Tunda suka je Lagos hutun kwana ɗaya tayi Ammi ta saka ta a gaba tana fimfata. Faɗa ta dinga yi mata akan bata son yin kwalliya da gyaran jiki dukda ta nuna mata kayan skin care ɗin da take amfani dasu bata yarda ba sai da ta kaita asibiti gurin likitan fata domin ayi mata recommending irin kayan da ya kamata tayi amfani dasu wa'yanda bazasu canza ainihin kalar fatarta ba. Bayan nan kuma ta saka ta a gaba sai da ta buɗe shafukan sada zumunta irin su Instagram da Twitter domin tallata hajarta. Takunkumi ta saka mata mai tsanani akan kada ta kuskura taga tana shashanci bayan business a page ɗinta kuma Khadijah tayi mata alƙawarin hakan. Abu kamar wasa tana faɗawa Hafsah ta Amatu dayake su tun asali suna yi sai gashi sai samun followers take yi. Duk wani abinda Ammi ke siyarwa to da anyi musu hoto zata saka kuma tace tana gama makaranta zata cigaba da yin order ɗin abinci. Sosai take jin daɗin hutun kuma Ammi da kanta ke ƙara koya mata tuƙi. Ta ƙara fresh, fuskar nan tuni ta ɗaina maiƙo kamar wadda ta shafa mangyada gashi kullum sai ƙara yarda da kanta take yi akan ita ma mutum ce mai daraja kamar kowa. Duk ƙarshen mako kuma sai sunje islamiyyar da Ammi take zuwa. Aji da seat ɗinsu ɗaya kamar ya da kanwa.
Ammi naɗe kafafunta tayi bata aikin komai ta sakar wa Khadijah ragamar kula da gidan kuma hakan yayi mata daɗi sosai tunda bata saba zama haka nan batare da tana wani abun ba. Da dare sun gama hira an watse ne ta dawo ta tarar da missed calls ɗin Khairiyyah wajen guda goma. Tun ranar da ta kirata a waya basu sake magana ko chatting ba saboda haka sai ta tsorata tana tunanin ko wani abunne ya faru tunda yaya Ba yana gidan har yanzu ance ya bari idan hutunta ya ƙare sai su tafi tare. Basu wani cika haɗuwa ba kuma hakan yayi mata yadda take so. Kiran Khairiyyah tayi a zuciyarta tana addu'ar Allah yasa dai lafiya ba wani abu mara daɗi ke faruwa a gidan ba.
"Khairee lafiya? Naga missed calls ɗinki dayawa bana ɗaki lokacin da kira kira. Su Ammah duk suna lafiya?"ta tambayeta bayan tayi mata sallama.
"Kowa lafiya. Ai nayi tunanin kina gani da gangan kika ƙi ɗauka shiyasa nayi ta kira. Yanzu Sabs wanne irin fushi kike yi dani har haka da kwata kwata zaki shafe ni a rayuwarki?"
"Ban gane na shafe ki a rayuwata ba, kinsan me hakan ke nufi kuwa?"
"Kin shafe ni mana har kowa ya gane an sakani a gaba anata yimin faɗa babu wanda ya bani uzuri ko ya tsaya sauraron ɓangarena. Kiyi hakuri a ranar raina a ɓace yake saboda munyi faɗa da yaya Sa'ad shiyasa na huce a kanki bawai don ina nufin kalmomin dana furta bane" kawai ta sake mata kuka wiwi kamar yarinya. Dariya ma abun yaso bawa Khadijah tunda salon dramar Khairiyyah babu wanda bata sani ba sai dai ta bawa wani labari.
"Allah Sarki to yanzu kukan da kikeyi na menene? Ni ban shafeki ba kawai kin ɓata min rai ne sosai. Khairiyyah ke sam ba'a sirri dake kuma idan ranki ya ɓaci sai ki yaɓawa mutum maganar da zata dade tana masa ciwo ke a ganinki ba komai bane kuma na tabbata hakanne ya haɗaku faɗa da yaya Sa'ad. Ke kin iya ɓoye min abinda ke faruwa kuma ya shafe ki amma ni nawa bakya tsayawa kiyi tunanin ko ina so ki yaɗa ko a'a. Kawai abinda kike tunanin shine daidai kikeyi kanki tsaye bakya tsayawa kiyi tunanin ko zanso hakan ko a'a. Wannan ba matsalarki bace, babban matsalarki shine ki fafawa wani. Hakan ya dace ? Idan nayi miki haka zaki ji daɗi? Ko Ammah baki faɗawa kina waya da yaya Sa'ad ba kuma ga abinda yake tsakaninku, na sani amma ban faɗa mata ba amma ke ban isa na faɗa miki abu ko ki gani a kaina ba sai kinyita yayatawa ai ba daɗi."
"Hakane, nayi kuskure kiyi hakuri in shaa Allah zan gyara. Fushin ya isa haka Khadijah dan Allah."
"Komai ya wuce ai babu komai. Ya IT ɗin kina zuwa ko zamanki kike yi a gida?"
"Kema kinsan ban isa ba. Zuwa ya zama dole Ammah ta kafa ta tsare ko ƙaryar ciwo nayi sai naje"
"Maganinki kenan. Allah ya bada sa'a" hira sukayi sosai har sai da Khadijah ta fara hamma tayi mata bankwana akan zasu yi magana gobe. Khairiyyah daɗi kamar ya kashe ta ko ba komai zasu daidaita da Ammah don turketa tayi sai da ta faɗa mata abinda ta aikata saboda kullum sai sunyi waya da Khadijah amma ko sau ɗaya bata taɓa ji suna waya da Khairiyyah ba. Faɗa tayi mata sosai da nasiha kuma ita kanta ta san bata kyauta ba. Cewa tayi zata fadawa Baffa ta dinga bata hakuri akan ta rufa mata asiri bazata sake kamanta irin abinda ta aikata ba.
YOU ARE READING
ƳAR BAƘA
General FictionSabirah baƙa ce. Irin baƙin nan mai maiƙo, ga muryarta mai kauri da amsa kuwwa. Tana fuskantar tsangwama da izaya kala kala a wajen mahaifiyarta da ƴan uwanta da babu wata ƙauna da shaƙuwa a tsaƙaninsu. Shin zata iya haƙuri da ƙulubalen rayuwa ko ku...