32

41 6 0
                                    


Umma ta shiga taskun rayuwa irin wanda bata taɓa hasasowa ba. A cell aka rufe ta da wasu ƙazaman matan daga ganinsu kasan babu alheri a tattare dasu. Gabaki ɗayansu riƙakkun ƴan tasha ne gashi banda zarni da wari babu abinda ke tashi a cell ɗin. Kuka Umma tayi kamar ranta zai fita amma a banza, tayi magiyar akan a barta tayi waya ko zata samu ta roƙi gafarar Ammi a fitar da ita daga cell ɗin amma babu wanda ya saurareta. Tun wata mata na rarrashinta har ta gaji ta rabu da ita suka saka ta a gaba da zagi da cin fuska akan idan tasan cewa tana tsoron a kulleta me yasa ta aikata laifi. Kowa da ta gani a wurin akwai abu mara kyau da ya shuka sai dai idan sharri akayi mata. Tun Umma na jiran ganin wani nata yazo har akayi sati babu su babu dalilinsu. Suhailan ma da take tunani zatayi wa Bashir magana babansa yasa a fitar da ita bata ganta ba balle tasan makomarta. A sati ɗaya ta rame tayi baƙi gashi wasu munanan kuraje sun feso mata a baki dakyar take iya cin abinci.

Tana zaune har da ɗaiɗaya aka kwashe mutanen da suke cikin cell aka miƙa su kotu saura ita kaɗai kuma har lokacin babu wanda yayi mata bayani akan laifin da ake tuhumarta da shi ko kuma yadda case ɗinta zai kasance.

Abba yana kwance a tsakar gida yana shan iska saboda bai fita kasuwa ba a dalilin ciwon kan da yake fama dashi ne yaji sallama a kofar gida. Amsawa yayi yana bada izinin shigowa saboda bashi da ƙarfin tashi kuma sanin cewa babu kowa a gidan sai shi kaɗai. Ƙanin Abbu wanda suke kira da Baba Usman da Baban Ammi ne suka shigo. Da mamaki Abba ya tarbe su domin rabonsa dasu tun yana asibiti da suka je dubashi.

"Kaine da kanka a gidan nan? Da ka aika nazo ai" Abba ya faɗa yana murmushin yaƙe saboda a tunaninsa sun zo akan zancen Umma ne ko kuma shima shari'ar zasu yi dashi duk da cewa mutunci sosai suke yi da Baban Sabirah don har kayan abinci sai da ya aiko masa dasu.

"Haba ai babu komai Malam Muhammadu. Ƙafar tawa tayi sauƙi ai shiyasa nake ɗan takawa"

"Mashaa Allah, Allah ya ƙara afuwa yasa kaffara "

"Amin Amin"

Sai da Baba Usman yayi gyaran murya sannan ya sake bawa Abba haƙuri akan abubuwan da suka faru.

"Fatimah ce da kafiya da muguwar zuciya har yanzu sai binta ake ta haƙura ta bar zancen nan taƙi. Shima yaya Umar (CP) ya biye mata an kulle mata babu wani bayani"

"Ai duk abinda za'a yi mata ta cancanci hakan. Ni banida matsala da ita da abinda ya shafe ta domin bama tare na riga da na sake ta. Zancen haƙuri kuma ai ku za'a bawa haƙuri da aka cuce ku"

"Babu wannan zancen. Komai ya wuce tunda Allah ya bayyana mana ita ai sai dai mu gode masa. Dama Babane yake ta tunanin kyautar da zai maka domin nuna godiyarsa akan riƙon da kayi wa Khadijah. Shine ma dalilin daya sa mukazo"

"Kyauta kuma? Haba! Ɗa ai na kowa ne kuma a matsayin ƴar cikina na raineta. Ba sai kunyi min komai ba wallahi. Babbar kyautar dana samu shine na sanin cewa tana cikin farin ciki da annashuwa irin wanda na ɗaɗe ina mata fatan samu. Wannan kaɗai ya isheni farin ciki" Abba yace yana girgiza kansa kuma yana mamakin dattako da karamcin mutanen.

"Akwai gidan dana gama ginawa zan saka haya shine naga ya kamata na mallaka maka shi duk da cewa kome zan baka a duniya bazan taɓa biyanka ba. Allah ya saka maka da alheri ya baka mace ta gari ya kuma ji ƙan magabata. Amin"

Shiru Abba yayi yana mamaki, sosai kyautar ta girgiza shi domin abu ne da bai taɓa mafarkin zai samu daga wurinsu ba. Godiya ya dinga yi kamar zai ari baki. A motar da suka zo suka tafi dashi aka nuna masa gidan flat me kyau da ɗakuna huɗu sai falo babba da dinning area da kitchen da store da banɗaki da ɗakin baƙi a waje. Gidan ya tsaru ginin zamani kuma an saka furnitures a kitchen, falo da ɗakuna biyu.

"Kayan ɗakin da komai na furnishings ɗin shine gudunmawar mu iyayen Khadijah wato yayye da ƙannen iyayenta"  Baba Usman yayiwa Abba ya yake ta kallon gidan cikin al'ajabi sai kwararo musu addu'a yake. Da yana da wayar zamani da tabbas sai ya ɗauka ya turawa ƴan uwansa. Sai da aka gama nuna masa komai hatta generator sai da aka siya masa sannan suka miƙa masa makullai da takardun gidan a matsayin mallakinsa.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now