16

65 6 5
                                    


Abin duniya goma da ashirinne suka taru suka yiwa Ummah yawa. Gashi tunda ta aurar da Suhaila bata sake jin labarin ta ba ko a waya, ga gidan babu yadda yake saboda Sabirah me yi masa bauta bata nan ita kuma bata saba ba, ga Abba ya miƙe ƙafafuwan sa ya zauna a gida bashi da niyyar komawa kan sana'arsa. Tayi tunanin auren Suhaila zai kawo mata alheri kala kala, zata dinga cin daɗi tayi brush da cinyar kaji duk juma'ar sati amma shiru kakeji kamar an aiki bawa garin su. Kuma ko wayarta a kashe take. Ta aika Abbas ya dubo mata ita yace maigadin gidan yace sunyi tafiya kuma baida masaniya akan ranar da zasu dawo. Da tayi wa Abba korafi cewa yayi aure dai Suhaila ta nuna tana so kuma yayi mata saboda haka taje can ta ƙarata babu abinda yayi masa zafi. Ta rasa mafita kuma yace duk randa ta sake fita ba tare da izininsa ba daga can ta wuce gidansu. Ita kuwa ina zata iya zaman zawarci a gidansu gotai gotai da ita? Tana jin sa wasu lokutan yana waya da Sabirah cikin nishaɗi haka ma Abbas da Imam wato ita Sabirah ta raina bata neman ta. Abun yayi mata ciwo sosai shi yasa ta faki idon Abban daya tafi masallaci ya bar wayar a chaji ta kofe lambar Sabirah. Sai da ta bari babu kowa a gidan sannan ta kira ta saukewa Sabirah kaɗan daga abinda ke cinta a rai. Ta tsorata sosai da gargaɗin da Umaimah tayi mata domin tasan ta farin sani kuma tasan zata aikata. Suby ƙawar Suhaila ta sa aka kira mata akan ta taimaka ta dubo mata halin da ƴar gaban goshinta take ciki. Anan Suby take sanar mata da cewa zuwanta gidan sau biyar amma an ce sunyi tafiya kuma basu dawo ba. Kuma itama bata samun ta a waya sannan lambar Bashir ɗin da take da ita bata shiga.

Amarya Suhaila kuwa tun daga daren farko ta san cewa ta tafka babban kuskure kuma ta ɗebo ruwan dafa kanta. Gabaɗaya Bashir ya canza mata daga mutumin da ta sani zuwa wata halitta daban da ko a mafarki batayi tunanin zama a inuwar aure tare da shi ba. Dokoki ya gindaya mata kamar haka;
Daga tashi sallar asuba babu komawa bacci.
Zamantakewar su zata kasance kamar na ubangida da baiwarsa. Wato batada ƴanci a gidan sai abinda yake so za'a yi.
Babu mai aiki a tsarinsa. Daga kan shara,wanke wanke, girki, bawa fulawowi ruwa, wankin manyan kayansa da ƙananan kayansa duk aikinta ne.
Baya son ƙazanta, zaman lafiyarta shine ta tabbatar da ko ina tsaf tsaf yake.
Bai yarda ta riƙe waya ba, don bai ga amfanin ta ga matar aure ba.
Bai yarda ta leƙa ko da ƙofar falo bane ballantana tayi mafarkin fita.
Dole ta dinga zuwa gaisheda mahaifiyarsa duk sati tana mata bauta. Amma ita da zuwa ganin gida sai bayan shekara.
Auren su auren zobe ne babu saki, babu yaji mutu ka raba takalmin kaza.
Dole ta koyi turanci amma sisin sa bazata yi ciwo ba. Tunda tayi masa ƙarya dole ta koya. Yadda zata yi kuma ba matsalarsa bace.
Idan yayi baƙi kada ta kuskura tayi tunanin fitowa domin baya son kowa ya ganta.

A darensu na farko ma ta daku, yayi mata dukan da tunda tazo duniya ba'a taɓa yi mata irinsa ba. Faɗa yake yana ƙarawa akan shi zata mayar ɗan iska ta gama yawonta a waje sannan ta aure shi kuma tace saboda shi tayi? Ai shi ba wawa bane yana sane da duk iskancin da take yi a bayan idonsa kafin tazo tana maƙale murya wai ita ƴar soyayya. Suhaila taci kuka ta gode Allah, kuma ta kira sunan Umma babu adadi. Bata da waya, wayarsa ko kyallinta bata taɓa gani ba gashi ya loda mata ayyukan da ko a gidansu bata taɓa yin irinsu ba.  Tun tana tsumayi tana jiran ganin wani daga ahalinta har ta haƙura. Zagi, duka, cin mutunci babu irin wanda bata gani a wajen Bashir. Idan tayi girki har juye mata yake yi a tsakar kanta ya zageta tas. Ya faɗa mata cewa yayi nadamar saninta, aurenta kuskure ne amma bazata ci bulus ba kuma shi gwara ma ya auri ƙanwarta ta take amsa mata message da ita. Duk abinda yake wa Suhaila babu abinda yafi baƙanta mata rai irin yanda yake kusheta yake yabon Sabirah. Kuma tayi imanin cewa bai taɓa ganinta bane shi yasa yake faɗin haka. Duk tayi baƙi ta rame don ko lefen dayace mata ya haɗa mata yana nan yana jiranta ƙarya ne.
Duk ranar juma'a sai ya tasa ƙeyarta sunje gidansu kuma ko window bai yarda ta kalla ba kanta a ƙasa har suje su dawo. A gidan su ma babu wanda ke mata kallon arziƙi haka ƙannensa zasu yi ta sakata aiki suna zaginta. Mamansa ko gaisuwarta bata amsa wa. Kalmar poor illiterate(talaka mara ilimi) kuwa taji ta ba adadi sai dai bata san ma'anar ta ba. Tana ganin rayuwa ta cin mutunci kuma babu yadda ta iya. Tayi kokarin guduwa bata san cewa akwai CCTV a gidan ba ai kuwa ya sakar mata karnuka daƙyar ta tsira basu mata illah ba.
Kullum neman hanyar tsira take bata saduda ba dan ta rantse da Allah bazata iya ba. Gwara ta koma gidansu ko kasheta Abba zai yi yayi amma ita da gidan Bashir indai ta samu ta fita har abada. Duk takunta akan idon Bashir ne tunda bawai yanada aikin yi bane shi yasa yake da lokacin ta. Aiki kuwa da ƙarfi da yaji sai da ta koya saboda indai tayi kuskure jikinta ne yake gaya mata. A haka har tafara laulayi ai kuwa taga tashin hankali da tijara irin wadda bata taɓa gani ba. Babu irin baƙar azabar da bata sha ba domin Bashir ta ƙarfi da yaji yakeson cikin ya zube amma dayake Allah yayi sai yazo duniya haka ya gaji ya haƙura a zuciyarsa kuwa sai fatan ɗan cikinta ya mutu yake yi kowa ya huta. Tayi magiyar ya kaita gida ko minti goma tayi har ta gaji ya hana sannan ciwo ko na menene ya hanata shan magani ballantana tayi tunanin zai kaita asibiti. Sosai take ɗanɗana kuɗarta gashi ita ba mai ibadah ba balle tayi tunanin miƙa lamuranta ga Allah. Sau tari ma mantawa take da wani zancen sallah ko kuma ta haɗa azahar, la'asar, maghriba da isha lokaci ɗaya. A haka rayuwa ta cigaba da gara mata cikin tsanani da ƙuncin rayuwa. Ga gida ya tsaru, ga kayan alatu da komai da ɗan Adam yake buƙata na jin daɗin rayuwa amma ko na sakan ɗaya bata taɓa jin daɗin su ba domin babu kwanciyar hankali dana ruhi.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now