4

80 10 0
                                    

ƳAR BAƘA
Written by Aishatu Humaira Bello
Humylash@Wattpad
BABI NA HUDU(4)

Maganganu tun basu shiga jikin Alhaji Abdullahi ba sai da ya fara yarda da cewa lallai Ummi ce musabbabin karayar arzikinsa. Nan ya fara kyarar ta da hantararta. Magana indai ta shiga tsakaninsu to Allah ya isa ne ko kuma yace yayi nadamar aurenta. Abu tun yana daga shi sai ita har ya fara affecting yaransu laifin uwarsu ya shafe su. Duk shaquwar dake tsakanin Nura da Baban haka yake rufe ido yayita jibgarsa akan dan karamin dalili. Tun yana kuka yana kokarin ganin yayi duk wani abu da zai faranta masa rai yayi masa murmushi ya ja shi a jiki kamar da har ya gaji ya watsar. Dalilin da yasa yake matukar jin haushinsa kuwa ya samo nasaba ne da irin zagi da cin mutuncin dayake yiwa Umminsa a gabansu. Duk wani burbushin mutuncinsa baya gani. Yana SS 1 Baban ya ƙara aure, danginsa suka aura masa me ƙashin arziki. Ta raina Ummi, ba irin maganganun da bata yaɗa mata suna ji suna gani basu isa su hana ko su rama ba. A haka rayuwar ta cigaba har Allah ya kawo dalilin farfadowar mahaifinsa; wani mutumi ya bawa aron kudade masu yawa da daraja da dadewa dan har ya sadakar ya gudu dasu. Ai kuwa nan aka sake yin caa akan Ummi, maganar da suke faɗa ta tabbata, daga auren amarya ko haihuwar fari batayi ba arziki ya fara dawowa Alhaji Abdullahi. Ummi batada ta cewa sai dai tayi kuka ta gode Allah, tana kuma rokon sa akan ya kawo mata ɗauki. Dalilin damuwa da halin ko in kula da Baban ke nuna mata ga tsangwama da nuna fifiko akan amaryarsa ne ta kamu da hawan jini wanda sai da tasamu partial paralysis. Tana cikin jinya kuma Baban ya koresu daga gidan nasu.
"Gayyar tsiya, wallahi nagaji da zama da ke da ya'yanki. Na samu na fara farfaɗo wa bazanyi sakacin da zai sa na koma gidan jiya ba. Ku tafi chan ku karata Allah ya raba nagari da mugu"

"Ai ma ya raba Baba tunda har ka koremu. Yanzu sai ka rubuta mata takardar ta mu wuce.  Kuma in shaa Allah mu da gidan ka har abada. Ka kwada arzikin ka cinye" Nura ya faɗa a hasale yana tattara akwatin su da amaryar ta watso.
"Nura bana ce kar ka yi magana ba? Me yasa kake son raina ya ɓaci ne a kanka? " Ummi ta faɗa tana share kwalla. Duk irin soyayyar da sukayi da Abdullahi, duk irin kyautatawar da biyayyar auren da tayi masa da abinda zai saka mata kenan? A tunanin ta ko bayan ransa bazai bari ta wulakanta ba ashe yaudarar kanta take yi. Rashin yarda da ƙaddara da son abun duniya sun rufe masa ido har yake korarta da ya'yan da take tunanin duk duniya babu abinda ya dauka da muhimmanci sama dasu. Ta tattara kan sauran kayan nasu ta ja hannun Nura dayake tsaye yanata huci kaman zai rufe Baban da duka da kannensa Faridah da Fiddausi. Gidansu ta koma batare da ya furta mata saki ba. Dayake mamanta ta dade da rasuwa sai yadikkonsu masifaffiyar matace kuma ta gagari hatta mahaifin Ummin shi yasa suka sha bakar wahala. Faridah da Fiddausi sun bauta mata sosai domin hatta abinci idan taga dama ba zasu ci ba. A haka suke ta hakuri a dayan bangaren kuma wan Baban nasu ya dauki nauyin makarantar su da suturar sallah dayake shi mai son alheri ne kuma bai manta irin halaccin da Ummin tayi masa a lokacin da suke da arziki ba. Yaso daukansu ya riƙe amma matarsa ta hana. Sanin cewa basu da tabbacin samun abinci kullum ne yasa idan ya dawo daga makaranta yake wucewa shagon ɗinki inda Ƙanin Umminsa ke aiki. Ai kuwa ba'a dade ba ya ƙware dayake yanada fasaha sosai har ya fara yin kananan ayyuka. Kudin dayake samu ne yake amfani dasu  wajen siya musu abinci da abubuwan buƙata sai ihisanin da Wan Baban nasu ke basu a matsayin pocket money. Haka rayuwar ta cigaba da tafiya har yagama secondary ya shiga jami'ar Maiduguri. Har lokacin kuma babu abinda ke haɗa su da mahaifin nasu. Zancen saki kuwa anyi aiken har an gaji yace shi bazai saki Ummi ba abinda ya sa amarya jin haushi da kishin ta kenan, a tunanin ta wani mugun abu Ummi tayi dayasa ya kasa rabuwa da ita. Haka zata wanko kafa tazo har cikin gidan tayi musu rashin mutunci son ranta ta tafi. A lokacin kuma ta haifi yara uku mata. Karatu bai hana Nura cigaba da ɗinki ba domin duk hutu sai yaje shago kuma dinkin maza da mata yake yi. Yana matukar kauna da tausayin Umminsa da yan kannensa shi yasa duk abinda ya samu a kansu suke karewa. Baya gajiya da tambayar su me suke so? Menene matsalar su? Wannan rufin asirin daya samu ne ya sama musu lafiya wajen yadikko domin tasan sunfi karfin wulakanci. Yana karatun yana ɗinki kuma ya haɗa da sana'a a cikin makaranta ba abinda baya siyarwa indai za'a samu riba. Ai kuwa Allah yasawa abun albarka sai ya kasance kafin ya kammala degree dinsa ya mallaki madaidaicin fili a cikin gari kuma har ya fara tara kudin gini.Babu abinda ya tsana a rayuwarsa sama da zancen mahaifinsa, da yanada hali ma da ya daina amfani da sunansa sai dai Ummi ta haneshi da yin hakan kuma tace ko bayan ranta bata yarda ya canza din ba. "Da  uba ake ado duk rashin dadinsa Nura" tana yawan fada masa haka idan taga alamar an bata masa rai akan Baban nasu.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now