Tun suna jiran Afnan ta tada daru akan ina mahaifinta ko a mayar da ita gida har suka sadaƙar akan cewa daman ta saba zama da wasu ba iyayenta ba har abun ya zame mata jiki kuma da irin ƙaunar da take yi wa Khadijah don duk inda tasa ƙafa tana biye. Tun ranar Hisham ya isa lafiya kuma sunyi magana sosai da Abbu har ya nemi Kawunsa a waya suka tattauna zancen da bai sanar da kowa ba sannan aka fara neman makarantar boko da islamiyyar da za'a saka Afnan domin an rigada an wuce ta don ma suna yi sosai da Khadijah suna ganin kamar baza'a samu matsala ba za'a saka ta a ajin daya dace.
"Nidai a shawara ta a saka ta a boko daban islamiyyah ma daban. Bana son makarantun da za'a kai yaro tun safe sai yamma ya wuni zur da wasu yaran da malamai aje a koya masa wasu dabi'un banza baka sani ba saboda da yaro ya dawo gida home work zai yi ya gaji sai bacci kuma karshen mako ma a kai yaro tahfiz ya wuni zur" Ammi ta faɗa lokacin da suka zauna suna duba makarantun da Abbu ya samo wa'yanda suke cikin estate ɗin.
"Nima nayi wannan tunanin amma idan Khadijah ta koma makaranta ke kin fita nima haka kuma bamu da mai aiki ya za'a yi kenan?" Abbu ya bata amsa.
"Sai kace marasa ƴan uwa Abbu? Babu damuwa kabar wannan a hannuna ba na faɗa maka Maman Ibrahim tunda mijinta ya rasu tace min tana son ta dawo nan da zama ta dinga tayani aiki ni nace ta dakata ba?"
"Ehh haka ne. Kuma kinga tsayayyar macece gata akwai iya bawa yara tarbiyyah. Ji Ibrahim da ƙanwarsa kamar ba a ghetto suka tashi ba." Abbu ya gyada kai cike da gamsuwa da zancen Ammi.
"Yanzu zan sanar da ita ta zauna cikin shiri idan munyi tafiyar nan mun dawo sai tazo kada sai Khadijah ta koma kuma yarinyar bata saba da ita ba tayi ta mata tijara idan bama nan"
"Kinyi tunani mai kyau Ammin Afnan domin dai naga alama ta kwace miki gwamnati Khadijah"
"Ai kuwa dai Abbu. Lokaci na basu kafin ayi ɗan karamin yaƙi a gidan nan" Khadijah ta faɗa tana aikawa da Afnan hararar wasa. Zama sukayi suka tantance makarantarda suka san ba'a koyawa yara aƙidar yahudu sannan da karatu sosai sai Ammi tace washegari zata shiga maƙotansu tunda su ma Hausawa ne ta tambayi inda yaransu ke zuwa islamiyyah. Ko babu komai dai sun samu masu zuwa da dawowa tare da ita.
Sai wajen goma da rabi Khadijah ta koma ɗaki ta tarar da missed calls ɗin Hisham da message akan dan Allah ta taimaka ta kira shi. Sai da tayi wa Afnan da ta dade da yin bacci shirin kwanciya ta tofe ta da addu'a sannan ta kira shi.
" Idan fa ka ishemu da kira don jin yaya Afnan take to tabbas zamu dawo maka da ita" ta faɗa cikin sigar wasa.
"Habawa sai kace wani mara kunyar suruki. Na tabbata Afnan tana cikin ƙoshin lafiya da kulawa mai inganci bani da haufi akan haka. Ni muryar aunty K kawai nake son ji don bazan iya bacci ba duk da cewa wuni nayi ina aiki ba tare da naji ta ba" ya bata amsa da confidence ɗinsa kuma babu alamar wasa a tattare dashi.
"Idan wani yaji ka sai ya zata muryata tanada daɗin sauraro ba maneji kawai ake yi da ita ba"
Nan da nan ransa ya ɓaci ya dinga yi mata faɗa kamar wadda ta aikata saɓo tun abun yana bata mamaki har ya koma bata dariya.
"Afwan Abban Afnan na tabbata yau da kana gidan nan sai ka zane ni da dorina."
"Idan akwai abinda yafi duka ma sai nayi miki. Ni fa Khadijah am not after beauty ( ba kyau nake bi ba) sannan Manzon Allah (SAW) ya ce ku auri mace domin kyaunta, ko arziƙinta ko kuma addininta amma auren mai addini yafi muku alkhairi. Saboda haka ni halinki nagani na fola miki kafin nagano cewa kinada nasaba mai kyau da arziƙi, dana zauna na miki kallon ƙurilla sai nagane cewa ashe dai niɗin na caɓa dayawa saboda kin haɗa komai da komai because you're just so beautiful whenever I see you, I struggle not to lose my breath ( kinada matuƙar kyau kuma duk lokacin dana ganki ina kokawa kada numfashina ya ɗauke."
YOU ARE READING
ƳAR BAƘA
General FictionSabirah baƙa ce. Irin baƙin nan mai maiƙo, ga muryarta mai kauri da amsa kuwwa. Tana fuskantar tsangwama da izaya kala kala a wajen mahaifiyarta da ƴan uwanta da babu wata ƙauna da shaƙuwa a tsaƙaninsu. Shin zata iya haƙuri da ƙulubalen rayuwa ko ku...