2

80 9 0
                                    

Umma tana shigowa gidan bayan sallar isha'i dabi'ar da Abbansu ya tsana kuma yasha mata faɗa akai banda yawan fitar da take yi akai akai sai kace wata dillaliya bayan bata aikin fari balle na baƙi ta hau kwala kiran Sabirah wadda ke zaune akan abun sallah tana bitar karatun islamiyyar da take zuwa.

"Na'am Umma Barka da zuwa" ta amsa tana tashi da sauri domin zuwa inda Umman ke tsaye tana jiranta.

"Barka dai" ta amsa a dakile. "Fatan kin kammala dukkan aikin dana saka ki?"

"Eh Umma nagama komai saura wanke wanke idan kin gama cin abincin zanyi in shaa Allah" ta amsa a zuciyarta tana addu'a Allah yasa karta bata wani aikin don ta gaji likis wanke wanken takeson yi sai ta saka haƙarƙarinta a katifarta ta huta.

"Ina Suhaila? Ko ita na hango a kofar gidan chan tana hira?" Har ta kai ga kofar daƙinta ta juyo ta tambayeta.

"Ina zato. Don bata faɗa min inda zata je ba".

"Uwarta ce ke da zata faɗa miki? Yarinya sai shegen manyan ce da baƙin munafurci. Idan ma baƙin ciki kikeyi saboda ke har yanzu baki da mashinshini sai dai ki mutu. Aikin banza kai. Daga dawowata na wuni a rana zaki ɓata min rai saboda ke kwata kwata ba'a abin arziki dake "

"Allah ya baki hakuri Umma" ta faɗa a dake zuciyarta na ƙuna amma a zahiri murmushi take. Idan da sabo ya kamata ace ta saba da halin Umman tasu amma mahaifiyar tace ko yaya ta hantareta sai ya taɓa mata zuciya.

Har Sabirah ta gama wanke wanken tayi bacci Suhaila bata dawo ba kuma dama dabi'arta kenan hirar dare kuma ta dade a waje idan Abba yana garine take haƙura. Burin Umma kuma bai wuce kayan maƙulashen da samarin ke kawowa suna ci ba wataran a sammata watarana kuma tanaji tana gani sai dai ƙamshi ya ishe ta a barta ta da sharar ledodi da safe. Inda Allah ya taimaketa kuma shine batada kwadayi da son abun duniya. Idan ta samu karba take tayi godiya idan bata samu ba ko a jikin ta. Tana dai fatan cewa ƴar uwarta ba lalata take ana bata kayan ba domin kuwa duk da batada samari tana jin labarin su da irin yanda suke amfani da kudi domin lalata rayuwar ƴan mata. Tana karance karance sosai dana Hausa dana turanci idan ta samu sukuni shi yasa take dokin zuwan ƴar ƙanwar Abbansu da ita kanta Innar tasu wadda take aure a Gombe. Auren wuri akayi mata kuma sai taci sa'a mijin nata ya barta tayi karatu domin yanzu haka lecturer ce a Gombe State University (GSU) kuma hulda da Khairiyyah wadda suke sa'anni shine ya saka take matuƙar ƙaunar yin karatun.

Washegari ta mugun ciwon kai da zazzaɓi ta tashi. Jikinta har rawa yake saboda haka ta kasa tashi tayi aikace aikacen data saba yi da safe. Jin shirun yayi yawa kuma Imam da Abbas zasuyi latti yasa Umma leƙa dakin don taga meke wakana. Ai kuwa tayi mummunan gani domin rashin lafiyar Sabirah yana nufin watan shan wahalar ta ya kama domin ko lokacin da take zuwa makaranta bawai an dauke mata ayyukan gidan bane. Komai ita keyi banda girkin rana. Shima lokuta da dama idan Umman ta harba yawon nata na fama ita takeyi.

"Ke kuma meye haka?" Ta tambaya.

"Zazzaɓi nakeji sai ciwon kai" ta furta dakyar tana fatan ganin damuwa ko tausayi a fuskar Umman kaman yadda take nunawa yan uwanta.

"Allah ya sawwaka. Bari na bawa Abbas Naira hamsin ya siyo miki paracetamol kisha" ta faɗa tana juyawa batare da tayi yunkurin tashin Suhaila da ko sallar asuba bata yi ba. Da Umma ta bawa Abbas kudin tana kici kicin haɗa wuta ta dama musu koko su sha su tafi ko da dumamen tuwon bai samu ba sai cewa yayi " Umma kinsan dai malaria ke damunta kuma maganin malaria yafi Naira hamsin"

"To ubana shugaban likitoci ai sai ka kwata ka siyo. Zaka bi ka isheni da sanabe. Wallahi ka kiyaye ni" tafiya yayi batare daya tanka mata ba yaje ya bugawa me chemist din gida tunda sassafe ne basu kai ga bude shagon ba. Daya dawo ya shiga dakin yana sauri ya shirya. Kwala wa Imam kira yayi akan yazo ya kawo mata abin karyawa taci tasha magani.

"Nida zan tafi makaranta kana gani nayi latti zakace na kawo ma wannan baƙar abinci. Ai ba kuturwa bace tazo ta dauka" wata irin tsawa Abbas ya daka masa sai da Suhaila ta tashi a firgice tana zare ido.  Da ƙunƙuni ya dauko sandararren tuwon datayi tun yamma ya dankwafar a kofar ya arta yayi waje saboda yasan cewa idan Abbas din ya kamashi me taimakon sa sai Allah.

"Kici kisha maganin ki kwanta. Idan bai sauka ba har na dawo sai mu koma Chemist din ko asibiti" ya faɗa a ƙage saboda yasan ya riga da yayi latti gashi akwai tazara sosai tsakanin gidansu da makarantar su inda yake SS 2.

"Nagode kwarai Abbas Allah ya saka da alheri " Sabirah ta faɗa a hankali domin tasan kuɗin leburancin da yakeyi ne yayi amfani dasu ya siya mata magani. Kuma tasan da bai tausaya mata ya siyo ba sai dai ta mutu tana shan paracetamol.

"Mtsw aikin banza kai daman akan wannan baƙa me baƙar aniyar kake wa mutane ihu a kunne. Zaka fice min daga daƙi ko sai na mareka?" Suhaila wadda har yanzu tsawar da yayi tana amsa kuwwa a kunnuwanta ta fadi. Kallon ki gwada ki gani Abbas yayi mata yasa kai ya fice. Duk rashin mutuncinta bata gwada wa a kansa saboda tun suna yarinta da ta taɓa cin zalinsa ya damƙeta da kyar aka kwaceta take shakkarsa. Har yau da tabon da yayi mata a jikinta. Ba sannu balle Allah ya sawwaka ta juya ta cigaba da baccinta hankali kwance. Sabira dakyar ta iya yin loma biyar na tuwon saboda taste dinsa kaman maɗaci haka take ji. Ta balli magungunan tasha ta kwanta tana fatan Allah yasa kar Umma tace ita zatayi girkin rana ai tasha magani ta warke. Batasan lokacin da baccin wahala ya fisge ta ba sai tashi tayi taga rana ta take. Alhamdulillahi jikin da sauki kuma kan ma ya daina mata ciwon da take daina gani da kyau. Tayi addu'a ta kwashe shimfidar shamulalliyar katifarta ta jingine ta a bango ta dauki kayan wankanta tayi hanyar banɗaki. A tsakar gida ta tarar da Umman har ta gama girki tana kishingide tana jin Radio.

"Umma sannu da gida" ta ɗan rissina ta gaida ta. Ga mamakin ta sai Umman ta amsa harda tambayarta jiki tace dasauki. A zuciyarta tana jin dadin taimakonta da Allah yayi Umman a ƴan mutuncin ta tashi. Ta fito daga wankan tayi sallah tana zaune a ɗaki Umman ta kirata.

"Sarkin kinibibi, abincin ne bazaki ci ba ko jira kike na taso na baki a baki?"

"A'a Umma daman yanzu zan taso na dauka. Sannu da aiki" ta fada cikin rawar murya bata son hargowar da Umman keyi saboda ciwon kanta. Dama sam Umman bata tausasawa indai a kanta ne. Ta tuttura abincin dakyar ta sake shan maganin ta kwanta jiran la'asar tana fatan samun sassauci sai tayi ko da wanke wanke ne gudun bacin rai.  A ranar dai kakarta ta yanke saƙa saboda Umman ce tayi komai kuma bata sakata a gaba da korafi ba. Washegari taji dama Sosai saboda haka ta cigaba da harkokin gabanta. Suhaila kuwa ko ci kanki bata ce mata ba har tayi ciwon ta warke. Idan da sabo yaci ace ta saba amma ina bazata iya jurewa ba, abun yana ci mata tuwo a kwarya.


Abbansu ya dawo da tsarabar kayan marmari dana gwari kala kala anata murna domin shi mutum ne mai wadata iyali iya karfinsa shi yasa ma Umman tasu ta naɗe kafa ko tunanin yin sana'a a cikin gida bata yi domin ta rage masa wani nauyi.

"Ƴar albarka ya naga duk kin rame?" Ya tambaya da kulawa yana kallon Sabiran dayake kwana ya tashi da tunani da kuma tausayinta.

"Naɗanyi zazzaɓi ne Abba amma naji sauki Alhamdulillah" ta bashi amsa tana jin dadin kulawar da take samu a duk lokacin da yake gida.

"Mashaa Allah. Allah ya kara afuwa yasa kaffara. Ya zancen sakamakon naku har yanzu? Munyi waya da innarku ta Gombe tace tana son saki  a makarantar da take aiki"  charaf a kunnen Umma.

"Malam wanne irin makaranta kuma? Makarantar ma a chan wata uwa duniya Gombe? Gaskiya bazata saɓu ba. Wannan wanne karatu kuma zata yi bayan wanda ta samu? Kana kallon Suhaila zaune a gida shekaru biyar kenan da gama Sakandire baka taɓa tunanin saka ta a makaranta ba sai wannan ? To aure zata yi duk da ma nasan sai dai a bada ita sadaka ga mara rabo" ta hayayyako da faɗa bata bari ma yaji amsa daga bakin Sabiran ba.

"Idan kin isa Habi ki hanani yin abinda nayi niyya kinji ko? Wallahi tallahi ko bayan raina sai Sabira tayi karatu da izinin Allah. Ita Suhailan taci jarabawar ne ko ta nuna ra'ayin ci gaba da makarantar na hanata? Sau nawa ina muku zancen ke da ita kuna shashantarwa? Nan da Khadijah (Innar Gombe) tazo da zancen wanne irin cin mutuncine baki mata ba?"

Sabirah dai dadi kaman ta tashi ta taka rawa ko ba komai zata yi nesa da gidansu ko Allah zai sa ta murmure ta sakata ta wataya kaman ko wanne ɗa me yanci. Kasan ranta tana addu'ar Allah ya sa taci exams din.  Nan faɗa ya kaure tsakanin Abba da Umman. Sam batajin dadin rashin jituwar iyayenta a dalilinta amma ya zatayi? Tana son fadawa Abban ya bata jarin da zata fara sayar da awara ko sau daya ne a sati amma jarabar Umma ta hana. Haka ta kwanta tana fatan Allah yasa zai kwana biyu a gidan sai ta sameshi da maganar. Ta gaji da zaman haka nan ba abin yi. Duk da tasan ba karamin aikin Suhaila bane ta cinye mata jarin da kawayenta.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now