tasa suka zama ƴan mata ne kuma dangin mahaifin su suke son aurar dasu ga ƴaƴan su. Da taƙi amincewa shine suka bita da zagi da cin mutunci kan cewa yaranta mata ne idan ba'a dangi ba babu wanda zai auri ƴar mace. Wannan kalma tayiwa Amatullahi ciwo shi yasa ta kuduri aniyar cewa zata jajirce tayi karatu sosai, zata yi iyaka kokarin ta taga ta taka wani tsani na rayuwa da babu mahaluƙin da zai kalleta yace mata ƴar mace ce ita kuma sai ta zama wata abu a duniya ko dan mahaifiyarta da ta sha wahala a kansu taji daɗi.

"Duk wani burina a rayuwa akan mahaifiyatane Sabirah. A kullum da tunanin hanyar kyautata mata da saka mata nake wuni saboda nasan cewa ko me zanyi mata a rayuwa ba zan taɓa biyanta ba amma dai zan kamanta kuma bazan taɓa daina yi mata addu'ar gamawa da duniya lafiya ba da samun masauki babba a gidan aljannah. Idan kika zauna kika nutsu kika duba mutanen da kike rayuwa dasu har ma wa'yanda baki haɗa komai dasu ba zaki ga cewa kowa da tasa matsalar, ta wani kuma tafi ta wani muni da tausayi.  Shiyasa kullum ake son bawa ya kasance mai godiya wa Ubangijinsa saboda dukkan wani tsanani yana tare da sauƙi. Sannan Allah yana jarabtar bayinsa ta hanyoyi da dama. Nasani cewa kina ganin kamar a duniya babu wanda ya kaiki damuwa da shiga tashin hankali ko? To da zaki zauna da mutane kowa kiji damuwar dake maƙale a kirjinsa sai kin kwana kin wuni kina istigfari da hamdala. Bance ki yarda ki aminta dani farat ɗaya ba domin ni shaida ce akan butulcin ɗan adam amma kuma ina so ki san cewa ni Amatullahi ba jahila bace kuma ina amfani da ilimina saboda haka bazanyi miki dariya ko na gujeki akan abinda baki da iko akansa ba"

Shiru ne ya wanzu a tsakaninsu Sabirah tana juya maganganun Amatullahi a ranta. Kusan shigen su Abba yake mata, Ammah, Khairiyyah, Hafsah, Baffa, Yaya Mubarak, Yaya Muhammad. Duk wani wanda tasan yana sonta yana ƙaunar ta tsakani da Allah irin kalaman da yake amfani dasu kenan. Tabbas bata son saɓawa mahaliccinta kuma batason ta zama mara godiya a gareshi akan ni'imomin da yayi mata. Ko irin mutanen dake kewaye da rayuwarta abun godiya ne. Tasan cewa tabbas tayi rashin kulawa da ƙauna ta uwa amma wa'yanda kwata kwata basu san tasu ba fa? Wa'yanda basu ma san yanayin fuskarta ko ɗumin ta ba fa? Su ce me? Basu daina rayuwa ba, suna rayuwa kamar kowa kuma cikin aminci idan basu faɗa maka ba bazaka taɓa tunanin hakan ba. Amatullahi ma kaɗai ta ishe ta misali domin ba don ta faɗa mata ba bazata taba kawowa a ranta cewa ita marainiya bace saboda babu abinda yake nuni da hakan a yanayin shigar ta ko kashe kuɗinta domin sau tari ita take siya musu handout kuma taƙi karɓan kuɗin a wajenta, sannan abinci ma tana yawan siya musu banda abin sha da ƙananan abubuwa kuma yawanci sai tayi musu guzurin kayan maƙulashe sannan tana siyan awarar ta bayan kostomomin data samu ta dalilin ta. Ya kamata ta wanke zuciyarta ta manta da duk wani tabon da mahaifiyar ta da ƴar uwarta suka yi mata ta fara rayuwa kamar kowa kuma ta fuskanci goben ta. Duk wanda ya kalleta yayi mata dariya ba da ita yake ba, shi da Allah, duk wanda ya zageta ko ya faɗa mata magana mara daɗi zatayi kokarin cire abun a ranta domin ta san harda rashin hankali da ilimi ke ɗawainiya da mutumin. Sosai maganganun Amatu sun shige ta kuma ta ƙara tabbatar da cewa ta samu abokiya ta gari wadda zata iya maye mata gurbin Hafsah a rayuwarta duk da cewa basu yada juna ba, zumuncisu kullum ƙara ƙarfi yake domin sune abokan shawarar junansu. Su faɗi tare su gudu tare.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now