49

93 8 0
                                    

Lokacin da Baffa ya kira Nura ya sanar dashi cewa Baba yana nemansa a Kano idan ya samu lokaci abun yayi matukar bashi mamaki da yi masa daɗi. Ya tabbatar da cewa mahakurci mawadaci duk da cewa yasha wahala sai yake ganin komai ya zo masa a saukake kuma a lokacin da bai taɓa tsammani ba. Ya tabbatar da cewa da bai yi wa mahaifiyarsa biyayyah akan abinda take so ba kuma ya auri Khadijah a wancan lokacin to haƙiƙa sai sun fuskanci kalubalen da zasu zo suna dana sanin yin auren. Ita uwa ita ce kan gaba a rayuwar duk wani ɗan halak, farin cikinta shine na mutum haka ma bakin cikinta sannan fushinta musiba ne. Sau tari sai ka dinga yin abubuwa baka ganin haske a cikin su, ko Allah ya azurtaka da komai amma baka da sukunin zuciya, ko kuma kaga kowa yana ci gaba a rayuwa har wa'yanda basu kaika komai ba kai kana zaune baka gaba baka baya, ka rasa ina matsalar take? To fushin mahaifiya na jawo hakan. Ita kanta wasu lokutan bazata san da cewa fushinta ke kassara rayuwarka ba. Shiyasa ake son mu kiyaye, mu bisu sau da ƙafa ko zamu rabauta duniya da lahira. A duniya bamu da kamar su. Su kaɗai ne ke mana son da babu son kai a cikinsa. Basa tunanin kansu, ko abinda zamu saka musu dashi, kansu tsaye suke yi mana komai da farin ciki a zukatansu kuma har abada bazasu goranta mana ba.

Su ma iyaye ajizai ne tunda halittar mu ɗaya dasu. Suna iya aikata kuskure kamar kowa, suna iya bauɗe hanya kuma Allah ya bamu damar bijire musu idan har abinda suka umurce mu ya saɓawa addini.  Duk irin wa'yannan abubuwan ne suka saka Nura yiwa Umminsa uzuri bisa ga laifin da ta aikata masa.

Da murnarsa ya sanar da ita abinda ake ciki kuma tayi matukar farin ciki har tana cewa ko zasu je tare?

"A'a ki bari mu fara zuwa da Musaddik tukunna, kinsan yanayin jikinki bazaki iya doguwar tafiya a mota ba"

"To amma gwara muje tare ai na ƙara basu hakuri" ta faɗa.

"Ummi zancen haƙuri ai ya wuce. Na tabbata da basu haƙura ba bazasu nemeni ba. Kinsan iyayenta da kakanninta ƴan can ne shiyasa" yayi mata bayani.

Cikin zumuɗi ya kira Musaddik suka tsayar da ranar tafiya karshen mako.

"Kun fara waya da Khadijan kenan?" Ya jefo masa tambayar suna gaf da kashe wayar.

"Kasan Allah, tsabar zumudi ban ma kirata ba"

"Kaji matsalar ai, kai sam baka amfani da iliminka na psychology wani sa'in. Idan baka kirata kunyi magana ba ta ya zata san cewa kana farin ciki ko a'a? Naga alama sai na zaunar dakai na koya maka yadda ake tafiyar da mata. Tunaninsu a bauɗe yake. Yanzu wannan shirmen da kake yi duk shi zaisa taga cewa baka wani damu da ita ba faɗa kawai kake don kaji daɗin bakinka."

"To baba, bari na kira ta"

"Ka kirani ko ma menene amma dai kasan cewa gaskiya nake faɗamaka." Daga nan musaddik ya kashe wayarsa don lokuta da dama Nuran haushi yake bashi a lamarinsa da Khadijah.

Da Nura ya kira ya fahimci cewa Khadijah tayi blocking layinsa daman ya dade da sanin tayi blocking dinsa a Whatsapp. Kiran Khairiyyah yayi yaci Sa'a ta shiga amma ta sanar dashi cewa basa tare, ya bari idan suka haɗu zata kirashi ta haɗasu a waya.

Shaf ta manta da zancen sai da suka koma gida bayan maghriba ya sake kiranta. Ba tare da bayanin wanda ke kan layi ba ta sakawa Khadijah wayar a kunne lokacin ita kuma tana sorting wasu laces da akayi order akan washegari zata kai tasha kafin su wuce makaranta saboda wadda ta siya kayan ƴar Maiduguri ce.

"Khadijah" Muryarsa ta doki kunnuwanta a bazata. Sai da gabanta ya faɗi tayi kokarin saita nutsuwarta kafin ta amsa.

"Na'am, Barka da dare"

"Barka dai. Kina lafiya?"

"Lafiya kalau Alhamdulillah" ta faɗa tana gallawa Khairiyyah da ta tsareta da ido tana sauraronsu harara.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now