36

68 7 2
                                    

Sai gaf da maghriba Yaya Sa'ad ya dawo ɗaukarta don har ta cire ran zuwansa ta canza kayanta zuwa wata free gown ta zaman gida. Horn ya dinga yi mata kamar wanda zasu tashi sama. Imam ta aika akan yace masa tana zuwa kaya zata canza. Wata sabuwar abayar da Ammah ta siya musu da Sallah ta saka kuma ta haskata sosai da yake tata sky blue ce. Bata tsaya wata kwalliya ba ta rataya jakarta tasa su Hauwa ɗaukar mata kayan tsarabar su maman. Sai da tazo buɗe murfin gaban motar ne ta lura da wannan abokin yaya Sa'ad ɗin a zaune shiyasa ta koma baya ta shiga da sallama suka amsa mata.

"La'asar din kenan? Ai har na cire kayana na hakura da zuwa sai gobe" Ta faɗa tana maka masa hararar wasa.

"Ayi min haƙuri ƴar Ammi. Hisham ne ya tsayar dani. Kinsan aminina ne tun primary school sai da muka shiga jami'a ne muka rabu kuma daga baya aka daina samunsa ashe mutumin barin garin yayi baki ɗaya ya koma ƙasar inyamurai" yayi mata bayani.

"Allah Sarki. Dole kam kuyi hirar yaushe gamo. Na yafe maka" Ta faɗa tana fiddo wayarta daga jaka domin ta amsa kiran dayake shigo mata. Khairiyyah ce ke kiranta. Kamar bazata ɗauka ba kuma sai ta ɗaga da sallamarta kamar kodayaushe.

"Haba Khadijah abun har yayi zafi haka da zaki isa amma ko arzikin text bazan samu ba bayan kin kira kowa a gidan nan hatta Baba Zuwaira?"

"Nasan Ammah zata faɗa miki cewar na iso lafiya ne. Kuma nasan ba damuwa kika yi da hakan ba shiyasa ban ɓata mana lokacin kira da amsawar ba. Nagode da kulawa sai anjima" bata jira jin me zata ce ba kit ta kashe wayarta. Bata jin daɗin yadda take yiwa Khairiyyan amma ko yaya ne tana son ta koya mata hankali yadda nan gaba ko a gigin hauka take bazata nemi ta taka ta ba. Har yau kalamanta nayi mata ciwo a zuciya.

"Hala keda mutuniyar ne?" Yaya Sa'ad ya jefo mata tambayar.

"Eh ita ce. Nasan kai kayi gulmata a wajenta "

"A'a wallahi. Ai mun dade bama magana. Faɗa muka yi sosai da ita. Ashe bata faɗa miki ba?"

"Ai kuwa dai ban sani ba. Amma dai kunji kunya. Tun yanzu kuna faɗa harda gaba na tsawon lokaci ina kuma anyi aurenku kuna zama a wuri guda? Yaƙin Badar za'a dinga yi kenan? Kamata yayi ku zauna kuyi maganar cikin lumana da fahimtar juna har kowa ya gane laifinsa ya gyara" Dayake tunda ta shiga motar Hisham baiyi magana ba shiyasa ta manta ta wanzuwarsa a motar ta saki jiki suna hira da ɗan uwanta. Har mamakin yadda take sakewa sosai dasu take yi saboda bata da saurin sabo kuma ba da kowa take surutu ba.

"Bazaki gane bane. Yarinyar na da matsala ne sosai. Bata da alƙibla kuma kanta yana rawa "

"Hakkun. Kuma da rawar kan nata kace kana sonta ba. Nasan cewa tanada halayen dake buƙatar gyara amma ai kai zakayi kokarin nuna mata hanya tunda tana sonka zata bari. Gaskiya bazan bari ka rabu da ita ba saboda ƴar uwata ce ita ma bazan so ayi breaking heart ɗinta ba. Sai danayi maka bayani saboda gudun hakan kuma kace kaji ka gani. Bai kamata ka sare ba tun kafin tafiyar tayi nisa. Allah ma ya taimake ni ban faɗawa iyayenmu ba"

Sosai maganganun ta suka daki Hisham har sai da ya muskuta ya sake juyowa yana mata kallon ƙurilla. Harara ta banka masa kafin ta sauke kanta ƙasa.

"Gaskiya ne sissy. Zanyi yadda kikace. Ayi haƙuri kada a ɗaure ni" bata bashi amsa ba saboda haka suka cigaba da hirar su da Hisham har suka ƙarasa gidan baba. Cewa yayi zaije ya dawo tace wallahi bata san zancen ba ya jira ta su gaisa ya kaita gidan mama idan yaso sai ya wuce yawonsa bazata rasa mai mayar da ita gidan Abba ba.

"Yaushe kika zama ƴar jidali ne Khadijah?"

"Zama daku ne ya mayar dani haka " ta bashi amsa tana shigewa cikin gidan Kakannata.

"Wannan sister ɗin taka captivates me. Ban taɓa ganin mutum irin ta ba"Hisham ya faɗa yana jingina bayansa da jikin motar.

"Allah ko? Ai Khadijah mutum ce. Kowa kuma yana sonta yana yaba halayenta" Sa'ad ya faɗa yana murmushi. Shi mutum mai halayen kirki a kodayaushe ana alfaharin saninsa ko mu'amala dashi.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now