42

40 10 0
                                    

Lokaci yana matuƙar gudu domin kafin ƙiftawa da Bismillah su Khadijah har sun gama aji uku. Duk da cewa sun ƙosa su gama makaranta amma kuma su kansu sunga saurin da karatun nasu yake yi.

"Allah dai yasa har mu gama baza'a tafi ƙaddararren yajin aikin nan ba" Amatu ta faɗa lokacin da suka fito daga jarabawarsu ta ƙarshe.

"Amin. Kamar kin shiga zuciyata nima addu'ar da nake yi kenan" Khadijah ta bata amsa.

Ta riga da ta gama shirin komai kawai jira take yi su gama jarabawa ta koma gida duk da cewa bata son ta ƙara zama a guri ɗaya da yaya Ba amma babu yadda zata yi kuma tunda ita ma ba zama take a gidan ba suna fita da Ammi sai take ganin kamar abun zai zo mata da sauki tunda shima ba zama yake ba.

"Sai wani murmushi kike zaki je kiga Ammi da Abbu"

"To ba dole na murmusa ba. Baki san yadda nake jinsu a raina bane"

"Ai dole. Bamu da tamkar su a rayuwarmu. Sune jigonmu kuma masu son mu a kowanne yanayi sannan duk lalacewarmu suna son mu a haka kuma suna iya yin kowacce irin sadaukarwa domin jin daɗin mu." Amatu ta fada.

"Zancenki gaskiya ne. Allah ya basu tsawon rai mai amfani mu kuma ya bamu ikon kyautata musu"

"Amin wallahi. Kamar kinsan buri na kenan a duniya. Shiyasa yanzu da muka fara harkar sayar da kayan nan dake har wani daɗi nakeji idan na bata kuɗi ko na siya mata abu ko na saka mata kati. Ina son samun rufin asiri ko don na ɗauki ragamar kula da ƙannena ita ma ta huta hakanan"

"Gaskiya dai mama jarumar mace ce wadda samun irin ta sai an tona. Ga hakuri gashi kuma ta dage ta baku tarbiyyah mai inganci. Allah ya saka mata da aljannah".

"Amin parrof me. Mu wuce gidan muyi abinda zamu yi kinsan nace miki yau zan fara siyar da zobo da kunun aya " Amatu ta faɗa tana jan hannun Khadijah saboda sun tsara cewa bayan sun kammala jarabawarsu Amatun zata yi mata kitso amma a gidansu Khairiyyah ba a gidansu ba kamar yadda suka saba.

"Haka ne fa. Na manta da hajjaju makkatu nake magana. Yi hakuri hamshaƙiya. Muje kada customers suzo ba'a haɗa ba"

"Yawwa ahh toh gwara dai ki dinga bi na a sannu"

Amatu ta yarfa mata kitso ƴan ƙanana masu kyau amma kememe taƙi yarda da ayi mata lalle ita kuma Amatu tace bata isa ba tunda ta saka ta asarar kuɗinta ta siya da lokacin da ta ɓata na shiga kasuwa to wallahi sai tayi mata. Haka suka dinga cecekuce sai da Ammah ta saka baki.

"To dai don Allah ko a yatsun ƙafa da hannu ne ki bari a saka miki"

"Amma Ammah ba wani fitowa zai yi bafa kiga ɓakina fa"

"Ke kanki kinsan kin washe kuma fatarki ta gyaru daman harda rashin gyara da kula. Ki tsaya kawai ayi miki lallen nan bana son musu. So kike kije wa Fatimah gida yarkace yarkace dake wato?"

Dole ta yarda akayi mata ba don taso ba tana ta ƙunci Ita kuwa Amatu ko a jikinta.

Taso su wuce da Khairiyyah amma taƙi amincewa kuma taƙi faɗa mata dalilinta na ƙin amincewa. Har zata faɗawa Ammah ta sa baki su tafi tare sai ta fasa saboda sanin cewa tunda Khairiyyah batayi niyya ba tsaf zata aikata suje kuma a ƙi zama lafiya. Sunyi sallama da Amatu da mutanen gidansu bayan ta kaita gidan da kanta tana karfafa mata gwuiwa akan sana'ar sannan kuma tace idan da wata matsala ta faɗa mata kuma tana shiga kasuwa zata nemo mata irin material ɗin da tace tana son ta fara siyarwa.

"Nagode kwarai parrof me. Allah ya dawo min dake lafiya. Ki gaida min da kowa dakyau"

"Nice da godiya. Zasu ji. Kada kiyi kewata da yawa"

"Mantawa da kowa nake idan ina tare da Ammi kema kin sani" Khadijah tayi mata gwalo ta wuce.

Washegari da safe Baffa ya kaita tasha ta shiga mota ta wuce Kano. Kamar wancan karo a gidan Abba ta sauka kuma anyi mata tarba mai kyau. A can ta samu Hafsah tana zaman jiranta.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now