Rukayyan Baba Umar CP ke ta fama da rashin lafiya tun bayan zuwan Hisham Kano domin ganawa da danginsa. Daga ka ganta kasan cewa tana cikin damuwa amma anyi juyin duniya ta faɗi matsalarta ta ƙi faɗa har aka gaji aka zuba mata ido. Har yaya Sa'ad da suke ɗasawa sosai sai da CP ya kira shi akan ya tambayeta amma tace babu komai. Gashi a asibiti likita ya tabbatar musu da cewa idan bata daina saka damuwa a ranta ba to tana gaf da kamuwa da ciwon zuciya.Bayan wani lokaci malaman da aka tura Abia domin karya sihirin da akayi wa Kawu Aminu sun dawo kuma Alhamdulillah anyi nasara domin ya tashi garau yana harkokinsa da ibadah. Godiya kuwa babu irin wadda bai yi musu ba kuma yayi alƙawarin da ya gama abubuwan dayake zai taho Kano dawowa ta har abada domin zaman can bai ƙare shi da komai ba sai nadama da dana sani. Da aka faɗa masa ɓatan matarsa da ƴar sa bai yi mamaki ba sai ma cewa dayayi bai wuce sun tafi wani daji neman matsafa ba. Ya kudiri niyyar daga matar tasa har ƴar tasa zai rabu dasu rabuwa ta har abada kuma sai ya saka Hisham ya rabu da ita saboda yasan cewa shima sun cutar dashi kuma dama ya haɗasu aure ne domin ko Allah zai sa a dace a dalilin Hisham ɗin Hamdah ta nutsu ta daina bin huɗubar mahaifiyarta.
__
Hankalin Umma ya kwanta ta samu natsuwa da lafiya domin har makarantar islamiyya ta shiga ta matan aure da ake yi asabar da Lahadi domin ta samo ilimin addini saboda tana da tabbacin harda ƙarancinsa yasa ta aikata abubuwan da ta aikata a baya. Suhaila dai tana Dawanau tana karban magani kuma ana samun cigaba shi kuma Bashir Allah Ya taimake shi wani abokin mahaifinsa ya samo masa aiki kuma Alhamdulillahi ya fara farfaɗowa. Darasin da rayuwa ta koya masa yasa bai daina zuwa kasuwa ba duk karshen mako domin neman na kansa kuma ya dage sosai da addu'a da neman gafarar Allah akan abubuwan daya aikata a baya. Yanzu a duniya bashi da wanda yake ganin girmansa sama Abba. Ya mayar dashi abokin shawara saboda duk abinda zai yi sai ya tambaye shi shawara.
A duk lokacin da malaminsu yake bayani ko tsoratarwa akan azabar kabari da kuma jahannama sai hantar cikin Umma ta kaɗa. Tana godiya ma Allah da tun lokaci bai kure mata ba ta samu tayi nadama kuma tana neman gafarar Ubangiji. Addu'a take Allah ya ganar da Suhaila ita ma ta shiryu kuma ta sake tabbatarwa cewa ita ma da laifinta akan taɓarɓarewar Suhaila. Maama da Abbas da Imam sai son barka domin bazaka taɓa cewa ba ita ta haife su ba.
_________
Tuni Khadijah ta koma Gombe suka cigaba da karatu gadan gadan ba hutawa. Wannan dalilin yasa kwata kwata bata da lokacin kanta balle na waya da Hisham shi ma kuma ayyuka sunyi masa yawa kuma yanzu dayake da mutanen da zai kira su kira shi sai hankalinsa yake daukewa akanta duk da cewa yana kewarta amma yana mata uzuri tunda da ta gama karatu yake son ayi bikinsu don har sun fara shirye shirye shi da Sa'ad. Yayi kuka ya godewa Allah lokacin da Kawu ya kira shi a waya yake sanar dashi cewa ya samu lafiya.
Yaya Bilkisu matar Yaya Muhammad ce ta haihu an samu ƴa mace an saka mata sunan Ammah wato Umaimah. Sai bidiri suke yi saboda sune masu girke girken abinci. Gabaɗayansu bakinsu yaƙi rufuwa saboda murnan an yi wa Ammah jika su kuma sun zama aunties. Tun safe suke gidan Bilkisu harda Amatu da taje yiwa mai jego kitso da lalle. Sai bayan azahar baƙi suka fara hallara duk da cewa ba wani gayya sukayi ba saboda Bilkisu tayi wa kanta karatun ta nutsu ta daina ɗabbaka bidi'a kamar yadda tayi a lokacin aurenta da yaya Muhammad. Duk wanda ya shigo su Khadijah ke masa maraba tare da bashi wurin zama da kuma gabatar masa da abinci. Suna zaune a gujerar robar da aka jera a filin gidan ne Sa'ad ya kira Khairiyyah tayi zumbur ta tashi domin ta kebe tayi wayar son ranta ba tare da sa idon Khadijah da Amatu ba. Tashinta kenan sai ga Faridah da ƙaton cikinta tayi sallama ta shigo. Khadijah bata gane ta ba saboda yadda fuskarta ta canza kuma dama can ba wani saninta tayi sosai ba.
"Khadijah! Ashe dama zan sake ganinki ? Ya kike ya kwana dayawa?" Faridah ta faɗa bayan sun gaisa Khadijah na kokarin nuna mata inda ya dace ta zauna. Kallon ban gane ki ba tayi wa Faridah.
YOU ARE READING
ƳAR BAƘA
General FictionSabirah baƙa ce. Irin baƙin nan mai maiƙo, ga muryarta mai kauri da amsa kuwwa. Tana fuskantar tsangwama da izaya kala kala a wajen mahaifiyarta da ƴan uwanta da babu wata ƙauna da shaƙuwa a tsaƙaninsu. Shin zata iya haƙuri da ƙulubalen rayuwa ko ku...