BABI NA UKU (3)
Bata samu damar yiwa Abban nasu magana ba har sai bayan yayi tafiya ya dawo. Domin tunda akayi zancen tafiyarta makaranta Umma ta hana su shaƙar iska a gidan da masifa har duka sai da tayi mata akan abinda bai taka kara ya karya ba. Kaman Abban yasan da magana a bakinta ya kirata lokacin da Umman ta tafi barkar haihuwa da handbag dinta Imam. Suhaila kuwa ta tafi yawo gidan makwabta neman magana da haɗa gurmi."Akwai wani abinda kike buqata ne? Omo da sabulun naki sun ƙare ko akwai saura?" Ya tambaye ta a tausashe yana kishingide a jikin pillow a daki.
"A'a Abba komai na buƙata ina dashi. Dama wata alfarma nake so kayi min"
"Fadi kanki tsaye mamana, indai bai fi karfina ba in shaa Allah zanyi miki"
"Daman kudi nakeso ka bani idan da hali sai na fara sana'ar soya awara a cikin gida ana shigowa siya. Naga ana samun alheri a harkar sosai " ta faɗa a kunyace tana wasa ta yatsun hannayenta.
" Kinyi tunani me kyau yar albarka. Kamar nawa kike ganin zasu isheki yin hidimar?" Ya sake tambaya yana jin kaunar yarinyar na sake ratsa shi. Ita Suhaila tafi kowa yawan bukata ta fi'ili kala kala da karya kuma ba abinda take tsinanawa daga aikin gidan har neman kudin. Amma ga kanwar bayanta nan wadda abu idan ba dole bane a mu'amalar rayuwar yau da gobe bazata taba buɗe baki tace tana so ko a siya mata ba tayi tunanin neman na kanta.
"Ban sani ba Abba. Ina dai so ne na siya komai nawa daga kan itace harda su kwalanda da matsami" kai ya jinjina cikin gamsuwa da tunanin nata domin kuwa yasan amfani da kayan Umman bacin rai da tashin hankali zai jawo a gidan.
"Kije ki rubuta duk kayan buqata in shaa Allahu idan na shiga kasuwa gobe ko jibi kafin na wuce kauye zan siyo miki sai a gwada farawa da kaɗan" murna da godiya a wurin Sabirah ba'a magana. Tayi ta kwararo masa addu'oin fatan alheri da gamawa lafiya domin kuwa ya gama mata komai. Duk da cewa aikin gidan duk yana wuyanta amma bazata bari ya shafi sana'ar tata ba.
"Tashi kije, Allah yayi miki albarka. Allah yasa wa sana'ar albarka yasa itace sanadin tsayawarki akan kafafunki ba tare da kin nemi taimakon kowa ba" ya sallameta tace amin tana shiga dankinsu ta daka tsalle tace "yes! Alhamdulillah"Kafin sati ya zagayo Abba ya mata siyayyar komai harda waken soya kwano goma kuma ya damƙa mata wasu kuɗaɗen domin siyan sauran kayayyakin da ake bukata. Tayi godiya har ta gaji domin tana matukar son ta dogara da kanta sanin cewa Allah da Abban nata ne kaɗai gatan ta a duniya. Da kuma aminiyarta Hafsat da take faɗa mata irin alherin da ake samu a sana'ar. Sosai take rawar jikin farawa kuma tun kafin ta faɗa wa Abba zancen take addu'a a cikin sujjada akan Allah ya saka albarka a neman kuma yasa kar Umman ta hanata. Da ta faɗa mata cewa tayi indai bazai shafi ayyukan da take mata a gida ba batada matsala. Taso ace ko addu'a ne tayi mata na fatan alheri da sa albarka amma dai hakan ma ta gode. Sannu bata hana zuwa. Suhaila kuwa dariyar shakiyanci ta sakata a gaba tanayi domin gani take babu me zuwa siyan awara wajen Sabirah. Ko anzo ma da anga yanayin kalar fatarta ta za'a kyamaci cin abu daga hannunta. Bata ce da ita komai ba duk da ranta ya ɓaci ta cigaba da shirye shiryen yanda komai zai wakana. Sun riga da sunyi zancen da Hafsah saboda haka tana tsammanin customers da kuma Abbas da yayi mata alƙawarin tallatawa abokansa da yan wajen da yake aiki. Imam ma dai yace zai fadawa abokan wasan sa amma da sharadin zai ringa cin ta kyauta kullum. "Banda abunka Imam yaya za'ayi ana abu a cikin gidanku ka siya ?" Jin hakan yayi matukar tasiri a kanshi don kuwa har yan gaba da layin su yayi wa shelar cewa ana siyar da awara me shegen dadi a gidansu.
Da yamma ta gama shirye shiryenta a nutse cikin tsafta sai ga sallamar Hafsah. Nan ta taimaka mata suka hada wuta a dan karamin murhun da Abba ya siyo mata. Tana suyar ita kuma tana yanka mata su albasa da cabbage da cucumber din da zata hada. Yaji kuwa daman ta siyo shi dayawa na tafarnuwa da citta a wajen Yayar Hafsah, wadda take sana'a sosai ba kama hannun yaro. Har tafara sadakarwa asara zata tafka don har tayi kasko biyu babu wanda yayi sallama. Kaman Imam ya gane yanayin da ta fara shiga sai gashi da gangun yara sa'anninsa da wa'yanda suka girme masa wajen su ashirin da sallamarsu suna hayaniya. Yana ta rattaba musu irin dadin da awarar gidansu take dashi, idan sunci bazasu sake marmarin cin wata idan ba ta gidansu ba. Da mamaki Sabirah take kallon sa, duk da tasan da batayi masa alkawarin ci kullum ba ba lallai ya shiga sabgar ta ba amma hakan ma taji dadi kuma ta gode. Nan da nan aka siye kasko biyun harda layi ana jira. Hafsah na zubawa ita tana soyawa."Assalamu alaikum, wai inji wani a bashi awara ta dari biyar " wani yaro ya fada daga bakin kofa.
"Kace ya ɗan jira a sallami na kan layi za'a soya masa" Hafsah ta amsa. Dadi kaman ya kasheta don tasan maybe ɗaya daga cikin samarin layinsu ne da tayiwa talla. Ai kuwa shi dinne domin da kanta ta fita bashi. Ya ciro daya ya dangwala yajin ya kai bakinsa. Wani irin dadi ne ya ratsa taste buds dinsa ga laushi da kamshin yajin ai kuwa kafin ya bar kofar gidan ya kusa cinye rabi. Yanata santi Hafsah kuwa tana cewa dan Allah ya fadawa sauran tunda shi ya dandana yaji yadda take.
Awara tayi albarka domin wa'yanda suka siya da wa'yanda aka bawa labari sai zuwa suke ƙari. Da sabirah taga ta kusa karewa ne tace a daina karban kudin mutane sai kuma gobe idan Allah ya kaimu. Ta soye sauran ta raba biyu. Kashi daya na yan gidansu dayan kuma ta bawa Hafsah a roba tace ladan taimako da kawo customers.
"Haba ƙawa. Kin san kin wuce haka a wurina. Irin haka ai sai ki cinye ribar " ta fada tana ture robar data miko mata.
"Malama na Umma ne idan ke bakyaso kuma na yau ne ai daga gobe kowa siya zai yi. Dan Allah ki karba ai bazan taɓa iya biyanki ba. Nagode kwarai Allah ya bar mu tare har aljannah."
"Amin kawas. Nima na gode" suka kwashe kayan suka wanke kafin Hafsahn tayi sallar maghib Sabirah ta rakata hanya. Duk bidirin nan da akayi Umma da Suhaila basa gida shi yasa akayi komai cikin salama da armashi. Umma kuwa tana chan a zuciyar ta tana fatan tayi wani abinda zatayi amfani dashi ta hana sana'ar dan bayan zancen karatu bata taɓa ganin ƴar baƙar a cikin walwala irin haka ba.
"Ai batada da mutunci ko kaɗan Umma. Na tabbata bata aje mana ba"Suhaila ta faɗa bayan ta gama yi mata famfo kuma tana Allah Allah su kwanta bacci ta kwashe kudin. Domin har ranta bata kaunar Sabirahn ta fita. Idan tana kwashewa tasan Abban nasu sai gaji yayi fushi ya daina bata shikenan kowa ya rasa. Basu samu yanda suka so ba kuma duk bakin cikinsu sun san cewa awara tayi dadi suka cinye tas suna tande baki amma ba su iya yabonta ba ko saka albarka. A gajiye take tibis saboda haka lokacin ma ta dade da yin bacci. Suhaila tayi duban duniya kudi sukace dauke mu inda kika ajiye mu. Daman ta ce Umman ta ringa karbewa tace a'a saboda Abba yace a bakin aurenta idan ta kwace wa yarinya kudin sana'ar ta indai ba ita ce ta bata ba. Tsaki dai a wannan daren Suhaila tayi yafi sau dubu. Tanata mamakin to ina Sabira ta kai kuɗin? To akwae wanda ya riga ta dauka ne ? To amma waye ? Tunda tasan Abbas baya shiga dakin su sai da dalili, Imam ma baida dabi'ar dauke dauke.
"Ai shikenan! Gobe ma ranace. Idan kinsan wata baki san wata ba" tayi kwafa ta juya zuciyarta fal baqin ciki.______________________________________
Zaune yake cikin office dinsa zuciyarsa kamar zata fashe saboda bacin rai. Ya kamata ace a matakin da ya kai a rayuwa shida mahaifiyarsa da yan uwansa sun wuce wulakanci a wajen mahaifinsa da matarsa da tun yana yaro ya tsaneta tsana me muni da ita da abinda ta haifa. Babu shaquwa ko kauna a tsakaninsu. Mantawa yake yi dasu tunda kiri kiri an koresu a gidansu na asali sai da Allah ya rufa masa asiri ya fara aiki da sana'a ne ya samu ya siya musu dan madaidaicin gida.
Dr. Nuruddeen A. Kumo kenan. Babban likita ne a fannin psychology yana aiki ne a Federal Teaching Hospital Gombe (FTHG). Kamilallen mutum mai addini da neman na kansa. Haziqi me fasaha da girmama nagaba dashi. A matsayinsa na babban da a wajen mahaifinsa da kannensa biyu mata. Ya taso a cikin gata da shaquwa irin ta ɗa da mahaifi. His father was his best friend, hatta abinci tare suke ci sai dai duk da haka yana da makon uwa da tausayinta. Don tun kafin yayi wayo sosai yake taimaka mata da ayyukan gida kuma duk abinda ya samo tare zasu raba. Mahaifinsa dan kasuwa ne hamshaƙi wanda sunansa yayi fice a ciki da wajen Gombe saboda haka basu san babu ba. Private schools suke yi kuma duk wani abu da dan gata ke takama dashi su ma anayi musu. Suna zaune cikin kwanciyar hankali, so da kaunar juna. Rayuwa suke yi cike da farin ciki da annashuwa. Kwatsam lokacin da yake secondary school sai iftila'i ya fadawa Mahaifinsa, yayi ta asarar dukiya ko su salwanta ko kuma ace anyi gobara wuta ta cinye. Sunga tashin hankali a wannan lokacin kuma sunyi kuka da tunanin irin rayuwar da zasu fara. Dayake mahaifiyarsu da suke kira Ummi mai tawakkali ce kuma itama ba yar kowa bace kafin ta auri Abdullahi Kumo sai tayi ta kokarin yin kananan sana'o'i a cikin gida domin rufin asirinsu a gefe daya kuma tana tausar mijin nata akan yayi hakuri ya rungumi ƙaddara. Nan fa yan uwansu suka sakata a gaba da maganganu marasa kan gado kan cewa itace me kashin tsiya shi yasa tunda aka auro ta arzikinsa ke tawaya instead of ya bunkasa. Haka dai suga cigaba da rayuwa yau fari gobe baki duk da yan uwan mahaifin nasa nada zumunci suna taimaka musu sosai shi yasa ma ba'a chanza masa school ba.
YOU ARE READING
ƳAR BAƘA
General FictionSabirah baƙa ce. Irin baƙin nan mai maiƙo, ga muryarta mai kauri da amsa kuwwa. Tana fuskantar tsangwama da izaya kala kala a wajen mahaifiyarta da ƴan uwanta da babu wata ƙauna da shaƙuwa a tsaƙaninsu. Shin zata iya haƙuri da ƙulubalen rayuwa ko ku...