11

58 7 3
                                    

Ba a ɗauki lokaci mai tsawo ba sai da Ammah da Khairiyyah suka tabbatar da sun wanke zuciyar Sabirah har ta saki ranta  tafara dariya, dayake bata da riƙo sam a rayuwarta saboda zuciyarta me kyau ce. Da yamma Yaya Muhammad ya kawo waken soya mai kyau wanda ba sai sun tsince dattin da ake iya samu ba. Khairiyyah ta kasa zaune ta kasa tsaye jira kawai take gari ya waye.
"Malama ki saka ranki a inuwa domin ba lallai bane na baki. Ƙamshi dai zai cika miki hanci domin banda ikon hanaki shaƙarsa"
"Ashe kuwa za'a yi ƙaramin yaƙi a cikin gidan nan. Garin Gombe bazai dauke mu ba"
"Ahaff a dake dai bazan daku ba. Ko za'a gwada ne ?" Sabirah ta daga mata gira tana ninke hijabin data idar da shafa'i da witiri. Al'adar ta ce tun lokacin da aka faɗa musu falalar kwanciya da alwala da kuma yin witiri kafin kwanciya bacci.  Hakan yana sakata nishadi domin duk wani abu da zai ƙara mata kusanci da Ubangiji da kuma gyara mata lahirarta da rayuwarta ta duniya tana  kaunarsa kuma tana jajircewa wajen aikata shi. Har ta koyawa Khairiyyah da walaha da nafilolin da ake yi biyu da asuba raka'atanul fajr, huɗu kafin azahar, biyu bayan azahar, biyu bayan maghriba sai shafa'i da witr kuma ta faɗa mata yadda suke saka mata nutsuwa a zuciya. Kafin zuwan ta Khairiyyah na wasa da lokacin sallah sai a kira ta shagala da karatu ko danna waya har lokaci ya ƙure amma yanzu da an kira tunda suna kusa da masallaci tana ganin Sabirah ta tashi ta ɗauro alwala ita ma take tashi. Asuba kuwa dama dole ta tashi tayi ta akan lokaci tunda Baffa yana dawowa daga masallaci yake kiransu falo karatu.
Addu'ar bacci tayi bayan ta maidawa Hafsah saƙon da ta turo mata akan akwai labari da ɗuminsa idan ta saka kati gobe zata kirata harda yi mata tsiyar da tana chatting ai da basai tayi asarar kuɗin kira ba. Allah ya kaimu kawai ta ce mata domin Hafsah ta haɗa kanta da aikin kawo mata rahoto akan abubuwan da suke faruwa a gidansu a bayan idonta. Tana mamakin cewa har ta kusa wata uku a Gombe amma ko sau ɗaya Umma bata nemeta ba, tana son kiranta domin ta haddace lambar ta a kanta amma kuma tana tsoron cin mutuncin da zai biyo baya akan ta ɗau lokaci bata kirata ba kuma bata son saɓa umurnin Abba. Haka dai ta cigaba da tunane tunane na banza dana wofi har bacci ɓarawo ya saceta. Khairiyyah kuwa bata ma saka ran kwanciya ba saboda suna chatting a group da ƙawayenta kuma duk hirar bata wuce ta yadda zasu kece raini a makaranta da shiga ta alfarma ba kuma suna taya ƙawarsu da aka siyawa mota a matsayin kyautar ta ta shiga jami'a murna. Sai kurantata suke suna da ma sune.

Washegari da sassafe wajen karfe tara Sabirah ta fara aikin awara. Mai aikinsu ta kai mata markaɗe ita kuma tana haɗa kayan da zatayi amfani dasu wajen yin sauce din da Ammah tace tayi saboda ya ƙarawa abun armashi ga kuma yajin yaya Haliman da ta kawo mata da take ta janjaninsa saboda daɗinsa da za'a yi amfani dashi wajen tallata wa makwabta. Kafin wani lokaci ta tafasa ta tace ta haɗe jikinta yanda ake so. Yankawa kawai Khairiyyah ta taimaka mata wajen yi saboda wai kada ta saka hannunta mai albarka azo a rasa gane daɗin awarar a dalilinta ne ko Sabirah.  Sabirah dai cewa tayi salon kada tayi aiki ta tayata ne amma babu wani zancen hannu mai albarka ita da banda kayan maƙulashe da abincin aljanu babu abinda ta iya.
"A haka dai naga ranar da kika zo gidan nan har waigi aka miki. Ina kallon ki fa harda suɗe kwano da hannu kanki na reto tsabar daɗi"

"Allahu yahdiki khairee. Kin fi karfina wallahi" haka suka cigaba da hirar su har komai ya kammala.  Zuwaira (mai aikinsu) tanata yi musu dariya idan kuma wajen raba faɗa ne sai ta saka baki ta bawa mai gaskiya gaskiyarsa mara gaskiya kuma ta basa laifinsa. Khairiyyah naɗe hannuwan rigar ta tayi sai da ta kusa cinye guda ashirin sannan ta magantu.
"Mazarkwaila sunan wani abu. To ai Zuwaira ina faɗa miki zaman nan dana yi naje kasashen duniya da dama kafin na dawo hayyacina" dariya suka kwashe da ita Sabirah ta saka hannayenta a bayan Khairiyyah wai zata tarota kada ta faɗi. Zuwaira ma ta yaba da dadin awarar kuma tanada yaƙinin cewa in Shaa Allahu za'a samu kasuwa mai albarka.  Zama sukayi akayi packaging iya adadin gidajen da Ammah tace a kai. Hijabansu Khairiyyah ta dauko a daki tace su wuce bayan Sabirah ta gama jerawa a wani kwando mai matsakaicin girma.
"Kije kawai zan taya Baba Zuwaira gyaran kitchen" ta faɗa tana rataya hijabin a saman ƙofa.
"Kinada matsala wallahi, ai gwara muje tare su ganki su tabbatar da cewa mutum ce ke sarrafa awarar da basu taɓa cin me daɗinta ba"
"Ko kuma suna ganin kalata suce bazasu taɓa iya cin abincin mutum mai muni irina ba"
"Haba Sabs, jiya jiyan nan fa Ammah ta gama yi miki faɗa akan irin wa'yannan zantukan naki marasa tushe da ma'ana. Shikenan dai bazan takura ki akan abinda bakida niyyah ba. Idan da rai da lafiya dai wataran zaku haɗu dasu" ta sa kai ta fice tana masifa ita kaɗai. Sabirah bata bi ta kanta ba tunda tasan gaskiyar abinda ke ranta ta faɗa suka gyara kitchen din tas ta koma daƙi. Har suka gama babu khairiyyah babu alamar ta. Ita kuwa tana chan duk gidan da ta shiga sai ta kasa ta tsare an ɗanɗana a gabanta an faɗa mata irin daɗin da awarar tayi an kuma tabbatar mata da za'a zo siya.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now