12

51 9 1
                                    

Da taga har an kwana an wuni Abba bai sake neman ta ba sai ta watsar da zancen domin tasan zai yi bincike kuma yayi abinda ya dace. Fatanta kawai Allah yasa Suhailan taji magana kuma ta nutsu ta daina shashanci. Awara ta samu ƙarbuwa domin mutanen Khairiyyah wa'yanda yawanci kawayenta ne sai yan uwansu na Gomben ke ta cewa suna so zasu bada oda. Ai kuwa babu ɓata lokaci Khairiyyah ta karɓa tace musu kuma in shaa Allahu zasu samu a goben. Wannan dalilin ne yasa Khairiyyah ta soke baccin safen da ta mayar al'ada tunda ta gama secondary. Sunyi aiki kuma awara ta bada kala yadda ya dace masu zuwa karɓa nayi, masu cewa a bawa ɗan saƙo nayi. Nan da nan Khairiyyah ta kira wata cousin dinta tace dan Allah ta haɗata da mai kai mata saƙo dayake ita harkar snacks take yi da cake da abinci haka. Yana zuwa suka ƙulla alaka dashi aka bashi da adireshin kowa ya tafi kaiwa. Shirin  zuwa kasuwa bayan la'asar suka fara domin siyo robobin da za'a dinga packaging dana yaji da sauce. Baffa da kansa ya basu kuɗi yace su siyo dukkan abinda ake buƙata kuma yanada abokin dayake harkar waken soya zai karbo musu buhu yanda za'a dade ana amfani dashi kafin ya ƙare. Sabirah rasa bakin godiya tayi sai hawaye kawai. Yace mata baya son shirme ai ita din daidai take dasu Khairiyyah a wajensa. Ammah dai cewa tayi ana fara lectures za'a daina yi kullum sai weekends saboda su samu damar yin karatu a nutse idan kuma akwai ranar da basu da lectures to sai a haɗa da ita. Sannan aka jaddada wa Khairiyyah dole ayi aikin tare da ita idan ba haka ba to sana'ar ta Sabirah ce kadai banda ita. Dariya tayi tace ai dole ta bada himma harka ta kuɗi ai ba abar wasa bace. Sun gama shiryawa suna jiran yaya Muhammad don cewa yayi shi gudunmawarsa kawai kaisu kasuwa ne don bashi da kudi shima nemansu yake ido rufe. Da suka je saukesu yayi yace yanada abubuwan yi saboda haka idan sun gama su samu Napep su koma gida.
"Ai da kasan haka zaka mana da ka bari mun taho a napep ɗin amma yanzu ya kakeso muyi da niƙi niƙin kaya?"
"Dayake kasuwar zaku siye gabaɗaya. Kin cika ƙorafi. Idan kayan sunyi yawa ku ajiye su a shagon yawale gobe sai na biyo na ƙarba" turo baki tayi ta rufe masa ƙofar Sabirah kuwa ta dade da fita tana jiranta.
"Kinsan halinsa kaifi ɗaya ne amma sai kin tsaya bata bakin ki"
"Ai ina ƙaunar ɓata masa rai ne wallahi"
"Allah yasa watarana yayi tamaula dake"
"Tamaula na nawa kuma? Kawai dai yanzu na girma ne, shiyasa ya daina" haka suka cigaba da tafiya suna hira da tsokanar juna cikin nishadi. Sabirah bata san me yake faruwa ba kawai sai ji tayi ta gwaru da jikin mutum. Yahsalam ta furta a hankali sannan ta ɗaga idanuwanta don ganin wanda ta buge ta kuma bada hakuri. Namiji ne bafulatani fari dogo. Ita ma kallonta yake yi.
"Dan Allah kayi hakuri ban sani bane" ta faɗa tana kokarin kawar da fuskarta saboda bata saka niƙabi ba.
"Babu komai. Ki daina tafiya kanki a ƙasa idan ba haka ba zaki dinga gware da jama'a especially cikin kasuwa sannan kina iya cin tuntube ki fadi."  Ya fada da dan karamin murmushi a fuskarsa.
"Lah! Kamar yayan Fiddausi wanda ya kaimu gida ranar post utme" Khairiyyah data zuba masa ido tayi caraf ta faɗa tana mamakin haduwarsu a kasuwa. Nan da nan Nura ya waigo domin sake kallon fuskar da ya tabbata ita ce ta yarinyar da ta hana shi sukuni tsawon watanni sai dai yayi rashin sa'a domin har ta sake sunkuyar da kanta. Tunani ya shiga yi lokacin da ta ɗago fuskar ta domin bashi hakuri amma dayake hankalinsa baya kanta bazai tantance fuskarta ba sai dai kawai yasan cewa baƙa ce. Yaso ya ɗago muryarta tun lokacin da ta bashi hakuri amma dayake sauri yake shi yasa bai bawa ƙwaƙwalwarsa wannan lokacin ba.
"Eh nine. Fatan kun samu admission?" Ya tambaya idonsa akan Sabirah. Roƙonta yake akan ta ɗaga kanta ya kalli fuskarta a ransa amma ko motsi baiga tayi ba.
"Mun samu har munyi registration lectures muke jira. Dan Allah ka bawa Fiddausi hakuri abubuwa ne suka min yawa shi yasa ban kirata ba amma in shaa Allah zan neme ta sannan kuma muna sayar da awara idan zaku siya. Ana oda ne saboda ba kullum za'a dinga yi ba saboda school, yanzu ma haka siyayyar abubuwan buƙata akan business din muka shigo yi kasuwa" Sabirah kaman ta tsaga ƙasa ta shige don kunya. Mamakin surutu irin na Khairyyah take yi. Neman customers ai ba hauka bane da zata saki baki irin haka tana zayyana bayanai kamar wanda ta daɗe ta sani. Ita shaf ta manta ma dasu duk da cewa  ranar da suka haɗu rana ce mai muhimmanci a tarihin rayuwarta.
"In shaa Allah" Nura ya furta kuma yaƙi tafiya kawai so yake Sabirah ta ɗaga kanta. Ganin cewa bai sake faɗan wani abu ba shiyasa Sabirah jan hannun Khairiyyah akan su wuce. Ai kuwa kamar wani mayen ƙarfe na jan Nura ya rufa musu baya. Kwata kwata ya manta da cewa sauri yake kuma yanada abubuwa masu muhimmanci a gabansa.
"Gaskiya ya kamata ki yiwa bakin ki linzami Khairee. Daga haɗuwa da mutum kawai ki saki baki waaaa kina zance? Ai sai yaga kamar bamuda hankali" Nura yaji ta faɗa da kakkaurar muryar ta da take da mugun daɗi a wajensa.
"To meye? Naga dai har gidan mu ya sani. Kuma da haka ake samun customers, kinga idan ma bai zo ba ko labari ya bama wani sai kiga an dace" dariya ce ta so kubce masa domin yau ya haɗu da wadda ta fishi son kudi. Kuma ai dole ma yazo siyan awara saboda shi masoyinta ne sosai yana yawan saka Faridah yi masa a gida saboda yana da kyankyami sosai.
"Ai shikenan. Tunda ke duk hanyar da aka ɓullo miki sai kin lauye"  binsu ya dinga yi har suka isa shagon da zasu siya robobin da suke buƙata. Kamar ance Sabirah ta juya ai kuwa tana juyawa suka haɗa ido ya sakar mata murmushin samun nasara sai dai kafin yace wani abu tayi sauri ta juya. Ko ba komai yaga fuskarta tunda daman abinda yake tsumayi kenan kuma na ƴan sakanni ne amma ya ga abinda take ɓoyewa. Baƙa ce amma shi ba bakin ya gani ba wani sassanyan kyau ya gani irin kyaun da sai an tona. Juyawa yayi ba tare da yace dasu komai ba. Zuciyarsa wasai kamar anyi masa kyakkyawan albishir.
"Ke anya mutumin nan yanada hankali kuwa? Bin mu fa yayi yanzu na juya na ganshi" Sabirah ta raɗawa Khairiyyah a kunne. Da sauri ta juya amma bata ganshi ba.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now