46

48 5 0
                                    

Sai da sukayi wata biyu da dawowa sannan suka samu lokacin zuwa Kano. A sannan Maman Ibrahim tayi sati Uku da zuwa gidan kuma ta saba sosai da Afnan don haka da ta wuce makaranta suka tafi don ma kada tayi ta kuka. Gwara idan ta dawo kawai taga basa nan. Abbu ma lokacin yayi tafiya saboda haka daga ita sai Mubarak da Afnan a gidan.

Suna sauka gidan Abba Khadijah taso ta fara zuwa amma Ammi tace tayi hakuri tukunna su fara zuwa gida ita ma tana son zuwa yi musu gaisuwa. Dayake hidimar biki ake a gidan sai basu samu kansu ba har sai bayan kwanaki uku sannan suka je. Abba yana ta tsokanar Khadijah akan ta zama ƴar lukuta kuma ya sanar dasu cewa har wurinsa Hisham yazo tare da Sa'ad. Tana mamakin dalilinsa na ɓoye mata saboda har lokacin bai bata labarin cewa yaje Kano da Gombe ba. Koma menene dalilinsa dai ya burge ta saboda ko babu komai ya nuna cewa ita ɗin tana da mutunci da daraja a idanuwansa kuma bashi da niyyar yaudararta. Su Fatimah da Abidah sai murna suke yayarsu tazo. A gidan Ammi ta barta akan zata ɗan musu kwana biyu kafin su koma Lagos.

"Maama ina yaya Suhaila kuwa ?" Khadijah ta tambaya tana suɗe kwanon miyar waken da Maama tayi a matsayin abincin dare. Imam yana daga gefe yana mata dariya wai kamar wata ƴar kauyen da ta shigo birni ta samu kayan daɗi.

"Tana can gidanta tana ƴan zabure zabure da sambatu ita kaɗai. Ta aikata abu kuma yazo yana damunta. Shima Bashir ɗin ance ya rabu da ita ya ƙi yana ganin shima harda laifinsa suka rasa yarinyar. Ya kasa saka ma ransa dangana."

"Ya kamata ayi wani abu akai ai. Ko addu'a sai a dage da yi mata kuma a kaita asibiti wataƙila abun ya taɓa kwakwalwarta."

"Abbanku ma yayi tunanin hakan. Bari ya dawo na sake tuna masa da zancen sai a kaita asibitin Dawanau domin addu'a dai anayi."

"Allah ya bata lafiya yasa wannan ya zama dalilin shiryuwarta "

"Amin yaya ƴar baƙa. Wallahi nifa kullum idan na kalleki mamakin canzawarki nake. Hatta muryarki ta zama ta ƴan gayu masu kwana a cikin AC, sai wani turance mu kike yi kina komai naki da aji" Imam ya tsoma musu baki. Me zasu yi idan ba dariya ba.

"Ka dai san baka wuce nasa Abbas ya dumama maka jiki ba ko? Har abada dai Imam bazaka daina neman magana ba wato? Yaushe nayi turanci tunda na shigo gidan nan fisabilillahi?"

"Ke kuwa ɗanawa yake yi ki bar min auta ya sakata ya wala" Maama ta faɗa tana musu dariya. Sun dade a tsakar gida ana shafta kafin kowa ya wuce makwancinsa.

Bayan ta koma gidan Mama sai ga Umma tazo wai taji suna gari shine tazo ta gaishe su kuma tayi godiya akan ɗawainiyar da ake mata.

"Haba Umma da baki zo ba ai. Nima inada niyyar zuwa na duba ki ban samu lokaci bane" Khadijah ta faɗa bayan ta miƙa mata ruwa a kofi.

"Ba komai Khadijah. Ai duk ɗaya ne. Allah ya saka da alheri yasa ki gama da duniya lafiya."

Ta dade a gidan kuma ko a fuska babu wanda ya nuna mata wani abu. Har ta tashi ta wuce. Mama dai sai da ta tanka tana yiwa Ammi dariya wai a lokacin da aka ga Khadijah yadda ta nuna ko sama da ƙasa zasu haɗe bazata taɓa yafe wa Umma ba yanzu gashi nan sun maida komai ba komai ba.

"Mama gani nayi duniyar nawa take ? Kuma ga Khadijah nan ta dawo hannuna kuma ko kashe ta zanyi bazai maida hannun agogo baya ba. Shiyasa kawai na tura mata aniyarta. Ko aurenta da ta rasa da inada hali dana mayar mata. Kawai dai bana son yin katsalandan a rayuwar auren wasu ne amma ina addu'a idan da rabo Allah ya sasanta tsakaninsu ta koma ɗakinta" Ammi ta bata amsa. Tuni Khadijah ta koma wajen su Rukayyah da Sa'adah suna hirarsu ta ƴan mata.

"Haka ne. Allah ya tabbatarwa kowa da abinda yafi alheri a gareshi."

"Amin".  Ammi mantawa take da cewa Mama surukarta ce saboda ita ta maye mata gurbin mahaifiya tunda ta rasa tata kuma macece mai gaskiya kuma bata da son kai. Ko laifi Abbu yayi wa Ammi rufe ido take tayi masa tas bata la'akari da wai shine ɗanta. Idan Ammin ce mara gaskiya ita ma haka take hukuntata daidai da laifin da ta aikata.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now