Satinsu ɗaya da gama jarabawa kamar yadda Ammah tayi mata alƙawari ta shirya zuwa Kano. Yaya Mubarak ne zai kaita a mota tayi kwanaki goma ta dawo. Sosai taji dadi kuma take zumuɗi. A cikin kuɗin da take tarawa na makaranta da Baffa yake basu duk sati tayi wa ƴan gidansu da Hafsah tsaraba. Atamfa mai kyau ta siyawa Umma, ƙannenta maza kuma takalma sai Abba yadin maza. Hafsah kuwa ta tara mata tarkace kala kala daga dangin turare, abun hannu, zobe da mayuka irin wanda take amfani dasu yanzu. Khairiyyah ta dage a je da ita amma fir Ammah taƙi tace ta zauna a gida. Tayi hakanne domin ta samu lokaci tayi wa Khairiyyan karatun ta nutsu akan dabi'arta ta son burge mutanen duniya ba iyayenta ko kanta ba domin tasan sai wani ikon Allah idan batayi spill ba tunda suna da prerequisite courses dayawa a department dinsu. Ta gama shirin ta tsaf sukayi sallama da mutanen gidan suka kama hanya. Tun suna hira har ta gaji ta fara bacci dayake cikin dare batayi baccin kirki ba. Addu'a kawai take tana roƙon Allah akan ya sanyaya zuciyar Ummanta kada ta yi mata cin mutuncin da ta saba. Bayan ta farka Mubarak ya sakata a gaba da tsokana harda cewa tana yawun bacci da gwarti. Ba zato ba tsammani taji yace "Meye tsakaninki da Nura wan Faridah?" Da mamaki ta kalle shi tace.
"Ni kuwa me zai haɗa ni dashi?" Kallon tuhuma ya bita dashi kawai sai ta yanke shawarar faɗa masa abinda ke faruwa. Bata boye masa komai ba tun daga ranar da suka fara haɗuwa har zuwa messages ɗin da ya turo mata. Rai a ɓace Mubarak yace " Ina fata dai kinyi blocking layinsa?""Eh nayi, sai dai a tsohuwar wayata ne watakila a wannan banyi ba kuma dayake banyi saving lambar ba bazan sani ba" ta bashi amsa tana mamakin abinda ya ɓata masa rai.
"Idan ya sake nemanki ki faɗa min" daga nan bai sake ce mata komai ba ita ma haka. Sai huci yake gashi ya fara sharara gudu. Har suka isa Kano babu wanda ya ce da ɗan uwansa wani abu. Dayake suna yawan zuwa tsaf ya gane hanyar ba tare da neman jagorancin Sabirah ba. Yana ajiye ta ko shiga gidan bai ba ya figi motar ya wuce. Galala tayi ta tsaya tana kallon ƙurar daya tayar kafin cikin sanyin jiki duk ɗokin da take ya zagwanye ta shiga cikin gidan da sallama. Dayake Abba ne kaɗai ya san da zuwanta shi yasa Imam da mamaki ya daka tsalle ya nufo ta yana ihun oyoyo yaya ƴar baƙa. Rungume shi tayi tana dariya kuma ko kaɗan bata ji haushin sunan da ya kirata dashi ba. Kallon takaici Umma take binsu dashi. Sai da suka nutsu sannan a hankali Sabirah ta ƙarasa inda Umman ke zaune a kan tabarma ta durƙusa tace
"Umma Barka da rana. Fatan mun same ku lafiya ya zafi?" Kamar bazata amsa ba kuma sai tace "Lafiya kalau" a daƙile. Haka suka zauna shiru kamar masu takaba na lokaci mai tsawo kafin Sabirah ta sake cewa "Su Inna na gaisheku" tsaki ta samu a matsayin amsar ta saboda haka ta tashi ta kwashe kayanta ta wuce daƙin su da yayi ƙura ga wani tsami da yake tashi. Bata huta ba sai da ta tabbatar ta gyara daƙin haka ma tsakar gidan kuma ta wanke bandaƙin. Gabaɗaya gidan yayi kaca kaca kamar babu mutane a cikin sa. Duk bidirin da Sabiran take Umma na zaune tana kallonta ko tari bai sille mata ba amma a ƙasan ranta wani daɗi take ji saboda ko babu komai baiwar gidan ta dawo zata miƙe ƙafa ta huta. Sosai tayi mamakin ganin yadda Sabiran tayi clean da ita baƙin nan ya daina maiƙo da naso ga fatar ta da alama tayi laushi kuma tayi kumari sosai ɗan kwas da ita ko mahassadi idan ya ganta yasan cewa tayi kyau sai dai cikas ɗinta ɗaya baƙin ta. Bata samu natsuwa ba sai bayan la'asar sannan ta shiga ɗakin Umman domin ta tambayeta abinda za'a dafa da dare.
"Dayake da bakyanan zama muke da yunwa. Bana son kinibibi da munafuncin tsiya. Ɓace min da gani" gwuiwa a sanyaye Sabirah ta fito daga ɗakin. Wanka tayi sannan ta ɗebi kayan da tazo dasu na Hafsah ta ƙunshe a hijabi. Da ta nemi izinin fita a wajen Umma sai da ta gama wulakanta ta kafin ta barta harda cewa zataje wajen ƙanwar uwarta da ubanta Hafsah.Ihun murna Hafsah ta saki lokacin da ta ga Sabirah saboda ta faɗa mata akan sai washegari zata zo kwatsam sai ta ganta.
"Amma kin shammace ni dayawa. Ina nan ina ta shirin tarbar manyan baƙin Gombe ashe ke kin gama haɗa min tsiya" dariya suka kwashe da ita kafin Sabirah ta shige falon domin ta gaida Umma da Yaya Halima. Duk sun nuna farin cikin ganinta da yaba yadda ta sake wayewa tayi fes da ita. Hira ce ta ɓarke tsakanin ƙawayen har aka fara kiran sallar maghriba kafin suka farga da lokaci. Sai da Sabirah taci lafiyayyen tuwon dawa da alkama da miyar kuɓewa ɗanya tayi nak kafin Hafsah tayi mata rakiya. Sai da sukayi sawu huɗu kamar yadda suka saba kafin suka haƙura suka rabu. Missed calls ɗin Yaya Mubarak Sabirah ta gani rututu data ciro wayarta a aljihun rigar ta dan shaf ta manta ma da ita kuma tunda ta kira su Ammah da Baffa tace sun isa lafiya bata sake bi ta kanta ba da zata fita ma sakata kawai tayi a aljihunta. Tana kokarin kiransa wayarsa ta sake shigowa.
"Ina kika shige ne Sabs?" Ya faɗa murya a raunane kafin ta bashi amsa ya ƙara da cewa "Dan Allah kiyi haƙuri da abinda ya faru ɗazu kada kiyi fushi dani ban san me ya hau kaina na aikata hakan ba " Dariya Sabirah tayi.
"Lah haba Yaya Ba, ko kaɗan banji haushi ba wallahi. Kawai dai aiki ne ya kacame min kuma naje wurin mutuniyar tawa munata hira ban ga kiranka ba sai yanzu"
YOU ARE READING
ƳAR BAƘA
General FictionSabirah baƙa ce. Irin baƙin nan mai maiƙo, ga muryarta mai kauri da amsa kuwwa. Tana fuskantar tsangwama da izaya kala kala a wajen mahaifiyarta da ƴan uwanta da babu wata ƙauna da shaƙuwa a tsaƙaninsu. Shin zata iya haƙuri da ƙulubalen rayuwa ko ku...