Nura yayi tsammanin cewa Sabirah bazata saurareshi da sauƙi ba shiyasa ko kaɗan ransa bai ɓaci ba. Yaji daɗi sosai na jin cewa tanada koƙari damuwa bata kawo nakasu a karatunta ba. Ya sake ɗaura ɗamarar taimaka mata ko ta wacce hanya ce har sai ta yarda ta ƙarbi tayinsa. Kasa haƙuri yayi da barin zancen a cikinsa shi yasa ya kira Musaddik ya fayyace masa komai kuma ya faɗa masa ita ce yarinyar da suka je siyan awara gidansu. Musaddik ya ƙarfafa masa gwuiwa domin yasan abokinsa dai ya kamu kuma tunda abinda bai taɓa tunanin zai faru da dashi bane shi yasa yake ganin tausayin yarinyar kawai yake ba so ba. Wucewa yayi asibiti ya gana da wa'yanda suke da appointment dashi daga nan ya wuce shagonsa na ɗinki domin kammala ɗinkin wani ɗan majalisa. Dayake shine telansa tun kafin ya fara mulki shi yasa bai yarda da bawa kowa ba shi da kansa yake masa ɗinki a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso tunda yana siyarda shadda da yadin maza tura masa kawai yake ta Whatsapp ya zaɓa a ɗinka masa.A gajiye yake sosai ga yunwa tunda dama shi bai san hutu ba tunda Babansu ya juya musu baya. Kullum a cikin faɗi tashi yake na ganin rayuwarsu ta inganta. Babban burinsa a rayuwa yayi suna yafi na mahaifinsa. So yake ya shafe tarihin A. Kumo, ya zamana idan ana labarin masu tashen arziki ko wa'yanda sukayi tashen arziki babu sunansa. Bai ga ta hutu ba idan har yana so hakan ta faru. Wani mutumi ya gani zaune a kofar gate din gidansa. Horn yayi wa maigadi ya buɗe masa. Niyyarsa idan yayi parking sai ya fito ya saurari mutumin. Mai gadin ke faɗa masa cewa mutumin ya dade yana jiransa tun yamma kuma yaƙi shigowa ya jira a rumfar mai gadin. Wucewa yayi domin ganawa da mutumin. Ga mamakinsa yana sallama muryar da bazai taɓa mantawa da ita ba ta amsa. A take ya murtuƙe fuskarsa kuma ya juya da niyyar shigewa cikin gida.
"Dan girman Allah Nura ka tsaya ka saurareni. Kayi min alfarma ko minti biyu ne ka bani a cikin lokacin ka" Baba ya faɗa muryarsa a raunane kamar zai yi kuka.
"Yau kuma da me kazo?" Nura ya tambaya. Kallonsa yayi daga sama har ƙasa take zuciyarsa ta karye domin kuwa mahaifin nasa ya rame ya kwanjame daga dukkan alamu ya dade yana jinya.
"Hakuri nazo na baku. Dan Allah kuyi hakuri Nura ku yafe min. Nasan Allah bazai barni ba da hakkin ku dana dauka" Nura ya dade yana mafarkin wannan rana, ya dade yana ayyana irin cin mutuncin da korar da zaiwa Baba duk ranar da ya tako inda yake da sunan neman gafara amma yau gashi a gabansa, a yanayin tausayi, yana bashi hakuri ya kasa katabus. Tausayi, ƙauna da kiyayyar mahaifin nasa ke dambe a zuciyarsa. Ya rasa wanne ɗaya zaiji kuma wanne zai yi amfani dashi. Bai san ya akayi ba, bai san me yaja shi ba kawai ji yayi ya furta kalaman da kwakwalwarsa taƙi aminta da cewa daga zuciyarsa suka fito "Shigo daga ciki muyi magana, bai kamata mu tattauna a waje ba" shige wa yayi cikin gidan ba tare da ya waigo yaga cewa Baban na binsa ne ko a'a kawai tafiya yake abubuwa da yawa na dawo masa kuma yana mamakin rashin aiwatar da kuɗurin daya ɗauka nayi masa rashin mutunci duk lokacin da suka haɗu.
Da sallama ya shiga falon akayi sa'a duk suna zaune suna kallo. Mutumin da ya shigo da sallama a bayan shi ne ya sa dukkan su tashi tsaye da mamaki a fuskokin su.
"Ummi ga mijin ki nan wai yazo bamu haƙuri" Nura ya faɗa a takaice. Gyada kansa Baba ya fara yi kamar ƙadangare kafin ya sunkuyar da kansa ƙasa.
"Nasan nayi muku laifi, nasan na cuceku na shiga hakkin ku. Na banzatar daku saboda son zuciya da abin duniya da suka rufe min ido gashi yanzu nazo ina dana sani mara amfani. Bansan me yasa nayi fatali da soyayyar dake tsakanina da ke ba Na'ilah, ban san me yasa nayi watsi da ya'yan da muka haifa muka raina cike da so da kaunar juna ba. Ban san me ya rufe min ido ya gusar min da hankali har na aikata hakan ba kuma zan iya rantsuwa da Alqur'ani cewar hakan ba yin kaina bane. Ku yafe min dan Allah da Manzonsa ko zan samu sukuni a zuciyata. Nasan da cewa ban cancanci hakan a wurin ku ba amma ku duba girman Allah ku yafe min" ya fashe da kuka mai tsuma rai jikinsa na rawa kamar mazari. Shiru dukkansu sukayi, Faridah sai hawaye take Fiddausi kuwa da tafi Faridah jin zafinsa idonta a karmashe yake. Ummi tasha tunanin ko asiri akayi wa mijinta amma asiri har na tsawon shekaru goma da ɗori? Wanne irin asiri ne zai yi tasiri akan mutum ya raba shi da iyalinsa gaba ɗaya. Tasan Abdullahi tafi kowa saninsa kuma kafin ƙaddara ta afka musu tana iya rantsuwa akan bazai taɓa iya aikata abinda ya aikata musu ba. Duka da zagi babu irin wanda bata sha ba a wurinsa sannan yanzu daga sama rana ɗaya yazo yace tayi hakuri ta yafe masa ? Akan me to? Tana sane da abubuwan dake faruwa da yaranta, tana sane da cewa Nura ya kyamaci aure saboda abinda ya faru dasu. Tayi masa shiru ne tana binsu da addu'ar samun abokan rayuwa na gari wa'yanda zasu mantar dasu duk wani ƙunci na rayuwa da suka shiga. Har yanzu tana jin haushin sa duk da cewa rayuwarsu ta inganta Allah bai bari sun wulakanta ba amma kuma idan tace ta yafe masa yaci bulus kenan? Idan bata yafe masa ba ita tana tunanin Ubangiji zai yafe mata kurakuranta ne da kuma mutanen da tabbas tasan a ajizanci irin nan ɗan adam ta saɓa musu? Tunani take yi barkatai ta rasa na kamawa sai ji tayi Faridah tace "Tashi ka zauna a kan kujera Baba. Da sanyi a ƙasan kuma naga kamar baka da lafiya" ba Baba ba hatta sauran halittun dake cikin falon sunyi mamakin jin kalaman Faridah.
A hankali ya tashi da niyyar komawa kan kujerar, jiri ne ya kwashe shi har ya kusa kaiwa Ƙasa Nura ya taro shi. Rabonsa da abinci bayan shayi kwanaki uku kenan ga kuma rashin lafiyar da ya kasa sanin tushen ta kuma ya kasa zuwa asibiti domin neman magani. Sannu suka dinga jera masa su kansu suna mamakin yanda zuciyoyinsu suka yi sanyi akan lamarin Babannasu. Zama yayi yana riƙe da kansa da yake juya masa. Hausawa sunyi gaskiya da suka ce tsakanin ɗa da uba da miji da mata sai Allah domin a lokacin har rige rigen yi masa abu suke. A take aka kawo masa ruwa yasha, Nura ya haɗa masa tea mai kauri ita kuma Ummi da ta manta yaushe rabonta da kitchen ta shiga ta dumama sauran farfesun dayake cikin freezer ta turara masa cous cous abincin da ya fi so. Fiddausi ma tanata zunɓure zunɓuren baki ta yanka fruits ta haɗa masa fruit salad me daɗi. Babu wanda yace masa komai amma sai kai kawo suke wajen kyautata masa. Abinda Ya sake karya zuciyarsa kenan, ya ƙara shiga halin dana sani da kaico. Da bai banzatar dasu ba ya tabbata da suna rayuwa tare cikin aminci da kula da juna. A ɗan ƙanƙanin lokaci sun manta da sharrinsa a gare su suna kokarin kyautata masa. Nura kiran wani abokin aikinsa yayi ya roƙi alfarmar dan Allah idan babu takura yazo ya duba masa mara lafiya a gida. Kafin ya karaso Abba ya cinye abincin nan tas sai kace wani mayunwacin zaki. Likita ya duba shi ya bashi taimakon daya dace amma yace su shigo asibiti washegari domin ayi gwaje-gwajen da ya dace a tabbatar da abinda ke damun Baban. Zama suka sake yi ya cigaba da basu hakuri da neman gafarar su. Kowa yace ya yafe Allah ya yafe mana baki ɗaya abinda ya sake karya masa zuciya kenan yayi ta kuka kamar ƙaramin yaro. Hatta Nura sai da ya zubar da hawaye. Anan suka buɗe babin hira aka dinga tuna baya da yadda suka kasance a cikin farin ciki. Sai kusan asuba taron ya watse Nura ya bar wa Baban gadonsa ya shimfida bargo ya kwanta a ƙasa. Dabi'ar baba ce kwanciya da karatun Alqur'ani kuma ga mamakin sa sai yaga Nura ma ya kunna wani MP3 sautin ƙira'ar Sa'ad Ghamdi na tashi a hankali. Wasu siraran hawaye ne suka gangaro kan kuncin sa. Lallai ya tafka babbar asara kuma yayi butulci mafi muni. Babu wanda yayi bacci cikinsu saboda kowa da kalar tunanin da yake. Da safe bayan sun kammala karin kumallo Nura ya ɗauki Baba a mota suka wuce asibiti.
YOU ARE READING
ƳAR BAƘA
General FictionSabirah baƙa ce. Irin baƙin nan mai maiƙo, ga muryarta mai kauri da amsa kuwwa. Tana fuskantar tsangwama da izaya kala kala a wajen mahaifiyarta da ƴan uwanta da babu wata ƙauna da shaƙuwa a tsaƙaninsu. Shin zata iya haƙuri da ƙulubalen rayuwa ko ku...