33

53 7 4
                                    

An gama duk wani shirye shiryen da za'a yi na bikin Faridah har lokaci kuma yayi saura ƴan kwanaki a fara. Sun shirya yin walima sai mother's eve sannan ɗaurin aure da kai amarya. Musaddik sai murna yake kamar ƙaramin yaro har abun ya fara bawa Nura haushi.

"Malam wai meye haka ne ? Akanka aka fara aure ne ko kuma yaya? Ka zauna kayita zumuɗi kana yangare wa mutane baki"

"Ina ruwanka dani? Ko yaya zan maka bayani ba fahimta zaka yi ba saboda haka Please allow me. Ka rabu dani na nuna farin cikin da nake ji. Mafarkin da na daɗe ina yi ne fa zai zama gaskiya kuma kace zaka hanani bayyanawa saboda a tunaninka kowa irin ka ne ko?"

"Me kake nufi da hakan? Meye haɗina da shirmen da kake yi"

"Babu babban yaya. Allah huci zuciyarka. Taso ka rakani shagonka na karɓi kayana. Kuma idan basu yi yadda nakeso ba kai zaka ɗauki asara don sai ka biyani kuɗin kaya da ɗinkin" Musaddik ya faɗa yana ɗaukan key din motarsa a saman madubin daƙinsa.

"For a person that will marry my younger sister ( a matsayinka na mutumin da zai auri ƙanwata ) kayi bala'in raina ni"

"Kafin na zama surukinka abokin kane ni kuma auren Faridah bazai canza hakan ba gwara ka sani tun yanzu. Babu zancen surukantaka a tsakaninmu"

" Zaka gane shayi ruwa ne yaro" Nura yayi kwafa ya fice daga ɗakin. Tun safe yayi wa Khadijah message sai duba wayarsa yake ko ta mayar masa da amsa  amma shiru batayi ba. Roƙonta yake akan ta bari ya kawo musu katin mother's eve ɗin gida harda na Ammah sai suje tare amma fir taƙi amincewa.

"Tunanin me kake yi ne? Ko har an kwace maka mintin zuciyar taka ne kana nan kana nuƙu nuƙu?" Musaddik ya jefo masa tambaya lokacin da ya lura ya lulaƙa duniyar tunani.

"Hmm kabari abokina. Khadijah sam ta kasa fahimtata. So nake su halacci bikinku amma taƙi yarda wai bata san a matsayin da zasu zo ba kuma bata so a tambaye su ta kasa bada amsa sannan har yanzu kasan bata sakewa a cikin jama'a sosai"

"Banda abunka ai tana da gaskiya. Taya zata halacci bikin gidanku kuma kaine ka gayyace ta ba Faridah ko Fiddausi ba? Hakan da tayi shine daidai kuma ta burgeni sosai wallahi na yaba da hankalinta"

"Yanzu a taƙaice dai kana nufin na saka Fiddausi gayyatar su?" Nura ya tambaya cikin jin daɗin shawarar Musaddik din.

"Ni dai bance ba. Kada taƙi zuwa ka huce a kaina" ya ɗaga hannayensa kamar me yin saranda.

"Allah ya shirye ka Musaddik"

"Amin tare dakai likita bokan turai"

Duk yadda Musaddik yaso zolayar Nura akan ya nuna cewa kayan basu yi masa yadda yake so ba kasawa yayi. Sai juya su yake yana wow wow wow. Wani abu sai ma ranar. Dariya sosai ya bawa Nura yace a tunaninsa suna ɗinkin banza ne ko tunda ake masa ɗinki a shagon an taɓa samun mishkila?

"To naji kada ka dame ni"  daga nan wucewa sukayi domin ƙarasa raba katin daurin auren a wuraren da basu kai ba.

"Ina kishinka ta wannan fannin. Kanada kyakkyawar mu'amala da danginka na uwa da uba saɓanin mu da wa'yanda muke mu'amala dasu basu da yawa" Nura ya faɗa cikin wata iriyar murya dake nuna yadda abun ke ci masa rai.

"Kaine baka so samun kusanci da su ba Nura. Kana da riƙo sosai kuma bakada yafiya. Mutanen nan tunda ka fahimci cewa ba haka aka barsu ba kamata yayi ka nemesu domin samun kusanci dasu ko don Baba Allah yayi masa rahama amma kayi watsi dasu kuma ka hana ƴan uwanka nemansu. Su kuma nasan kunyar tunkararka suke yi saboda sanin halin ka. Kana da lokaci har yanzu da zaka gyara zumuncinku kuma idan da kyakkyawar zuciya kayi hakan Allah zai dafa maka komai yazo da sauƙi"

"Na ƙudiri niyyar da zarar Faridah ta zama tawa zan haɗata da ƴan uwanta tunda ta bar karkashin ikon ka. A wannan zamanin da naka ma yake cutar da kai bazai yiwu ace matata bata da wani bangon dafawa ba daga danginta. Kama ji na gaya maka" Musaddik ya faɗa yana aika masa da harara.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now