Kamar yadda Mama ta faɗa, Baba Umar (CP) sai daya binciko dangin Hisham kuma yasa aka kawo su har ofishinsa a mutunce. Dayake mara gaskiya ko a cikin ruwa sai yayi jiɓi tun kafin su san dalilin kiransu ofishin komishinan ƴan sanda suka fara tonawa kansu asiri da rantse rantse akan sharrin shaiɗan ne. Ƙannen mahaifinsa biyu ne da wansa guda ɗaya ke da alhakin haɗa gobarar da tayi ajalinsu kuma a gabansu wutar taci ta cinye su saboda rufesu sukayi a cikin store yadda ko an kawo ceto baza'a fara tunanin dukkansu suna ciki ba. Ran CP yayi matukar ɓaci yace akan wanne dalili suke neman ran ɗan uwansu? Wai hassada ce da kuma ganin yafi su rufin asiri don sai bayan sun kashe shi kuma Hisham ya tsere sannan suka fahimci cewa wadatar zuciya ce kawai da samun mace ta gari da kuma yana da zuciyar yin alheri shiyasa suke yi masa kallon hamshaqin mai arziki.
Tun da ya fara aikin ɗan sanda yaga abubuwa kala kala, aikin son zuciya da rashin imani amma wannan ya taɓa masa rai sosai. Ya za'a yi mutum ya kashe dan uwansa ta hanya mafi azabtarwa kuma ya tsaya a wurin ya tabbatar da cewa wannan ɗan uwan nasa da ahalinsa sun ƙone kurmus kuma ya cigaba da rayuwa kamar komai bai faru ba duk da cewa daka gansu zaka fahimci basuda nutsuwar zuciya da ta ruhi.
"Shi Hisham ɗin da kuka so aika shi inda kuka aika iyayensa da ƴan uwansa kuma ina kuka cilla shi?" Ya tambayesu babu rahama a kan fuskarsa.
"Wallahi yallaɓai guduwa yayi tun muna saka ran dawowarsa har muka yi tunanin ko mota ta kaɗe shi ya mutu. Har ɗan leƙen asiri muka saka a dangin mahaifiyarsa amma har yanzu Allah bai sa ya bayyana ba." Ƙaramin cikinsu dake ta zufa duk da akwai AC a office ɗin ya faɗa yana magiya.
"Good. Haka nake son ji amma ka sani ban yarda daku ba. Duk inda Hisham yake sai kun nemo shi kuma sai an yanke muku hukuncin kisa daidai da abinda kuka aikata. Kun dai san a doka ko bayan shekaru ɗari ne za'a iya hukunta ku kuma gashi da kanku kun tonawa kanku asiri.Bama buƙatar wata shaida. Kun hutar da Shari'a."
"Gwara ayi mana hukuncin tun a gidan duniya ranka ya daɗe mun amince. Billahillazi bamu san inda wannan yaron yake ba." Babban wansu ya faɗa saboda ta kai ga baya iya baccin arziki sai yayi ta mafarkai masu abubuwan tashin hankali dana tsoro. Abu kaɗan ke firgita shi gashi duk ya'yansa babu nagari, matansa kullum cikin tashin hankali suke, ga babu tayi masa yawa duk kuɗin da suka handame sun ƙare. Dayake shine babba kuma shine ya bada shawarar su haɗa gobara a gidan marigayi Abubakar shi ya dauki kaso mafi tsoka.
"Su waye ƴan uwan mahaifiyar tasa?"
"Akwai ƙanwarta, sai kuma wanta amma shi yana can kudu tun bayan rasuwar daya zo ta'aziyyah bamu sake ji daga wajensa ba amma mun samu labarin cewa matarsa ce ta mallake shi ta kafe shi a can bata bari ya raɓi yan uwansa. Sai kuma ƙanin mahaifin ita babar Hisham ɗin wanda shine ya raine su. Akwai sauran dangi amma wa'yannan sune mafi kusanci dashi" Na tsakiyar ya bada bayani.
"Mashaa Allahu. To yanzu ku taso muje chan sai ku faɗa musu abinda kuka aikata. Idan kuka nemi kuyi min gardama to ba shakka da ankwa zaku fita kowa ya ganku. Na tabbata kafin ku ƙarasa gidajenku labari sai riga ku isa. Shawara ta rage a gareku."
Sum sum suka tashi suka yi hanyar ƙofa. Murmushin takaici yayi kafin ya mara musu baya. Lokacin da suka isa gidan ƙanin kakan Hisham na wajen uwa sun same shi a kwance cikin yanayin rashin lafiya sannan ita ƙanwar mamansa ke jinyarsa. Duk da cewa ta san fuskokinsu, tayi mamakin ganinsu a wannan lokacin bayan shekarun da aka ɗauka babu wanda ya waiwayesu. Idan ma taje domin samun labarin Hisham rashin mutunci suke yi mata. Tabarma ta shimfiɗa musu ta kawo musu ruwa sannan ta koma ta zauna tana sauraren abinda ya kawo su. Shi kansa baban addu'a yake Allah yasa suce masa sun ga Hisham domin duk cikin yaran ɗan uwansa yafi ƙaunar maimuna mahaifiyar Hisham.
A tsanake a sigar da bazai tayar masa da hankali ba CP yayi masa bayanin cewa ana zargin kashe iyayen Hisham akayi sannan shi kuma Hisham yana raye kuma cikin ƙoshin lafiya. Bai sanar dashi cewa mutanen dake gurfane a gabansa sune suka aikata kisan ba amma ya faɗa masa suna kan bincike kuma in shaa Allahu zasu karɓi hukunci wajen hukuma yadda ya dace.
YOU ARE READING
ƳAR BAƘA
General FictionSabirah baƙa ce. Irin baƙin nan mai maiƙo, ga muryarta mai kauri da amsa kuwwa. Tana fuskantar tsangwama da izaya kala kala a wajen mahaifiyarta da ƴan uwanta da babu wata ƙauna da shaƙuwa a tsaƙaninsu. Shin zata iya haƙuri da ƙulubalen rayuwa ko ku...