Yaya Idris ne ya haɗa Abba da wata bazawara a anguwarsu. Mace ce mai haƙuri da yakana ga sanin ya kamata. Tasha wahala sosai a hannun mijinta da danginsa gashi ita take ɗawainiya da hidindimun gidan amma a hakan bata wuce gori da cin mutunci ba harda duka a gaban ƴaƴan da suka haifa. Tasha wahala kuma kowa yana tausaya mata har Allah ya kawo karshen zamansu da rai yayi halinsa. Mijin nata ya fita yawon da ya saba mota ta kaɗe shi ko shurawa bai ba yace ga garinku. Mutuwar ta kaɗa ta da yaransu guda uku amma ƴan anguwa kowa murna yake mata akan ta rabu da alaƙaƙai dayake marainiya ce kuma gidan da aka riƙeta ma batada gata shiyasa tsawon shekarun da ta ɗauka tare da mijinta ko ƙara bata taɓa kaiwa ba saboda tasan babu abinda za'a yi akai sai dai ace mata tayi haƙuri.
Zuwan Abba na farko wurinta ƙin amincewa tayi dashi saboda bazata iya tafiya ta bar rayuwar ƴaƴanta mata biyu da namiji ɗaya ta tagayyara ba tunda tun mutuwar ubansu babu wanda ya bata tallafi ko na hatsi ne ita ke faɗi tashinta akansu. Murmushi Abba yayi yace mata ai yana sane da yaran dake gabanta kuma in shaa Allahu indai aurensu ya tabbata zai yi iya kokarinsa wajen tallafar rayuwarsu tunda shima akwai yara biyu a gabansa kuma ita ce zata kula da tarbiyyarsu.
"Amma baka ganin akwai takura? Yara har uku kuma a yadda rayuwar nan ta koma komai yayi tsada?" Ta tambayeshi.
"Babu takura mana. Ɗa ai na kowa ne kuma ba su suka kashe mahaifinsu ba sannan ina kwadayin ladar da zan samu na kula da marayu kinga dukkanmu rufawa juna asiri zamuyi"
"Haka ne. Zanyi tunani kuma zanyi shawara da yaran nawa. Nagode da kulawa" ta bashi amsa a kunyace. Ba wata babba bace amma wahalar rayuwa ya tsufar da ita sai take yi kamar an ƙara mata shekaru goma a saman asalin shekarunta. Lokacin da Abba yaji labarinta yayi matukar tausaya mata shine ma babban dalilin dayasa ya tunkareta. Sunanta Halima babbar ɗiyarta Fatima shekarunta goma sha biyar sai mai bi mata Abidah sha uku sai autansu Kamal me shekaru goma. Nutsattsun yarane masu tarbiyyah da girmama na gaba dasu ga wadatar zuci da haƙuri da juriyar yunwa duk da cewa mahaifiyarsu na iya kokarinta wajen ganin cewa basu kwanta da yunwa ba sai dai yau da gobe sai Allah. Wataran duk buga bugar da zatayi sai ta rasa abinda zata basu.
Ba'a yi wata biyu da haɗuwarsu ba suka fahimci juna har ta amince aka ɗaura musu aure ta tare a sabon gidan da Baba ya bawa Abba a matsayin kyauta. Suhaila ƙaramin hauka ta kusa yi da ta samu labarin domin duk badaƙalar da ake yi bata sani ba sai bayan an ɗaura auren Abbas ya shigo da fara'a a fuskarsa irin wadda bata taɓa gani ba yace mata sunyi sabuwar uwa da ƴan uwa kuma anjima zasu tare.
Ɗaki ɗaya Abba ya bata sai nashi sai ɗayan na yaranta mata ɗayan kuma na Imam da Kamal sai ɗakin waje ya kasance na Abbas. Katifu ya saka a ɗakin yaran kafin Allah ya hore ya siya musu gado. Da Khadijah ta samu labarin auren nasa a wajen Ammah murna tayi sosai ta kirashi tana yi masa fatan alheri da alkawarin idan akayi hutu zata zo domin ganin gida da sabuwar Ummansu. Ya yaba da hankalinta saboda tunda gaskiya ta bayyana bata taɓa canza masa ba ko ta daina bashi girma kamar yadda ta saba bashi a baya ba. Kati da kuɗin da take tura masa akai akai ma bata daina ba sannan sosai take janshi a jiki duk da cewa yana baya baya da ita.
"Abba zamu turo maka da gudummawa kuma idan ana buƙatar wani abu dan Allah ka sanar dani"
"Babu wata gudunmawar da zan ƙarba. Bayan kayan da kika ɗinkawa Imam da Abbas shine zaki ƙara daura wa kanki ɗawainiya duk ribar sana'arki ta kare a kanmu?"
"Amfanin neman kenan ai Abba. Dan Allah kada kace a'a kuma idan banyi muku ba wa zanyi wa? Ya jikin Husna kuwa? Ranar munyi waya da mama tace yaya Suhailan tana asibiti jikin yarinyar ya tashi" Ta tambaya Muryarta cike da tausayin Husna har da Suhaila ma.
"Dasauki Alhamdulillah. Ai sai haƙuri tunda haka Allah ya ƙaddaro mata. Sai dai fatan samun sauƙi daga Allah"
"To Allah ya bata lafiya. Yawwa Abbu yace Abbas yakai takardunsa wajen Baba Usman zai sa a nemar masa gurbin karatu a BUK. Shaf na manta ban faɗa masa ba"
YOU ARE READING
ƳAR BAƘA
General FictionSabirah baƙa ce. Irin baƙin nan mai maiƙo, ga muryarta mai kauri da amsa kuwwa. Tana fuskantar tsangwama da izaya kala kala a wajen mahaifiyarta da ƴan uwanta da babu wata ƙauna da shaƙuwa a tsaƙaninsu. Shin zata iya haƙuri da ƙulubalen rayuwa ko ku...